Follow us on social media
Showing 141001 words to 144000 words out of 147042 words
Chapter 48 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
ta ho nan ki hau nawa bayan da kika saba hawa.."
Basira ta faɗa tana leka Hanan sai ko ta makale bayan uwarta tana kallon Basira.
"Ba ki tahowa ko?
Ta faɗa tana miƙa mata hannu kawai sai ta saka kuka tana kiran Mahmah, Ummu na dariya ta ce"Hanan ke da Basirun na ki."
Haka Hanan ke kiranta su yi ta dariya ita da su Mami Basira tun tana masifan cewa ni da na reneki ki san sunan kowa daidai amma ni basiru kika mayar da ni har ta zo ta haƙura domin ya kama bakinta.
"Ba ruwana in ta ce ba za ta sake goya ki ba."
Ummu Salma ta faɗa tana dariya.
Kamar kuma tana ji sai ta daina kuka ta kura ma Basiran ido tana kallonta sai ga shi da kanta ta miƙa mata hannu ita kuma ta kama tana faɗin" Yauwa Hannatuna."
Tana dariya dariya yarinyar ta bar bayan uwar tata ta haye na bayan Basira tana zillo.
"Basiruu."
"Ke ni sunana Basira ba Basiru ba."
"Basiru.."
"Kai wannan yarinyar, to ke ma Habu ba hannatu ba."
Ummu na gefe tana cin dariyanta.
"Ku je falo Basira bari na haɗo mata tea ɗin."
"To, na ji jikinta da ɗumi ya kamata ta sha maganinta na rana."
"To ta sha tea ɗin sai na ɗauko mganin ki ba ta yar rigimar nan ai sai ke Basira."
Ta fice tana dariya.
Basirace ta taimake ta har ta samu ta haɗa mata tea ɗin bayan ta kawo mata ta bata ta sha, sannan wajen shan mgani sai da aka yi mata ɗure ba ta son magani tana ta kuka da rigima bayan nan Basira ta yi mata wanka ta sauya mata kaya sai barci bayan ta goyata ram a bayanta da zani.
Mami ba ta nan ta shiga cikin makaranta gidan daga Ummu ne sai Basira Faruku na makaranta sai biyar da rabi zai dawo tunda nan Al'areeb yake yi a Kaduna yana primary 6, Islam dai ana bording zaria can FGGC BASAWA tana jss2 yanzu sai an yi hutu take zuwa gida amma suna zuwa yi mata visiting zuwa ma biyu duk Ummu ke zuwa ita da Basira da Faruk Hamisu ke tuƙasu.
Daddy kuma ba ya nan ya yi tafiya kasar Turkey ya fi sati acan.
Sai a lokacin itama Ummu ta samu ta ɗan sake yin wanka ta sauya kaya wayarta ta ɗauka ta shiga shafukanta tana ganin video ɗin da ta yi ɗazu ta fara ɗora shi a kan Youtube sai kuma nan da nan ta yi sharing ɗin shi zuwa Handles ɗinta na sauran shafukan sada zumumta an yi mata comments amma duk akan godiya da yabawa ne sannan da masu cewa suna gane koyarwaanta don Allah ta buɗe musu online class mana, itama tana so ta buɗe amma ba yanzu ba sai ta sake tara yawan mabiya.
Bayan ta gama duba shafukanta sai ta shiga kan whatsApp ɗin ta, tana duba saƙonni, ko wata biyu ba su yi da dawowa daga Jimeta ba tun bayan barin ta gida sai a lokacin ta sake komawa Jimeta shima ya kama dole ne Baɗɗo ce ta gama makaranta shi ne ta je mata graduation Mami ba ta samu zuwa ba daga ita sai Hanan suka tafi kwananta goma ta dawo Kaduna duk da ta yi kewar garin amma ba ta jin za ta sake zaman garin ya wuce na sati biyu ba, yanzu Ummu Salma yar kaduna ce ba yar Jimeta ba.
Hamma Saddam ne ya yi mata sako tana dubawa ta ga ya ce" Ke nifa ina Lagos."
Mamaki take yi sai yanzu ta san dalilin da ya sa Hamma Saddam ya zaɓi shiga Camp a garin Lagos.
