Follow us on social media

Showing 15001 words to 18000 words out of 147042 words

Chapter 6 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

huɗu ba ka ci abinci ka kwanta kana tashi ka koma bakin aiki, sau tari shi ya sa ba ya kiran waya da rana sai cikin dare ko asuba, wani lokacin ma sai a yi kwanaki ba a samu wayar sa ba.


*littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*




*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/BxcTrVcz7GoIDzbqZTpIxF?mode=gi_t

*03*

Daga Daura bayan an gama ɗaura aure Abuja aka sake dawo da Amarya tunda anan ne ƙayattace gidanta yake a cikin jerin gidajen masu kumbar susa da faɗa a aji a ƙasar gabaɗaya. A ranar aka yi buɗar kan Amarya a gidan iyayen ango, tab an yi ɓarin miloyoyi wajen buɗan kan Amarya kamar kuɗi ba matsala ba ne a wajen su,  shi kan shi Ango dangin Amarya sun fanshe shi da miloyoyi, Matar Hamma Lamiɗo miliyan biyu ta fanshi kan Ango a madadin ita da Mijinta Yariman Daura, Muhammad Nasiru Muhammad Daura(Lamiɗo).

MC da aka gayyato domin gabatar da program ɗin ta kacame da guɗa tana yi ma Balkisu kirari.

"Takawarki lafiya Uwargida kuma Amarya a gidan Yariman Daura. Muhammad Lamiɗo ke ya zaɓa ke ma shi kika zaɓa, ɗiyar masu sarauta kike kuma Yariman daura ne mijin ki, sannu ƴar sarki matar ɗan sarki, uban ki sarki mijin ki ma zai yi sarki in sha Allahu, kuma za ki haifi Sarki da ikon Allah
Sannu likita bokan turai, uwar Sultan kike sannan ke ce kika haifi Beena. Na gaishe da sarauniya Balkisu, na gaishe da Matar Yariman Daura takwarki lafiya Gimbiya Balkisu Zinariya."

Sai dai kawai aka ga ta saƙa ma MC ɗin kuɗi a hannunta waje ya ɗau tafi Ummu ranar ba abin da ta yi sai faman bin shagulgulan bikin nan, matar nan ta Hamma Lamiɗo hadaɗɗiya ce ranar ma shigar lafaya ta yi, ta saka wani material gangariya daga ganin shi ya ba ma wasu nairori baya.
Tabbas ta cancanta domin zinariya ce.

Duk da Hamma Lamiɗo ba gwanin ta ba ne, ita ma matar tashi wata doguwar mu'amala ba ta taɓa haɗa su ba, amma dai ita a karan kanta tana yin matar saboda yar gayu ce mai kyau ce mai kama da model ce, ga ƴaƴan su farare gwanin ban shawa'a in ka ga rayuwar wasu sai ka yi tunanin wataƙila su suka zaɓa ma kansu, to komai na rayuwa na duniya sun same shi a hannu, suna yadda suka ga dama da shi.

Ita kanta irin mijinta ne ba ta samun zama, a ƙiyasin kirgin Ummu Salma sau biyu Dr Balkisu ta taɓa zuwa gidan su zuwa na musamman da ta kwana fiye da ɗaya.

Akwai zuwan da ta yi bayan auran su da Hamma Lamiɗo, to bayan shi ta yi biyu haihuwan matar Hamma Kabiru da yake wannan Aminin shi ne ta zo, sai wani zazzaɓi da Ammah ta yi mai zafi har ta fara sambatu hankula sun tashi, kowa ya ɗauka Ammah lokaci ya yi ashe zafin ciwo ne, suna Abuja lokacin kafin ta koma Lagos da zama ta zo duba Ammah, a lokacin Sultan na ƙarami to bayan shi
Yanzu daga baya tana biyo shi in ya zo hutun karshen shekara, tunda sai ya fara sauka a Jimeta ya gama kwanakin sa a nan suke wucewa Daura.

Daga ita har mijin nata suna yin wuyar gani, hutun na shi kuma a shekara sau ɗaya ne, in salla ne ma baya daɗewa za su fara sauka nan Jimeta su yi kwana biyu daga nan su wuce Daura saboda wasan hawan salla akwai ma sallolin da aka yi yana can bakin aiki bai ma samu zuwa ba.

