Follow us on social media
Showing 126001 words to 129000 words out of 147042 words
Chapter 43 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
ganni ya san ba sonki yake yi ba sha'awarki ya ke ji, tun a lokacin muke tare muna soyayya a ɓoye, saboda ke ba zan hana zuciyata abin da take so ba Ummu Salma."
"Me ya sa to ya aure ni baI aure ki ba?
Ummu ta samu karfin gwiwan tambayan Shamsiya domin ko hawaye ma ba ta ji ya kawo mata ba zuciyarta ke suka tana hasaso mata wasu abubuwan, au da man Shamsiya ce masoyiyarsa da yake ta magana a kanta ita ko me ta yi ma su Habib da suka zaɓi su yi mata wannan yankar ƙaunar.
"Ina son Habib ina son abin da zai saka shi farimciki. Yana tsananin sha'awarki kuma yana so ya kauda wannan sha'awar ni kuma a gida ba za a bari na yi aure a lokacin ba. Shi ya sa na ba shi daman ya aure ki amma na shekara ɗaya ya yi amfani dake son ranshi ya sake ki zuwa lokacin ni kuma na shawo kan matsalata a gida. Mun yi da shi ba zai bar ki ki samu ciki ba, amma sai da kika ɓata mana plan din mu."
Nan ta shiga ba ta labarin duk yunkurin zubar da cikin da Habib ya yi mata da saninta domin tare suke shirya komai.
"Ki ma gode ma Allah na baki aron shi, ki kuma jinjina mini yadda na bari kika fara ajiye ƙwaan Habib a mahaifarki kafin ni, saboda haka godiya ya kamata ki yi mini Ummu domin na ba ki aron abin da na fi so a duniya."
Ta gama faɗa tana fuskanta ta. Ummu ta yunƙura ta miƙe tana jin ɗan cikinta na haɗewa waje ɗaya saboda halin da ta ke ciki, cikin ido ta kalli Shamsiya kafin ta ce" Ai ban neme da ki ba ni aron shi ba Shamsiya. Me ya sa kuka yi mini haka? Riban me za ku samu?
Ta faɗa cikin soyewar zuciya.
"Na samu riba, domin Masoyina ya biya bukatarsa, ni ma kuma na samu nawa biyan bukatar, ga shi za mu yi aure."
"Shamsiya mijin da na au"
"Haramun ne? Ai ya sake ki, kuma ko bai sake ki ba zan iya auransa in na ga dama. Amma ni ba zan iya zaman kishi dake ba shi ya sa nace ya sallame ki daga rayuwar mu."
"Da man ba don Allah kike tarraya da ni ba?
"A baya don Allah na ke zaune dake amma daga lokacin da kika auri Sweety na tsane ki Ummu Salma."
Ta dakata tana kallon Ummu da ta koma tana mirmishi kamar mahaukaciya
"Kuma na ja baya dake ne saboda bana son alaqar mu, bana son ki a rayuwata. Ki je ki cigaba da rayuwarki amma ki manta da kin taɓa sanina ballatana Habib. Mu zama kamar mun shuɗe daga tunanin ki."
Ummu ta girgiza kai ba za ta iya fassara a yanayin da ta ke ciki ba.
"Sannan kar ki damu kaf dangina ba su nan kin auri Habib ba, sun san shi ne kawai a matsayin sa na mijina."
Ta faɗa tana kashe mata ido ɗaya cikin dariyan shaƙiyanci.
"Na gode, da man tabbacin nake son sani tunda kuma na same shi daga wajen ki ba komai."
Ummu ta faɗa cikin aro jarumta.
Kawai sai ta juya za ta bar ɗakin tana jin maranta na daurewa a waje daya, ga ɗakin na juyawa mata amma ta daure.
"Ba ki ji ba."
Ummu ta juyo tana kallon ta.
"Na so ki zubar da cikin nan, watakila da kin iya samun wani wanda zai kwashe ki, amma kika yi taurin kai ki ji be ki fa yanzu? Wa zai kwashi bazawara mai ɗa, ɗan ma mai kama da ɗan shege tunda uban cikin ya ce ba ya so"
Ta gama faɗa tana kwashewa da dariya har tana tafa hannuwanta
Juyawa kawai Ummu ta yi ta fice daga ɗakin tana jan kafa, ita dai ta san ta bar gidan ta kuma yi tafiya mai nisa a hanya kafin ta samu abin hawa.
