Follow us on social media

Showing 6001 words to 9000 words out of 147042 words

Chapter 3 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

nan har Saudiya a matsayin namijin da ya ƙera sa'a ga ilmi ga martaba ga sanin ya kamata ga iya soyayya, a kalla a shekarunsa ba zai gaza talatin da biyu ba 32. Shi ya sa yana cikin jerin layin matasa masu jini a jika, ma'aikacin banki ne shi ya sa ya zama ɗan gayu na karshe da kwatance.
Habib Idris Mai imani ya kai  ya haɗu ya gaji da haɗuwa da duk macen da ta mallake shi zai zama abin alfarinta.

"Baby ki tashi mana."

Ya faɗa bayan ya yarfa mata ruwan dake gashin kansa.
Mirmshi ta yi masa shima ya mayar mata da martanin mirmishin nata.

"Tashi ki yi wanka ki ba ni abinci yunwa na ke ji Baby."

Ya sake faɗa cikin yar shagwaɓa, hannunta guda ɗaya ta mika masa lokaci ɗaya tana faɗin" Noori ka ɗaga ni."
Ta faɗa tana mele masa baki.

"Baby me ke damun ki yau? Kin gaji ne da yawa?

Ya faɗa yana rike hannunta da taimakon shi ta miƙe zaune.

"Baby are you sick?

Ya faɗa yana kallonta ganin ta lamgwaɓe kai.

"Ban sani ba Noori amma jikina ya yi weak"

Da sauri ya matso gabanta ya dafa goshinta kafin ya ce" Kuma tempereture ɗin ki is Normal."
Shagwaɓa fuska ta yi kafin ta ce" Ni ma ban san meke damuna ba Noor."
Kallonta ya yi kafin ya kashe mata ido ɗaya yana sake faɗin.
"Ko ni ne Baby?
Ture shi na yi ina faɗin" Yau ne farkon mu?
"Baby to amma ai yau na kai farmaki na da kyau ko?

Sake ture shi ta yi sannan ta miƙe ya taimaka mata yana tura ta bakin tiolet.
"Baby yunwa."
Ya sake faɗa da karfi gwiwa ta tura ƙofar toilet ɗin ta shiga tana faɗin" 5 minutes."
Ta faɗa tana mai rufe ƙofar, da kallo ya bita kafin ya yi mirmishi. Wardrope ya buɗe ya ɗauko saukaƙkun kayan barci ya saka riga mai gajeren wando falo ya fita ya sauya tasha zuwa tashar ƙwallo mintina goma tsakani Ummu Salma ta fito itama cikin rigar barci mai shara-shara wacce ba ta wuce gwiwarta ba.

Abinci ta jera bisa dinning, yana daga can a falo ta kira shi.

"Noori Dinner is ready"

Da sauri ya taso, ita ta ja masa kujeran ya zauna yana faɗin" Thank you Baby."
"You are always welcome Noori na."
Mirmishi ya yi mata lokaci ɗaya yana kashe mata ido ɗaya, kau da kai ta yi tana yar dariya.

White rice ne da miyar allayahu, sai zoɓo da tea, tare suka ci abinci suna yi suna hiran su ta masoya.
Bayan sum gama suka shiga tiolet suka wanke bakin su, Ummu-Salma ta kwashe abin da suka ɓata zuwa kitchen sannan ta koma falo wajen Habib da ya rage hasken falon ta naɗe a jikin shi, suna kallo suna hira suna kuma soyayyar su.

****

Duk da yanayin Ummu-Salma da Habib ya gani bai saka ya ɗaga mata kafa ba, kafin su kwanta sai da ya maimaita. Can cikin dare ma sai da ya tashe ta tana so ta ce ya ƙyaleta ba ta jin daɗin jikinta amma ta kasa, yana dawowa daga sallar asuba ma sai da ya yi duk yadda ya ga jikin Ummu-Salma ya yi laushi a cewarsa jarumatarsa ce ta ƙaru, shi ya sa ta makara sai wajen bakwai saura ta iya ƙarfin halin tashi ta shiga kitchen, da ya ke girki Hobby ɗin ta ne garin fulawa ta iya sarrafa wa, cikin lokaci ta kwaɓa fulawa ta sarrafa shi zuwa Naan Bread.
Tun da tana da kayan lambu, nama ne babu sai ta yi amfani da ƙwai.

