Follow us on social media

Showing 21001 words to 24000 words out of 147042 words

Chapter 8 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

jininta O Negative. Na sauran kuma duk AB Negative ne.

Suna cikin mota a hanyar komawar su gida, kamar Habib zai ta shi sama. Ummu ta kasa yi masa mganar siyan mgani ganin fuskar shi tumu tumu ba annuri daga gani ba ya cikin natsuwarsa. A ƙofar get ɗin su ya sauke ta bai shiga ba tana kuma sauka bai ce mata komai ba ya fizgi mota a guje ya wuce ba domin ta yi saurin matsawa ba da ya take mata ƙafa.
Har ya ɓace ma ganinta bakin ta bai rufu ba saboda mamaki.

"Me ya samu Noori kuma?

Ta faɗa a fili saboda tunda suka yi aure bata taɓaa ganin shi cikin firgici da zafi haka ba.
Jiki a sanyaye ta shiga compound ɗin su har ta buɗe ɗakin ta shiga jikinta bai dawo daidai ba, mamakin yanayin yadda Habib ya yi mata yafi ba ta mamaki ta ɗauka cikin tattali da murna zai dawo da ita gida amma sai ta ga akasin abin da ta yi tunani, sai dai ta yi masa uziri da cewa watakila wani abu ne ke damun shi.
Takardan cikin ta ɗauko duk da ba gane yaren na likitoci take yi ba amma kallo kawai na saka ta farinciki, tana shafa cikinta tana jin murna da farinciki nan da watanni takwas za ta zama uwa.

****

Habib tun da ya fizgi motar nan a guje bai ci burki a ko'ina ba sai da ya isa haraban bankin su, a parking space ya faka motar shi amma bai fito ba kansa ya dafe da hannu biyu yana jujjuyawa.
Kafin lokaci ɗaya ya zaro wayarsa cikin aljihun wandon sa ya lalubo wata lamba da ya yi ma saving da M.S.
wajen saƙo ya shiga ya fara rubuta mai lambar saƙo.

"An sake samun matsala Ummu-Salma ma da ciki a karo na biyu."

Ya tura da mintina huɗu yana zaman jira riƙe da waya a hannun shi sannan mai lambar ya dawo masa da amsa.

"Again kuma? Habib wasa da hankalina kake yi? Da man ai ka san za ta iya samun ciki tun da mahaifarta lafiya lau. Sai da na ce ka yi mata planning ko a ɓoye ne amma ka ƙi amincewa. To na rantse da Allah ba zan amince ba, in farko ya zama kuskure wannan ganganci ne."

Jikinsa na rawa ya sake rubutawa ya tura.

"Ki yi haƙuri ki bar wannan mganar yanzu dai mene ne mafita?

Yana turawa da mintina biyu aka dawo masa da amsa.

"Ka fi ni sanin mafita. Ni dai ina so ka sani bayan ni babu wata macen  da ta isa ta haihu da kai Habib. Ni ce uwar ƴa'yan ka nan duniya. Ka tuna da hakan"

Sai da ya share zufa duk da A.C ɗin dake cikin motar, daga ganin shi yana cikin tashin hankali.

Yana shirin sake rubuta wani sakon ne wani ya sake shigowa.

"Ka tuna da alƙawarin mu shekara ɗaya ka ce na baka za ka cire Ummu Salma daga rayuwarka na har abada. Yanzu kuna da wattani takwas da aure. Wattani huɗu suka rage maka Habib."

Sai ya dakata yana mai kallon saƙon zuciyarsa na bugawa da gudu fat! fat.
Ajiyar zuciya ya sauke a jere kafin ya ba da amsa.

"Ina sane da komai. Zan kuma ɗau matakin da ya dace."

Yana gama turawa, ya rufe wayar ya mai da ta cikin aljihun wandon shi, sai da ya ɗan natsa sannan ya ɗauki brief case ɗin sa ya fito daga motar bayan ya kulleta cikin Sassarfa ya nufi katafaren ginin ma'aikatan su na First bank.