Ashe saboda ya je ya huta a gidan Hamma Lamiɗo ne.
Hotuna ne ya turo mata sama da goma, har da wasu ma yana driving a wata mota mai kyau da tsada.
"Ni fa har motar Hamma Lamiɗo nake hawa yanzu"
Ta tuna mganarsu ta kwanaki da ta tambaye shi motar waye yake aro yana ta wayon gari ya ce tashi ce ashe wasa yake yi mata.
Yanzu ma hotunan shi ne a bakin ruwa kala kala.
"Ya mutanen gidan?
Haka kawai ta rubuta masa saƙon ya maka biyu domin ta san yana online, Hamma Saddam da waya kamar 5 and 6 ne.
Tun bayan barin ta Jimeta ba ta sake ganin Hamma Lamiɗo ba wataƙila Mami na haɗuwa da shi tunda ta je Jimeta sosai a wannan shekaran amma ita ba ta sake ganinsa ba kuma ba ta sake bibiyan labarin shi ba, ta dai san ya biya ma Hamma Abdullahi da Hamma Abdulrrahaman tare da matansu sun je Umra tare da Ummin ikki da babansu Baɗɗo, a shekaran da ta dawo Kaduna itama Daddy ya biya musu sun je gabaɗaya acan suka haɗe a masauƙi ɗaya ma suka sauka ta kan ji ana hiran ya yi kaza ya yi kyauta kaza amma ita dai tunda bai taɓa yi mata ba, ba ta taɓa damuwa da shi ba.
Hamma Abdulrahim ne ta ga ya saka hoton shi cikin likitoci turawa kamar yana can ƙasar waje alhalin yana Abuja yana Housemanship ɗin shi a asibitin NIZAMIYE HOSPITAL ABUJA.
Bayan ya dawo ya yi jarabawa ta Medical and Dentel council of Nigeria.
(MDCN) Sau ɗaya ya yi kuma ya samu nasara.
Abdulrahim kamar wani bature daman ga shi jajir da shi ɗabi'unsa ma da komai na shi ya koma na turawa, hausa ma tana neman ɓace masa magana kaɗan turanci fillanci ko har ya fara mantawa shi da ya shafe sama da shekara bakwai a kasar Singpore.
Da ya dawo Ammah ta yi ta masifa, in suna hira ya dinga yi mata turanci.
"Buraubaka, tir da wannan kasar turawan tunda ya sa ka manta da al'adanka ka kwaso mana daɓi'an turawa."
Lokacin da ya zo Kaduna ne ya ke ta ba ma Ummu labari tana cin dariya.
Har waliman dawowarsa an yi amma Ummu ba ta je ba Har Mami taje shi ne bayan ya natsa ya huta ya zo ya ganta kwana biyu ya yi suka sha hira suka fita yawo cikin gari kafin tafiyarsa.
Tun da yanzu Ummu har driving ta koya kuma ta iya, tana tuƙa motar Mami wani lokacin.
Ummu Salma ba ta taɓa tunanin da gaske rayuwarta za ta sauya ba sai ga shi Ubangiji ya sauya mata rayuwa, rayuwar da ba ta yi hasashe ba, lokacin da suka zo Kaduna ga shi dai gidane amma ta yi ta baƙunta da rashin Sabo ba abin da za ce da Mami da Daddy sai godiya domin sune tsanin da rayuwarta take kai a yanzu. Sun kula da ita da lafiyanta da ita da abinda ke cikinta, da karfi da yaji suka yakice damuwa da tunani a zuciyanta.
Kwanan ta arba'in a Kaduna ta haihu a asibitin kuɗi na Garkuwa, aiki aka yi mata domin ta yi doguwar naguda, an samu nasaran ciro mata ya mace wacce ta saka ma suna Hannatu suna kiranta Hanna, Daddy da Mami su suka yi mata komai, raguna biyu Daddy ya yanka mata kuma ya shirya taron suna.
