Follow us on social media
Showing 87001 words to 90000 words out of 147042 words
Chapter 30 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
Abdulrrahman shi ya faɗa ma Kabiru ya dai bar maganar ne amma ba wai don ya fahimci Baffa ba, ai tunda ya nuna shi ba shi da mutumci gwara suma su nuna masa yan zamani ne, bai karanta takardan sakin ba amma duk kalaman dake ciki Abdulrrhaman ya karanta masa tun yana Jalingo.
Ba kwana zai yi ba a ranar yake so ya koma amma ya ce zai dawo tare da Adda Safinatu da yara su duba Ummu su ɗan kwana biyu. Hamma Abdulrrahman ya tafi saboda akwai in da zai je shi kuma sai ya shiga falon Ammah su sake gaisawa tun da lokacin da ya shigo gidan tana da baƙi, labari kamar ana ta aike maƙota duk sun ji labari ana ta shigowa yi ma Amma jaje har Baffa in ya fita haka za a tsayar da shi ana masa jaje, to ai tunda lamarin ya faru ba wanda ya isa ya hana a yaɗa labarin
Ko Ammah abin da Hamma Kabiru ya ke faɗa mata kenan ta lallashi Baffa ya bari su yi ƙaran yaron nan.
"Baffa ba zai amince ba Kabiru ku bar maganar nan kawai."
"Ammah to sai ya kashe mana ƙanwa! Kin ga yadda Ummun ta koma ne?
Amma ta yi shuru tunda ita dai ba ta je asibitin ba Baffa ma ya kasa zuwa amma dai sun yi waya da Ummin ikki ta ce mata ta samu sauƙi tana ta barci dai. Gwara ta samu barcin ko za ta samu yar natsuwa.
"Kawai Baffa ya koma gefe ya bar mana faɗan nan. Wallahi ko ba mu tura yaron nan gidan yari ba sai ya gane ba shi da wayau sai ya san ba a taɓamu a zauna lafiya. Ɗan iska kawai ni da man bai yi mini ba yana wani sunkunyar da kai kamar nagari Ammah ki tsoraci mutum mai kirki da surutun tsiya daga baya sai ya aikata mugun abu. Nonsense kawai"
Amma ta ɗan murmusa ba ta yi magana ba, in dai Kabiru ne da man karatun sa kenan ta kiyayi mutumin da ya cika kirki ba shi da gaskiya. Sake gyara zama ya yi yana kawo maganar da ta wuce wai bai so da man a yi ma Ummu aure ba kamar ya san abin da zai faru daga karshe kenan.
"Yanzu Ammah ina daɗin abin da ya faru? Ummu ƙaramar yarinya ta zama bazawara ga ƙaramin ciki. Haba don Allah in da a ce yarinyar nan ta ji maganar mu da yanzu ta kusa gama Degree ɗin ta da yau ba ta can akwance rai a hannun Allah saboda wani stupid irin yaron da ta aura"
Amma dai ta yi shuru tana sauraran shi yana ta faɗa yana nuna mata harda kuskuren Baffa da itama ma kanta tunda Baffa na jin maganarta ba ta hana a yi ma Ummu aure a wancan lokacin ba.
"Kabiru ka ishe ni fa. Baffan ne ke da laifi? In ya tara sani zai aura ma ta shi? Kaddara ne kuma mu duka musulmai ne musan karɓan kaddara gare mu wajibi ne."
"Amma ki gane magana ta mana. Me ya sa aka goya mata baya! Da a lokacin ke da Baffa kun dage mata wallahi da ta koma makaranta ta bar ra'ayin aure. But kalli abin da ya faru at the end Ammah Rayuwarta ta da dawo baya fa."
"Haka Allah ya hukunta Kabiru ni ko Baffan ka ba mu isa mu sauya faruwan haka ba"
Shi dai sai wani kawo na shi tsarin yake yi Ammah ta gaji ta yi masa tsawa tana faɗin" Kabiru zan ci maka mutumci ba za ka bar ni na ji da damuwata ba, ka zo kana damuna da turancin ka na banza da wofi."
