Follow us on social media

Showing 24001 words to 27000 words out of 147042 words

Chapter 9 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

fara takawa zai wuceta zuwa bedroom.

"Sannu da zuwa Noori."

Ta faɗa tana nufarsa, bai tsaya ba amma ya amsa da yauwa a ɗakune yadda ta bar fuskar shi a cunkushe ɗazu to a yanzu ma haka ya shigo
Tana ƙoƙarin karɓan jakar hannun shi ya wuce ta da sauri zuwa cikin bedroom tana jin ƙaran yadda ya rufe ƙofar da ƙarfi. Ummu salma ta yi sansarairai a tsaye ta kasa motsi saboda mamaki da al'ajabi a wattani takwas ɗin da suka yi da aure ita da Habib ba su taɓa riskan wannan matakin ba sai yau.

Ajiyar zuciya ta sauke, komawa ta yi ta zauna tana sake karfafa ma kanta gwiwan ba komai yana fushi ne ya ɗauka ta san tana da ciki ne ba ta faɗa masa ba. Tana nan zaune sama da mintina talatin sha biyu saura na dare sannan Habib ya fito daga cikin Bedroom, ya sauya kaya zuwa wani gajeron wando da farar singlete da alamu wanka ya yi ko kallon ta bai yi ba ya wuce kitchen ya ɗauko ruwan gora ya fito da shi a hannu ita kuma ganin haka ya sa ta miƙe jikinta har yana rawa.

"Noori."
 
Ta faɗa cikin sanyi da karyewan murya.

Sai da ya sha ruwan rabin goran  sannan ya ɗago yana kallonta cikin wani irin kallo da ya sanyaya mata jiki.

"Ga abinci."

Ta faɗa tana nuna masa Dinner ɗin da ta gama shirya masa komai tun ɗazu.

"Na ƙoshi."

Haka kawai ya faɗa lokaci ɗaya yana sauke goran hannun shi  a saman dinning ɗin ya wuce ta ya koma ciki, da sauri ta bi bayan shi ta ci sa'a bai rufe ƙofar ba.
Yana zaune a gefen gado yana duba wayarsa ta shigo gefensa ta zauna tana neman kwanciya  a saman kafaɗan shi ya yi saurin matsawa gefe, Ummu ta saki baki tana kallon shi.

"Noori."

Ta kira shi da mamaki a muryanta bai amsa ba ya dai kalleta a tsaye da idanuwansa fuskar nan ba fara'a.

"Me ya faru ne?

Banza ya yi da ita sai ma ya cigaba da duba wayarsa.

Sai ta yi mirmishi kafin ta ce.

"Wai akan mganar ciki ne?

Ga mamakin ta  sai ya amsa mata da cewa.

"E."

Ta ɗauka tunanin ta gaskiya ne yana fushi ne akan yana tunanin ta sani ba ta faɗa masa ba, ba ta san tunanin Habib a lokacin ba.

"To ka yi haƙuri Noori na, wallahi da gaske na ke yi nima ban san ina da ciki ba."

Har ta gama mgana bai ɗago ba, yana cigaba da latsa wayarsa.

"Ka ji Allah ban sani ba ka yarda da ni."

Matsowa ta sake yi kusa da shi tana mai riƙe hannun shi guda ɗaya tana sake marairaicewa da muryan tare da shagwaɓan da ta san yana kunna shi.

"Am sorry Noori na.
Baby ce fa? Za ka iya fushi da ni?

Ta faɗa tana mai kwantar da kanta a saman kafaɗan shi.
Sai ya sake matsawa da mamaki ta sake ɗagowa tana kallon shi kafin ta samu damar mgana ya miƙe tsaye.

"Ummu-Salma ina son na yi mgana da ke."

Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai kallonta a mganar shi da yanayin shi babu wasa ko kaɗan.

"Magana kuma? Wata mgana?

Ta faɗa cikin mamaki gabanta na faɗi kaɗan-kaɗan.

Bai amsa mata ba sai ya koma can farko gado ya zauna sannan ya juyo yana kallon Ummu-Salma da ta daskare a zaune saboda ita fa ba ta gane ma yanayin Habib ba gaskiya

"Ki natsu ki fahimci umarnin da zan ba ki."