Baɗɗo da su Ummin ikki da matan su Hamma Abdullahi duk sun zo Kaduna taron suna Umma Balki da Umma A'i ma sun zo Umma Balki sai da aka yi arba'in ta koma Mubi ita ta yi ma Ummun wankan jego mai tsada, Baffa ma ya tako har Kaduna ya ga Hanna amma ban da Ammah sai dai ta gan ta a hoto. Kaf yayyenta ba wanda bai kira ta ba, sannan sun tako tare da iyalansa ita da Hanan sun ga gata sosai, kuma ga shi yarinyar ta taso da ƙiriniya kowa na son ta Daddy ko kamar shi ne mahaifinta yadda in dai yana gida tana tare da shi haka ma Mami shi ya sa su ta fara kiran sunayensu bayan ta fara iya magana sai Faruƙu da Ilam wato Islam ko Mahma sai daga baya ta fara iya faɗa, gata na duniya Hanan ta na gani kuma tana kan gani komai na rayuwa ba abinda suka nema suka rasa Daddy ne da Mami ke tsaye kanta ita da yarta.
Har kuma gobe Habib bai nemeta ba, itama ta manta da wanzuwarsa a rayuwanta ba za ta ce ta manta gabaɗaya ba, domin ba zai mantu ba, amma ta kan daɗe ba ta tuna ba in ta tuna ita kaɗai ta yi ta kuka, Rayuwarta ta ya sauya a Kaduna Mami macece mai kirki da yaƙana kaunar da take yi mata ko rabin shi ba ta nuna ma Lamiɗo, ba ta zuwa ko'ina tana gida daga baya ne ma ta fara bin Mami zamfara in za ta je ganin Dangin Daddy, bikin Baraka ne farko, amma ba ta bin ta Jimeta itama ba ta matsa mata tunda ga waya tana mgana da kowa daga gida.
Tun kafin ta yaye Hannan Hamma Kabiru ya matsa wai sai ta koma makaranta ita kuma har abada ba ta son karatu shi ya sa a wannan karon ma ta turje, Daddy da Mami suka goya mata baya dole suka ƙyaleta, da ta watsar da girke-girkenta sai dai kawai tana yi a gida, tunda ta hana Mami ɗaukan mai girki tace ita za ta dinga yi, Mami ce ta matsa mata ta dawo dashi, ta kuma ce za ta neme mata catering school ko wani program haka ta shiga domin ta sake ƙwarewa haka ko aka yi Mami ta nema mata ta shiga yanzu haka a Kaduna tana da certifacate sama da huɗu na catering da program kan abin da ya shafi girke-girke kuma da shawaran Mami da na Baɗɗo tare da na Hamma Saddam tare da Hamma Abdulrahim ta ƙirkiri sabon account da sabon suna lokaci ɗaya kawai tunanin yin amfani da sunan Hanan ya zo mata. Hanan Baba Jimeta sai ta ke amfani da Hanan B Jimeta.
Ta fara video tana ɗorawa a youtube na girke-girke duka-duka wattani shidda ne da fara abin amma har ta ɗan fara tara mabiya da farko har ta sare da karfin gwiwansu ta cigaba a hankali ta buɗe sabbin accounts a Tiktok da instagram.
Daddy kuma ya gwangwajeta da sabuwar waya Mami kuma ta siya mata ringlight kayan girki da komai akwai su a kayattacen kitchen ɗin Mami, wanda wasu ma saboda kyan kitchen ɗin ya sa suke kallon Videos ɗin Hanna Delicouis ba a ganin fuskarta in ta ɗora videos ɗon sai dai a hangi rigarta daga ƙasa haka sai maganarta, ga shi yanzu wasa wasa videos ɗinta suna ta tafiya a kafafem sada zumumta mata da dama suna ƙaruwa da ita saboda ta iya koyar da komai a saukaƙe.
A dalilin Mami da Daddy ta je Umra sau ɗaya ta je Niger sun je Ghana, a Nigeria kuma sun je Abuja da Kano. Daddy na da gidaje a Kano da Abuja haka kawai in yara sun samu hutun makaranta zai kwashe su suje su huta na kwanaki, idanuwanta sun buɗe tunda suna yawan fita yawon buɗe ido, babu in da ba ta sani a garin Kaduna ba.
Wani lokacin ma har cikin makaranta ta sha raka Mami, zuwanta Jimeta wannan karon sai da ta zama abar kallo, Baɗɗo ita kanta ta zo Kaduna sau biyu sai da ta yi mamakin ganinta.