Ta san kamar hankalinta ya gushe domin ba ta ma san har ta faɗi sunan anguwarsu ba, ita dai an sauke ta a bakin titin gidansu ta sauka ta ba shi kuɗinsa sannan ta yi tafiya zuwa gida da kafafunta.
Ba ta kuka ba ta komai amma tana ji kamar yau za ta bar duniya.
Masallatan anguwan har sun idar da sallar isha'i wasu ma sun daɗe da idarwa.
Ta shiga gida ba ta damu da Ammah ko Baffa su ganta ba.
Ba ta damu da su tuhumeta ba.
Kawai ta faɗa ne kai tsaye.
Hamma Lamiɗo na tsaye wajen ɗakin Baffa yana waya ya juya baya. Ba ta san shi ba ne sai da ya juyo shima ya ji ana ta jefa kafafuwa ne yaraf yaraf shi ya sa ya juyo.
Ido huɗu suka haɗa domin akwai hasken wuta a tsakar gidan.
Mamakin ganinta yake yi ga ciki a gaba sannan yarkace-yarkace kamar ba ta cikin hayyacinta. Ta kalle shi cikin wani yanayi shi dai juyawa kawai ya yi ya cigaba da wayarsa ita kuma ba ma ta shi take yi ba da sauri ta faɗa falon Ammah.
Tana shigewa ya bi bayanta
Da kallo cikin mamakin me ya fitar da ita a cikin wannan daran? Me ya same ta ya ga kamar ba ta da lafiya. Duk da fa ya daɗe bai ganta ba, ba haka take ba.
Sai kuma ya yi tunanin watakila ciki ne ya mayar da ita haka.
Yana gama wayarsa ya koma cikin ɗakin Baffa abinci yake ci aka kira shi a waya ya ta shi.
Ammah kuma ta shiga ciki ta je yin sallah. Komawa ya yi gaban abincin shi Baffa na gefen shi da man Ammah ce ke hiran bayan ta tashi sai ɗakin ya yi shuru.
Shi Lamido da man bai iya hira ba shi kuma Baffa sanin halin shi ya sa bai ma bata bakin shi ba
Ammah na ɗakinta ta idar da salla ta ji kamar an shigo
Ta fito haka dai daidai lokacin da Ummu ta shige ɗakinta ta rufe kofa.
Sai Ammah ta ɗauka ita ce ta fito falo ta koma, domin ba ta san Ummun ba ta a gidan ba, bayan fitan ta Lamiɗo ya zo suna ɗakin Baffa gabaɗaya.
Daga nan kawai ta fice ta koma ɗakin Baffa.
Ummu ta sulale a kasan cafet tana jin zuciyarta na zafi kamar za ta mutu. Abubuwa suna gilma mata. Shamsiya da Habib.
Me ta yi musu da za su lalata mata rayuwarta haka?.
Shamsiya fa da suke ƙawance tun suna yara ita ce ta ci amanarta da namijin da ta ba ma Amanar rayuwarta.
So take yi ta daina jin zafin da ke ji a cikin zuciyanta.
So take yi duk wani damuwarta da take ji ta daina jin su, so take yi ta bar duniyan nan ko za ta samu yar salama.
Amsar kuwwan Kalaman Shamsiya sun kasa barinta ta huta, sun saka ta jin gwara kawai ta ji shuru gwara ta sama ma kanta natsuwan zuciya.
Miƙewa ta yi tana layi ta isa gaban madubi ta ɗauki reza sabuwa a cikin kwalinta ta buɗe. Rezan ba na ta ba ne na Ammah ne kwali ɗaya take siyab itama shekaranjiya cizgiya ne ya fito mata a gefen hannunta sai ta yi ma Ammah magana ta bata, bayan ta cire sai ba ta mayar mata ba sai ajiye a saman madubin ɗakin.
kallon kanta take yi a madubi tana tunanin yanzu rayuwarta ba ta da amfani hijabin jikinta ta cire ta na kallon cikin jikinta.
Ba amfanin ta haifa ma Habib yaro ko yarinyar dake cikinta domin bai cancanta ba, yadda zuciyanta ke zafi ne take son kawai ta hutar da kanta.
