Follow us on social media

Showing 129001 words to 132000 words out of 147042 words

Chapter 44 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

da ruwan hawaye.
Sai da ya gama rubutun shi sannan ya ɗago yana kallonta lokaci ɗaya yana mika ma Nurse ɗin dake gefen shi fayel ta rankwafa ta amsa cikin ladabi.

"Duk suna waje."

Ya faɗa yana nuna mata kofa.
"Suna jiran mu gama aikin mu sai mu ba su damar su shigo su duba ki."

Ya sake faɗa yana ɗan wasa da biron hannunsa.
Kuka kawai Ummu take yi hawaye har sun jika mata gaban riganta, wannan ɗacin da zafin da ta so ta kashe kanta saboda shi, shi ne yanzu ya taso mata yana yi mata maƙakin a kasan zuciyarta ga shi yanzu ta sanya iyayenta da yan'uwanta a cikin damuwa.

"Ummu Salma."

Ya sake kiran sunanta.

"Za ki iya tuna dalilin da ya sa kika tsinci kanki a asibiti?

Ya tambaya kai tsaye yana mai kallon ta.
Hawaye suka sake kece mata zata tuna mana. Za ta tuna cin amanar da ƙawarta Shamsiya ta yi mata tare da Habib, wadanɗa suka ba yar da guddumuwa wajen gurguta yau ɗinta da gobenta. Har a yanzu kalaman Shamsiya na yi mata amsa kuwwa a cikin kanta ba za ta taɓa mantawa da abinda ya same ta ba, domin wannan baƙin cikin watakila in bai yi ajalinta ba, to har ta koma ga Allah yana nan a cikin zuciyarta kuma yana saka ma gangar jikinta ciwo.

"Kiin tuna?

Ya sake tambayanta

Kai ta gyaɗa masa cikin kuka da hawaye, shessheƙa take yi tana jin zuciyanta na bugawa da sauri da sauri.

"Kin san cewa tun shekaranjiya da daddarre aka kawo mana ke ba kya numfashi?
Ummu ta kalle shi cikin mamaki.
"Tun shekaranjiya?
Ta maimaita a saman laɓbanta.

"Daƙyar muka iya ceto rayuwanki, ga shi kina da juna biyu ga shi kin zubar da jini kin shiga hatsari sosai da yasa ko bayan mun ceto numfashin ki, mun sanya miki oxygen amma ba ki farfaɗo ba sai yanzun nan."
Majina ta ziraro ma Ummu amma ta kasa iya wani numfashi.

Kuka kawai take yi hawaye suna zubowa wasu na sake kwaranya.
Nadama take yi, dana sanin me ya sa ta aikata abin da ta aikata? Lalle Allah na son ta da ya sake ba ta wata damar a karo na biyu.

"Kin yanka hannun ki sau biyu kuma yanka mai zurfi. Kin zubar da jini sosai da ya sa sai da ɗan'uwanki ya ba ki jininsa leda biyu muka sanya miki. Ba domin shi ba, da wataƙila wajen neman jinin lokaci ya ƙure har ki mutu bamu samu damar ceto rayuwarki ba."

"Allah sarki ɗan'uwa. "
Ta san ma Hamma Kabiru ne ya bata jininsa kamar yadda a baya ya taɓa bata jininsa.


"Me ya sa kika yi yunkurin kashe kanki Ummu Salma?

Dr Ahmad ya tambayeta kamar yadda yake a rubuce a jikin ɗan aninin dake jikin rigan likitancin jikinsa.

Kuka Ummu Salma ta fashe da shi muryanta baya fita, bai hana ta ba gwara ta yi kukan ko zuciyanta za ta samu salama.
Yadda take rera kukan ne, abin tausayin duk wanda ke kusa da ita yake kuma sauraranta. Kuka ne mai taɓa zuciya kukan nadama da bakin ciki.
Nurses ɗin dake gefensa har akwai wacce ta yi ƙwalla jikinsu duk ya mutu.

"Ke fa musulma ce, kin ta so gidan tarbiya da gata, ko daga yadda yan'uwanki suka cika asibitin nan saboda ke na shaida ke yar gata ce, wani dalili ne zai sa ki yi yunkurin kashe kanki? Kin manta duk wanda ya kashe kansa kafiri ne? Ko kin manta cewa da kin mutu a lokacin wutar jahannnama za ki shiga?
Tsoro da wani irin imani suka sake kama zuciyar Ummu, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin dake ɗakin.

