Follow us on social media
Showing 105001 words to 108000 words out of 147042 words
Chapter 36 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
zai goge miki dukkan wani bakin cikin da kika taɓa shiga a rayuwarki."
"Ka yi hakuri Baffa."
Ta faɗa cikin kuka tana toshe bakinta da hijabin hannunta.
"Ka yi hakuri Baffa, in sha Allahu na daina."
Ta sake faɗa cikin kuka.
Baffa ya ji daɗi ya jinjina kai kafin ya ce" Allah ya sa Auta. Ina fatan Ubangiji ya sake sauƙaƙa miki."
Ta amsa da Amin a hankali tana mai sharan ƙwalla ta jima a ɗakinsa yana ta yi mata nasihan kafin ta koma ɗakin Ammah.
Ammah ko sai da Ummu ta bar ɗakin Baffan sannan ta shiga tana faɗan cewa Ummu Salma ba ta bukatar lallashi, in ba ta bayan gida aka fito mata ba haka za ta zauna tana neman kashe kanta saboda wanda bai san tana yi ba.
"Jamila."
Baffa ya kira sunanta, ta kalle shi amma ba ta yi magana ba.
"Ki yi haƙuri da Auta, don Allah ki yi haƙuri da ita domin a halin da take ciki tana bukatar lallashi da ban baki ba faɗa ba."
Ammah ta yi shuru ba ta yi magana ba.
"Na san kina ƙoƙari amma don Allah ki ƙara kin ji ko?
Ya sake faɗa yana riƙo hannunta guda ɗaya.
"Ba ki ce komai ba.'
Ammah ta yi jim kafin ta ce" Baffa cewa fa take yi wai har yanzu tana son yaron nan wai kuma tunda ya rabu da ita ba za ta sake yin farinciki ba,"
Ammah ta faɗa cikin takaici in ta tuna maganar sai ta ji zuciyanta na zafi.
"To ai wannan sai a hankali Ammah, a sannu sannu duk za ta manta da komai. Ke dai kawai ki ɗan bata lokaci."
Ammah ta ɗan ɓata rai kafin ta ce" To Baffa wani irin so kuma! Kalli fa wulaƙanci da tozarcin da ya yi mata amma ita har yanzu son shi take yi?
Baffa ya yi mirmishi kafin ya jinjina hannunta a cikin na shi yana fadin" Ina ruwan zuciya Ammah, ba laifin Auta ba ne bata da alhakin sarrafa zuciyarta. Amma lokaci ne wallahi tallahi za ta manta da komai, watakila sai dai in ta kalli abin da ke cikinta bayan ya fito duniya ta iya tuna da shi"
Ammah ta yi shuru tana kallon shi sai ya gyaɗa mata kai kafin ya cigaba da faɗin" Na baki tabbacin haka, ki dai kawai ki ɗan kara mata lokaci."
Sai Ammah ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Shike nan Baffa Allah ya ba ta dangana."
Ya amsa da Amin yana faɗin" Ko ke fa matar Baffa"
Ammah ta yi mirmishi ba tare da ta yi magana ba.
Fita ta yi zuwa kitchen ta shako wani ƙaramin faranti da kulolin abinci sai ruwa da kofi ta kai ma Baffa yana ci suna ɗan taba hira kaɗan kaɗan ita kuma tana gefen shi tana yi masa fitita da mafici tunda ba wuta sun ɗauke.
"Baffa gobe fa su Lamiɗo na hanya."
Kai ya ɗan jinjina kafin ya ce" Na ji Abdullahi na maganar shi zai je fillin jirgi ma ya taho da su."
Ammah ta washe baki tana faɗin" Haka ya ce mini, Baffa Lamiɗo fa ya fi wata biyar rabon shi da garin nan"
"Zai yi gaskiya."
Ya faɗa yana kai cokali bakin shi cike da shinkafa da wake jallop.
Ammah ta cigaba da faɗa masa ta kira Ummin ikki ta faɗa mata gobe za ta zo ta taya ta girkin da za ta yi musu na tarba.