Ba tare da tunanin komai ba ta ciro rezan ta daidaita tsitsiyan hannunta na hagu za ta yanka lokaci ɗaya tana mai runtse idanuwanta hawaye na wanke mata fuska, sai ƙaran vibration ɗin wayarta ya dakatar da ita wayar na kan madubin ne, idanuwanta na ganin duhu amma sai da ta ga sunan mai kira, Sisna Baɗɗo ce take kiranta a lokacin da ba za ta saurare ta ba, a lokacin da ba za ta iya amsa wayarta ba.
Tana mai zubar ƙwallah wasu na fitowa wasu na ƙoran wasu ta sake daidaita hannunta
ta yanka sai ga jini ya tsartsu, ta runtse ido tana jin wani irin zafin azaba na ratsa ta daga ƙafafunta har saman ƙwaƙwalwarta.
Sake yanka hannun nata ta yi a karo na biyu jini ya sake tartsuwa, ta sake runtse ido sabo da azaba mai raɗaɗin da ya dabaibaye jinta da ganinta tana gani jininta na zuba a kan madubi yana gangarawa a kasan cafet da gudu kamar an buɗe famfo.
Azaba take ji amma kuma tana jin daɗi yanzu za ta daina jin abin da take ji a cikin zuciyanta. Gwara ta mutu in ta mutu za ta huta.
Tana mai kallon kanta a madubi tana hawaye ta fara ganin kanta biyu biyu kafin ta ji jiri ya kwashe ta, ta yi baya ta dafa gado amma ina ya rinjayeta, tuni idanuwanta suka hau lumshewa jikinta ya saki da ta kasa iya riƙe kanta
nan ta sulale ta faɗi kasa ta gefen hagu.
Hannunta kuma har a lokacin bai daina zubar da jini ba, ga rezan da ta yanka kanta nan a yashe a gefen ta
Ta ji daɗi domin jinta da ganinta ya tsaya cak zuciyarta ta daina aiki ta daina jin komai ta samu salaman da ta ke fata.
Ta ji ɗif, ta samu natsuwa ta samu hutun zuciyan da take muradi.
*1k on Telegram 09069067488*
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/GKzdnJ5Gb62IjjqT6AYpcC
No. 1 online shopping kenan inda zaku sami duk wani kaya da ku ke buƙata, tun daga kan kayan kicin, laceses, atamfofi, shaddoji kayan yara maza da mata ,da uwa uba magungunan supplements wadanda ba su da illa na manyan mata inda zaki fito ki yi das da ke ki zama abin sha'awa, ga kuma Arabian sabaya powder wacce baki taba cin karo da irin ta ba, ke dai maza shigo ki kwashi romon arziki a gidan mutunci da karamci a kai Miki kaya har inda ki ke babu fargaba.
*20*
*DAAMA SPECIALIST HOSPITAL*
NO:70 72 Abubakar Atiku Rd. Jimeta Adamawa.
VIP:Room 23.
Ta daɗe tana jin wucewar iska a cikin kunnuwanta. Sannan kanta ya yi mata nauyi sosai tana ji kamar an ɗora mata katon dutse, idanuwanta take so ta buɗe amma ta kasa ji take yi kamar an danne idanuwanta nata da wani abu mai nauyin gaske. Tana ta ƙokarin motsa gangar jikinta lokaci ɗaya da fitar da numfashi sosai amma ta kasa jikinta ya tamke, ko ɗan yatsanta ba ta iya ɗagawa sai ma take ji kamar wuyanta ya rabu da gangan jikinta ne. Sannan bakinta da wani abu an yi mata takumkumi da ya hanata damar iya sakin numfashi sosai.
Tana jiyo ɗan maganganu daga can nesa da ita amma ba za ta tantance komai ba, tana cikin kamar tsakanin rayuwa da mutuwa ne. Komai daga nesa take jin sa kamar ba a kusa da ita ba ne, tunani take ko dai ta mutu ne tana cikin kabari, tabbas ta mutu ƙasa ne ya danne ta da ya sa ta kasa motsa gangan jikinta.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Ta furta a cikin zuciyanta, tana ta ƙokarin buɗe idanuwanta ta kasa sai da ta daddage sannan ta samu nasaran buɗe kumburarrun idanuwanta da suka yi mata nauyi kamar an ɗora mata jakan duwatsu a sama, dishi dishi ta fara gani kafin ganin ta ya ɗan fara washe.