Ko kafin takwas ta yi ta jera komai a saman dinning. Ta koma bedroom ta tashi ta Habib ta taimaka masa ya yi wanka, ya tsuke cikin suit masu ruwan  baƙi da ruwan toka. Tare suka zauna zaman ƙaryawan Naan bread ɗin suke ci haɗe da tea Habib na gutsira yana yi mata santi.

"Baby ina son wannan abin. Ya ma sunan shi?

Tana dariya ta ce" Naan Bread Noori, amma wannan mai ƙwai ne ba nama ba."

Sai ya jinjina kai kafin ya ce" A online clases ɗin ku aka koya miki?
Bayansa ta dafa kafin ta ce" Noori na santi."
Sai da ya kurɓi tea kafin ya ce" Ba santi ba ne, Allah Baby yana da daɗi, in dai kika yi shi ai ina cewa yana da daɗi ko?

"Yes My Noori."

Hira suke yi, jefi-jefi ita tea ɗin ma kawai ta ke kurɓa saboda zuciyarta ta ji tana tashi tun da safe, shi ya sa ma ba ta ci ba naan bread ɗin ba.

Habib wayarsa ce a hannunsa yana ta dubawa. Lokaci ɗaya kuma yana cin abinci.

"Baby."

"Naam"

"Ashe kuna da biki ban sani ba?

Sai ta kalle shi cikin mamaki.

"Noori Biki kuma?

"Yes"

Ya faɗa yana karkata mata wayar ta leƙo da kanta sai ta yi arba da zafafan hotunan Badia'tu yar sarkin Daura.

"Ba bikin gidanku ba ne?

Ya faɗa  yana sake tura abin da ke hannunsa a baki lokaci ɗaya yana korawa da ruwan tea.

"Oh ai fa."

Ummu-Salma ta faɗa tana kauda kanta.

"Ammah za ta je?

"Za ta je mana. Kai ma ka sani"

"Mami fa? Itama za ta je?

Sai ta kalle shi kafin ta ce.

"Kai ma ka san Mami ba za ta je ba."

Sai ya jinjina kai yana cigaba da kallon wayarsa kafin ya ce" Baby da kin tambayeni da na bar ki, kin raka Ammah dagaa ganin bikin nan za a sha shagali."

"Uhm"

Ta faɗa ba tare da ta sake mgana ba.

Dariya Habib ya yi kafin ya ce" Am just joking. In kika tafi ni kuma ya za ki yi da ni?
Hararan shi ta yi, yana sake yin wata dariyan ya ce.

"I love you Baby."

Juya masa ido ta yi sannan ta yi masa fari, jinjina kai ya yi kafin ya ce" Ki bari kafin na ce mu shiga daga ciki."
Tana jin haka ta yi saurin gyara zama tana faɗin.

"Za ka makara fa Noori?.

"Ina sane da time fa Baby."

Sai ta jinjina kai, ba ta yi mgana saboda cikinta ne ta ji yana juya mata.

"Baby."

"Noori."

Sai da ya kalleta kafin ya ce.

"Hamma Lamiɗon to zai je can Daura ɗin ne?

"Ban sani ba Noori."

"Serous fa?

"Allah fa ban sani ba."

Ta faɗa tana mai kallon shi.

"Ko Ammah ba ta faɗa miki ba.?

"Ba ta faɗa mini ba Noori."

Ta faɗa cikin gajiya da tambayoyin.

"Noori yau kuma Hamma Lamiɗon kake son gani?

Ta  faɗa tana kallon shi mirmishi ya yi kafin ya ce" Ba laifi ba ne, kin manta sau ɗaya na taɓa ganin shi, shima daga nesa kafin na karisa ya shige cikin mota."

Baki ta taɓe kafin ta ce.

"Uhm"

"Baby ke dai kawai ki ce jininku bai haɗu ba, kuma saboda kin ƙi karatu ne "

Wani kallo ta yi masa da ya sa ya fara dariya kafin ya ce.
"Baby gaskiya na faɗa, nima fa ta shafe ni kamar baya sona saboda ke."

Kai Ummu-Salma ta girgiza kafin ta ce" Shi wannan yana neman dalilin tsanar mutum ne? in dai haka ne kowa ya tsana kenan."

"Me ya sa kika ce haka?

"To ban da Ammah wa ke ganin dariyan mutumin nan! Ko Baffa a ginshiƙe yake masa mgana. To bari ka ji ko su Hamma Jibril a takamance yake yi musu mgana, ballanta irin mu ƙananun ƙwari."