Ta yi kiɓa ta sake fari ta zama wata babbar mace lalle kwanciyar hankali ma ni'ima ne.
"Auta ke ce kika zama giwa haka? Ai ke da uwar taki ma sai a rasa uwar da yar."
Ammah ta faɗa domin in suka jera da Mami kamar yaya da ƙanwa a jami'ar da Mami ke koyarwa da suka fara ganin Ummu sun ɗauka kanwarta ce, sai da ta ce ɗiyar yayanta ne suka saki baki, Baffa kam bakinsa yaƙi rufuwa.
"Auta Auta an zama uwa manyan mata."
Haka yake faɗa, Hanan ko kiyuwa ta fara yi musu farkon zuwan su, sai da Ammah ta yi mata jan ido sannan ta shiga taitayinta ta yi ta kuka tana rigima Baffa me mai lallashi ya ce shi kan ai ya ga mata, dole ya yi biyayya Ammah ko ya ce kishi take yi ta ga wacce ta fi ta jan fata.
Ammah cikin gatsale ta ce bai ko yi dace ba ana ta dariya.
Hanan kuma ba ta iya kiran sunan Baffa ba sai dai ta ce Bacca.
Ammah ta yi ta masifa tana faɗin ke ba sunan mijina Bacca ba sunan shi Baffa in ba ki iya faɗa ba ki yi shuru ki bar ɓata masa suna, sai suka koma suna ba ma mutane dariya.
Kowa ya zo ya ga Ummu sai ya yi magana haka da ta je gidan su Baɗɗo su kaltume suna ta mamakin sauyawarta ta zama wata mai tsada da ita.
Ummin ikki sai da ta ce ina surukin da take jira, Ummu ta yi dariya ba ta ce komai ba, domin ita a zuciyanta ma ba ta son duk wani namiji in dai da aure ne, aure ya fita kanta gabaɗaya. Yadda ta tsani Habib haka ta tsani kalmar aure, ta je Mubi saboda an yi rashi ɗiyar Umma Salmatu ce ta rasu wajen haihuwa, nan ma suka yo ma ta caa kan maganar aure har da su Baffa Umaru shi ya sa ta baro musu garin ma gabaɗaya.
Ita yanzu me za ta sake tsinta a aure da za ta sake yi? Ai tana jin babu sauran wani abun da ba ta gani ba, yanzu abin da ke gabanta kawai ba ma Hanan tarbiya amma a zuciyanta ta yi kudiri ita da aure har gaban abada. Tana ganin ta rasa komai, ba ta da wani sauran wani abu da rage mata da za ta sake takama da shi, Habib ya gama da komai kafin ya cire ta daga rayuwarsa.
***
Sai bayan la'asar ta fito daga cikin ɗakin ta a baya a ɗaki ɗaya suke kwana da tare da Islam amma tun bayan da ta haihu Mami ta gyara mata ɗakinta ita kaɗai, balle ma yanzu da Islam an fara zama yan mata shekarunta sha huɗu, Faruƙu ne goma. Kicthen ta shiga ta duba abin da za ta sarrafa na dare yau ko abincin rana ba su yi ba ita da Basira tea suka sha Hamisu kuma da kuɗinshi ba zai jira su ba, Sunusi kuma ya yi aure matarsa na aiko masa da abinci, Mami ma tana maganar za a gyara musu bangaren waje kawai ta dawo kusa da shi.
Alele kawai ya faɗo mata a rai sai ta ce bari ta yi musu mai nama a ciki sai ta yi musu miyar source ɗin ƙwai store ta shiga ta ɗobe waken suna da ƙaramin turmi ta ɗan saɓa shi ta wanke ta niƙa shi a blander wani katon friza ne a kitchen din cike da kayan amfani, nau'ikan nama ba wanda babu sai dai kawai a ɗauka in za a yi amfani da shi.
Tana kitchen ɗin tana aiki Mami ta shigo gidan ba ta sani ba sai da ta leƙo kitchen ɗin ta yi mgana.
"Ya Ummu sannu da aiki."
Haka Mami da Daddy ke kiranta hatta Hanan ta kama wani lokacin haka take kiranta.