Farin POP ta fara cin karo da shi lokaci ɗaya da karamar farar fanka a sama tana gudu sosai, shi ne iskar da take jin ƙaran wucewarsa a a cikin kunnuwanta.
So take yi ta tuna abin da ya faru da ita amma ta kasa tuna komai, tunanin ta ya fi karkata da cewa ta mutu ne, to amma in har ta mutu to nan ba a cikin Kabari take ba, domin a cikin kabari babu rufin ɗaki sannan babu fanka.
A hankali a hankali ganin ta ya fara washewa. Daƙyar ta iya ɗan waiga damanta da hagunta, daga lokacin ne ta fahimci kamar tana asibiti ne domin a yanayin ɗakin ita kaɗai ne a kan ƙaramin gado sannan ta ga tsitsiyan hannunta guda ɗaya da ƙarin ruwa.
Me ya same ta? Me ta sa take kwance a asibiti?
Tana so ta yi tunanin yanayinta na ƙarshe amma ta kasa, kanta ya yi mata nauyi kamar ba na ta ba.
Tsil ta ji daga gefen cikin ta, sai ta ɗan daga idanuwanta, ciki ta gani ya yi tsini a jikinta gabanta ya faɗi ras! A lokaci ɗaya kuma tunanin abin da ya sameta ya fara dawowa cikin kanta daki daki.
"Hasbunallahi wani'mal wakeel."
Hawaye ne masu zafi suka fara gangaro mata ta gefe da gefen idanuwanta masu raɗaɗi sai a yanzu ta samu damar kuka sai a yanzu ne nadama da dana sani suka rufeta sai a yanzu ta ke tunanin da a ce ta mutu fa? Shike nan ta mutu a kafira sai a yanzu ta tuna da Baffa da Ammah, sannan sai a yanzu ne ta tuna da sauran yan'uwanta amma a lokacin idanuwanta sun rufe zuciyanta ta ƙuntata fatan ta kawai ta yi nesa da jin zafin zuciya da raɗaɗi burinta ta samu salama da raɗaɗin dake taso mata a cikin kasan zuciyanta. Amma ina haƙanta bai cimma ruwa ba, ga in da ta kare nan, wataƙila Allah ne yake son ta shi ya sa ya ba ta wata damar.
Ƙokarin tashi take yi amma ta kasa tana cikin wannan yanayin ne aka buɗe kofar ɗakin lokaci ɗaya wata nurse da fararen kaya ta bayyana a cikin ɗakin.
Cikin ruwan hawaye Ummu Salma ta ɗago kanta tana kallon Nurse ɗin da ta shigo.
"Laa kin farka?
Nurse ɗin ta faɗa tana kallon Ummu kafin lokaci ɗaya ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Ummu ta bi ta da kallo a tunaninta in ta ƙariso za ta ce ta taimaka mata ta zauna sannan ta cire mata wannan igiya mai takumkumi da yake hanata numfashi da magana.
Tana cigaba da ƙoƙarin tashi zaunen aka sake buɗe kofar aka shigo. Wannan karon ba iya mutum ɗaya ba ne, likita ne akan gaba sanye da rigansu na likitoci da zugan wasu Nurses guda uku daga bayansa ciki har da wacce ta fara shigowa da farko.
"Ma sha Allah"
Ta ji ya faɗa lokaci ɗaya yana ƙarisowa gaban gadon da take kwance.
Kallon shi ta yi da idanuwanta da suka shige ciki mamaki ta yi da jin abin da ya faɗa ba ta yi tunanin ma musulmi ba ne sai da ya sake magana sai ta sake shan mamaki.
"Sannu ko?
Ya sake faɗa yana kallonta da ɗan mirmishi a saman fuskar shi.
Bayan musulmi ne, ashe ma yana jin hausa ba ta ɗauka ma yana ji ba ganinsa jajir kamar bature.
Idanuwanta ta ɗan motsa tana cigaba da ƙokarin tashi ta zauna.
"Kina so ki zauna ne?
Ya tambayeta. Ita kuma sai ta lumshe idanuwanta ta sake buɗe domin ba zata iya ɗaga kan ta ba, ji take yi kamar kanta zai rabe gida biyu.
"Okay.."
