Follow us on social media

Showing 96001 words to 99000 words out of 147042 words

Chapter 33 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

san shi, har ma wani lokacin yana yi masa kyauta

"Alhaji barka da zuwa."
Bafullatanin maigadin ya faɗa da hausar sa irin ta fulani.

"Yauwa."

Habib ya faɗa yana mirmishi, get ɗin ya ruga ya buɗe masa shi kuma ya sulala motar tasa zuwa cikin haraban gidan da ga motoci nan guda uku a haraban gidan, alamun megidan yana ciki tunda yaran gidan ba sa tuka kansu a mota sai in kin yi aure baban zai ba ki mota amma in dai kina gida direba ne zai kai ki duk in da za ki je, kuma ya koma ya dawo da ke.

Habib ya daɗe yana tunanin kamar gidan da ya zo sun fi ƙarfin shi amma in ya tuna yadda soyayyar su ta fara sai ya ji ya samu ƙarfin gwiwa da yadda abar kaunarsa ta ba shi tabbacin duk abin da suke so shi mahaifinsu ke so, kuma shi ya yarda da kan shi duk da shi ɗan talakawa ne amma yana da ilimi da dukkan nagartan da duk in da ya je za a ba shi aure.

Bayan ya daidaita motarsa a haraban gidan ya ɗau wayarsa ya yi kira.

"Gani na iso haraba."

Ya faɗa yana mirmishi.
Daga can bangaren aka ce.
"Na ga zuwan ka, ina sama ina hangen ka a cikin mota."
Jin abin da ta ce ne ya sa ya ɗaga kai yana kallon saman, dai dai lokacin da aka saki labule aka juya. Mirmishi ya yi zuciyarsa har wani rawa rawa take yi saboda yadda yake daraja wannan ranar.





*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t


*15*

*DUALA ROAD. APAPA LAGOS NIGERIA*
*NO:447.*
Teusday, 2:30pm.

Wata baƙar mota ƙiran TOYOTA(PRIUS) ta fito daga General Hospital dake Apapa Lagos (C9R9+QG7 Abaraham adesanya road) da misalin ƙarfe biyu da rabi na ranar talata gabaɗaya gilasan motan tintec ne shi ya sa ba lalle na waje ya iya ganin na ciki ba. Gudu motar ta yi ta shararawa a kan shararen titunan da ke Apapa na garin Lagos ba daɗewa sai ga shi  motar ta iso anguwan Duala road a bakin wani katafaren gida mai blue ɗin get lambar gidan 447.

Hon motar ta yi ba ɓata lokaci kawai get ɗin gidan ya wangale motar ta sulala cikin haraban gidan, kusa da wata mota itama kirar toyota amma camry dake fake a haraban gidan motar ta tsaya.

Daga can cikin parking space kuma akwai wata ɓakar RAVA ita ma ƙirar Toyota.
Yanayin parking ɗin da ta yi ba ta daidaita tsayuwar motar ba
Da gudu bayarben megadin tare da wani matashi suka rugo a guje har suna bangazan juna wajen buɗe murfin motan sannan bayan sun buɗe suka rankwafar da kawunansu a ƙasa a tare suka haɗa baki wajen faɗin.

"Welcome Mah."

Haka suke faɗa, kuma ba su daina faɗa ba, sannan wacce suke kira da Mah ɗin har a lokacin ba ta sauko daga motar ba, sai da tafi mintina goma sannan kafaarta ɗaya ta fara saukowa farar kafa da wani takalmi mai igiya baki hill mai tsini sannan ta sake sauko da ɗayan kafar nan ma sai da ta ɓata lokaci kafin jikinta da ita kanta su bayyana a waje.

Farar mace ce doguwa mai kaurin jiki jikinta sanye da riga da wando suit na mata masu ruwan toka, wondon yana da buɗewa ta ƙasa, saman rigar jikinta rigan likitoci ne, a jikin ɗan wani anini da ke jikin rigan an rubuta DR. BILKISU BAYERO.
Sannan kanta ta yane shi da wani baƙin mayafi mai santsi idanuwanta ɓoye cikin wani baƙin glass. Kyakyawa ce domin fuskarta doguwa ce ga dogon hancin ta har baƙa yanayin fuskarta ba wani fara'a, hannunta riƙe da jakarta na hannu ƙarama baka yatsunta sanye da zabban gold guda biyu masu kyau da tsari.