"Komai ya faru dake ki gaya ma Allah Shi zai yi miki mganin komai. Mu musulmai ne mun san yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau yana cikin imani ne. "
Ya sake faɗa yana mai kallonta.

"Ina so ne, ina so ne na daina jin zafi da radaɗin dake cikin zuciyata."

Ummu ta faɗa cikin matsanancin kuka majina da hawaye na kwanraya.

"Me ya sa ba ki karanta Qur'ani ba? Me ya sa ba ki kira sunan Allah ba! Yana sane da halin da kike ciki, da kin daga hannun kin roƙesa salama da amimci da ya sama miki ba sai kin yi tunanin kashe kan ki ba Ummu Salma."

Kuka kawai take yi tana jin kamar ta  mayar da hannun agogo baya.

"A lokacin da kika yanke shawaran kashe kanki ba ki yi tunanin wannan ran dake motsi a cikin ki ba ? Da kin mutu fa? Da kin kashe rai biyu? Sannan kin manta da iyayenki da dangin ki? Kin yi tunanin yadda za su dauwama cikin kuka in har kika bar rayuwwansu?

Ummu ta fara girgiza kanta tana cigaba da kuka.

"Mahaifiyarki ana taho dake ta faɗi, kina ciki muna ceto rayuwarki ita kuma tana kwance ana daidaita numfashinta."

"Wayyo Ammah."

Ummu ta faɗa kamar za ta shiɗe."

"Mahaifinki duk da ya yi dauriya amma kuka yake yi yana fargaba rasa ki, yayyenki maza duk da suna da jarumta sun shiga damuwa saboda ke, yau da ace kin mutu kina tunanin za su manta irin mutuwar da kika yi? To har abada ba za su taɓa mantawa ba."

Ummu na kuka tana numfarfashi, ba ita kaɗai ba hatta Nurses ɗin nan suna ta goge ƙwallah

"Kin yi sa'a. Allah na son ki ya sake ba ki wata dama. Ina so ki sani ki yi ta neman gafaran Allah ki kuma tuna kowani tsanani akwai sauƙi a wajen Allah."

"Astagafurullah"
"Allah na tuba."
Ummu ta faɗa cikin matsanacin kuka kamar ranta zai fita.

"Daga yau in tunanin kashe kanki ya sake zuwa cikin tunaninnki. To ki tuna da abubuwa guda uku, na farko yadda za ki koma gaban Allah a matsayin asararriya na biyu kuma halin da iyayenki za su shiga saboda ke. Na uku kuma ki tuna ke musulma ce, kuma duk musulmin kwarai yana da imani sannan ya yarda kaddara mai kyau ko mara kyau."

"Na tuba Allah ka yafe mini."
Take faɗa tana jin wani irin tsoro na sake shiga cikin zuciyanta.

"A matsayina na likitan da ya karɓi case ɗinki har ya ceto rayuwanki, shi ya sa na baki shawara sannan a matsayina na musulmi na tunasar dake abin da kika manta, in kin shiga damuwa ko baƙin ciki ki yi kuka har sai kin gaji amma ki yi addu'a ki karanta Qur'ani ki samu salama, kar ki yadda ki bari tunanin sake aikata irin haka ya sake shigarki, ki sani in a wannan karon kin rayu watakila na gaba ba za ki rayu ba Ummu Salma."
Ya gama faɗa lokaci ɗaya yana mai mikewa tsaye.

"Na gode Dr."

"Sunana Ahmad Salisu."

Ya faɗa yana kallonta.

"Ya isa haka, ki sassaita kukan ki saboda yanayin jikin ki."
Kai ta gyaɗa masa hawaye na kece mata.

"Allah ya ba ki lafiya."
Ta amsa da Amin
Kafin ya wuce nurses ɗin suka bi bayan shi jiki a sanyaye.

"Ku ba ma Family ɗinta damar ganin ta."

Ya faɗa ma Nursea ɗin kafin ya fice daga ɗakin su bi bayan shi.
Bayan fitan shi kuka Ummu Salma ta cigaba da yi har da shessheƙa.
Sai dai kukanta ya tsaya ne lokacin da ta ji an buɗe kofa ta ɗago jiƙakkun idanuwanta tana kallon kofar shigowa.

Sai da ta ga yan'uwanta suna shigowa. Wani na ture wani, Mami ce akan gaba sai Baɗɗo bayan ta Adda Suwaiba ce, sai Adda Ummu Sulaim, Sai iklima sai Umma Balki sannan mazan suka biyo bayan su.