Duk da itama tana da halin ɗagawa da ji da kai bai damu Ummu ba, ita dai bata ba ta haushi sannan tana burgeta ,hankalin ta bai kwanta ba sai da aka gama shagulgulan bikin nan sannan ta bari waya ta huta daga hannunta ta samu ta kira Ammah a waya ta gaisheta sama sama ma suka yi mgana tana cikin hayaniya ta ce za ta kirata ba kuma ba ta kira tan ba. Sai ta kudirta cewa in Ammah suka dawo za ta je har gida ta yi mata sannu da zuwa.

****

*NO. 224 NDC QUATERS. KADUNA NAGERIA.*
*9:47AM*

Da sassarfa take sauko wa daga kafar bene lokaci ɗaya hankalinta na kan agogon I.wacth ɗin dake maƙale a tsitsiyan hannun ta na hagu,  lokaci take dubawa domin tana da aji ƙarfe goma da rabi na safiya yau ɗin nan

Falon ƙasa ta sauƙo da yake shuru ba ka jin motsin kowa, farar mace ce doguwa mai ɗan kaurin jiki, tana sanye da wata gold ɗin atamfa mai ruwan ganye shi yasa mayafin jikinta ma da takalminta haɗe da jakan dake hannunta masu kalan ruwan ganye ne.
Hannayenta da zobban gold guda biyu da a warwaro suna ƙyalli, haka wuyan ta wani ɗan kunnen gold ne da sarƙan shi mai kyau da yarari.
A ƙiyasin shekarunta ba za ta wuce 52 ba sannan ba za ta gaza ba, amma a kallon farko za ka fahimci mace ce mai ilimi da gayu.

Sake duba lokaci ta yi, kafin ta ɗago kanta tana sake nazarin ƙayattacen falon mai kama da aljanar duniya. Falon babba ne domin saitin kujeru ne sama da guda huɗu saboda tsabar girman falon.
Zama ta yi kan ɗaya daga cikin kujerun falon lokaci ɗaya tana sauke jakar hannunta daga gefenta.

"Baraka."

"Baraka."

Ta shiga kiran ta wacce aka kira da Baraka, da fito da sauri daga wani koridon dake yamma, matashiya ce domin ba za ta wuce 20's ba har gabanta ta ƙariso ta durkusa lokaci ɗaya tana faɗin.

"Barka da fitowa Mami."

"Kin tashi lafiya Baraka?

Ta amsa mata, muryanta da ɗan asset na fillanci, lokaci ɗaya tana ciro wayarta daga cikin jakar dake gefenta.

"Lafiya lau Mami."

Jinjina kai ta yi kafin ta ce" Kin gama gyara ko'ina ko?
"Na gama Mami, saura na kitchen ne kawai."
"Da kyau Baraka shi ya sa nake son ki saboda zafin naman ki."
Dariya ta yi kanta na ƙasa itama Mamin murmusawa ta yi kafin ta ce" Yau na ga mutumin naki bai yi rigiman tafiya makaranta ba"

"Bai yi ba Mami, na lallashe shi da cewa zan goya sa in ya dawo."

Mami ta yi dariya har haƙoranta suka bayyana farare, da haƙoran makka a bakinta.

"Baraka ina ta ya Faruk kewa ranar da Iya tace a maida ke gida."

Baraka sai ta dukar da kai ba ta yi mgana ba Mami na ta dariya kunya take ji domin an saka ranar auranta karshen shekara nan za su ma yar da ita gida, daga can garin megidanta suka ɗauko ta Ɗan marke, ta fi shekaru biyar tare tasu tun ba ta kai haka girma ba.

Miƙewa ta yi, kafin ta ɗau jakarta Baraka ta yi saurin riga ta ɗauka lokaci ɗaya tana faɗin" Mami ba ki karya ba za ki fita?

"Sai na dawo Baraka."

Sai ta jinjina mata kai, suna tafe har habaran gidan makeke mai cike da motoci ga su nan kala kala sun kai guda biyar,  duka na kamfanin Toyota ita ma wata fara ta nufa camry da ita za ta fita yau, jakarta ta karɓa lokaci ɗaya tana cewa.