Taku ta fara yi cikin taƙama da isa kamar yadda ya zame mata jiki da daɓi'a, ko kallon ma'aikatan da suke rankwafe suna yi mata sannu da zuwa ba ta yi ba ta yi wucewarta ta nufi wata ƙofa babba mai kyau da tsari sai da ta saka password sannan kofar ta buɗe ta shige kuma ta rufe kanta, sai da ta ɓace ma ganin su sannan Maigadi Baban Adila ya koma wajen aikin shi da sauri ya yin da James mai kula da tsaftan haraban gidan sannan kuma shi driver ne shi ke kai yara makaranta ko ya kaisu wajen wassani ko kuma in fita ya kama ma'aikatan gidan, Uwar ɗakin na su ba kodayaushe take yadda a tukata ba ita ke tuka kanta wani lokacin Megidan kuma ba mazauni ba ne, in ma ya dawo ba ya fita ko'ina in kuma fita ta kama shi ba na kusa ba sai dai na nesan da filin jirgi kawai ake kai shi.
Shi ya tsaya ya shiga cikin motar ya gyara parking ɗin sannan ya ciro makullin ɗin lokaci ɗaya yana fitowa ya kuma rufe motar.

Ita kuma tana shiga makeken falon gidan mai ɗauke da kayattatun kujeru saiti biyu, sallaman ma da ta yi a ciki- ciki ta yi amma ƙaran tsinin takalminta ya bayyana shigowarta falon yan aikin ta suka rugo zuwa gare ta.

Sabuwa wata yar dattajiuwa ta karɓi jakar hannunta sannan ta duƙa tana faɗin" Barka da dawowa Uwar ɗakina."
Hadiya kuma yar yarinya ce matashiya itama duƙawa ta yi tana faɗin" Barka da dawowa ranki ya daɗe."
Ma'aikatan cikin gida huɗu ne Sabuwa da Hadiya daga masaautarsu ta taho da su tun auranta da Lamiɗo aka ba ta su, sai  Anitha da Debora anan garin ta ɗauke su, Anitha ce mai kula da Sultan da Beena duk abin da ya danganci abincin da za su ci, kwanciyar su ta shin su, aikin makaranta da shirya su komai da komai dai yana sarƙe a wuyan ta ne,
Karatu na musamman ta yi
akan sanin kula da yara.
Ita kuma Debora mai kula da girkin gidan gabaɗaya cikakkiyar Chef ce da ta karanci nau'in girki a jami'a ita ce ke da alhakin kula da duka wani abinci a gidan.

Sabuwa kuma amintattaciyar hidiman Dr. Balkisu ce, duk wani abu da ya shafe ta yana wuyan Sabuwa ne, gyaran ɗakin ta gyaran kayan ta, cin abincin ta da duk wani abu da za ta bukata Sabuwa ke kula da shi, ita kuma Hidaya ita ce mai kula da share share duka gidan da tsabtace ko'ina har ɗakin mai gidan ita ke da alhakin tsabtar gidan ko'ina ya yi kal yana tashin kamshi wannan nauyin yana wuyan ta ne.

Har ta zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun falon ba ta amsa musu gaisuwar su ba. Debora ce ta ɗibo ruwa mai sanyi daga despenser a wani kofin tangaran mai kyau da tsada ta kuma ɗora shi saman wani kyakyawan faranti mai kyau ɗan caras da shi. Shi ta kawo mata bayan ta rankwafa ta miƙa mata tana faɗin" Welcome Mah."
Sai da ta yi kamar ba za ta miƙo hannu ba sannan ta mika ta karɓa ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙa mata da sauri ta tashi cikin girmamawa ta bar falon.