Domin daga karshe sai ya koma yana yi mata mgana da turanci sai da ya ji Ammah ta buɗe masa wuta sannan ya ɗaga hannuwa sama yana dariya.
"Afuwan Ammah na yi shuru."
Ya faɗa cikin harshen fillanci wata uwar harara ta maka masa da ya sa ya ɗinke bakin shi, shuru na wani lokaci sai da ta sauka don kanta ta tambayi Safinatu da yara, duk da ta kira ta waya ta yi mata jaje, ya ce duk suna lafiya yana tunanin za su zo karshen wata su yi musu ko kwana biyu ne Ammah ta ce Allah ya kaimu ya amsa da Amin.
"Ammah gaskiya ya kamata in Ummu ta haihu ta koma makaranta."
"To Baffa."
Ta faɗa cikin gatse tana hararan shi sai ya yi shuru yana dariya.
"Amma shawara ce fa."
"Ba'a son shawaran naka"
"Allah ya ba ki haƙuri Amman mu."
Ya faɗa yana ɗan mirmishi, sake maka masa harara ta yi shi kuma sai ya kwashe da dariya.
"Allah ya huci zuciyar Amman Lamiɗo"
Kamar ya sani sai ko ga shi ta yi mirmishi dariyan ya sake yi kafin ya ce" Da man na sani sunan Amini ne kaɗai zai saka ki dariya."
Amma ta yi mirmishi kafin ta ce" Kwana biyu ma ba mu yi waya ba. ya ko san abin da ya faru na Auta?
"An ya! Kamar bai sani ba don ko shekaranjiya mun daɗe muna waya kuma ban ji ya yi mini magana ba ina tunanin bai sani ba."
Amma ta jinjina kai kafin tace" Ko jiya na gwada lambarsa ba ta shiga. Haka ma Fatima itama ba na samun ta a waya."
"Mami fa kamar ba ta ƙasar, kwanaki mun yi chart da ita tace mini suna Paris."
Amma ta ce" An yi haka na manta Baffa ya faɗa mini sun yi tafiya. Lamiɗon ne na damu amma tunda har ka yi magana da shi yana lafiya Alhamdulillah."
Hamma Kabiru ya ce" Lafiyan shi lau Amma ga ma wani labari mai daɗi."
"Me ya faru?
"Kin kusa fara ganin ɗanki yanzu akai,-akai."
Amma ta washe baki tana fafin" Kai don Allah?
Hamma Kabiru ya gyara zama yana faɗin." Wallahi a shekaranjiyan da muka yi waya yake faɗa mini kamfanin Chevron da ya nemi aiki da su daman can kwanaki ya faɗa mini sun yi online interview. To sun ba shi aiki nan da wattani biyu zai fara aiki da su in sha Allahu."
Amma ta washe baki kafin ta ce" Ma sha Allah. To shi wannan kamfanin anan ne ko? Ba sai ya yi ta yawo a cikin jirgin ruwan ba ko?
Hamma Kabiru ya yi dariya kafin ya ce" Ammah duka kamfanonin na gida Nigeria ne, sai dai shi wanda Lamiɗo ke aiki da su yanzu kamfanin Nigerian Port Authority su jirgin da yake tuƙawa suna jigilan mutane ne da kayan masarufi suna zuwa ƙassashe da yawa kuma suna ɗaukan lokaci shi ya sa yake daɗewa bai zo ya ga mutane ba. Ammah ko a can Lagos ko Balkisu ba ta cika ganinsa ba sai su zo Tashar jirgin ruwa dake Apapa Lagos sau nawa bai je gida ba saboda aikin yana da ɗan tsauri shi ya sa na bashi shawaran gwara ya sauya kamfani wanda zai dinga zuwa gida bayan sati biyu ko uku in ya daɗe ne wata ɗaya."
Ammah ta gyaɗa kai tana faɗin" Haka ne, ya fara tara iyalai bai kamata yana yin nisa da gida lokaci mai tsawo ba gaskiya ka ba shi shawara mai kyau Kabiru."