Habib ya kwashe da dariya ganin yadda matar tashi ta haɗe rai, tissue ya ɗauka yana goge bakin shi kafin ya ce.

"Kuma Ammah tafi son shi da ke ba Baby."

"Ta fi son shi da kowa ma Noori. Ni ai na bar masa ita na kama Mami na da Umman ikki."

Ta faɗa tana juya masa baki, miƙewa ya yi yana faɗin" Baby is time."
Itama sai ta mike, bedroom ta koma ta ɗauko masa briefcase ɗin sa ta dawo falon suka rumgume juna sai da ya sumbaci bakin ta kafin ya ce.

"Baby take care kin ji ko."

"In sha Allahu"

Ya hana ta masa rakiya a haraba shi ya sa iyakarta kofar falo ya fita tana ɗaga masa hannu har ta za ta rufe ƙofar sai ga shi ya dawo da sauri yana faɗin.

"Baby key ɗin mota ko a kafa kike son na je wajen aikin yau?

Sai ta juya da sarssarfa ta koma ciki ta ɗauko masa, bayan ta kawo masa sai da ya sumbaci hannun sannan ya wuce yana faɗin

"I love you Baby."

"Love you too Noori na."

Hannu ya ɗaga mata, itama ta daga masa sannan ta rufe ƙofar. Dinning ɗin ta koma ta zauna domin ba ta ƙoshi ba sauran Naan bread ɗin da Habib ya rage ta ɗauka ta ci guda ɗaya ta hada da ruwan tea, Allah ne ya sota da ta yi amai saboda zuciyarta ta yi ta tashi sai da ta sha ruwa sai ta ji zuciyarta ta kwanta

Tunani take yi ko dai ciki gare ta? Sai ta fara tunanin yaushen da rabon da ta ga al'adanta? Tun bayan ɗaukewar jinin nan na ɓarin da ta yi ba ta sake wani jini ba, tsalle ta buga ita kaɗai a falo da gudu ta ruga ɗaki ta dauko wayarta Habib ta so kira sai kuma ta fasa kar ta ɗaga masa hankali.
Sai ta mai da alkalan kiran ga Sisna amma ba ta ɗauki wayar ba wata kila ta shiga cikin makaranta ne
Sai ta bar mata saƙo.

"Albishirin ki. Ina tunanin ina da wani cikin SisNa."

Ita kaɗai a gaban madubi tana shafa cikinta tana kallo, farincikinta ya kasa ɓoyuwa wani irin murna Habib zai yi in ya san tana da ciki? Ba ta da tabbaci amma alamominta na kwana biyun nan ya fi kama da na masu juna biyu, sai a lokacin ta kula da nonuwanta sun tasa, kuma da man cikinta na farko kafin ta yi ɓarin shi a Nono ya fara nuna kansa kenan wannan ma anan zai fara bayyana kan shi?

Wata zuciyar na faɗa mata kar ta faɗa ma Habib sai ta je asibiti an tabbatar mata sannan sai ta faɗa masa cikin mamakin da tasan murnan da zai yi ba ƙarama ba ce, saboda lokacin da ta yi ɓari ya shiga damuwa sosai har ta dinga mamakin haka yake son haihuwa? Ko da yake in ta yi duba da gidan da ya fito gidan yawa ne shi ya sa zai so shima ya tara yara kamar mahaifinsa.

*littafin Fargar Jaji na kuɗi ne a manhajar Telegram akan #1k. Tura Kuɗin karatun ku ta wannan acct ɗin 9069067488 JAMILA UMAR OPAY sannan sai ku tura shaidar biya ta waɗannan lambobin kamar haka.*

09069067488.
08032773332.

*Yan kasuwa masu buƙatar a tallata muku hajojinku a cikin wannan kayattacen labarin za ku iya tuntuɓata kai tsaye ta wannan lambar 09069067488 Na gode.*

*Janafty*
*Sat, 05. June 2025.*
5:53pm.
*Posting on 17/04/2026*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*


To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

https://chat.whatsapp.com/IF0uPZWtcCOIczsjhdCbIZ?mode=gi_t


https://www.arewapen.com/u/jamilaumarjanafty

*02*
_JIMETA: Zone 3_
*10:30pm.*

Alhaji Hadi Baba na zaune a gefen gadon dake cikin turakan shi, wasu takardu ne a hannun shi yake dubawa sanye yake da jallabiya mai ruwan madara, kansa da tsilintsilin furfura wani siririn farin gilashin ne a idanuwansa wanda in zai karanta wani abu yake amfani da shi saboda raunin ganin sa.