"To ke ki bari surukan ki su zo su yi girkin mana."
Da sauri Ammah ta ce" A'a Lamiɗo ya ce na yi masa tuwon shinkafa miyar zogale. Kuma kasan in bani na yi girki ba yana ganewa."
Baffa ya kalleta kawai ya yi ɗan mirmishi.
"To uwar Lamiɗo."
Ammah ta kwashe da dariya Baffa na kallonta yana jin sanyi a ran shi, gabaɗaya ta faɗa damuwar halin da Ummu ke ciki na ta sukanta a ciki, shi ya sa ta yi ta rama a tsaye amma yau saboda zuwan Lamiɗo ta saki har yana ganin dariyanta kuma farincikinta ya kasa ɓoyuwa shi kan shi ya tabbata Ammah renon ɗa na cikinta ta yi ma Lamiɗo shi ya sa take jin sa fiye da ƴaƴan cikinta.
Shi dai har ya gama cin abincin Ammah na yi masa hira kan zuwan Lamiɗo yana jinta kawai yana mirmishi.
Suna cikin ɗakin ne ma Baɗɗo ta zo gidan, har ɗakin Baffa ta shiga suka gaisa ta ce daga makaranta take ta biyo.
"Sannu Baɗdo, Ammah ba ta abinci ta ci.".
Baffa ya faɗa yana kallon Ammah.
"Ta je Kitchen ta ɗiba mana"
Baɗɗo ta amsa da bari ta yi salla tunda tana makaranta aka yi la'asar kuma tana sauri ba ta tsaya ta yi acan ba.
Ɗakin Ammah ta shiga Ummu na kurya cikin ɗakinta kwance tana tunani ba ta ma ji shigowar Baɗɗo ba sai da ta ji ta faɗo saman gadon sannan hankalinta ya dawo kanta.
"Kina kwance kullum kullum dai Sisna?
Ta faɗa tana mai kallon Ummu Salma da ta ɗan tashi zaune tana kallon ta.
"Daga makaranta kike?
Ta tambaya, daidai Baɗɗo na sauke jakar hannunta lokaci daya da yaye mayafin jikinta.
"E na ce bari na ɗan leko ki kwana biyu? Ya jikin! Ina fatan dai ba wata matsala,?
"Babu."
Ta faɗa a sanyaye.
"Kin tabbata?
"Allah bana jin komai, sai yar kasala ne da ɗan ciwon kai."
"To magungunanki sun ƙare ne?
Sai ta ɗan jinjina kai kafin ta ce" Bai wuce in na sha yau da gobe ba."
"Yakamata mu koma asibiti "
Baɗɗo ta faɗa tana kallon cikin jikin Ummu.
"Cikin fa har ya ɗan turo"
Ummu ta bi cikinta da kallo saboda riga da sikat ta saka shi ya sa sai cikin ya ɗan turo
Shuru kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba
"Kila fa in muka koma su ce ki fara zuwa awo".
Ummu ta kalli Baɗɗo na wani lokaci nan ma ba ta yi magana ba.
"Me ya faru?
"Sai na haihu har abin da na haifa ya girma bai san uban shi ko ba ta san uban ta ba?
Ta tambaya idanuwanta na cikowa da ƙwallah.
Baɗɗo ta ce" To wa ya ce ba zai san uban shi ba? Za a faɗa masa komai har labarin tun yana ciki uban ya ce ba ya bukatarsa."
Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa.
"Bari na yo alwala'
Tana gama faɗin haka ta shige tiolet domin ba ta san ma ta tsaya Ummu Salma na damunta da mganganu kan Habib wallahi ta tsane shi ta tsani ma jin sunan shi
Fatan ta yadda ta tsane shi itama Ummu ta tsank Habib amma ina, ita har gobe tana begensa tana ganin zai iya neman ta, ta manta da cewa ya ce ya riga ya gama amfana da ita.
