Follow us on social media

Showing 144001 words to 147000 words out of 147042 words

Chapter 49 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

Ni dai Allah ban yarda da shi ba."
Abin da kawai taji tana faɗi kenan.

Sai kuma in da ta ce" Baffa ni fa ba wai na ƙi mganar ba ne, sam shi da ƴata ba su dace ba. Ba za ta iya da halin bamuden ɗan Ammah ba."
Kamar ta so ta ɗau saunar mganar, Hamma Lamiɗo ne Mami ke kira da wannan sunan amma kuma yarta ta fa? Wacce take nufi.

"To Baffa muna hanya ne, zan kira ka in mun koma gida"
Bayan ta katse wayar kuma ba ta ba da wata kafa da za a fahimci wani abu ba, sai ta bige da jan Ummun da wata hiran da ya sa ma ta manta da wayar Mamin, bayan sun koma gida kowa ya shiga ɗakinsa, daga nan ba ta sake jin wata mgana ba.

Bayan isha'i sai ga Baffa ya kira Ummu Salma a waya bayan sun gaisa kamar kullum ya ce ina amaryansa Ummu ta ce ta kwanta.

"Ummu Salma."
Tunda ta ji Baffa ya kira sunanta  ta san akwai magana a bakinta.
"Naam Baffa."
"Wane ni a wajen ki?
"Kai mahaifina ne"
"Alhamdulillah kin san duk abin da zan yi ga rayuwarki ba nufin na cutar dake ba ne ko Auta?

"Na sani Baffa."

Har idanuwanta sun fara tara ƙwalla saboda ba ta son me ya faru ba.

"A lokacin auran ki na farko ban yarda an yi miki dole ba. Duk abinda kika nuna baki so ni ma zan ce bana son shi. Har kuma yanzu da kike bazawara kina da haƙƙin sake yi ma kanki zaɓi a karo na biyu."
Baffa ya yi shuru yana jan nunfashi.
Ummu har ta fara kuka, tsoro take ji kar Baffa ya ce ta yi aure, ba za ta iya masa gaddama ba amma tabbas hakan cutuwa ne a gare ta.

"Ummu Salma."

"Naam Baffa."

"Jiya an zo neman auran ki a wajena."
Gabanta ya amsa ras!
Jikinta har ya fara rawa.

"Kuma wamda ya zo ɗin ba zan iya hana shi ba, na hango miki kyakyawan rayuwa tare da shi."
"To Baffa."
Ta iya faɗa tana kuka.
"Ba dole zan yi miki ba, amincewarki  nake nema Auta, in har kin amince gobe da safe ni da yayyenki dake kusa zamu jagoranci ɗaurin auran ki."

Wannan ba amincewa ba ne, Umarni ne Baffa ke ba ta amma a fakaice duk yadda ta tsani aure ba ta isa ta yi ma Baffa gaddama ba su suka tsaya ma rayuwarta kuma ba ta isa ta bijire ma mganarsa ba.

"Kar ki damu in ba ki amince ba, ba komai sai na bashi haƙuri."

Ya faɗa cikin wani yanayi a muryansa akwai zumuɗi daga a farko, daga karshe shurunta sai ya sanyaya ma muryansa ƙarsashinta.

"Baffa."

Ta kira shi cikin muryan kuka.
"Naam Auta, kuka kike yi ne?
"Aa Baffa."
Ta faɗa tana share hawayenta da hannunta.

"Kar ki damu na ce in ba ki amince ba sai na ba shi haƙuri."

"Aa Baffa."

"Kin amince?

"E Baffa."

"Kin tabbata?

"Na amince Baffa, in dai ka amimce nima ba ni da ja."

"Na amince da shi Auta, wallahi ina mai yi miki rantsuwan da cewa yadda zai kula da kansa haka haka zai kula da ke Auta."

"To Baffa."

Ta faɗa tana danne kukanta

"Allah ya yi miki albarka Ummu Salma, yadda kika karɓi tayina Allah ya wanzar da farimciki a rayuwarki ta har abada. Na gode miki Allah ya gode miki Auta."

"Amin Baffa."

Ta faɗa tana jin sanyi a zuciyanta.
Baffa kuma jin ba ta tambayi ko waye ba shi ya sa bai faɗa mata ba suka yi sallama suna gama waya ta tashi da gudu ta fita ta haura sama zuwa ɗakin Mami tana kuka, Mami na zaune gefen gado waya take yi sanda Ummu ta faɗo tana gunjin kuka ai sai ta saki wayar saman gado ta nufeta cikin rawan jiki.