Da kai kawai ta amsa ma Hidaya da Anitha da ke faman gaishe ta sannan ta ɗaga musu hannu alamun su watse, ba sai ta yi magana ba zaman su da ita na tsawon shekaru uku ko sama da haka ba sai ta yi magana ba sun san abin da take nufi.
Sabuwa ce kawai ta rage a wajen itama tana jiran uwar ɗakin nata ne, sai da ta gama zamanta shuru kawai idanuwanta a lumshe tana ɗan hutaawa sannan ta miƙe da sauri Sabuwa ta rigata mikewa ta yi gaba da sauri wani korido suka shiga, Sabuwa ta buɗe wata ƙofa tana biye da ita a baya suka bayyana a wani ƙaramin falo kayattace. Nan ɗin ma ba su tsaya ba wata ƙofa Sabuwa ta sake buɗewa sai ga su a wani babban bedroom mai ɗauke da gado wanda ya ji shimfiɗun alfarma da wawaken wardrope daƙin very neat,  sannan yana tashin wani ƙamshi mai daɗi ga wani sanyi sanyi mai shiga ƙashi yana saka natsuwa da jin daɗi.
komai dai na cikin muhallinsa tana shigowa a gefen gado ta zauna lokaci ɗaya tana warware mayafin da ta yane kanta da shi, ita kuma Sabuwa sai ta isa ma'ajiyar jakunkunanta ga su nan a jikin wani ɗan katako dogo sama da guda ashirin ta ajiyeta a muhallinta sannan ta koma da sauri ta duka a gabanta ta cire mata takalmin kafar nata shima ta koma ta ajiye shi a wani ɗan dirowa mai faɗi in da takalmin suke a jere resas ba adadi ga su nan kala kala iya kallon ka har ka ɓace ƙirgawa.

Sai da Sabuwa ta kwashe komai da Balkisu ta watsar a saman gadon mayafinta da jaket ɗinta tare da glass ɗin ido ta shiga clotheset ta mayar mata a jikin hanger sannan ta rankwafa tana faɗin" A fito lafiya Uwarɗakin"
Ta faɗa cikin ladabi da kai ta ɗan amsa mata lokaci ɗaya tana ɗan mikar da kafafunta a saman tattausan cafet ɗin da ke malale a kasan Bedroom ɗin. Alamun gajiya a tare da ita har Sabuwa ta buɗe kofa za ta fice Balkisu ta kira sunanta a hankali.

"Sabuwa."

Da sauri ta juyo ta dawo da gudu ta duka a gabanta tana faɗin" Uwar ɗakina"
Ta faɗa cikin ladabi da ƙaskantar da kai kallonta ta yi na wani lokaci idanuwanta manya suna mai lumshewa suna buɗewa cikin sanyin murya ta ce" Bai fito ba?
Ta faɗa tana ɗan sauke kallon ta akan Sabuwa.
"Bai fito ba, tunda kika fita bai fito ba Uwarɗakina."
Sabuwa ta faɗa cikin ladabi, Balkisu ba ta bukatar ta yi magana ko hannu ta nuna sun san abin da take nufi
Ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta ce" Na sallame ki Sabuwa zan huta"
Ta faɗa cikin sanyin murya kasa ƙasa kamar ba ta son yin magana

"To to a huta lafiya Uwar ɗakina."

Tana gama faɗin haka ta miƙe da sauri ta fice lokaci ɗaya tana rufo ƙofar saboda Uwar ɗakin nata ba ta son sauti ko ƙara ko hayaniya hatta ƴa'ƴanta sun san yanayin gidan duk da suke yara suna da natsuwa sai gidan ya yini tsit ba ka cin motsin kowa, kowa na bangaren shi yana gudanar da rayuwarsa suma ɗin ma'aikatan gidan suna shashen su luf, sanin masu gidan duka ba sa son hayaniya sun fi son su ji ko'ina shuru.