Alwala ta ɗauro ta zo ta yi salla bayan ta idar ta fita ta je ta ɗibo abinci ta zo ta hau gadon tana ci suna ɗan taɓa hira da Ummu, ko da ta kawo mata maganar Habib Baɗdo za ta ɓata rai ta kauce da hirar.
"Har yanzu Habib bai kira ki ba?
Ummu ta tambayeta tana kallon ta.
"Ni bai kirani ba, tunda ya sake ki na goge lambar shi a cikin wayata."
Ta ba ta amsa tana mai cigaba da cin abincinta.
"Me ya sa kika yi saurin gogewa? Da kin kira shi, kin tambaye shi me ya sa ya yi mini haka?
Baɗɗo ta kasa haɗiye abincin da ta saka a bakinta tana kallon Ummu da mamaki.
Ganin har ta fara hawaye.
"Baɗɗo na kasa mantawa da Habib. Wallahi a mafarkina da farke na duk tunaninsa ne."
Ta karishe faɗa cikin kuka.
"Kowa laifina yake gani, ba laifina ba ne, zuciyata ne har yau tana son Habib na kasa jin na tsane shi. Nima ina so na tsane shi, amma na kasa ya zan yi? Na rasa yadda zan yi da rayuwata."
Ta ƙarishe faɗa tana mai fashewa da kuka
Baɗɗo ta yi shuru ta ma kasa mgana, maganganunta sun ƙare duk wani kalami na lallashi ta gama zayyana ma Ummu amma har yau ba ta gane annabi ya faƙu ba.
"Ni ba ni da abin da zan kira Habib na faɗa masa. Domin duk wani abun da za mu sani ya sanar damu. Ummu ki saka a ranki ko da ganganci Habib ya kira ni sai ya yi nadama wallahi, domin ba zan raga mishi ba. Tunda shi batulu ne kuma mayaudari, sannan maganar kina son shi, ko kin kasa tsanar shi duk bai ta so ba, ki yi ma kanki faɗa Ummu cewa fa ya yi bai taɓa son ki ba, don jikin ki ya aure ki. Kuma ya gama amfana da ke shi ya sa ya sake ki, da cikin shi amma bai damu ba, to ke ki yi tunani da hankalinki wanna mutumin da ya gama yi miki haka ne zai dawo gare ki? To ko ma ya dawo da sunan mene? Bayan abin da ya haɗa ku ya riga ya kawo karshensa duka. Ko kin manta saki uku Habib ya yi miki ne Ummu Salma?
Ta gama faɗa tana kallonta.
Ummu tana hawaye ta ce" Ban manta ba"
"To gwara ki tuna cewa har abada aure ya haramta tsakaninki da Habib a yanzu. Kuma koma bai haramta ba shi baya sonki ba kuma zai dawo gare ki ba, in ma za ki yi daina tunanin ki cire sa a cikin zuciyarki ki cire shi, in kuma ba za ki iya ba har yanzu kina son shi to ki ba da himma. Amma ina so ki sani ko mutuwa kika yi wallahi tallahi Habib ba zai damu ba domin ba shi da asara."
Baɗɗo ta faɗa tana zare ma Ummu Salma idanuwanta domin yau itama ta kai ta bango.
Ummu ba magana sai kuka, tana faɗin kowa haka yake ce mata ko jiya ma Ammah ta yi mata faɗa yau ma Baffa ya yi mata nasiha.
"To ai duk muna son ki ne, gaskiya ce mai ɗaci muke faɗa miki. Bayan mu masoyan ki, ba wanda ya san zafin ki Ummu Salma."
Ta faɗa tana ɗan sassauta fushinta.
Ummu na kuka take faɗin" Ina so na manta nima ina so manta. Amma na kasa."
Sai gunjin kuka, tausayinta ya kama Baɗɗo dole ta sauke filet ɗin abincin hannunta a saman dirowan gado ta karisa wajen Ummu ta rumgumeta tana lallashinta.
"Ki yi hakuri, ke ce za ki yi ma kanki wannan yaƙin. Ki koma ga Allah ki roƙesa ya cire miki, in sha Allahu zai cire miki."