Hamma Kabiru ya karɓa da cewa" Shi ne fa har sun ɗauke shi aiki yanzu ya rubuta takardan ajiye aiki da kamfanin da yake yi ma aiki yanzu sun ƙi saka hannu. Kin san Lamiɗon naki gifted ne suna son shi duk cikin matuƙan jiragensu ba kamar shi, yana musu aiki tukuru sannan yana da jajircewa akan aikin shi aiki yake yi musu tukuru bai damu da jikinshi ko gajiya ba shi ya sa ba sa son rabuwa da shi."
"To ai sai dai su yi haƙuri mu ma muna son ganin shi sannan muna son ya riƙa hutawa"
Ammah ta faɗa tana dariya.
Tun bayan faruwan al'amarin Ummu sai yau Amma ta saki ranta hiran Lamiɗon da suka yi da Hamma Kabiru.
"Ai zai samu hutu da lokaci ishasshe sosai Ammah. A yadda na yi binciken sabon kamfanin da zai fara aiki da su, suna sauyin matukan jiragen in wannan yaje ya yi kamar wata ɗaya to za a bashi kamar break na sati ɗaya yaje gida ya gana da iyalai da yan'uwa sannan ya dawo kuma kin ga su babu daɗewa sosai kamar na wannan aikin."
"Gaskiya wannan ɗin yafi Kabiru to shima duk tuƙin jirgin ne?
Hamma Kabiru ya sake gyara zama yana faɗin" E mana shi ma kamfani ne kamar wanda yake aiki da shi a yanzu amma suna da ɗan bambamci.
Shi wannan kamfanin na Chevron Nigerian Limited.
Kamfanin dake da alhakin fitar da Mai kasashen waje domin a cire su kalanzir, fetur, dessel, LLG. Suna da jirage da matuƙa jiragen dake da alhakin fita da man zuwa waje da dawowa dashi bayan an tantance shi. Su kawai aikin su fita da man zuwa ƙasar waje domin a tantance a cire abubuwan da na lissafa miki, kamfanin na haƙo Mai ne kuma suna da jirage da matuƙan da ke jigilan Mai zuwa in da za a tace shi a fidda abubuwa masu amfani a jikinsa yadda za a dawo mana da shi mu samu damar amfani da shi kin gane Ammah.?
"Na fahimta Kabiru. Ubangiji ya tsare mana ku. Shi kuma Lamiɗo Allah ya sa ya fara a sa'a Allah ya taimake shi ya tsare shi."
Ammah take faɗa Hamma Kabiru na amsawa da Amin Amin.
" Ya ce ƙarshen watan nan ko ba su saka masa hannu ba zai dawo gida ya yi hutu sosai kafin ya fara aiki da sabon Kamfanin."
"Allah ya amince. Allah ya ba shi nasara."
Sun ɗan jima suna ta hira rabin hiran ta su duk akan Lamiɗo ne sai wajen biyar saura Hamma Kabiru ya yi sallama da Ammah da Baffa ya kama hanyar Jalingo tunda motarsa ce tafiyar awa uku ce zuwa da rabi.
Ummu kuma sai da ta yi kwana huɗu a asibiti sannan aka sallame ta tare da dokokin likita, ta riƙa samun hutu da barci sannan sun ba ta bedrest ga maganguna har da na barci tunda an faɗa musu ba ta samun barci cikin ta kuma ya na gabda shiga wattani huɗu likita ya ce tana buƙatar kulawa da an ga wata matsala a dawo da ita asibiti sannan ta riƙa cin abinci mai gina jiki saboda inganta lafiyan abin da ke cikin ta.