Ya faɗa lokaci ɗaya ya kalli Nurse ɗin dake gefensa da ido kawai ya yi mata magana nan da nan sai gata ta nufo ta, ta saka hannu ta cire mata abin da ya tare bakinta daga magana da shakar numfashi da kyau.
Sannan kuma ta cire mata zaren karin ruwan dake tsitsiyan hannunta na hagu, amma ba ta cire canula ɗin ba sai a lokacin ma ta lura hannunta ya kumbura sosai watakila an yi ta fama kafin a samu jijiyar ne.
Hannunta na dama Nurse ɗin ta kama za ta ɗan dago ta, ita kuma sai ta yi amfani da hannunta na hagu ta ɗan dafa gefen gado lokaci ɗaya ta ji wani mugun zafi ya ziyarce ta har ƙwaƙwalwa.
"Wash..!
Ta faɗa cikin fitan hayyaci murya a dashe.
"Sorry, ki yi a hankali kin san left hand ɗinta akwai rauni."
Sai da ya faɗa haka sannan ta iya duba hannun nata na hagu, dai dai ta ɗan ɗagota ta zauna tana jin bayanta na sagewa saboda kwanciya.
Rabin hannunta na hagu yana nannade da bandeji ne, ƙura ma hannu ido ta yi tana kallo hawaye na sake biyo kumatunta kamar an buɗe famfo.
"Sannu ko?
Ta ji an sake faɗa sai ta ɗan dago tana kallon likitan lokaci ɗaya ta na ɗan gyaɗa kanta dakyar.
Kujera suka matso masa da shi wata fara ya zauna a gabanta, ɗaya Nurse ɗin ta miƙa masa Fayel ɗin Ummu Salma a hannun shi ya buɗe yana dubawa.
"Ummu Salma Hadi Baba right?
Dr. Ahmad ya faɗa yana sake kallonta ta cikin farin gilashin dake fuskarta.
Nan ma kai ta gyaɗa masa cikin karfin hali, jin ta take yi kamar ba ita ba komai na jikinta ya yi mata kamar ba nata ba.
Doguwar rigar dake jikinta ne na ranar da abin ya faru amma an yanke duka hannuwanta watakila da aka kawota asibiti ne wajen sauƙaka ma likitoci aiki ne ya sa suka yanke sannan mamaki take yi anan ta kwana ne? Tunda dai dai ta san lokacin da ta yi ma kanta illa, dare ne amma yanzu tana facing window ɗin ɗakin tana kuma ganin haske alamun kamar yamma ne ko rana.
"Ba abin da ke damun ki ko?
Ta ji likitan ya sake faɗa yana kallonta kuma da harshen hausa yake yi mata mgana.
Idanuwanta ta lumshe ta sake buɗewa alamun babu abin da ke damunta, sai nauyin jikinta da ciwon kai.
Dakyar ta iya buɗe baki ta ce" Kai na "
"Sannu."
"Da jikina kamar ba nawa ba."
Ta faɗa lokaci ɗaya hawaye na kece mata wasu na zubowa wasu na sake tunkuɗowa.
"Sorry duk zai bari in sha Allahu."
Ya faɗa yana mai kallonta.
"Ya hannun ki? Ba wani pain?
Sai ta ɗan bi hannun da kallo kafin ta ɗan gyaɗa masa kai.
"Babu."
"Ya kike jin cikin jikin ki? Ba wata matsala dai ko?
Ya tambaya yana mai sake nazarinta.
Yana kallonta a matsayim mai sa'a a halin da aka kawo ta, bai ɗauka za ta tashi ba.
"Babu,"
"Amma ina jin motsi."
"Lafiyan jaririyan dake cikin ki ne, mun yi miki scanning mun gamsu da cewa jaririn dake cikin ki bai shiga hatsari ba."
Ya faɗa yana ɗauko biro daga gaban aljihunsa ya fara rubutu a cikin fayel ɗin dake hannunsa.
"Ummu Salma."
Ya kira sunanta yana cigaba da rubutunsa.
"Naa'm"
Ta amsa cikin dashewar murya.
Shuru ya yi bai sake magana ba, ita kuma tana hawaye tana tunanin ita kaɗai ne? Ina Ammah ina Baffa? Ina sauran danginta? Ba ta gansu ba.
"Ina iyayena?
Ta faɗa gashin idanuwanta jike