Sallaman matarsa ne ya katse masa nazarin takardun dake hannunsa, ya ɗago kansa lokaci ɗaya yana mai amsa mata cikakkiyar sallaman kamar yadda ta yi.

Dattijo ne mai cikar kamala da haiba, fari ne amma ba shi da haske sosai wataƙila ya yi sirki shekarunsa na haihuwa za su kai 66 amma hutu da jin daɗi sun saka fatarsa da yanayin jikinsa suna ƙaryata shekarunsa
mai ɗakin sa yake kallo dai-dai lokacin da ta ƙariso gaban shi.

"Baffa ba ka kwanta ba?

Ta faɗa da muryanta da ta cakuɗe irin na fulani lokaci ɗaya kuma tana nufar can ƙurar ɗakin in da ta ijiye mganin sauron da ta kunno a hannunta a saman wata kwalba lokaci ɗaya tana sake faɗin" Na manta yau ban yi maka feshin magani ba Baffa."

"Sannu da ƙoƙari. Na gode."

Ya faɗa da cikin harshen fillanci, dawowa ta yi zuwa gefen shi ta zauna tana kallon shi, itama ita ya kalla amma bai yi mgana ba sai ta fara dariya tana faɗin" Baffa me kuma na yi ni Jamila?
Kai ya girgiza kafin ya ce" Ba ki yi komai ba."
Agogon da ke sama ta ɗaga kai tana kallo sha ɗaya saura daga nan ta gano laifinta.

"Baffa ka san ina da tafiya a gaba na ina can ina ta ƴ'an kimtse-kimtse ne "

Ta sake faɗa tana yi masa mirmishi, takardun hannun shi ya adana a cikin dirowan gefen sa, sannan ya mai da hankalin shi a kanta, ba ta damu da jiran amsar shi ba har ta miƙe, farantin kwanukan abincin da ta kawo masa tun bayan dawowarsa ta sumguma tana faɗin" Bari na kai wannan kitchen na dawo Baffa."
Daga haka ta sake ficewa shi dai kawai ya bita da kallo yana mai girgiza kai, lokaci ɗaya yana sakin mirmishi.

Mintina huɗu sai ga ta ta sake shigowa da sallama wannan karon har sai da ta tura ƙofar daƙin lokaci ɗaya tana cewa" Baffa ko za ka sake fita ne?
Sai da ya amsa mata da kai kafin ya amsa mata da baki.

"A'a"

Ta fara tahowa zuwa gare shi, shi kuma yana kallonta, Jamila (Ammah) ko da shekaru suka tura kyanta da dirin ta bai samu wani tawaya ba, ko yanzu da yake kallonta yana ganin kyawunta na shekaru sama da talatin da auran su, ita ce dai Jamilar da ya aura yarinya yar shekaru sha shidda a lokacin, ita ce wacce Gwaggo ta yi masa auran gata da ita(Allah ya gafarta mata) ita ce kuma a yau uwar zaratan maza ginannu har guda bakwai, uwa kuma ga Muhammad Lamiɗo, kuma uwar Auta Ummu-Salma, har yau hasken fatarta ba ta dishe ba, da ya ke fara ce sosai mahaifiyarta kafin rasuwarta Nenne tsada ake kiranta saboda tsabar jan ta, sannnan kaf ya'yan su jan fatan ta suka ɗauko a kammani ma ta rinjaye shi, duk da mutane da dama sun sha cewa shi da Jamila suna ɗiban kama, tun da su ɗin jini ɗaya ne, wani lokacin Amma ba uwa ce kaɗai a wajen ƴa'ƴan shi ba hatta shi kan shi uwa ce gare shi, in ta rufe shi da faɗa kamar Gwaggo, shi ya sa ya sha cewa Ammah mata ce, ƙawa ce Aminiya ce sannan uwa ce a gare shi da ƴa'ƴan su gabaɗaya. Da yake kuma ya aure ta da ƙananun shekarun a wancan lokaci yanzu ma take cikin shekarunta na hamsin da shidda, babban yaron su Jibo ya zo duniya tana da shekaru goma sha bakwai, sau tari in suka jera da Jibril kamar ƙaninta yake ba ɗanta ba, yadda tserensu yake kamar a jere da juna. Sannan ta mori jikinta ba da ta kiba kuma ba ta da tsawo, gajera ce tsawon da yaran suke ɗaukowa tsawon uban su ne shi Alhaji Hadi Baaba.