"Baraka ki kula da gidan sai na dawo."

Sai ta jinjina kai kafin ta ce" To Mami Allah ya dawo dake lafiya."
Lokaci ɗaya tana mai ɗan ramƙwafawa alamun ladabi, tana ƙoƙarin buɗe mota wani matashi ya rugo da gudu ya zo ya buɗe mata.

"Barka da Safiya Mami."

Sai da ta shiga cikin motar ta zauna sannan ta amsa masa.

"Ka tashi lafiya Hamisu?

Ya amsa cikin ladabi kafin ya ce" Lafiya lau Mami.. za a fita ne? Allah ya tsare ki ya sa ki dawo lafiya."
Mami na mirmishi ta amsa kafin ta ce" Ba wata matsala ko Hamisu?
Yana sosa kai ya ce"Hajiya Baraka ba ta ba ni abin karyawa ba goma ta kusa ta san ni mutumin kauye ne da wuri na ke karyawa amma Baraka sai sha biyu na rana take kawo mini abin karyawa fisabillahi fa Mami."

Kafin ya dire maganarsa ya fara sha harara wajen Baraka, Mami tana ta dariya diraman Hamisu da Baraka. Kuma duka daga gari ɗaya suke Abban islam ne ya ɗauko Hamisu yana kai yara makaranta sai ɗan aike-aike da kula da fulawoyin gida.

"In ka matsu sai ka shiga ka dafa."

Baraka ta faɗa sannan ta yi tsaki ta kama hanyar komawa cikin gida.

"Mami kina dai jin ta dai ko?

Mami na dariya haƙoranta a waje kafin ta ce" Na ji ta Hamisu ƙyale ta."
Jakarta dake kan kujeran mai zaman banza ta buɗe ta ɗauko masa 5k yan dubu dubu ta miƙa masa ya rankwafa ya karɓa.

"Ka siya wani abu ka ci, ka rabu da ita lokacin da ta kawo maka sai ka ƙara"

Washe baki ya yi kafin ya ce" Na gode Mami, Allah ya tsare gaban ki da bayan ki. Allah ya raya miki yaran ki cikin aminci, yadda kika ɗauke mu da mutumci kina saka mana da dukkan alheri ke ma Allah ya saka miki da alheri."
Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" To sai na dawo Hamisu."
"A dawo lafiya Mami Allah ya tsare."

Ya rufe mata ƙofar motar ya ruga da gudu wajen Sunusi maigadi, itama sai ta kunna motar ta yi riverse ta dumfari get tana zuwa da man Sunusu ya buɗe mata sai ta tsaya ta ɗan sauke gilashi bangarenta suka gaisa cike da mumtatawa.

"Sunusi ina sane da mganar mu. Jibi Abban islam zai dawo za mu yi mgana da shi in sha Allahu."

Ya jinjina kai kafin ya amsa" Allah ya dawo da shi lafiya Hajiya. Na gode sosai da karamcin ki."
Kai ta gyaɗa masa kafin ta ce" Ba komai, sai na dawo"
"Allah ya tsare ki Hajiya."
Ta zuge gilashin sannan ta taka mota ta fice shi kuma ya rufe get ɗin ya koma saman farar kujeran da ya tashi kusa da Hamisu suka cigaba da hiran su, kuma duk na yabon kyawawan hallayan Mami ne na kirki.

Sannu sannu tana ta tafiya har zuwa cikin garin kaduna, daga nan ta ɗauke hanyar jami'ar ta Kaduna, Kaduna state University KASU.  In da anan take koyarwa a Department ɗin Biology. Har cikin department ɗin su ta shiga da motar ta, ta yi parking ɗin ta in da aka tanada domin parking ɗin motoci, tana ƙoƙarin fitowa daga motar ne ta ji wayarta dake jikin jaka ta ɗan yi ƙara alamun an tura mata saƙo da kamar ba za ta duba ba, saboda ita saƙonni ma sun isheta a waya ba ta dubawa gwara mutum ya kirata da ya yi mata saƙo.