Bayan sun dawo gida Hamma Abdulrrahman ya sake zaunar da ita daga shi sai ita a ɗaki ya sake yi mata faɗa daga karshe ya koma lallashi ya faɗa mata ga dokokin likita sai ta kiyaye ma kanta da shiga damuwa in tana son ta tsira da abin da ke cikin ta, bai barta ba sai da ta yi masa alƙawarin za ta daina damuwa sannan za ta kula da kanta ko domin abin dake cikinta da take jin wani son shi na ƙaruwa a tsakiyar kirjinta ba kukan sakin da Habib ya yi mata take yi ba har yanzu kukan bakin ciki da faɗa da zuciyarta da har lokacin ba ta daina son Habib da tunaninsa ba. Tana yi iya yin ta domin ta manta da shi amma ta kasa da ta keɓe shikenan za ta yi ta tunanin shi da irin good momories ɗin su tare da juna ba ta ma sanin lokacin da ta ke fara kuka.
Ba za ta taɓa mantawa da Baɗɗo ba sai da ta kwana goma da ita tana kula da ita sannan ta koma gida tunda sun koma makaranta. Sannan Ummin ikki ma kullum sai ta leƙo kowa dai burinsa ta samu ta sake ta fara walwala. Ga Baffa da duk ya sakar ma Hamma Abdullahi harkokinsa yana zaune a gida saboda ita. Shi dai nasihan shi ta daina damuwa ta yadda da kaddaranta. Ammah ma tana nuna nata kulawan amma in ta yi lallashin ta gaji za ta fara masifa ne da faɗa, ga Hamma Saddam ma yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen zama da ita yana yin duk wani abu da zai sanya ta farinciki, haka ma Hamma Abdulllahi, da matan su in ba su zo ba yau ba za su zo gobe su Hamma Jibo duk da ba sa kusa duk ranar duniya sai ta yi magana da su ta wayar Amma tunda ita wayarta tana cikin kaya ta kashe kanta ma ba chaji, ganin yadda kowa ya damu da ita ya sa ta rage damuwa amma Allah kaɗai ya san halin da zuciyarta ke ciki tare da Ammah suke kwana Baffa ne ya ce ta riƙa kwana da ita amma in ba magungunanta ta sha ba tana daɗewa tana juye-juye ba ta samu barci ba gani take yi kamar a mafarki wai yau ita ce a gida a matsayin bazawara. Ba ta sare ba tunani take da yaƙinin cewa Habib zai dawo ya neme ta, tana ma mantawa da cewa har abada yanzu ta haramta ga Habibu ita soyayyar shi ta gama rufe mata ido da duk abin da ya yi mata ta kasa jin tsanar shi ta kasa daina son shi, duk da tana son ta tsane shi ɗin amma ta kasa tunda ba ita ke da alhakin sarrafa zuciyar ta ba.
Hamma Abdulrah. yana can kasar turai ya ji labarin abin da ke faruwa shi auren ma baya nan aka yi sai ga shi yana can komai ya ƙare. Ya shiga damuwa sosai barin ma da Saddam ke ba shi labarin yanayin da Ummun ke ciki Vedeo call ya kira aka bata ya yi magana da ita kuka kawai take yi tana ma kasa mgana shima daga ƙarshe kashewa ya yi ya fashe da kuka, yana da saurin kuka da tausayi shi ya sa bai sake kira ba sai dai duk lokacin da ya yi magana da wani na gida zai ce a gaishe masa da Ummu, ba ya son su sake magana ta saka shi kuka ga shi yana shekaran ƙarshe ne karatu yake yi kamar injin ya yi ya gama shima ya dawo gida cikin ahalinsa.
Mami ma suna Paris Hamma Saddam ya faɗa mata halin da ake ciki ai a daran ta matsa ma Abban islam cikin kwana biyu suka dawo gida Nigeria. Washe gari kuma suka sake biyo jirgi zuwa Jimeta. Tun da Mami ta zo ta ke kuka kowa ya san kukan da take yi kuka ne na fami daga tsohon gyambon dake zuciyanta. In ta kalli Ummu sai ta ji kukanta ya kasa tsayawa ta yi kuka kamar ranta zai fita sai da Baffa ya zauna yana ta ba ta baki Abban islam na gefe domin ko ya ba ta baki ba ta yin shuru sai ta ce wai ba zai gane yanayin ba ne.