"Subhanallah Ummu me ya ke faruwa ne?

"Mami."

Ta faɗa cikin gunjin kuka lolaci ɗaya tana faɗawa jikinta.

"Shi, bar kuka yi mini bayanin abin da ya faru."
Ta faɗa tana janta gefen gado suka zauna.

"Mami aure Baffa zai yi mini"

Mami ta zaro ido kafin ta ce" Aure kuma? Da wa?
"Ban sani ba Mami"
Ta faɗa tana tsiyayan hawaye.
"Yanzu Baffa bai bar mganar nan ba? Na ce nima ban amimce ba. Yanzu ma da Abban Islam muke mgana shima ya kira shi ya faɗa masa, kuma da alamu ya goya ma Baffa baya."
Kukan Ummu ya ɗauke kenan kowa daman ya sani? Har Daddy ma ya amince kenan

"Bar kuka, in dai ba ki so ba wanda zai yi miki dole."
Wayarta ta jawo za ta kira Baffa.
"Baffan zan kira."
Da sauri Ummu ta riƙe mata hannu lokaci ɗaya tana mai girgiza mata kai.

"Ki bari na kira shi na ce ba ki so."

"A'a Mami, ki bar shi kawai."

"Me ya sa? Kin amince kenan?

Ummu na hawaye ta ce" Na amince Mami, ba tilas ba ne sai da Baffa ya nemi zaɓina."
"Tilasa ne mana ai ba ki ga wanda za a aura miki ba, ballatana ki ji kina son shi har ki amince da shi."
"Mami ba komai in dai Baffa ya amimta da shi a wajena Amintattace ne."
Mami ta yi shuru tana kallonta.
"Kin tabbata? In dai ba ki so zan ta da auran nan"
Da sauri ta sake girgiza kanta.
"Aa ina so Mami kar ki yi mgana."
Sai Mami ta sake yi mirmishi.
"To share hawayenki, ɗiyar albarka"
Sai ma ta taya ta ta share hawayenta.

Sannan ta riƙe hannuwanta tana faɗin" Ki natsu kin ji ko? Ki yi ta addu'a in sha Allahu kin samu sauyin rayuwa. Ina tare dake har numfashina na ƙarshe."
Sai Ummu ta fashe da kuka ta faɗa jikin Mami.
"Mami Allah ya bar min ke."
"Amin ɗiya ta."
Ta daɗe a ɗakin Mami suna ta hira, sai daga baya ta koma ɗakinta, ranar ta sha kuka amma ta kwana salla da addu'an neman zaɓin Allah.

Kuma da garin Allah ya waye ta samu natsuwa amma tana cikin fargaba, tun safe Mami ta fita Faruku ma na makaranta daga ita sai Baraka.
Ba wanda ya kira ta ballatana ta ji ko an ɗaura auren ko ba a ɗaura ba

Can wajen huɗu da wani abu na yamma tana ma zaune ne ta idar da sallar la'asar ne  Daddy ya kira ta da lambarsa tana ta mamakin yaushe ya dawo?
Amma abin da ya tambayeta ne ya sa ta fara rarraba ido.

"Ummu Salma gamu a masallaci za a ɗaura auran ki, nawa kika yanke Sadakin ki?

"Naam"

Ta faɗa cikin rashin sanin madafa.
"E nawa kika yanke masa?
"Daddy duk abin da ka ce."
"Aa haƙƙin ki ne."
"Dubu dari."
Ta ji bakinta na faɗa.
"Tana jin Daddy na maimaita ta ce Dubu ɗari daga nan ta ji mganganun mutane ta cikin wayar sannan Daddy ya kashe wayar, abin mamaki yaushe Daddy ya dawo? Ba daɗewa Mami ta dawo da ta ba ta labarin Daddy ya kirata kamar fa yana Jimeta.

"Yana can, Baffa ya ce sai ya dawo shi zai ba da auran ki."

Mami ta faɗa cikin fara'a. Daga gani abun ya yi mata daɗi.

"Shi ne ya ta so a yau, saboda shi ne ma ya sa daurin auran ya kai bayan la'asar."