Kallonsa kawai take yi amma ta kasa mgana sai dai ta kasa haɗiye miyau a bakinta saboda faragaba da tarardadi

"Ina sauraran ka."

Ta faɗa dakyar cikin rauni har idanuwanta sun fara cikowa da ƙwallah tun kafin ma ya faɗi mganar.

"Ummu-Salma."

Ya kira sunan ta a kausashe, sunan da ba taɓa jin ya kira ta ba tun tana gida da Baby yake kiranta har bayan auran su bai sauya mata suna ba shi ya sa jin yau yana kiran ta da sunan ta cikin kaushi ba tausasawa jikinta ya fara rawa cikin tsoro ta amsa.

"Na'am. "

A muryan ta kamar saura ƙiris ta fashe da kuka.

"Umarni na ke so na ba ki, ta wani fanni kuma ba Umarni ba ne."

Ita dai ta ƙura masa ido, ta kasa cewa komai amma ta matsu ya faɗi abin da zai faɗa kafin  zullumi ya ɗauke mata numfashinta.

"Ina son a zubar da cikin jikin ki Ummu-Salma."

Ya faɗa yana mai kallonta domin ganin yanayin ta.
Ita ta ko sai ta ji kamar ba ta ji da kyau ba ya sa ta sake tambaya.

"Naam me ka ce?

Ta faɗa tana mai ƙura masa ido, kamar ta ji Habib na maganar ciki, me ya ke cewa ne?

"Na ce ina so a zubar da cikin nan."

Ido ta zaro kafin ta ce" Wa ni  ci ki.?

Ta faɗa a rarrabe cikin tashin hankali.

"Wanda ke jikin ki."

Ya faɗa ba tare da ɗar ba, kuma babu nadama a mganarsa.

Sai Ummu ta fara mirmishi kafin ta ce.

" Haba Noori ka bar irin wannan wasan don Allah ba na so."

Ta faɗa lokaci ɗaya tana girgiza kanta. Domin a tunanin ta wasa ya ke yi, ita kuma ba ta son irin wannan wasan, duk duniya a yanzu ba wanda ya isa ya raba ta da cikin jikinta sai wanda ya ba ta, amma ba dai wani mutum ba.

 "Wasa ka ke yi ko Noori?

Ta sake faɗa tana kallon shi.

Amma sai Habib ya miƙe a fusace har yana nuna ta da hannu.

"Kin ga wasa a mgana ta! Ko kin ga fuskata da alamun wasa?

Ya faɗa a fusace, jikin Ummu na rawa ta miƙe, cikin mamaki da aljabi ta ce" Cikina zan zubar Noori?
"E haka na ce"
"To saboda mene? Cikin yana da wata matsala ne?
"Ba shi da wata matsala, amma ni ne zai iya kawo ma matsala a rayuwata nan gaba."

Ummu cikin rawan baki da na murya ta ce
"Ban ga ne ba?
"Ai ba za ki gane ba. Malama ni dai ga abin da na ce. Ciki za a zubar da shi."
"Aa"
Ummu ta faɗa hawaye na zubo mata cikin kuka ta ce" Me ya sa zan zubar da cikina? Cikin sunna ne ba na shege ba."
Ta faɗa cikin zubar hawaye

"Ni haka na ce za a zubar da shi."

"Ba zan iya ba. Ba zan iya zubar da cikin nan ba,  haka kawai sai ka ce na zubar da ciki kuma ba da wani ƙwaƙwaran dalili ba"

Ta faɗa tana share ƙwalla kafin ta matsa kusa da shi tana cewa" Noori ni ce fa, ka tuna lokacin da ka shiga damuwa da na rasa cikina na farko me ya sa ba za ka yi murna da samun cikina a karo na biyu?
Me ya sa ka canza? Ciki fa ka ce na zubar? Zunubi fa kake so mu aikata."
Ta ƙarishe faɗa tana ƙoƙarin riko shi da sauri ya kauce yana faɗin

"Ni ba damuwa na shiga don cikin ki ya zuɓe ba, ko bai zube ba za ki zubar da shi. Murna na yi lokacin da ya fita ba baƙin ciki ba.".

