Follow us on social media
Showing 93001 words to 96000 words out of 147042 words
Chapter 32 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
ta da ƙawarta Shamsiya tun suna yara. Kamar yadda aka san Shamsiya a gidan su Ummu haka aka san Ummu Salma a gidan su Shamsiya duk da mahaifiyarta ta rasu tun tana ƙarama matar mahaifinta da suke kira Anty ke riƙonta.
Da za ta tafi bayan ta yi ma Ammah sallama ta ce ta gaida mutanen gidan.
"Ammah don Allah ki yi haƙuri da maganganun da na yi ɗazu ba ki fahimce ni ba ne ba da wata manufa na yi maganar ba na damu da abin da ya faru da Ummu Salma sosai Ammah."
Shamsiya ta faɗa bayan ta duƙa har kasa a gaban Ammah.
Ammah ta yi mirmishin su manya kafin ta ce" Kar ki damu na fahimce ki. Ki gaida gida mun gode."
Har haraba Ummu Salma ta raka ta. Direban gidan su da ya saba kawo ta shi ne ya zo ɗaukan ta.
Sai da suka tafi sannan Ummu dawo cikin gida ta iske Ammah na zaune a falonta kamar yadda suka bar ta.
"Har ta tafi?
Ammah ta tambaya tana kallon Autar na ta
"E ta tafi Ammah."
Ta faɗa a sanyaye cikin dashewar murya kamar ba ta son magana. Sai Ammah ta ɗan gyaɗa kanta amma ba ta yi magana ba.
Shuru na wani lokaci Ummu na tsaye ita ba ta koma ɗaki ba sannan ita ba ta zauna ba Ammah na lura da ita amma ba ta nuna alamun ta fahimci tsayuwarta a wajen ba sai ma ta yi kamar hankalinta na wajen tibin da yake ta ɓaɓatu. Nan ko tana lura da duk motsin Ummun, tana kare mata kallo daga tsaye har cikinta ga shi nan ya fara turowa ta cikin doguwar rigar dake jikinta amma fa Ummu ta zube ta rame duk ta lalace kullum sai jan fuska da kumburarrun idanuwana saboda kuka, tausayinta take ji in ta kalleta sai ta tsine ma Habibu tsinuwar da ba ta so ya koma ga Allah bai ga sakayya tun a duniya ba.
"Ammah."
Ummu Salma ta kira sunan Ammah, ba ta amsa ba amma ta ɗago tana kallon ta.
Sai kuma ta yi shuru ta kasa magana.
"Me ya faru?
Ammah ta tambaya tana mai tsare ta da idanuwanta lura da cewa kamar akwai magana a bakin ta.
"Da ma Ammah.."
Sai ta yi shuru ta kasa mgana.
"Dama mene ne? Wani abu kike so?
Ammah ta tambayeta cikin kulawa.
"Aa dama mganar da kika ji Shamsiya na yi ne."
"Uhm sai aka yi ya ya?
Ammah ta faɗa har lokacin ba ta daina kallon ta ba.
Sai Ummu ta daburce kafin ta fara mgana tana in da in da.
"Da ma, zan ce ne kar ki ji haushin ta, ba da wata manufa ta faɗi haka ba."
"Madallah."
Ammah ta yi saurin katse Ummu Salma saboda ba ta son ma tana tuna mganganun yarinyar suna kona mata rai, suna sakawa tana jin kamar yarinyar za ta fita daga zuciyarta. Ta so ma ta ce mata in saboda su ko Ummu take kiran Habibu to kar ta sake sai kuma ta ga kamar ta yi tsauri da yawa shi ya sa ba ta yi maganar ba, amma sam maganganun yarinyar ba tausayawa ga halin Ummu ke ciki sam.
Ummu Salma ta gaji da tsayuwa, ganin Ammah ta yi mata banza daga ƙarshe ma cikin ɗakinta ta shiga ta ce za ta yi salla dole itama ta koma ciki ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta tayar da salla. Bayan ta idar sai ga Baffa da Hamma Saddam sun shigo falon Ammah, sai ta fita falon ta duƙa ta gaishe da Baffan tun da tun safe sai yanzu suka sake samun zama
"Auta ya karfin jikin?