Jakarta ta jawo ta ɗauko wayar na ta iphone 14 ce, tana dannawa haske ya kawo sai ta ga saƙo ne daga My First Daughter, sai da ta murmusa ta manta yau Jumma'a da man ƙa'ida ne duk ranar irin ta yau Ummu Salma tana tura mata saƙon barka da Jumma'a kuma tana jin daɗi sosai.

"Barka da Jumma'a Mami na. Allah ya tsare ki da tsarewarsa. Allah ya ba ki abin da kike nema duniya da lahira. Ubangiji ya yi ma rayuwarki albarka. Happy Jumma'at mubarak."
  
Har ta gama karantawa da mirmishi a saman fuskarta, latsa lambar Ummu ta yi, jiya da daddare ta so kiranta sai ta sha'afa gwara ta kira ta yanzu kar ta sake mantawa.
Ringing ɗaya zuwa biyu Ummu-Salma daga can garin Jemeta ta ɗaga kiran.

"Mami na"

Ta faɗa daga can bangaren cikin murna da bayyana har a muryanta.

"Naam Daughter kuna lafiya?

Ummu ta amsa mata, suka gaisa daga can bangaren Ummu ta ce" Mami na ina su Islam?
"Suna makaranta."
"Yaushe za su zo?
"Sai sun samu hutu za mu taho gabaɗaya Daughter."

Daga can bangaren Ummu ta yi tsalle kafin ta ce" Mami na da man na yi kewar ki."
"Nima na yi kewar ɗiya ta."
Habib ta tambaye ta sai ta amsa mata da cewa ya tafi wajen aiki.
"Ki gaishe mini da shi."
"In sha Allahu Mami na."

"Daughter na siya miki kayan measurement ɗin fulawa, har spicess na kayan girki suna nan in zan taho zan taho miki da su in sha Allahu."

"Na gode Mami na. Allah ya saka miki da alheri."

Ta faɗa muryanta cike da murna, Mami ta amsa da Amin kafin ta ce" Take care na shigo cikin makaranta ne

"To Mami Allah ya ba ki sa'a."

Daga nan suka yi sallama.
Tana shirin mai da wayar cikin jaka ne, sai kuma ta fasa saboda wajen messages ɗin ta 99 ta gani alamun tana da saƙonni da yawa nufinta ta shiga ta yi delete all, duk MTN ne sai na bankun nan ta, amma sai me tana shiga sai ta bige da ɗan dubawa, tana ɗan jan ƙasa ta ga wata lamba ta turo mata saƙo, yanayin lambar ne ya sa dole ta shiga saƙon domin special number ce.

"Za a yi auran ɗiyarki Batula. Ko ba ki zo dan ni ba ki zo don Lamiɗo, in shi ma ba za ki zo domin shi ba to ki zo domin gudan jinin da Allah ya haɗa a tsakanina da ke. "

Na farko kenan na biyu kuma cewa aka yi.

"Tun da ba za ki samu zuwa ba Batula ba, ko yaran mu ki bar su su zo don Allah Batula."

Ko bai saka sunan shi ba,  ko bai ambaci wata magana da za ta nuna shi ɗin ba ne, to shi ne domin nan duniya mutum ɗaya ne ke kiranta Batula ko Baffa Fatima ya ke kiranta, tuni fara'an dake saman fuskarta ya gushe cikin lokaci ƙalilan fuskarta ta sauya ta yi wani ja saboda bacin rai.

Hannunta na rawa ta goge saƙon gabaɗaya daga wayarta. Tana mamakin yadda aka yi ya same ta? Ita dai ta san ta rufe duka layukan da ya ke kiran ta da su, sai daga baya ta duba sai ta fahimci ya sauya wata lambar ne me ya rage tsakanin su? Ɗan shi ne kuma ba ya tare da ita, yana tare da shi me ya sa ita ba zai ƙyale ta ba? Ta ce ta yafe masa amma ba za ta bari mu'amalan wai Uba da uwa ta haɗa su ba.  Tana da miji shima yana da matan shi, ɗan shi kuma ya san in da yake ba to bini-binin na mene ne? Ita fa har abada ba za ta yi wani aminci da su ba, babu sauran wani aminci har abada atsakanin su.