*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/BxcTrVcz7GoIDzbqZTpIxF?mode=gi_t



*04*

*9:43pm*

Har zuwa lokacin Habib bai dawo ba, Ummu ta kira shi sau uku bai ɗaga wayarta ba daga karshe ma sai ta ji ta daina samun shi kwata-kwata.
Zaune take a falo saman ɗaya daga cikin kujerun da suka yi ma falon ƙwanya, tun ɗazu ta gama girki ta yi wanka tana jiran dawowar Habib amma har zuwa wannan lokacin bai shigo ba, kuma bai saba yin dare a waje ba sai da dalili mai karfi.

Tunaninta da hasashenta bai taɓa kawo mata matsalan daga ita ba ne, tagumi ta yi ta ƙura ma talabijin ido a tashar tauraruwa an saka wakar Salin smart na Labarina. Amma hankalinta da nazarin ta ba ya wajen, idanuwanta na juyawa akan allon talabijin ɗin amma tunanin ta da dukkan zuciyarta yana kan Habib.

"Me aka yi masa?

Ta tambayi kanta sau shurun masaki a cikin zuciyarta ko daga ɗazu bayan dawowarsu daga asibiti ta yi ma Habib wani laifi ne? Ya iya hangen ta da tunanin ba ta hango wani laifin da ta yi masa ba, fuskar sa da ayyukansa sun sauya ne daga lokacin da ya samu tabbacin tana da shigar ciki, daga lokacin Habib ya sauya sauyawar da ta kasa gano dalilin shi, kuma zuciyarta ta aminta da shi, shi ya sa ba ta yarda ta kintsa mata wani mugun tunani a game da shi. Ƙarfafa kanta take yi da cewa watakila wani ne ya ɓata masa rai, amma Habib sai ya fi kowa murna da samun cikinta anan duniya.

Tun da ya sauketa a bakin get ta shigo gida take nazarin abin da ya faru amma ta kasa gano bakin zaren. Ko da daddaren nan sai da ta yi Amai bayan ta yini kwanciya saboda kasalan da ta rufe ta amma ba ta biye ma yanayin jikinta ba yamma na yi ta miƙe ta yi ma Habib girki, soyayyan taliya da Nama mai kayan lambu da ya ke ana gobe su Amma za su dawo ya ɗauke ta sun je kasuwa sun yo cefane mai yawa tana da komai na buƙata kayan miya ta ñika shi ta tafasa shi yana cikin Frezer ɗiɓa kawai take yi in ta tashi amfani da shi.

Wayarta ta sake jawowa yanzu kam har goma ta wuce amma babu alamun Habib, tunanin ta ya sake karkata kan ko dai yana fushi da ita ne ya ɗauka ta san tana da ciki ba ta faɗa masa ba? Tuna haka ya sa ta yi mirmishi ita kaɗai ta san ma saboda haka ne ya ke fushi yaƙi dawowa gida da wuri, in ya dawo za ta bashi haƙuri in dai Habib ne ba ya  iya dogon fushi a kanta saboda yadda yake tsananin sonta da gudun duk wani abu da zai ɓata mata rai.

Gajiya ta yi ta zaman shuru sai ta yi tunanin bari ta kira Bestie sai dai wayar na ta ringing ba ta ɗaga ba, sai ta ma yar da akalan kiran ga Baɗɗo ita dai ta ɗauka sun yi mgana ga shi tana so ta sanar da ita tana da ciki amma kamar an matse bakinta ta kasa faɗa mata, ba su daɗe suna waya ba saboda ta ce mata tana karatu sun fara jarabawa a satin nan da ya shiga. Ta tambayi Habib sai Ummu ta yi mata ƙaryan ya biya ta gidan su bai riga ya ƙariso ba.

"Allah ya ba ki sa'a da nasara SisNa."

Ummu ta faɗa cikin mirmishi lokaci ɗaya tana shafa cikinta. Domin in ta tuna nan da wattani takwas ita ɗin uwa ce kuma mai uba irin Habib sai ta ji kamar ba macen da ta kai ta farinciki anan duniya.

Daga can bangaren Baɗɗo ta amsa ma ta da Amin,  sannan suka yi sallama bayan Ummu ta ce a gaishe mata da Ummin ikki.