Kanta na ƙasa tana sanye da hijabinta dogo da ta yi salla da shi ta amsa cikin sanyin murya.
"Na ji sauƙi Baffa."
"Kin tabbata ba in da ke yi miki ciwo?
Sai ta gyaɗa kanta sannan ta amsa da cewa ba in da ke yi mata ciwo.
"To Baffa ka tambayeta tana cin abinci?
Hamma Saddam ya faɗa yana yar dariya, da a baya ne harara zai sha a wajen Ummun amma yau kallon shi kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba.
"Tana ci mana ko Auta?
Ya tambaya yana kallon ta.
"Ina ci Baffa, yau ma ba ka ga taliyan da na ci ba."
Ta faɗa da ɗan mirmishi. Sai ta ga Baffa na dariyan jin daɗi da man abin da take son gani kenan.
"Madalla da Auta. Sannun kin ji? Allah ya raba ki da cikin jikin ki lafiya."
Kanta na ƙasa ta amsa da Amin a cikin zuciyarta, sai dai idanuwanta sun cika da kwallar tausayin kanta da na iyayenta.
"To gwara dai ki riƙa ci Ummu ko za ki yi kumari, kin gan ki kuwa? Kin ga ƙasusuwan da ke wuyan ki kuwa?
Ya faɗa yana yar dariya cikin zolaya sai a lokacin ta ɗan murmusa kanta na ƙasa.
"Kyale shi Auta. Za ki yi kiba har sai ya ce ki bar ta yi yawa."
Ita dai kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabinta. Baffa da Hamma Saddam suna ta hiran su, lokaci bayan lokaci suna ɗan sako ta a ciki koda ba za ta yi magana ba har Ammah ta idar da salla ta fito suka cigaba da hiran tare.
"Yaushe hutun na ku zai ƙare ne Saddam?
Baffa ya tambaye shi, kai tsaye ya ce sati na sama za su koma zai bari sai upper week sannan zai koma makaranta. Baffa da Ammah suka yi masa fatan alherin da suka saba a koda yaushe suna nan zaune suna hira har aka kira sallar isha'i Baffa da Saddam suka tafi masallaci itama Ammah ta shiga ciki domin ta gabatar da na ta, sai ita ma Ummu Salma ta tashi ta koma ciki tana da alwalanta ta tayar da salla.
Bayan ta idar ta fita tsakar gida zuwa kitchen ta zubo taliya ta ciko miya saboda cikinta kamar an yi yasa yanzu tana yawan jin yunwa sosai ba kamar baya ba.
Tas kuma ta cinye tana suɗan kwano, har Hamma Saddam na yi mata dariya Baffa ya ce in bai isheta ba ta je ta ƙaro ta ce ta koshi da yake a falon Ammah ta zauna tana cin taliya su kuma suna dawowa masallaci nan suka sake yada zango.
Har wajen goma na dare tana falon tare da su Baffa suna ta hira, ita dai ba ta magana amma kuma zama cikin su yana rage mata damuwa da shiga tunani da ɗaki take shigewa zuwan Mami ne yasa dolenta ta fara fitowa falo. Sai da ta fara hamma wajen sha ɗaya saura na dare sannan Baffa ya ce ta je ta kwanta Hamma Saddam ma ya yi musu sai da safe ya wuce ɗakin sa. Ummu kuma bakin ta kawai ta wanke ta sha magungunanta ta kwanta ba daɗewa sai barci.
Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya da daɗi ba daɗi. A bangaren Ummu Salma rayuwa ba daɗi amma tunda ita musulma ce ta yarda da kaddara kuma tunda tana da rai da lafiya dole za ta cigaba da rayuwa a hakan nan, ta ɗan rage kuka yanzu amma duk lokacin da ta tuna sai ta koka ita kaɗai a ɗaki ta yi kukanta har sai ta ƙoshi sannan ta share hawayenta ta dangana tunda ba ita isa ta mayar da hannun agogo baya ba. Mai afkuwa ta afku ba ta kuma da yadda za ta yi ta gyara abubuwan da suka riga suka lalace tun daga farko.