Ya faɗa yana kallon ta, cikin ɗimuwa da firgici Ummu ta zare ido, kafin ta kifta idanuwanta amma ta kasa mgana domin sai ta ji wani abu ya tokare mata maƙogwaro

"Kin ji da kyau, saboda haka na ba ki  kwana uku ki yi shawara. Duk da Umarni ne ba zan miki dole ba amma ki sani zubar da cikin nan kamar makullin auran ki ne, taurin kai kuma na ƙin zubarwa dai dai ya ke da rasa komai na ki, in na ce komai ina nufin komai. Kuma wallahi sai  kin yi nadaman saɓa ma umarnina."

Yana gama faɗin haka ya fice ya bar mata bedroom ɗin. Ummu ta rasa wani tunani za ta yi, sai take ganin kamar a mafarki gaskiya ne abin da ke faruwa ko ƙarya, amma kuma kamar da gaske, ganin ta kawai ta yi tana tafiya a falo ta iske Habib zaune a saman kansa ta tsaya tana kallon shi cikin mamaki, so take yi ta ga shin Habib ɗin ta ne ko sauya mata shi aka yi amma ba ta gano wani abu da zai saka Habib ɗin ta ya sha bambam da wannan dake zaune a gabanta ba.

Tashi ya yi zai bar mata falon da sauri ta sha gaban shi tana faɗin" Noori an ya kasan me kake faɗa kuwa?
Ta faɗa muryanta na rawa kaɗan ya rage  ta fashe da kuka

"Kwana uku na ba ki , ki yanke ma rayuwarki hukunci. Kwana uku kacal."

Ya faɗi haka sannan ya raɓa ta gefen ta ya bar falon, nan ƙasan cafet Ummu ta durƙushe tana mai fashewa da kuka, ji take yi kamar ba ita ba zuciyarta na zafi kirjinta wani abu ya tokare mata da ya kasa wucewa kuka  ya sake kece mata, tunani take yi ko Habib ya fara shaye-shaye ne yau wata ƙila ya sha wacce ta fi karfin ƙwakwalwarshi shi ne ta faɗa masa ba daidai ba, amma ta ya ya zai ce ta zubar da cikin jikinta cikin sunna ba ta taɓa jin maganar da ta ruguza zuciyarta kamar wannan mganar ba, me mganganunsa suke nuna mata! Me ya sa ta ji zuciyarta na yi mata rawa akan Habib? Me ya sa yau ya sauya mata? Me ya sa zai yi haka?

Kuka take yi kamar ranta zai fita, tana kuma dafe cikinta da ta ji wani kaunar shi na ratsa jinin jikinta, tun tana gida ita mai sha'awar yara ce duk in da ta ga yaro sai ta ji da man na ta ne, ɓarin ta na farko kuka ta dinga yi sai da Ummin ikki ta yi ta lallashin ta. Ammah kuma faɗa ta dinga mata da cewa ba Allah ne ya ba ta ba, sai ta yi haƙuri shi zai sake ba ta wani, to ga Habib na faɗin da man ko cikin bai bare ba za a zubar da shi, an ya yana cikin hayyacinsa kuwa ita ce fa Ummu-Salma da ya ke so kamar ransa, ita ce matarsa da ya ke burin ta zama uwar ƴaƴan shi, me ya sa yanzu zai zo yana wasu mganganu?

Ta kasa gano dalili, ta fi tunanin wani abu Habib ya sha da ya birkita masa tunani amma a cikin hayyacinsa ba zai ce ta zubar da gudan jininsu ba. Wataƙila zuwa da safe zai dawo hayyacinsa ya ba ta haƙuri ya fahimci kuskuren da ya yi, ita kuma za ta yafe masa ta rufe mganar nan har duniya ta naɗe ba wanda zai ji

"Habib na shaye-shaye ne?

