ENGLISH DESCRIPTION
DACEWA
When East Meets West
Aneesah has everything every woman dreams of. A devoted fiancé, a respected family, loyal friends, and a wedding only hours away.
Then, in a single night, everything falls apart.
The bride disappears on the eve of her wedding. When she returns, she brings back pain, tears, and accusations that threaten to destroy her future forever.
The love she trusted begins to crumble. The people she believed in start turning against her. The man who should protect her faces the greatest test of his life, while another proud and mysterious man enters her world in a way no one could have imagined.
Will truth overcome lies?
Can a broken heart learn to trust again?
What happens when East meets West in a life where love, tradition, pride, and destiny collide?
HAUSA DESCRIPTION
DACEWA
Lokacin da Gabas ta Haɗu da Yamma
Aneesah tana da komai da kowace budurwa ke mafarki. Kyakkyawan saurayi mai sonta fiye da komai, iyali masu daraja, abokai na gari, da kuma bikin auren da ya rage sa'o'i kaɗan ya tabbata.
Amma cikin dare guda, komai ya rushe.
An sace amarya a daren daurin aurenta. Da ta dawo, ta dawo da raunuka, hawaye, da zargin da zai iya lalata rayuwarta har abada.
Soyayyar da ta gina tsawon lokaci ta fara girgiza. Mutanen da ta yarda da su suka fara juya mata baya. Wanda ya kamata ya kare ta ya shiga cikin mafi wahalar jarabawa, yayin da wani mutum mai cike da girman kai ya shiga rayuwarta ta hanyar da babu wanda ya zata.
Shin gaskiya za ta yi nasara akan ƙarya?
Shin zuciya za ta iya sake amincewa bayan cin amana?
Me zai faru idan Gabas da Yamma suka haɗu a cikin rayuwa ɗaya, inda soyayya, al'ada, girman kai, da ƙaddara suka yi karo?