"Laa Mami yaushe kika dawo?
Ta faɗa tana kashe blander ɗin tunda ta gama niƙa waken.
"Yanzu na shigo me aka yi mana ne na fara jin ƙamshi?
Mami ta faɗa tana ɗan shigowa kitchen ɗin kaɗan.
"Mami alele mai nama zan yi mana ko kina son wani abu ne?
"Aa ki yi mana yaushe rabo na da alala, amma ki yi mana na manja."
"To Mami."
"Ina Hanan yar rigima? Ya zazzaɓin ya sauka?
Ta tambaya tana buɗe fridge ta ɗauko rowan gora Ummu kuma ta ɗauko mata kofin tangaran a wani dirowan kitchen ɗin ta mika mata ta tsiyaya ruwa.
"Ta ji sauƙi ta na can bayan Basira."
"Ban gan su a falo ba."
Mami ta faɗa bayan ta gama shan ruwan.
"Ƙila suna bangaren Basira."
"To bari na je na watsa ruwa. Kafafuwana sun gaji Ya Ummu."
"Mami za a yi tausa anjuma."
"Yauwa yar albarka."
Mami ta faɗa tana dariya sannan ta fita, Ummu ta amsa da Amin tana ɗan mirmishi har ta fita sai kuma ta dawo tana faɗin" Baffa ya kira ki kuwa?
Ta tambaya tana tsaye a ƙofar kitchen.
"A'a Mami."
Sai ta kalleta ganin ta yi shuru.
"Me ya faru Mami?
Ta tambaya a ɗan tsume.
"Aa ba komai, kawai na tambaya ne."
Tana gama faɗin haka ta wuce tana faɗib" Na shiga ciki."
Mamaki ya kamata, me ya faru ne? Mami ba ta saba mata irin waɗanan tambayoyin ba, suna waya da Baffa kusan ko da yaushe yana kiranta amma itama tana yawan kiran shi saboda yadda suke daɗewa suna hira, saɓanin Ammah da suna gaisawa da tambayan yara hiransu take katsewa. Sai ba ta saka tunanin komai ba, sai ta ɗauka ko Baffa ne ya kira ta yau shi ya sa take tambaya kanta tsaye ta cigaba da aikinta tana sanye da riga da wando kalan ruwan ƙasa yan pakistan Mami ce ta siya mata su a Saudiya ta ce ma zaman gida ne.
Mami kuma na shiga bedroom ɗinta dake saman bene ta watsa jakanta saman gado lokaci ɗaya ta ciro wayarta ta kira wata lamba, sai da ta katse ba a ɗaga ba ta sake kira nan ma shuru.
"Kai."
Ta faɗa tana cije baki, tiolet ta faɗa ta yi wanka ta fito kenan ɗaure da babban towel a ka kira wayarta ganin mai kiran yasa ta ɗauka da sauri.
"Na ji shuru har yanzu."
Magana aka yi mata daga can bangaren sannan ta gyaɗa kai tana faɗin.
"To ka tabbata dai cikin satin nan, ba fa da wasa na ke yi ba da gaske nake yi."
Daga haka ta katse wayarta tana ɗan wani nazari kafin lokaci ɗaya ta saki mirmishi ita kaɗai.
Daga ita sai Allah sai zuciyanta sai wanda suka yi waya suka san abin da take ƙullawa.
****
*Sunday*
Daddy bai dawo ba, Mami ta ce akwai wasu sabbin shigowan motoci ne da zai yo oder shi ya sa ya ɗan jima, sun saba duk karshen sati su kan ɗan fita yawo cikin gari tare da Mami da Barira da Faruƙu, yau ma ko da Daddy baya nan sun fita bayan la'asar suka je Shoprite su ɗan biya store suka yi tsince tsince, suna mota a hanyar dawowa gida Hamisu ne ke tuka su a wata mota ƙiran toyota RAV4, Baffa ya kira wayar Mami sun daɗe suna mgana abin da ma yasa Ummu ta gane Baffa ne ta ji Mami na ambaton sunan shi duk da ba ta fahimci kan me suke magana ba, tunda ita Mami faɗi kawai take yi" Kuma ka yarda da maganansa Baffa?