Wata zuciyar ta tamabaye ta, ko ba ya yi wataƙila dai jiya ya fara haka ta ba ma kanta amsam yunwa ta ke ji, amma ta kasa iya saka ma cikinta komai anan saman cafet ɗin ta kwana sai gabda asuba ta koma ɗaki, ta iske Habib na ta barci sai ta lallaɓa ta kwanta a gefen shi tana sauke ajiyar zuciya idanuwanta sun kumbura saboda kuka da man ita mai saurin kuka balle ta samu dalili, cikin lokaci barci ya kwashe ta duk da kanta na ciwo ba ta tashi ba sai da ta ji ƙaran ruwa a banɗaki sannan ta san asuba ta yi. Habib ne ya fito sanye da jallabiya ko kallonta bai yi ba ya saka hula ya fita zuwa masallaci.
Ita kuma daƙyar ta lallaɓa itama ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta ta da salla.

Ta idar kenan Habib ya shigo jallabiyan jikinsa ya cire daga shi sai ƙaramin wando ya koma ya kwanta. Ita kuma sai da ta gama addu'o'in ta sannan na nannaɗe darduman ta ijiye ta tare da hijabin nan saman side drower na gadon. Habib idanuwansa biyu yana latsa wayarsa yau asabar ba fita aiki.

"Ina kwana Noori."

Kamar bai ji ba sai da ta sake maimaitawa sannan ya amsa da lafiya kamar ba ya so har yana juya mata baya.
Ajiyar zuciya ta sauke ko a cikin Sujjadan ta sai da ta roƙi Allah ya dawo da hankalin Habib jikinsa ita fa a tunanin Habib ba ya cikin hayyacinsa ne.

Gefen sa ta koma ta kwanta tana cigaba da saƙe-saƙe.
Saboda rashin barcin da ba ta yi ba ya sa ta ji barci na shirin fizgan ta sai dai me? Kamar a mafarki ta ji Habib ya matso kusa da ita, yana shafa ta sai da ta yi mirmishi a fili a tunanin ta Habib ya dawo hayyacinsa ne tuni ta zage ta bashi dukkan halin kai, da a ce Ummu ta san manufar Habib a kanta da ko sama da ƙasa za su haɗe ba za ta sake ba shi jikinta ba.

Da safiyar ma da ta ɗumama musu taliyar ya ci sai ta dafa musu ruwan tea suka haɗa da shi, kuma a gida ya yini bai fita ba duk da bai sakar mata fuska ba amma in ta yi masa mgana zai amsa sai dai ba cikin walwala ba, sai dai yinin nan da ya yi a gida Ummu-Salma ta gane ba ta da wayau ita ya yi ta moruwa ita kuma jin daɗi take yi a tunanin ta ya bar wancan mganar ganin bai sake yi mata ba, har wani zumuɗin ba shi haɗin kai ta ke yi yana ta murzanta ko tausayi ba shi da shi a kanta alhalin a daran ranar ma ta ci abinci kenan ta amayar da shi duka kuma bai saka ya ɗaga mata ƙafa ba. Haka ma washegari a gida ya yini sai da yamma ya samu fita shima bayan duk ya gana sakar mata gajiya, Ummu ba ta damu ba tuni ta manta da mganar Habib a tunaninta ya dawo cikin hayyacin sa ya bar mganar, tun da kuma ta ga yana cin abincinta sannan yana neman ta a shimfiɗa sai ta yi tunanin addua'nta ce ta karɓu Habib ya dawo cikin hayyacinsa. Shi ya sa ma ba ta yi mganar da kowa ba hatta Bestie ko da ta kira ta a ranar lahadi suka daɗe suna magana tana ta tambayanta.

"Bestie kina dai lafiya ko?

Ita kuma ta ba ta tabbacin lafiyan ta ƙalau, a tunaninta ta rufe mganar ba wanda zai ji.
Sai dai abin da ba ta sani ba Habib zai yi silan tarihin auren ta da shi zai zama abin tunawa gare ta da ahalinta na har abada.

Abin da ba ta sani ba game Habib, ko ta manta ya ce lokaci ya ba ta. Wataƙila yana jiran cikar wa'adin kwanakin da ya ɗiba mata ne"

****

Monday.

Tun a daren jiya da zazzaɓi ta kwana da asuba ma sai da ta yi amai amma a haka Habib ya neme ta, ta fara jan jikinta da wannan rashin tausayin da Habib ke nuna mata. Za ta gama yin Amai amma sannu Habib ba zai ce mata ba.