Ummu ta amsa da cewa wallahi tana yi tana addu'a amma kamar sai kara gaba tunaninta akan Habib yake, ita kuma Baɗɗo na sake ba ta tabbacin kar ta gaji ta cigaba da kai kukanta wajen Allah zai kawo mata ɗauki.
Da lallashi da ban baki Ummu ta yi shuru.
Sannan Baɗɗo ta karishe cin abincin ta ta fita da filet ɗin zuwa kitchen ta haɗa wanke-wanken ta wanke sannan ta share tsarkar gidan Ammah na ta saka mata albarka.
Sai da ta yi mangariba sannan ta yi shirin tafiya.
"Ke wai na ji Ummi na faɗin gobe Hamma Lamiɗo zai zo tare da iyalansa."
Baɗɗo ta faɗa lokaci ɗaya tana gyara zaman jakarta a saman kafadanta.
Suna tsaye a tsakar ɗakin Ummu ta zumbuɗa hijabin da ta yi salla da shi za ta ɗan rakata haraban gida..
"Uhm haka na ji Ammah na faɗa."
Ummu ta faɗa cikin basarwa.
Bata son ya zo, haka kurum ba ta son su samu baki anan kusa, ita dai da Baffa ya sani ya barta ta bi Mami Kaduna da ta fi samun kwanciyar hankali.
Dazu ma da Baɗɗo ta yi mata maganar waya ta ce sun yi waya da Mami ta ce za ta aiko mata da sabuwar waya da layi, wayarta ba za ta iya amfani da ita a yanzu ba.
"Ai Ummi ta ce tun safe tana nan gidan Ammah ta ce ta zo ta taya ta abincin tarban shalelen Ammah.."
Ta faɗa tana yar dariya
Ummu ta kalleta kafin ta ce" Uhm kin san halin Ammah, in ban da ma ɗaukan ma kai, girki ko su Adda Suwaiba ba za su yi musu ba? In su Hamma Jibo ne za su zo ban taɓa ganin ta yi musu girki na musamman ba amma Hamma Lamiɗo duk abin da yake so ita ce za ta yi masa."
Ummu ta karishe faɗa da jin haushin Ammah haka kurum mutum kato da iyalansa amma har yau ba ta daina wahala a kan shi ba
"Ke ko ɗan gaban goshin Ammah ne, naji ma Ummi na faɗin za su kwana biyu."
Ummu ta yi shuru ba ta sake magana ba tunani take yi in da hali ta guje ma gidanan har sai sun tafi, duk da ba dariya za su yi ma kaddaranta ba, ita kawai tana kunyar ya zo ya ganta a gida kawai a ce mijinta ne ya sake ta sai abin ya yi mata wani iri.
Bayan Baɗɗo ta yi ma su Baffa sallama Ummu ta tafi rakata har haraban gidan, suna tafe Baɗɗo na tambayan ko Shamsiya ta zo? Ummu ta ce ta zo kwanaki ta ma ce za ta dawo amma ba ta dawo ba.
"To watakila ta koma makaranta ne"
Baɗɗo ta faɗa Ummu ta yi shuru kafin ta ce" An ya! Ko dai ta ji haushin mganganun da Ammah ta faɗa mata ne"
"Me kuma ya faru?
Baɗɗo ta faɗa tana zare idanuwaanta.
Nan Ummu ta kwashe komai ta faɗa mata.
"Kin san halin Amman taki, ba ta da haƙuri ta yi ta masifa."
Ta karishe faɗa tana kallonta.
"To ai ban ga laifin Ammah ba, itama dai Bestie ba ta yi nagana mai kyau ba duk wannan abin da Habib ya yi miki sai ta ce laifin ki ne? Haba ko Habib ta sani ba ke ba ai ta faɗi gaskiya ballanta ta sanadinki ta san Habib ɗin, ai wallahi Ammah ta yi mini daidai ko ni ce a wajen haka zan yi mata."
Ummu ta kalleta kafin ta ce" Ku yi ma Bestie uziri kin san yanayinta da gidan su."