Har yau kuma Ummu ba ta bi ta kan wayarta ba, tana nan a kashe a cikin kayanta. Duk wanda zai yi magana da ita sai dai ta wayar Ammah. Baɗɗo ce ta ce ta ɗauko wayar ta dawo amfani da ita wataƙila za ta deɓe mata kewa, amma ina ba za ta iya sake amfani da wannan wayar ba matuƙar akwai abubuwa da dama da za su iya tuna mata da Habib da irin rayuwar da suka yi mai daɗi a baya shi ya sa ba ta jin za ta iya amfani da wayar a yanzu in ma za ta yi amfani da waya sai dai sabuwar waya da sabon layin da ba zai tuna mata da komai ba.
In ta zauna tana tunanin farkon rayuwarta da Habib har zuwa ranar ƙarshe da komai ya ƙare. Sai ta ji da man ace ba ta san shi ba, domin sanin shi bai ƙare rayuwarta da komai ba sai ci baya. Ya shigo rayuwarta domin ya lalata mata gobenta kuma ya yi nasara. me take yi haka? me ya sa ta kasa tsanar Habib? me ya sa ta kasa mantawa da shi? me ya rage mata, ba ta da komai domin bai bar ta ba sai da ya ƙwace duka martabanta ya lalata mata rayuwarta ya juya baya ga gudan jinin su? me ya sa ba za ta yanke tsammani ba, ba ta da wani abu da zai sake jan hankalin wani namiji a kanta HABIB ya riga da ya lalata duk wani ƙwanjinta akan ko wani namiji a duniyar nan.
****
* SATURDAY:MURIVILL HOTEL YOLA, ADAMAWA OFF GIREI ROAD.
ROOM:226.
*8:21Pm*
Habib ne tsaye a gaban madubin dake ɗakin Hotel ɗin da ya zama gidan shi a halin yanzu tun bayan rabuwar su da Ummu Salma.
Turare yake fesawa bayan ya gama ya ɗauko wata hula baƙar dara ya ɗora saman sumar kansa da ta sha gyara tunda ya ɗan tara suma. Jikinsa kuma wata farar shadda ce tana maiƙo da yarari daga ganin ta ma sabuwa ce yau ya taɓa sakata saboda yadda take maiƙon sabunta.
Kallon kansa kawai yake yi a madubi yana mirmishi shi kaɗai saboda yau ranar ta musamman ce a gare shi da abar ƙaunarsa. Yau ne rana ta farko da za ta gabatar da shi a wajen mahaifinta a matsayin wanda take so kuma take mafarkin aura. Gabaɗaya jin sa yake kamar yana yawo a saman gajimare saboda tsabar farinciki. Ya saka kaya sama da kala goma ba su dace da ranar yau ba, ga su nan duk ya zube su a saman gadon dakyar ya samu waɗanan na jikinsa suka dace da yanayin yau ɗin.
Agogon fata baki ya saka a tsitsiyan hannunshi na hagu yana sake kallon kanshi a madubi yana sake yin sakin ɗan mirmishi. Ya ɗauko wani bakin booth ɗin takalmi yana sakawa kenan aka kira wayarsa tun kafin ya duba ya san ita ce domin sun yi magana da ita bayan ya fito wanka ya tabbatar mata da mintina goma zai gama shiryawa ya fito.
Sai da ya gama saka takalmin sannan ya ɗauki wayar dake gaban madubin farinciki ya sake dabaibaye shi ganin ita ce ta kira shi.
"Gani nan zuwa Sweety."
Ya faɗa cikin wani amo bayan ya ɗaga kiran.
"Kar ka bar ni na saƙe wajen jiran ka Habib."
Daga can bangaren ta faɗa cikin muryan shagwaɓa.
"Gani nan zuwa In sha Allahu."