Bayan sun gama wayar Data ta buɗe ta shiga tiktok tana kallon girke-girke akan account ɗin Maryama Kitchen. Duk yadda ta ke son abin da ya shafi girki, in tana kallo ma wani nishaɗi take ji amma yau kwata-kwata ba wannan nishaɗin sai ta ji ma komai ya fita daga kanta kawai sai ta kashe datan, saboda kar ta zauna shuru ya sa ta fara duba contact ɗin ta. Lambobin da ba su da amfani take bi tana faman gogewa domin wasu lambobin ma sai su shekara ba su yi waya ba. Wasu ma duk sun daina amfani da layukan.

Lokacin da ta iso jerin sunayen Yayyenta da ko wanne ta yi masa saving da Hamma sannan da sunan mutum a gaba. Tsayawa ta yi tana kallo Hamma Mustapha ne suka ɗan jima ba su yi mgana ba. Kuma yana da ƙoƙarin kiranta lokaci bayan lokaci, ba za ta iya tuna last da suka yi waya da shi ba. Ita kuma ta sha'afa ganin bai kira ta ba, kuma ita ba ta kira shi ta gaishe shi. An ce ka gaida mai gaishe ka duk cikin yayyenta ta fi son Hamma Mustapha yana da sauƙin kai da sanyin hali ga haƙuri da kawaici hallayan Baffa kaɗan ne bai deɓo ba.

  Yana da son ƴan'uwan shi sosai, saɓanin irin su Hamma Kabiru da bashi da kula kwata-kwata, duk a cikin su Hamma Mustpaha ne da Hamma Jibo suke ji da ita, to sai gwara ma Hamma Abdulrrahaman, shi Hamma Abdullahi in ya gan ka dai zai yi murnan ganin ka amma don bai gan ka baa zai damu da neman ka ba. Kar su Hamma Kabiru su ji labari, shi a motor ɗin shi cewa yake yi in ka ji shuru lafiya ne. Baya neman mutane in kuma ya gan ka ba zai yi murna ba in ma bai gan ka ba zai damu ba kuma ba zai tambaya ba. Shi ya sa Ummu ta sha faɗin cewa suna da kamanceceniyar halayya da Hamma Lamiɗo, wataƙila saboda tare suka yi wasan ƙasa suka kuma girma tare shi ya sa wasu hallayan na su marasa kyau suke kamanceceniya da juna.

  Hamma Mustapha ta latsa ma kira, ringing ɗaya ana biyu ya danna mata busy, ta sani da man ba ya ɗaga kiranta. Shi zai kashe sannan ya kira ta. Cikin minti ɗaya sai ga shi ya biyo bayan kiran da sauri ta ɗauka cikin zumuɗi.

"Hamma ka manta da ni "

Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar za ta yi masa kuka.
Daga can bangaren ya yi dariya har tana fidda sauti.

"Wane Hamma ya manta da Autan Ammah. Kina raina ayyuka ne suka yi mini waya a kwanaki nan. Kina lafiya?

Ya faɗa daga ƙarshe yana sirka mganar shi da yaren fillanci.

Ta amsa mishi itama cikin harshen fillancin, sun gaisa cikin fara'a da tambayan iyalan shi, da ya ke shi Gombe yake aiki can ya ke zaune da iyalansa.

"Ina Adda Aisha? Ina su Mahma da Baffan mu?

Duk ya ce sun yi barci saboda makaranta gobe Adda Aisha yanzu ta bar ɗakin sa.

"Ka gaishe mini da ita sosai."

"Zan faɗa mata Autan Ammah. Ya wajen megidan na ki?

Tana shafa cikinta cikin mirmishi ta ce" Duk muna nan lafiya Hamma. Yaushe za ka zo?

Sai da ya yi tunani kafin ya ce.

"Kin san ga aiki sannan yara suna makaranta itama Aisha tana makaranta ko?

"E na sani Hamma."

"To sai mun samu hutu za mu zo mu yi ko sati ɗaya ne in sha Allahu."

Cikin murna ta ce" Allah ya kawo ku lafiya Hamma."
Ya amsa da Amin.
"Ba dai wata matsala ko?
Ya tambaya sai ta amsa mishi da babu wata matsala ya ɗauka za ta yi masa sallama ne tun da dare ya yi sai ya ga ta fara zaro wata hiran.