Bayan fitan Sabuwa ta daɗe zaune tana ɗan daidaita jikinta kafin ta miƙe tiolet ta shige  bayan mintina goma sai ga ta ta fito sanye da rigan wanka fara sama sama ta ɗan shafa lotion a saman fatarta wacce ke wani irin shining ds glowing na jin daɗi da hutu clotheset ɗin ta buɗe ta shiga ba daɗewa sai ga shi ta sake fitowa sanye da wani riga da wando pick, wando dogo ne ya na da ɗan faɗi ta kasa rigar ma haka ba ta kama ta ba amma kayan suna da laushi da ɗan shara shara tunda har ana iya ganin farin pant ɗin jikinta da brazeya ɗin da ta sanya. Gashin kanta a tsife yake yi ba ta da wani suma amma saboda yana shan gyara yana nan mai kyau da shi, ta ɗaure shi da band sannan ta saka wata hula pick tsakiya a buɗe daga saman ne an yi tuntu na kwalliya mai zanen heart. Ta manta da wayarta a jikin jakar da ta shigo da shi sai ta isa wajen kafafunta na lumshewa a cikin lausasan cafet ɗin da ke Bedroom ɗin mai buzu buzu, ta isa wajen jakar ta ɗauko a hankali ta ciro wayarta ƙiran Iphone 16, sannan ta sauke jakar a in da ta ɗauke ta.

Kan makeken gadon da ke bedroom ɗin ta kwanta sannan ja jawo farin bargo mai laushi ta rufe kafafunta, ta ɗan duba wayar na wani lokaci kafin ta sauke ta a gefenta ta juya ta sake juyawa sannan idanuwanta suka fara lumshewa a hankali a hankali kafin barci mai nauyi ya ɗauke ta na gajiya domin tun safe yau take asibiti tana ganin patients.

***

Ƙarfe 3:45pm Balkisu ta tashi daga barci, har an fara kiran salla a wasu masallatan dake kusa da su har da ma waɗanda ke nesa. Duk nauyin barcinta lokacin salla na yi kamar tana ji a jikinta za ta tashi. Shi ya sa in za a tambaye ta a zamanta da Lamiɗo na shekaru shidda wani hali mai kyau ta koya daga gare shi za ta ce tsaida salla a kan lokacin ta. Tunda take da Lamiɗo ba ta taɓa ganin lokacin salla ya wuce sa da gangan ba. Mutum ne mai kiyayewan lukatan salla duk abin da yake yi koma mene ne salla na gaba da komai, ta taɓa tambayan shi ya ya yake yi in lokacin salla ya shiga kuma sai aka yi rashin sa'a yana tuki a lokacin? sai ya ba ta amsa da cewa in ya zo bakin gaba zai tsaya ba zai cigaba da tafiya ba sai ya yi salla, ko ya san wannan ka'idar shi ne in dai a lokacin tukinsa ne.

Tun ba ta saba ba har itama yanzu daɓi'an ya zame mata jiki, tana kokarin kiyayewa lukatan salla. Yanzu ma mika ta yi sannan ta sauko da fararen kafafunta daga saman gado lokaci ɗaya tana mikewa. Tiolet ta shiga ta dauro alwala sannan ta fito ta daidaici gabas ta shimfiɗa darduma babba a ɗan koridon cikin bedroom ɗin nata, ta ɗauki dogon hijabin da take salla da shi a goge a saman side drower ɗin gadon. bayan ta idar da sallar ta ɗan ɓata lokaci tana kirga yatsun hannunta kafin ta shafa adduar'ta a fuskarta lokaci ɗaya tana mikewa ta ninke darduman da hijabin jikinta ta mayar da su ma'ajiyar su. Wayarta ta ɗauka ta sake duba lokaci.
Huɗu har da mintina goma,
wani takalmi ta saka mai taushi na zaman cikin gida sannan ta buɗe kofar bedroom ta fita ba ta zauna a falon bangarenta ba sai ta fita can main falo in da ta iske Debora na faman kwashe lunch ɗin da ta dafa tun ɗazu amma daga matar gidan har Maigidan da ya dawo jiya ba su sauko ba, kuma a ƙa'ida ba za su ci ba sai dai a kwashe a sake jera Dinner wanda aka sake dafawa.