Daga haka suka yi sallama, suna katse wayar ya turata cikin aljihun wandonsa tare da wallet ɗinsa bai tsaya kwashe kayan da ya watsar a tsakiyar ɗakin ba ya suri key ɗin motar shi da na ɗakin ya fice bayan ya rufe ƙofar ya tura komai cikin aljihun wandon sa ya sauka ƙasa zuwa haraban hotel ɗin suna ta gaisawa da ma'aikatan wajen a wattani biyun da ya kwashe a hotel ɗin ya saba da duka ma'aikatan wajen ba laifi, Tun ballanta ƴan ƙananun kyatttukan da yake yi musu, yau ma saboda yau ɗin rana ce ta musamman a wajen shi. motarsa ya shiga da yau ya kaita wanki ta yi fess yadda motar take fess shima haka yake fes, ya fiddo kuɗin sabbi yan ɗari biyar biyar ya kira wani ma'aikacin hotel ɗin yana daga cikin masu kula da tsaftan ɗakunan Hotel ɗin sunan su ɗaya shima Habibu sunan shi, kuma in dai ya ga Habib ya yi ta masa kirari kenan shi ya sa tasu ta zo ɗaya.
Kuɗin sun kai 20k ya ba ma Habibu ya ce ya raba shi da sauran ma'aikatan gabaɗaya.
Har ƙasa ya duka yana godiya lokaci ɗaya yana masa kirarin da ya saba.
"Allah ya taimake ka ranka ya daɗe Allah ya ƙara arziƙi da wadata."
Habib ya yi dariyan nishaɗi kafin ya ce" Amin Habibu na gode da addu'arka kamar ka san yau rana ce ta musamman a waje na."
"Allah ya kara maka farinciki da wadata Megida."
Ya riƙa amsawa da Amin kafin ya rufo motar ya daidaita zaman shi sannan ya tayar da motar ya yi riverse ya yi hon megadi ya buɗe masa get ya fita, yana tafe yana jin nishaɗi har redion motar ya kunna da wakar Auta waziri yana tafe yana kaɗa kai kamar wani kadangare.
Tun a daran ranar da ya saki Ummu Salma bai yi barci ba sai da ya gama haɗa dukkan abin da yasan mallakan shi ne gari na wayewa karfe shidda na safe ya kwashe komai zuwa mota ya bar gidan. Yadda suka rabu haka yake so alaƙarsu ta ƙare na har abada.
Hotel ya je ya kama ya saka kayan shi a ciki, tunda gidansu yanzu ba shi da mazauni kuma ba shi da in da zai je ya zauna, gidanshi da yake ginawa ba a gama ba, gidan da Ummu Salma ta yi ta mafarkin shi a matsayin ita ce za ta shige shi abin da ba ta sani ba bai kafa ginin gidan nan da sunan ta ba sannan zanen gidan ma ba zaɓin ta ba ne na masoyiyarsa ne da suka shirya sabuwar rayuwa tare, an kusa gama ginin gidan tunda yanzu tayels ake sakawa na ɗakuna da tiolets da an gama za a yi filista da fenti shike nan shi kuma a yadda yake so bikin shi kar ya wuce wata biyu saboda ya ƙosa ya mallaki masoyiyarsa sannan yana son ya samu natsuwa. Tunda har yau za ta gabatar da shi ga mahaifinta an gama mgana, da man a cikin wata ɗaya ta bayyana shi a wajen iyayenta da y'anuwanta mata a matsayin wanda take so yana zuwa gidan su zan ce yau ne za su haɗu da mahaifinta. Jin sa yake yi kamar sabon haihuwa saboda farinciki kamar bai taɓa aure ba. To kamar bai taɓa ba ne domin Ummu Salma amfani ta yi masa kuma tunda ta gama amfaninta ya fitar da ita daga rayuwarsa, sai yanzu yake jin kansa sakayau kamar bai da wata damuwa. Duk da ya ɗan fuskanci ɓacin rai daga wajen Gwaggo da Abba Alhaji Sheriff amma duk ya jure.
Gwaggo haka ta yi ta masa faɗa bayan an ɗan lafa da faruwan lamarin ya je gidan, ba shi da masaniya amma ya san labarin rabuwansa da Ummu Salma zai je musu kuma zargin shi ya tabbata. Mahaifinsa dake kwance haka ya riƙa son ya yi magana da shi amma ya kasa sai kuka hawaye na ziraro masa ta gefe da gefen idanuwansa.