"Auta dare ya yi, kar ki bar megidan na ki shi kaɗai."

Sai ta kasa mgana, jiki a sanyaye suka yi sallama in ta ce Habib bai dawo ba zai saka ayar tambaya, ko ba ma haka bai kamata ta faɗa mishi wani abu ba, yau dai zumumci take jin yi wayar Hamma Jibo ta kira shi, shi dai ba ta same shi ba Adda Nauwara ta ɗauka ta ce ya shiga wanka.

"Ummu yanzu da daren nan? Ko kewar mu kike ji ne?

Nauwara ta faɗa tana dariya, sai Ummu ta rufe fuska kamar tana ganinta itama tana dariyan, yara ta tambaya itama ta ce duk sun kwanta dare ya yi, suna ta hira da Nauwara har Hamma Jibon ya fito ya karɓa shima suna gaisawa sai da ya ce.

"Autan Baffa ko akwai damuwa ne?

"Ba komai Hamma kawai na kira ka ne na gaishe ka."

"To na gode. Ki kwanta kin ga dare ya yi, da safe za mu yi waya."

Da haka shima ya sallame ta, sai bayan sun gama wayar ne ta ga Hamma Mustapha ya tura mata 10k,  duk da ya san ba ta buƙatar komai amma shi mai kyauta ne da alheri shi kafin ta yi kukan wani abu ya ba ta saƙon godiya ta tura masa da addu'an Allah ya sa ya gama da duniya lafiya.
lambar Hamma Abdulrahim ta gani shi da ya ke ba ya ƙasar sai dai in shi ya kira ka ko da yaushe wayarsa ba ta shiga. Amma suna mgana a chart sosai har Vadeo call suna yi wani lokaci in karatu ya yi musu sauƙi tana kewar shi ko bikinta bai samu zuwa ba ya fi shekara rabon shi da zuwa gida amman ya ce ya kusa kamallawa gabaɗaya shi ya sa zai jima a can kafin ya dawo gida.

Da har ta wuce lambar Hamma Kabiru, sai ta dawo bari dai ta kira shi, ko ba komai ɗan'uwanta ne kuma ba za ta biye ma halin shi ba, in ta duba ma ai akwai jininsa roba biyu a cikin jikinta. Sai ta latsa masa kira har ta katse bai ɗauka ba taɓe baki ta yi a cikin ranta ta ce ka huta.
Agogon wayarta ta sake kallo sha ɗaya har da mintina ta gota. Tagumi ta sake yi cikin bugawar zuciya sake kiran lambar Habib ta yi amma ba ta shiga ba.

Niyyarta ta kira ko ƙaninsa Maharazu acan gida ta ji ko yana gida ne tana cikin neman lambar ne kiran Hamma Kabiru ya shigo mata sai ta ɗauka.
A ginshiƙe ya yi mata sallama da muryan nan ta shi a cunkushe kamar mara lafiya ta amsa ita ta fara gaishe shi ya amsa da lafiya jin ya yi shuru itama sai ta yi shuru sai ta rasa ma abin da za ta ce masa, ba wani shaƙuwa sosai a tsakanin ta da shi ba kamar sauran yayyen nata.

"Mene ne haka, na zo na ga kiran ki ba na kusa. Na zo na gani na kira kuma kin yi shuru."

Tana so ta yi magana kamar an ɗinke mata baki ta kasa.

"Ke in ba ki da abin cewa zan kashe wayata. Kin san aikin da na katse ne na kira ki?

Ya faɗa cikin faɗa shi da man ko mganar arziƙi ce ta faɗa ce a wajen shi.

"Hamma."

Ta faɗa a sanyaye tana jin hawaye suna cika kwarmin idanuwanta.

"Me ya faru?

Ya faɗa a hankali jin muryanta ta yi sanyi alamun kamar za ta yi kuka, duk da ya san Ummu da shagwaɓan tsiya sai dai ganin dare ya yi yasa ya yi tunanin ba lafiya.

"Ki yi mgana mana."

Ya faɗa da karfi.

"Hamma."