Cikin ladabi Debora ta rankwafa tana yi ma Balkisu barka da fitowa cikin harshen turanci.
Ba ta amsa ba sai da ta zauna saman kujera mai zaman mutum biyu.
Sannan ta ɗaga mata hannu.
Wayarta ta ɗauko tana ɗan dubawa ita kuma Debora ta gama kwashe komai zuwa katon kitchen din da ke can yamma da falon sannan ta dawo ta duka gaban Balkisu tana tambayanta ko akwai abin da take so cikin harshen turanci, domin gidan ba a cika yin hausa ba, matar gidan turanci take yi haka ma yaranta. In har ta yi hausa sai dai in za ta yi magana da Sabuwa ko Hidaya su da suke yan kauye ba arabi babu boko.
Amma kaf ma'aikatan gidan masu ilimi ne, kamar yadda ma mallaka gidan suke da tarin ilimi da nasaba.

"Coffea."

Haka ta faɗa kamar bakinta na ciwo, in da sabo sun saba da yanayin ta. Gidan nan kamar wata masarauta ce ta yan boko domin sarauta da ji da kai tare da takama da ƙasaita masu gidan sun iya shi, to yar Sarki ce fa jinin sarauta a jininta yake yi, maigidan ma jinin sarauta ne, kamar ma ya fi matar gidan ji da sarauta komai na shi na dabam ne.
Da sauri Debora ta koma kitchen ta haɗo mata coffea a cikin wani karamin jug mai kyau sannan ta ɗauko wani karamin faranti fari ta ɗora akai sannan ta kawo mata ta kuma jawo mata ƙaramin table din tangaran ɗin da ke falon ta ɗora komai a kai sannan ta duka ta zuba mata ta zuba kaɗan ta ji Balkisu ta ce

" Is ok."
A hankali.

'Yes Mah."
Debora ta faɗa lokaci ɗaya tana mika mata, sai da ta yi sama da sakwan goma sannan ta miƙa dogon hannunta ta karɓa ta rike a hannunta amma hankalinta na wajen wayarta sannan duka kafafunta suna miƙe a saman kujeran da take zaune ne.

Har Debora ta kwashe komai ta koma kitchen mug ɗin na hannun Balkisu ba ta fara sha ba sai can sama da minti uku sannan ta iya kai shi bakinta ta ɗan kurba sau ɗaya ta mayar da shi saman ɗan teburin gabanta ta ajiye ta cigaba da duba wayarta.

Gidan ya yi wani irin shuru sai wucewar iskar A.C ko tibi ba a kunnawa a gidan yara ne kuma suna da shi a ɗakin su, suma ba sosai suke kallon ba in ma za su yi volume kaɗan ne ko na falo ba mai jiyowa, Balkisu ba ta son hayaniya shi ya sa duk abin da zai saka ta ta ji ta takura ba ta yin shi, to ita data ke ma kwana a gidan koda yaushe kenan ba maigidan da sai ya yi wattani biyu uku ba shi a gidan ba.

Ta yi zaman sama da awa ɗaya a falon nan bayan Debora ba wanda ya sake giftaawa. Sau uku ta kurɓi coffea ɗin da aka kawo mata daga nan ba ta ƙara ba.
Agogon wayarta ta duba biyar da mintina an kusa tashin su Sultan daga makaranta.

Dan ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko da ƙafafunta ta sauke su a saman wani cafet mai taushi da kyau a ido. James ba ya bukatar sai an tunasar da shi lokacin tashin su Sultan ya fi kowa sani tunda alhalin kai su da ɗauko su yana wuyansa ne, tana zaune ta ji an buɗe get an fita daga gidan ka'ida ne da wuri yake zuwa yana bakin makaranta yana jiran su za a tashe su sannan ya ɗaukosu su dawo gida.

Karfe ,5:30pm na yamma ake tashin su kuma tun 7am suke tafiya makaranta tana haɗe da boko da islama ne mai suna AL.TASLEEM ISLAMIC SCHOOL.
Suna karatu tun daga saturday har Wednesday. Thurday ne da Friday ba sa karatu.

Miƙewa tsaye ta yi ɗauke da wayarta a hannunta sannan ta fara takawa cikin wani irin taku na ɗaya bayan ɗaya kamar ba za ta taka ƙasa ba, lokaci ɗaya ƙafafunta dake sanye cikin tattausan takalmi suna nitsewa cikin lallausan cafet ɗin daya malale falon gabaɗaya wata kofa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login