Hamma Abdullahi ne ya shigo bayan sa kuma Hamma Mustpaha, Hamma Abdulrrahman sai Hamma Kabiru ne ya zama karshen shigowa. Ba Ammah ba Baffa haka Ummu ta faɗa a cikin zuciyanta, a tunaninta ko suna baya ne ba su shigo ba amma sai ta ga Hamma Kabiru da ya zama karshen shigowa ya rufe ƙofar sannan ba ta ga Hamma Jibo ba, sannan ba ta ga Hamma Saddam ba, shi da man baya nan ya koma makaranta.

Baɗɗo da Mami suna rige-rigen ƙarisawa gare ta cikin wani yanayi a saman fuskokinsu.

"Ma sha Allah. Sannu Daughter."

Mami ta faɗa tana zama gefen gadon data ke kwance har tana rumgumota ta gefen hannunta na hagu.
Jin ta a jikin Mami kawai sai ta saki kukanta wiwi kamar karamar yarinya nadama ya sake kamata ta.
Ta saka kowa ya zo, zuwam kuma ba na lafiya ba, ba kuma zuwan shiri ba.

"Shii is ok. Mun gode ma Allah tunda kin farfaɗo, kukan ya isa haka."

Mami take faɗa tana bubbuga bayanta.
Baɗɗo ma kusa da Mami ta zauna tana mai kallon Ummu idanuwanta cike da hawaye ga shi sun kumbura.
Tun shekaranjiya take kuka ba ta daina ba.
Sai aka koma ita ake ba hakuri ana lallashi.

"Sisna"

Baɗɗo ta faɗa tana mai riƙe hannun Ummu wanda aka cire ma ƙarin ruwa.

"Sisna me ya sa?

Baɗɗo ta sake faɗa lokaci ɗaya tana mai fashewa da kuka.
Ummu ma hawaye suka sake kece mata kamar an ɓude famfo.

"Ku yi haƙuri."

Ta faɗa a hankali bakinta na rawa.

"Shii. Ya isa nan asibiti ne."

Mami ta faɗa tana mai share ma Ummu hawaye da mayafinta jikinta har da majina.

"Bar kuka kin ji ko? Mun gode ma Allah da kika rayu."
Mami ta sake faɗa tana share mata hawaye.
"Mami."
Ta kira sunanta cikin dashewar murya da kuka.
"Naam My First Daughter."
"Ku yafe mini Mami."
Ta sake faɗa lokaci ɗaya tana mai fashewa da kuka.
Sake rumgumota Mami ta yi, itama hawaye sun kawo mata saboda tausayin halin da Ummu ke ciki.

"Ya isa, is ok kin ji.?

Ta sake faɗa tana mai ɗan tapping ɗin bayanta alamun lallashi.
Sannan ta sake ɗagota tana mai share mata hawaye da gefen mayafinta.

"Sannu Ummu kin auna arziƙi."

Umma Balki ta faɗa cikin wani yanayi.
"Amma dai abin da kika yi sakarci ne, gabaɗaya kin ɗaga mana hankali? Haka ake yi? Kan ki farau mutuwar aure?
Ta faɗa cikin faɗa, da man ita da Ammah ne a ɗakinsu suke da faɗa

"In da kin mutu fa? Wani hali iyayenki za su shiga! Jamila tana ganin halin da aka kawo ki rai ƙwai kwai ta yanke jiki ta faɗi yanzu in da ya zo da karan kwana fa? Me za ki faɗa ma Allah, ke kin kashe kanki bakincikin ki ya kashe uwar da ta haifeki duk saboda namiji? Namijin banza, namijin ƙanin ajali to ni a matsayina ta uwarki na ce in kika sake ma tuna wannan maci amanan ba mu yafe miki ba shashasha kawai."

Ta gama faɗa har tana nuna ma Ummu Salma ɗan yatsa wacce ta lafe a jikin Mami tana ta kuka.

"Umma ku yi haƙuri."

"Kaniyarki da haƙurin, sakarya, ba ki da tunani ne! Ina ilimin ki da hankalin ki yake Ummu Salma? Kawai ki yanka kanki kamar a wasan ƙwaiƙwayo"
Ummu kuka take yi har yana ba da sauti ga hawaye ga majina.
"Na yi nadama."
Ta ke faɗa muryanta na shaƙewa.

Mami ke lallashinta amma faɗan Ummu Balki ne ya sa kukanta yaƙi tsayawa.

"Umma Balki don Allah ki yi haƙuri a bar maganar nan tunda dai ya faru kuma an ci sa'a abin ya zo da sauƙi ba sai a yi hakuri ba."
Mami ta faɗa tana kallon Umma Balki.