Sai da ta zauna kusa da shi sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Ya juyo yana kallonta ita kuma sai ta saka hannu ta zare masa gilashin fuskar shi lokaci ɗaya tana faɗin" Baffa a cire gilashin hakan nan, ko nima sai da shi kake iya ganina tarwai?
Dariya ya yi har sai da haƙoran shi suka bayyana a waje.

"Ahto Baffa ba amana a ce ba ka gane ni sai ka sanya gilashin ƙara karfin gani."

"Ammah ba ki da dama."

Ya faɗa da sautin muryan shi ya saba da kiranta Ammah kamar yadda yaran su, suke kiran ta ba ma shi ba kowa yanzu Ammah ne yara da manya. Shi kuma da man ita ce take ce masa Baffa kafin yaran su su tashi da sunan a bakinta.

Akwai wata rana da ya shuɗe Saddam na zolayanta da cewa.
"Amma wai kema Baffa Baffan ki ne?
Dakuwa ta yi masa kafin ta ce. "A'a naka ne mai uba, to ni ce mai Baffan gabaɗaya ku duk yan cikon banci ne."
Suna falo ne suna karyawa a wata safiya shi kan shi sai da ya yi dariya da kalamanta
Ammah ce, ba ta da dama mace ce mai jajircewa kan mijinta da ƴa'ƴanta mai son zumunci da yaƙana ce, amma kuma ba ta da haƙuri Amma mace ce da ba ta ɗaukan Nonsense  tana da faɗa da zafi, zafin namanta har a jikinta da kazar-kazar ita ce mata ɗaya cal da Alhaji Hadi Baba ya mallaka a matsayin mata anan duniya amma ko yanzu da shekaru suka tura ba ta taɓa jin ta gaza daga hidimta masa ba.

Yanzu ɗin ma cewa ta yi ya kwantar da kansa saman filo, ta jawo kafafunsa a saman cinyarta tana matsa masa a hankali cikin kulawa tana faɗin.
" Baffa ya kamata ka huta. Kwana biyun nan ba ka samun zama sosai."
Sai da ya dan muskuta kafin ya ce" In na zauna gida na huta sauran harkokin nawa wa zai yi mini?

"Ka bar ma Baba"

"Ban da abin ki ai ko a yanzu shi ke yin harkokin, shima abin a tausaya masa ne ba ya cikakken sati tare da iyalansa."

Amma ta jinjina kai kafin ta ce" To shi yanzu jininsa yake Baffa kai kuma jiya ba yau ba, ni dai ka dinga hutawa kar wata rana aga tsoho na ya faɗi."
Ta ƙarishe faɗa tana masa dariya da man in tana jin nishaɗi ɗan tsohona take kiran shi, kai ya jinjina kafin ya ce.
"Tun da haka kike bukata ai haka za a yi uwar Lamiɗo "
Ta sake faɗaɗa mirmishinta ba ta dai ce komai ba tana cigaba da matsa masa kafafuwansa.

Idanuwan Baffa na lumshewa domin akwai gajiya a jikinsa Ammah dai sai dai Allah ya yi mata albarka ta san shi fiye da yadda shi ya karance ta. Mubi ya je shi da Abdullahi duk da ba shi ya yi driving ba doguwar tafiya yanzu na bashi wahala ko don shekaru sun tura ne? Shi da a shekaran baya a jihohin Nageria ba in da kafarsa ba ta ka da sunan kasuwanci ba. Kasuwanci ma irin na shi na siyan injinan manyan motoci ƙananu da manya da kuma wasu part-part na jikin mota ya daɗe yana wannan harkan kafin daga baya ya fara sirkawa da harkokin siyar da motoci sanadin haɗuwar shi da Alhaji Isa Ɗanmarke.
amma yanzu saboda girma da shekaru in ya yi doguwar tafiya a mota sai ya ji duk ya gaji sauƙi sauƙin ta ma in a jirgi ne.

"Saddam ya dawo gidan nan kuwa?

Ya tambaya cikin sanyin murya.

"Tun ɗazu fa ya dawo muna tare da shi, ya so ma ya jira ka har ka shigo sai ya ce mini kansa na ciwo zai shiga ya sha mgani, wataƙila lokacin da ka shigo ya kwanta ne."

"Me ya sa yake jira na?

Ya tambaya har lokacin idanuwansa na lumshe.

"Gobe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login