Ransa ya ɓaci ya yi baƙin ciki sannan ya sake jin tsanar Ummu Salma a cikin zuciyarsa. Sanadiyarta iyayensa sun yi fushi da shi. Gwaggo ma sai da ta yi kwanaki ba ta amsa gaisuwarsa har ƴan'uwansa mata wasu sun nuna ba su ji daɗin abin da ya aikata ba shi kuma sai ya ce ai ita ce ta ci ƙwalan shi ta ce in ya cika haihuwan uwarsa da ubansa ya saketa shi ne ya sake ta. Wasu dai sun yarda wasu kuma ba su aminta da maganganunsa ba, kamar Gwaggo da jinsa kawai take yi ta san ya faɗa ne domin ya kare kansa. Haka ya yi ta zuwa Gidan Alhaji Sheriff kusan sau uku amma ba ya ganin shi ya ƙi bari ma su haɗu kwata-kwata, amma duk da haka bai haƙura ba sai ya bi ta hannun Baba Usman da lallashi da daɗin baki ya samu shi ya saurare shi, duk ya ɓata ma Ummu Salma suna a idanuwansa da cewa ba ta da tarbiya rashin kunya take yi masa shi ya sa ya sake ta kuma ma ita ce ta neme sakin, Baba Usman ne ya shiga tsakiya ya sulhutansu da Alhaji Sheriff ya kuma haɗa su waje ɗaya suka yi magana. Habib ya duka yana ta bashi haƙuri Baba Usman na kora wajibin cewa yarinyar ce ashe ta ce sai ya sake ta shi dai Alhaji Sheriff jin su kawai yake yi yasan ƙarya Habibu yake yi ya dai faɗa ne domin kawai ya samu hanyar kare kan shi.
"Koma mene ne wannan ya zama tarihi tunda ya sake ta ta koma gidansu magana ta kare. Habibu kai ba yaro ba ne daidai gwargwado kana da ilimin ka, ka san abu mai kyau da aka sin shi. To ka sani in har kai ne ka yi zalunci Allah ba zai barka ba, in ma ita ce ta zalunce ka duk Ubangiji na gani kuma zai yi ma duk wanda aka zalunta sakayya"
Abin da ya faɗa masa kenan a lokacin da ya sake rankwafa yana sake bashi haƙuri sai ya ɗaga masa hannu yana sake faɗin.
"Ni fa ba ka yi mini komai ba Habibu. Ka je kawai Allah ya kyauta na gaba."
Duk da haka bai haƙura ba yana zuwa gidan shi sannan yana kiran shi a waya har dai ya samu ya ɗan sauko daga fushin da yake yi da shi, shi da man burin shi kenan saboda nan da lokaci kaɗan amfanin su zai ta shi kuma in babu su ba zai samu cikar burin shi ba shi ya sa bai gaji ba sannan bai sare ba, Baba Usman ma duk ya siye shi da kuɗi sannan haka ya yi siyayyan kayan abinci ya kai masa, gidansu ma duk ya kashe bakin su da kuɗi suma ɗin kayan abinci ya siya musu duk da daman ya saba yi, yan'uwansa mata kuma duk ya kashe bakin su da kyauttuka har Gwaggo ma bakin ta ya yi shuru shike nan babin Ummu Salma ya kare a gidansu da zuru'an su gabaɗaya yanzu ne zai sake buɗe ma rayuwarsa wani sabon shafi.
Kai tsaye anguwar Barraks road ya nufa, ya yi parking ɗin motarsa a wani babban gidan bene mai makeken bakin get. Bai yi hon ba sai da ta ya kira ta ya ce ga shi nan a ƙofar gida sai ta ce kawai ya shigo gata nan fitowa. Sai a lokacin ya yi hon megadi ya leƙo shi kuma sai ya zuge gilsshin bangaren da yake zaune ya gane shi baƙon gidan ne tunda yana zuwa kuma ya