"Ke ma Fatima kaniyarki? Ke ce ke ɗaure mata kugun ta yi sakarci sannana za a yi mata faɗa ba? Kenan ma abun da ta yi mai kyau ne."
Mami ta yi shuru jin an zage ta.
Su Hamma Mustapha da suke ɗakin sun yi shuru kamar ruwa ya ci su.

"Ki yi haƙuri Umma tunda muna asibiti ne."

Adda Suwaiba ta faɗa, itama tsaraban hararan ta samu da ya sanya ta kama bakinta ta yi shuru.

"Ai Umma abin da kika yi ya yi daidai. Ni ba domin na lallashi kaina ba, na so ne ina shigowa na falla mata maruka goma sannan na taka wuyanta sai ta kusa mutuwan da gaske sannan zan ƙyaleta."
Hamma Kabiru ya faɗa cikin kaushin sa.

"Yauwa, faɗa mata ina daɗin shi ai ko ba a mare ta ba, a yi mata faɗa shi dukan in ta warke a yi mata tunda ba ta da tunani haka kurum, kin tayar mana da hankali mun kasa sukuni da fargaba."
Umma Balki ta sake faɗa cikin yanayin faɗan ta.

"To a dai yi haƙuri tunda muna asibiti ne."

In ji Hamma Mustapha da ya faɗa yana kallon Ummu dake kuka kamar ranta zai fita duk tausayin ta ya gama kashe masa jiki.

"Ni ban taɓa tunanin Ummu za ta iya yin wannan sakarcin ba wallahi."
Hamma Abdullahi ya faɗa yana ɗan cije leɓensa na ƙasa.

"Ni wallahi wani takaici na ke ji in ma tuna akan wani sakarai wanda rayuwarta ba ta da amfani a wajen shi ta so kashe kanta. Wallahi ji nake yi kamar na kamata da duka."
Hamma Abdulrahaman ya faɗa yana mai jin takaici na taso masa.

"Don Allah ku bar wannan maganar har mu koma gida."
Mami ta sake faɗa tana kallon su Hamma Abdullahi.

"Gaskiya ko don natsuwar ita Auta."
Ummu Sulaim ta faɗa tana kallon Ummu cikin tausayawa.

"Sai fa mun faɗa mata Mami, mu dai kar ta yi sanadiyar mutuwar Ammah, in hakan ya faru wallahi ba za mu yafe mata ba."
Hamma Kabiru ya faɗa yana balla ma Ummu Harara kukan banza take yi, shi da za a bar shi da ya lallasa ta, in aka tsaya ana jin tausayinta gaba ma za ta sake aikata irin haka. Dukkansu suna wajen aikinsu ta ɗaga musu hankali ta sanya sun baro komai sun taho saboda ita.

"Hamma."

Ummu ta faɗa cikin matsanancin kuka.

"Ina Ammah?
Ta faɗa tana ware idanuwanta akan dukkansu.

"Tana gida tare da Ummi."

Iklima ta faɗa cikin sanyin jiki.
Halin da ta ga Ummu ya sake tsoratar da ita ga lamarin maza.

"Kar ki damu ba abin da ya same ta, suma ne ta yi tana farfaɗowa suka koma gida."

"Baffa fa?

Ta sake tambaya cikin muryan kuka.

"Yana gida amma Baba ya kira shi a waya ya sanar da shi farkawanki na san yana tafe."
Mami ta fada tana mai sake share ma Ummu hawaye.
"Ki daina wannan kukan, likita ya ce kar mu saka ki kuka, su na son ki samu hutu saboda jinin ki ya ɗan yi sama.".
Kanta ta ɗan gyaɗa, a tunanin ba su san abin da ya saka ta yanka kanta ba, ta ɗauka kawai suna tunanin saboda sakin da Habib ya yi mata ne.

Gabaɗaya suka yi ta masa sannu tana amsawa. Ba su wani daɗe ba mazan suka fita tunda ta farfaɗo zaman asibiti kuma ya kare, Baɗdo kawai aka bari da Mami, su Adda Suwaiba ma sun bi mazajensu zuwa gida tunda tun safe suna asibitin.
Ummu ta tambayi Baɗɗo karfe nawa ta ce mata biyar da rabi na yamma.
Sai ta ɗan runtse idanuwanta sannan ta sake buɗewa tana kallon Baɗɗo, an samu sa'a Umma Balki ta bi su Hamma Abdullahi zuwa gida.