Yadda ya ke son ta ta ɗauka tare za su yi wannan laulayin amma sai ta ga aka sin haka.
Ya ganta kwance cikin bargo tana rawan sanyi amma ya ce ta tashi ta sama masa abin karyawa, haka nan ta tashi tana makyarkyata ta fita zuwa kitchen buredi ta gasa masa a ovean ta dafa ruwan zafi ta so ko ƙwai ta soya masa amma ta kasa sai ta haɗa masa da sauran cake ɗin ta yi bai ida ƙarewa ba.  Ba ta ma tsaya ba ta koma ta kwanta shi kuma sai da ya ci ya yi nak sannan ya fita ba tare da ma ya yi mata sallama ba.

Haka Ummu ta yini kwance da zazzaɓi sai can zuwa yamma ne ta ji sauƙi tun da ta sha paracetamol komai babu a cikinta ruwan lipton ta dafa ta sha sannan ta yi wanka ta ji ta ɗan samu sauƙi. Shi ne ta rarrafa ta yi ma Habib friederice mai nama tunda ba ta da hanta, abin ya ba ta mamaki ganin da wuri yau ya dawo tun kafin isha'i
Sai da ya ci abinci sannan ya fita sallar isha'i kafin ya dawo Ummu ta sake yin wanka duk da ta na jin kamar zazzaɓin zai dawo mata tana jin sanyi-sanyi.

Sai ta saka wata doguwar riga ta haɗa da rigan sanyi saboda ta fara rawan sanyi. Komawa ta yi ta kwanta ta rufa da bargo saboda har kanta sara mata yake yi, Habib na dawowa ya biyo ta har cikin ɗakin ganin ta a kwance bai sa ya yi tunanin ba ta da lafiya ba kawai sai ya saka hannu ya yaye bargon da ta rufa da shii.

A kasalance Ummu ta ɗago tana kallon shi.

"Ta shi mu yi mgana."

Ya faɗa a kausashe.

"Noori ba ni da lafiya zazzaɓi na ke ji."

Ta faɗa cikin rawan sanyi tana ƙoƙarin sake jan bargon ta rufa ya fizge cikin mamaki ta kalle shi kafin ta samu damar magana ya tare ta da cewa.

"Kin manta da maganar mu ne?

Gaban Ummu-Salma ya faɗi ras!. Cikin rawan baki da na jiki ta ce. "Wa ta maga na."?
Ta faɗa cikin mutuwar jiki, maganar cikin ne! Kar dai a ce Habib bai manta da mganar nan ba, kar dai a ce yana kan bakan shi.

"Kin manta ne? Mganar da muka yi da ke ranar. Da man kwana uku na ba ki ki yi tunani ki yanke shawara, yau kuma cikon kwana uku shi ya sa na ce ki ta shi ki faɗa mini matsayar ki "

Ummu ta ji kanta ya sake sarawa da ƙarfi da man kaɗan kaɗan yake ɗan sara mata. Maganar Habib ya sa ta ji kamar gefen kanta zai cire kallon Habib take yi cikin mamaki da gaske ya ke yi?

"Me kika yanke? Za ki zubar ko a'a?

Ya faɗa yana mai kallonta.

Ummu ta runtse ido kafin ta buɗe tana mai dafe kanta.

"Habib wai da man da gaske kake yi?

"Wasa na ke yi miki?

Ya katse ta a fusace.

"Na ɗauka ba ka cikin hayyacinka ne."

Ummu ta faɗa masa ido cikin ido saboda tana so ta samu tabbacin lafiyan Habib ƙalau.

"Au kin ɗauka na fara shaye-shaye ne?

Ya faɗa cikin riƙe haɓa, ita kuma Ummu sai ta ma yar da kanta a saman fito ta ma kasa magana mamaki take yi wai da gaske wannan abin da ke faruwa da gaske yake faruwa!


"Ummu-Salma."

Ya kira sunanta ta amsa ta na mai sake ɗagowa a lokacin ita gani take yi wasa ne ba gaskiya ba ne abin da ke faruwa.

"Kin ga wasa a magana ta ne?

Shuru ta yi masa ba ta yi mgana kawai sai ta ji ya daka mata wani matsanacin tsawa har sai da ta firgita

"Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login