Ta sake faɗa tana kallonta.
Ummu dai ta kasa magana saboda yadda jikinta ya yi wani sanyi ƙalau Mami ta shiga kiran Basira wacce ta fito tare da Hanan biye da ita tana ganin Mami ta nufeta tana kiran sunanta.

"Mami oyoyo."

"Oyoyo Hanan."

Mami ta faɗa tana cafe ta, tare suka zauna saman kujeran falon tana shafa kanta.
"Barka da dawowa Mami."
'Yauwa basira."
Sai ta kalleta yadda ta ɗan rankwafa cikin ladabi
Ummu ta juya za ta bar falon kenan Mami ta kalli Basira tana faɗin" rangwaɗa ma Ya Ummu guɗa yau an ɗaura mata aure Basira."
Ai Basira na jin haka ta miƙe ta rangwaɗa guda har sai da Uummu ta toshe kunnuwanta ta bar falon da gudu Mami ta bi ta dariya Hanan ma na ta yata.

"Ma sha Allah, Allah ya sanya alheri Mami."
"Amin Basira.  Yau ki shiga kitchen Amarya ba yanayi gobe ayi abinci da yawa Hamisu zai kawo takeway, za a fita a yi sadaka."
"Allah ya biya ki Mami."
Ta amsa da Amin nan ta bar falon tana ta ya Ummun Murna domin ta ɗan san wani labarinta, tana tausayin kanta amma tana tausayin Ummu Salma duk da tana cikin gata.

Ummu Salma ɗaki ta shige tana ta kuka, ba ta taɓa hasaso ma kanta a aure awannan tsakanin ba, sai ga shi kaddara ta sake juya rayuwarta a karo na biyu, wayarta ma kasheta ta yi domin ba ta son ma a dame ta. Mami ma ba ta sake nemanta ba, sai dare da Daddy ya dawo ya kirata.

"Ga Sadakin ki, na ba da auranki akan dubu ɗarin da kika lamince."

Daddy ya faɗa bayan ta karɓi kuɗin a farin takarda. Mamaki take yi, kenan da gaske ne?

"Allah ya ba ku zaman lafiya. Kin yi dacen samun nagartattacen miji Ummu Salma."

Kowa na faɗin ta yi dace amma ba a faɗa mata waye mijin ba, itama ba ta son sani shi ya sa ba ta tambaya ba.
Har da goro da dabino da minti duk Daddy ya taho da su, ita dai kuɗin kawai ta karɓa ta koma ɗaki ta tasa su gaba tana sharɓan kuka komai ya dawo mata sabo, yanzu kuma ina za ta je? Wata rayuwa za ta sake faɗawa? Menene makomar Hanan?

Washegari tun safe Mami da Basira suka shiga kitchen jalop din shinkafa da nama suka dafa aka saka a takeway ɗari har da matar Sunusi ta zo ta taya su aiki Ummu na ciki ba ta fito ba, ta dai fito sun gaisa da Mami, ba ta kawo dalilin auran ta ne ya sa Mamin yin Sadaka ba, da yake ta san suna yi duk karshen wata amma yau ɗin na daban ne har da drink da ruwa.
Hamisu ya fita da shi a mota zai je makarantan almajirai a hayin banki zai raba musu.

Ummu abincin ma ba ta ci ba sai da Mami ta leƙo ta yi mata mgana sannan ta fito ta sha tea, ga shi dai ita ta amimce amma kuma abin duk ya dame ta. Ta yi na farko ba ta dace ba yanzu kuma ba ta san wata irin kaddara za ta sake faɗawa a karo na biyu ba.

Sannan da ta kunna wayarta kowa fatan alheri yake yi mata cikin yayyenta,  Hamma Jibo har da cewa Amarya, shi ko Hamma Mustapha wani suna ya kira ta da shi our princess
amma ba wanda ya kira sunan mijin da  aka aura mata, itama ba ta tambaya ba har Baɗɗo da suka yi waya murna take yi mata.

"Sisna, tabɗijam kin samo mai zafi wannan karon. Cancaɗi."

Amma ba ta faɗa mata waye ba, itama ba ta ce tana son sani ba.

"Sisna, ni fa bana son auren nan. Ban zan iya ma Baffa Gaddama ba ne."

"Sisna, ai wannan auren na musamman ne, ya doke wannan auren naki na farko, tab ai tazaran kamar tazaran kasa da sama ne, Habibun banza shi ko a hanya bai isa ya haɗa kafaɗa da mijin ki na yanzu ba wallahi."