Mami kuma mijinta ya kirata a waya sai ta fita daga ɗakin bayan fitan su ne Ummu ta kalli Baɗɗo lokaci ɗaya tana fadin" Yanzu kwana biyu na yi a asibiti ban san in da kaina yake ba?
Ta faɗa cikin sanyin muryan da ta disashe da kuka.

"E, tunda aka kawo ki kina emargency sai yau ne ma da safe suka kawo ki wannan ɗakin."
Ummu ta dukar da kanta saboda hawayenta da suka kawo

"Allah na tuba."

Ta faɗa tana kecewa da kuka wannan karon Baɗdo aka bari da lallashi.

"Why Ummu Salma?
Akan Habib ko akan Shamsiya?
Da sauri Ummu ta kalleta cikin mamaki.
"Da man kin sani?
Ta tambayeta cikin raunin murya.

"Na sani, ai dalilin kiran da na yi ta miki a daran shekaranjiya kenan ba ki ɗaga kirana ba. Nima a status ɗin wata course mate dina na gani, ban taba tunanin Shamsiya za ta iya cin amanarki ba. Amma ban yi mamakinta ba, daga baya ta sauya dake sai da haka ta faru na fahimci dalilinta na kare ma Habibu ashe maciya amana ne."
Ta gama faɗa cikin bakinciki da takaici.
Kuka kawai Ummu ke yi kamar ranta zai fita.

"Na tsani Habib, na tsani Shamsiya. Ba zan taɓa yafe musu ba.'

Ummu ta faɗa majina na zilalo mata.

"Ki tsane su, amma ki fara cire su daga tunanin ki da rayuwarki gabaɗaya. Ba su da amfani kuma in dai amanace da suka ci taki su je ga su ga duniyanan nan da ikon Allah sai Allah ya saka miki."
Baɗdo ta sake faɗa itama tana hawaye

"Shamsiya fa? Ashe duk abin da Habib yake yi mini da sanin ta.".
Nan Ummu ta fara ba ta labarin yadda suka yi da Shamsiya a gidan su.
"Ni dai na san na dawo gida cikin baƙinciki, ina so na ji zuciyata ta daina kuka, baɗdo ban san me ya sa na yi tunanin kashe kaina ba ni dai kawai ina so na samu salama ne a cikin zuciya ta."
Ta faɗa tana mai gunjin kuka.
Baɗɗo ta rumgumeta ta gefe tana ɗan bubbuga bayanta alamun lallashi.

"Ni ce na fara iskoki kwance jini na tsiyaya a hannun ki. Daman da na yi ta kiran ki baki ɗaga a daran na ce ma Ummi zan zo wajen ki, ina zuwa na samu Ammah da Baffa tare da Hamma Lamiɗo a dakin Baffa bayan mun gaisa sai na shigo ɗakin ki na iske ki kwance ba numfashi a tare dake nan fa na fasa ihu su Baffa suka rugo zuwa ɗakin ki."
Ummu na cigaba da tsiyayan hawaye tana sauraran Baɗɗo

Baffa da Ammah sun shiga tashin hankalin da suka kasa iya baki wani taimako. Ba domin Hamma Lamiɗo na nan ba da watakila jininki ya tsiyaye mu ba mu samu mafita ba."
Cak kukan Ummu ta tsaya ta da kukanta ta yi kasaƙe tana kallon Baɗɗo cikin mamakin jin sunan wanda ta ambata.
Tabbas a ranar ya zo, amma ita tama manta da shi kwatakwata.

"Shi ya yanki zanin ki ya ɗaure hannun ki zubar jinin ya tsaya. Sannan shi ya ya ɗauke ki cak zuwa mota da ni da shi da Ammah da Baffa muka kawo ki wannan asibitin cikin tashin hankali."
Ummu ta sake ƙura mata ido cikin mamakin wai Hamma Lamiɗo ne ya yi mata haka? Da man yana da tausayi.? Ita kallon mara tausayi take yi masa wanda bai damu da kowa ba.

"Dakyar suka karɓe ki, sun ce case ne na hatsari suna bukatar yan sanda Hamma Lamido ne ya yi cuku cukun da suka karbe ki. An yi nasaran ceto numfashin ki amma suka ce sai an sanya miki oxygen kuma kina bukatar jini, ga shi Hamma Kabiru ba ya kusa ana maganar a je a duba a lab a ko za a samu wanda zai dace dake, kawai Hamma Lamiɗo ya ce jininsa O ne, nan take kuma aka je aka gwada shi ba wata matsala aka ɗibi leda biyu aka sanya miki a daran nan."
Ummu sai da ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login