Ummu Salma kukanta ya dawo sabo da zuwan Mami da kukan da take yi, tausayin Ummu Salma take ji duk da ta ɗan fi ta shekaru ita lokacin ko ashirin ba ta cika ba ta faɗa wannan kaddaran amma duk yadda za a fassara lamarin ba wanda zai gane yanayin sai wanda abin ya faru da shi.
"Baffa yaron nan ya cutar da Ummu Salma. Muma ya cutar damu kuma wallahi sai Allah ya saka mata."
Mami take faɗa tana kuka kamar ranta zai fita.
"Ummu ki yi kuka ki yi ta kuka ko za ki sami salama. Amma kar ki yi dogon damuwa cuta za ta kama ki, in kuma hakan ta faru za ki samu cikin damuwa."
Haka take ta faɗa ma Ummu lokacin da ta rungumeta a jikin ta dole Alhaji Isa Ɗanmarke ya nemi hotel ya kwana washegari ya juya Kaduna tunda yara na gida tare da su Baraka, ya bar Mami a Jimeta ita ta ce ya tafi kawai za ta zo daga baya.
Zuwan Mami ya tado ma Ummu taɓon ta amma kuma ta samu sauƙi saboda Mami ta zaunar da ita, ta ba ta labarin rayuwarta da yadda ta yi gwagwarmaya da kaddaranta daga ƙarshe ta yi nasara da yadda Ammah da Baffa suka yi ta ƙoƙari a kanta.
"Ummu Salma akwai zafi na sani amma sai kin daure. Yanzu ki sani ke uwa ce a gobe. Ki kula da kanki saboda abin da ke cikin ki, ki yi haƙuri ki yi haƙuri ki cire damuwa a ran ki, in kin ji kuka ki yi kuka domin shi kaɗai ne zai samar miki da salama."
Haka take ta faɗa mata cikin ƙarfafa mata gwiwa.
"Za ki ci wannan jarabawar Ummu. Za ki yi nasara kamar yadda na yi. Muna nan dake Allah zai kawo miki wanda zai share miki hawaye. Shi kuma Habib sai ya yi Fargar jaji da ikon Allah."
Ummu Salma tana kuka ta nuna ma Mami jikinta tana kuka take faɗin" Mamina wa zai aure ni a haka? Me na ke da shi? Ba ni da budurci ba ni da jiki mai kyau, nonuwana sun kwanta, ciki gare ni Mami nan da wata biyar zan haihu na buɗe na zama uwa na shayar da jariri, Mami ki faɗa mini wa zai kwashe ni a haka? Me ya sa shi da ya fara bai ƙarisa ba Mami na?
Haka Ummu ke faɗa tana ta gunjin kuka.
"Allah zai kawo shi, wanda ba jikin shi yake so ba ke yake so Ummu in kina tunanin ba zai yuyu ba ki riƙa duba rayuwata. In kika kalle ni za ki samun ƙwarin gwiwan cewa ke ma komai zai wuce zai zama sai labari, sai dai ki tuna ki yi mirmishi ko kin yi kuka sai dai ki yi kukan farinciki da tuna rayuwar baya."
Ita dai Ummu Salma jin Mami kawai take yi ba ta san irin yadda zuciyanta ta so Habib ba ne. Ba ta san yadda jikinta da rayuwarta ya saba da shi ba ne, shi da ya fara me ya sa bai ƙarisa ba? Me ya sa ya rabu da ita? Ta amince za ta zauna da shi ya yi ta moran jikinta har illa masha Allah, amma yanzu da ya sake ta ina za ta je? Ji take yi kamar ta rasa komai na rayuwanta ne in ta ce komai tana nufin komai, mafarkin ta burukanta da dukkan wani tanadinta na rayuwa Habib ya yi sanadiyar da yau ita Ummu Salma ta dawo ba komai ba, ya kuma ma yar da rayuwarta kwanko babu wani abin mamora a rayuwarta a yanzu.
Kwanan Mami biyu da zuwa Jimeta sai ga Hamma Mustapha da iyalan shi a rana ɗaya