Ummu dai ba ta biye ma Baɗɗo ba, ba ta son ma tana jin sunan Habibu saboda tsanar da ta yi masa.
Har Ammah da suka yi waya ba ta nuna mata wani abu ba sun dai gaisa kamar Yadda suka saba, kuma ta ji ta duk a cunkushe ba cikin walwala ba. Baffa ne ma da suka yi waya ya dinga saka mata albarka cikin farincikin da ta jima ba ta ji shi a cikin sa ba.

Sati ɗaya da ɗaurin auran ta, har a lokacin ba ta saki jikinta ba. Sukuku take, da gaske ne ta tsani aure domin ta tabbata ba komai cikinsa sai baƙin ciki da da dana sani, ta fa gwada kuma ba ta dace ba.

Amma ba ta da yadda za ta iya tunda ta amsa ma Baffa an riga kuma an ɗaura baƙin alƙalami ya riga da ya bushe.
Mami kamar murna ma take yi domin ba ta ga alamun ta damu da ganin yanayin ta ba, tunda aka ɗaura auren nan duk dare sai ta yi kuka, so kawai take yi ta samu wani dalilin da za ta sauwaƙe ma kanta wannan auren, in ta tuna auren sai ta tuna makomar rayuwanta anan gaba, ba ta san mijin ba amma ta fi karkata tunaninta da wataƙila daga can Mubi ne tunda ta ga kowa ya san shi.

Ranar Ummu ta yini  cikin nazari, duk hanyar da za ta ɓulle da ita sai kuma ta je karshe ta iske a toshe take, yini ta yi a ɗaki ba ta fito ba kamar wata mara lafiya
Hanan na wajen Basira, kamar ta san yanayinta na yau ba ta zo ta yi mata rigima ba. Tana kwance Basira ta zo tana faɗa mata Mami ta yi baƙo, mamaki ya kamata wani irin baƙo kuma? Kuma Basira ta ce yana Falo, kafin ta fita ta yi ta kiran wayar Mami ta ji ko ta san da zuwan baƙon amma wayarta ba ta shiga shi ya sa ta saka mayafin abayan dake jikinta ta fita zuwa falon Mami.
Duk a tunaninta tunda aka ce ya shigo har falo to ko daga Jimeta ko daga cikin dangin Daddy shi ya sa ta fita kanta tsaye ba fargaba.

Mamaki ya sandarar da ita lokacin da ta yi arba da ganin Hamma Lamiɗo zaune a falon Mami yana ɗauke da Hanan a jikinsa tana ta wasa da sajen fuskar shi.

Sanye yake da farar shadda, har tana ƙyalli kansa da hula amma saboda suma a saman gashin hulan tasa baƙa ta tsaya.
Ya ji shigowarta amma bai iya ɗagowa ya kalleta ba.
Ummu ta ce a ranta lalle Mami na da Babban baƙo
Domin tunda ta zo gidan ba ta taɓa ganin ya zo ba sai yau.
Me ya kawo shi? Ta tambaya a cikin zuciyarsa.

"Ko kin manta Mami mahaifiyarsa ne?

Wata zuciyar ta tunasar da ita abin da ta manta. Har ga Allah mantawa take yi da Mami ce ta haifi Hamma Lamiɗo.

"Barka da zuwa Hamma Lamiɗo."

Ta faɗa bayan ta ɗan ƙariso falon. Da farko ta so ta yi wucewarta ne saboda Mami ta tsaya da kuma tuna ya fa taimake ta, da jininsa take rayuwa a yanzu.

"Lafiya."

Ya amsa mata, sau ɗaya ya kalleta bai sake ba, wasa yake yi ma Hanan. Ta so ta yi komawarta ɗaki ne domin ita yanzu neman ma kanta mafita take yi amma ganin yadda ya ɗauki Hanma ya sa ta ji sanyi a zuciyarta, ko ita bai yi mata kallon Daraja ba ta ji daɗi da ya yi ma Hannan kallon mutumci shi ya sa
ta je kitchen ta haɗo masa ruwa da lemu, Daddy ba ya nan ya je Abuja tun jiya amma a yau Mami ta ce zai dawom