  Sai yanzu ne ya san da gudun jinin da ya haɗa su? Sai yanzu?  Ai lokaci ya kure musu, kurewan da ba za su iya gyara abin da suka lalata shi sama da shekaru talatin ba. Sai yanzu ne Fargar jaji ya kama su? Ba su da sauran abin da za su iya yi a yanzu, gabɗaya ta rasa natsuwarta in ta fita a haka ma ta je aji  ɗalibai za su fahimci yanayin ta ba daɗi shi ya sa ta yi zamanta cikin mota tana faman sauke ajiyar zuciya.

Wai saboda Lamiɗo! Waye wani Lamiɗo! A lokacin da ya ke zanin goyo da jinin haihuwa a jikinshi da ba a samu damar wanke shi ba, mahaifiyar shi ba ta duba Lamiɗon a lokacin ba, ba ta duba shi ba ta saka ya yi ma rayuwarta mummuman taɓon da har ta koma ga Allah ba za ta taɓa mantawa ba. Shi kuma ya aiwatar da Umarnin mahaifiyarsa saboda kare martaban masarautar su me ta aika ta? Wani laifi ta aikata da za a sake ta a lokacin da zufan naguda bai gama safka daga jikinta ba? Saboda ita ba yar masu kuɗi ba ce, saboda ita ubanta ba sarki ba ne, tuna haka kawai in ta yi sai ta ji yanayin ta cikin kuka, yanzu ma hawaye ne suka kece mata, shi ya sa har abada ta tsani duk wani abu da ya shafi Sarauta daga kowani bangare ne, abin da ta sani su ɗin masu son kan su ne marasa adalci abin da suka yi mata ya munin da har abada ba ta fatan kafarta ta sake takawa Daura, tun bayan fitar ta ɗauke da jinin haihuwar dake jikinta ta yi alƙawarin ita da wannan garin har abada.

Duk da ko da har gobe akwai dangin mahaifiyarsu a garin ba ta taɓa jin marmarin sake saka kafarta a cikin sa ba, domin a cikin sa ta samu farinciki amma kuma ya gurɓata da baƙincikin rayuwarta duk farincikin da rayuwarta da ta ke ciki yanzu da ta tuna da rayuwarta ta baya sai ta ji komai na duniya ya yi mata ƙunci. In tana tuna wahalar da ta sha, deperession ne ya nemi kama ta, Allah ya saka ma Baffa da Ammah da alheri sune suka zama silar da ta zama Fatima a yau, in ta kalli rayuwarta yanzu sai ta ji ba za ta iya saka ma Baffa da Ammah ba domin sun yi mata komai anan duniya.

Ammah kuma ita ce ta sakar ma ɗan ta, ita ce ta yi wahala da shi, shi ya sa nan duniya kowa ya shaida Lamiɗo ba shi da wata uwa sama da Ammah itama ta shaida haka, yadda ta wahala da Kabiru haka ta wahala da Lamiɗo, kawai ita mahaifiyarsa ce a haihuwa, Ammah kuma uwa ce a gare shi da ta sadaukar da duka rayuwanta wajen kula da shi.

Hawayenta take sharewa, tana jin sanyi a cikin ranta tunda tun a duniya Fulani ta ga sakamakon ta, domin sai da ta zo ta roƙe ta gafara akan abin da ta yi mata sannan ɗan da ta guda tun yana cikin jinin haihuwa shine Sanyin idaniyar masauratar Dauran da suke taƙama da shi, ko a haka aka tsaya sun ga sakamako mai kyau, su ƴa'ƴan sarakunan da ta aura masa ba su iya ba ta abin da take so ba, dole dai sai ita ita ɗin da ba ƴar kowa ba ita ce ta sama mata abin da take muradi, to a haka aka tsaya ita Fatima ta yi nasara.

Tissue ta zaro daga cikin motarta ta goge fuskarta a fili ta furta" Allah ya jiƙan ka da Rahama Abba. Marigayi tsohon Sarkin Daura Muhammad Shitu Daura."
Tana tuna yadda ya ƙauna ce ta wata ƙila da yana raye da an yi mata adalci. Shi ne ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login