Ta sake kiran shi a raunane lokaci ɗaya hawaye na zubo mata muryansa kawai da ta ji sai ta ji wani irin abu ya sauko mata mai kama da rauni, sai ta ke jin kamar ta yi tsuntsuwa ta ganta a gaban shi kawai shi take son gani domin ta fi wata uku ba ta saka shi a idanuwanta ba, tunda shima a Jalingo ya ke aiki can ya ke zaune da iyalansa yana zuwa amma ita tana gidan ta in dai ba hutu suka zo shi da iyalansa ba ba ta samun ganin shi.

"Lafiya wai kike ta kiran sunana kuma ƙin ki mgana."

Hawayenta ta yi saurin sharewa.

"Mijin naki ne ya yi miki wani abu?

Ya faɗa kai tsaye domin shi abin da zuciyarshi ta kitsa masa kenan.

"Aa Hamma."

"To A'a me ye? Ke ba na son fa shanshanci in ba ki da abin faɗa zan kashe waya ta ina da abun yi."

Jin abin da ya ce ne ya sa cikin yar shagwaɓa ta ce" Hamma na kira ne fa na gaishe ka "
"Ƙarya ne"
Ya faɗa kai tsaye.
"Wallahi Hamma."
"Gaisuwan ne sai da daddare za ki kira ni Ummu?

Kanta ta sosa kafin ta ce" Ni ban ma lura da dare ya yi haka ba Hamma."
Kai ya jinjina kamar tana ganin shi kafin ya ce" Ko dai ba ki da kuɗi ne? Kin talauce ne?
"Kai Hamma."
Ta faɗa tana rufe bakinta.

"To ni dai ba saba kira na ki gaishe ni kika yi ba Ummu Salma."

Ya faɗa kai tsaye saboda haka ɗin ne suna daɗewa ba su yi mgana ta waya ba.

"Ina kiran ka mana Hamma."

"Ba na son ƙarya kina dai kiran su Mustapha amma  ba ni ba. Ko da ya ke kin ce kin fi son su ni ina da mugun hali irin na Lamiɗo ko?

Ummu ta rasa in da za ta saka kanta saboda kunya da nauyi. Ashe ya ji wannan mganar? Amma abin mamaki wa ya faɗa masa?.

"Kin yi shuru ko ba haka na ji kina faɗa ma Baɗɗo ba."

Tabbas an yi haka tun kafin ta yi aure ne. Suka taɓa hiran a ɗakin Ammah ne su ba su taɓa sanin ya ji ba in ba za ta manta ba yana garin lokacin wataƙila ya zo shigowa ɗakin Ammah ne ya ji suna hiran

"Duk mugun hali na ina da kirki Ummu. Lamiɗo ma don ba ki zauna da shi ba ne he is a nice person."

Ta aminta da kirkin shi tun da shi uwa ɗaya ce ta haife su amma gwara shi akan wancan, ita dai ba ta yarda da cewa wai Hamma Lamiɗo is nice person ba.

"Ka yi haƙuri Hamma. Ba.."

Ya katse ta da sauri yana cigaba da faɗin" Hallaya ce Ummu. Wani haka Allah ya hallice shi ba ya son shiga rayuwar kowa. Kamar ni nan na fi son shuru fiye da komai, kamar Lamiɗo ya fi son rayuwa kamar yadda kika ga yana rayuwa, amma duka muna da kirki ba mugaye ba ne kamar yadda kika ɗauka ba."

Tana danne bakinta kar ta yi dariya ta ce" Na fahimta Hamma."
"So ko gobe ki daina yanke hukunci kan mutumin da zama mai tsawo bai haɗa ku ba."
Ta amsa masa da toh, suna ma cikin wayar ne ta ji ana taɓa kofa.

"Sai da Safe Hamma a gaida Adda Safina da su Yusra."

"Za su ji, da safe zan saka miki ko na kati ne domin na san dalilin kiran kenan."

Tana so ta ce ba haka ba ne sai har ya kashe wayarsa dai-dai lokacin da Habib ya shigo falon da sauri ta miƙe tana kallon shi cikin mirmishi, shi ko gogan kallo ɗaya ya yi mata bai sake ba, yana rataye da jakarsa ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login