Har ta kawo ruwan ta ajiye ta fita falon bai ɗago ba, itama ba ta damu ba ɗaki ta koma ta yi kwanciyarta tana cigaba da sabon lissafin da ya kamata tun bayan auran da aka ɗaura mata, tunani take yi me ya sa Allah bai amsa addu'arta ba? Ita da har a masallacin Madina ta roƙesa da Allah ya sa ta mutu ba ta sake aure ba. Me ya sa kuma Kaddara ta sake buɗe mata wani sabon shafin rayuwa? Ba ma batun ba ta son mijin da aka aura mata ba, auren ne gabaɗaya ba ta so. Ta ma manta da baƙon Mami ta na ciki tana tufka tana famam warwara
Har Mami ta dawo  ba ta sani ba sai da ta shigo ɗakinta sannan a lokacin ta san ta dawo

"Kika zo nan kika kwanta Ummu?

Mamin ta faɗa tana kallon ta.

"Mami sannu da zuwa Yaushe kika dawo?
Ummu ta faɗa tana ɗan miƙewa zaune a saman gadon data ke kwance.

"Ban daɗe da dawowa ba. Sai kika bar baƙo shi kaɗai a falo Ummu?

"Mami to na ga Hamma ne ya zo, kin san shi ba ya son hayaniya shi ya sa na baro falon na dawo ɗaki ."
Ta faɗa tana ɗan mikewa zaume.

"To mijin ki ne, in ba ki zauna ba ai ba za ku fahimci juna ba."

"Na'am"

Ummu Salma ta faɗa tana kallon Mami domin sai ta ji kamar ba ta ji daidai ba.

"Ko ba ki san baƙon ki ba ne?

Mami ta sake faɗa tana kallonta.
Ummu ba ta son ta dire ƙasa ba sai da ta ganta a tsaye kan kafafunta.

"Baƙo na kuma?

Ta faɗa cikin mamaki.

"Baffa bai kira ki ba?

Mami ta sake tambaya, domin sun yi mgana da Baffa shi ya faɗa mata Lamiɗon zai zo su yi magana da Ummun a tunanin ta Baffan ya kira Ummun ya sanar mata.

"Mami."

Tana ta yi magana amma ta kasa jikinta ya yi wani irin sanyi.

"Ki gyara jikin ki, ki je ki same shi."

Mami ta faɗi haka da sauri lokaci ɗaya kuma tana barin ɗakin.
Ai sai Ummu Salma ta ji kamar ta daina jin mgana ta kurmance, kamar shiga da fita haka ta ji kalaman Mami.

"To mijin ki ne, in ba ki zauna da shi ba ta ya za ku fahimci juna?

Idanuwanta sun fito waje saboda firgici da razana, in dai har ta ji daidai to Mami na nufin Hamma Lamiɗo ne mijin da aka aura mata.

Innalillahi wa'inna ilaihirraju"um."

Ta faɗa a zucci da sarari lokaci ɗaya ta ɗora hannu akai ta fashe da kuka.

"Ina ni ina Hamma Lamiɗo, wallahi bana son shi."

Take faɗa tana kuka lokaci ɗaya ta koma ta zube kan gado, ji take yi kamar ta yi hauka, ina, ina za ta iya zaman aure da Hamma Lamiɗo, ai an gudu ne ba a tsira ba, sai ta ke jin kamar ta fita ta yi ta gudu kar ta tsaya, ita da ko inuwa ta minti goma ba ta taɓa haɗawa da shi ba, ta ya ya za ta iya haɗa inuwar aure da shi? Mafitan ta na ƙarshe shi ne ta samu mijin ta roƙe shi ya sauwake mata domin ba za ta iya masa biyayya ba, amma jin wai Hamma Lamiɗon ne mijin tuni lissafinta ya ƙwace. Ko burkutu ta sha ba za ta iya doguwar magana da shi ba, in tunanin ta ma ya kawo mata sunan shi ji take yi kamar ta haukace. Innalillahi ta shiga ta uku ta lalace. Ita Ummu Salama ina ita ina Hamma Lamiɗo?



Ƙarshen littafi na ɗaya.

Akwai sauran tafiya, mun gama shimfiɗa yanzu muka kwarari doguwar tafiya. Ga dai Lamiɗo ga Ummu Salma, mu je zuwa domin ganin yadda tafiyar za ta kai su.
Ku biya kuɗin karatun ku na La shakka babu nadama a cikin wannan tafiyar in sha Allahu.


*littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login