Baɗɗo ta taɓe baki kafin ta ce" Haba koma dai mene ai ke tata ce, in ba ta tausaya miki ta ba ki baki kan abin da ya same ki ba, bai kamata ta zauna a fuskarki tana cewa ke ce da laifi ba, kuma har tana fadin cewa ba za ki samu kamar Habib ba ni wallahi kalamanta ma sun saka ta l zube mini a idanuwana Habib ɗin banza? Wallahi sai kin samu wanda ya fi shi kuma ta jira ta sha kallo."
Ummu dai ba ta kara magana ba ganin Baɗɗo ta ɗau zafi ta samu suka yi sallama ta tafi, ita kuma ta dawo cikin gida. Itama fa kalaman Shamsiyar sun ba ta mamaki ita ce ta farko da ta fara cewa Habib ba shi da laifi. Sannan ta yi mamakin rashin dawowarta sannan ko a waya ba ta kirata ba, ai tana da lambar Ammah.
amma ba ta kawo komai a ranta ba, Ammah na ɗakin Baffa ta ɗau wayarta ta kira ta har sau biyu ba ta ɗauka ba, sai daga baya ta kirata tana ce mata ba ta gida ne da yake ta koma makaranta.
Sun ɗan jima suna hira Shamsiya ta bata hakuri kan cewa komawarta makaranta ne ya zo a gaggauce shi ya sa ba ta dawo ba. Amma kafin su yi sallama sai da ta yi ma Ummu tambaya.
"Yanzu Bestie haka za ki yi renon cikin nan ki haife shi a ƙasƙantan ce! Alhalin uban cikin ya ce ba ya so?
"In shi ba ya so ai ni ina so. Kuma da ikon Allah zan haifi abin da ke cikina da goyon bayan iyayena da dangina"
Ummu ta bata amsa muryanta a raunane domin kuka na shirin ƙwace mata..
"Tabɗijam. To Allah ya kyauta."
Ta faɗa cikin ganin karfin halin su tunda wanda ya yi cikin nan ya ce ba ya so to me kuma za a jira da shi? Kafin su yi sallama ma wayar ta katse kamar katin ta ne ya kare. Ranar kamar an yi ma Ummu Salma fami kan damuwarta ta kusa raba dare tana koke-koke ballanta da Ammah ba a wajenta ta kwana ba, ganin ta yi kuka ba zai fissheta ba ya sa ta tashi ta je ta ɗauro alwala ta fara salla daga zaune domin jiri take gani addu'a take yi Allah ya cire mata soyayyar Habib a cikin zuciyanta ko za ta samu salama.
Ba ta samu barci ba sai da ta yi sallar asuba shima ba daɗewa ta tashi da ciwon kai da jiri, tana kuma karyawa sai amai kamar za ta yi amayar da hanjin cikinta, sannan da ta shiga tiolet sai ta ga jini a ruɗe ta fito ta faɗa ma Ummin ikki da ta zo gidan tarban su Hamma Lamiɗo. Baffa baya nan ya shiga cikin gari tare da Abdullahi can harkokinsu.
Sai kawai Ammah ta ce Ummin ikki ta raka Ummu zuwa asibiti, tare suka tafi har da Adda Suwaiba da tun safe suna gidan.
****
Ƙarfe biyu saura na rana Hamma Abdullahi ya je filin sauka da tashin jirage na YOLA INTERNATIONAL AIRPORT JIMETA. da kuma motar Hamma Lamiɗo wata hilux ƙiran Toyota da alamu dai Hamma Lamiɗo na son mu'amala da motocin kamfanin Toyota.
Lokacin da suka iso gidan su Ummu ba su daɗe da dawowa daga asibiti ba, cikinta ya shiga wattani huɗu amma likita ya ce ya yi rauni ta riƙa samin hutu sannan jininta ya yi sama again, ba kuma ta samun isasshen barci. Amma dai ya rubuta magunguna sannan ya ce nan da sati uku za ta fara zuwa awo, suna son ta samu hutu sosai sannan ta riƙa cin abubuwan da za su gina mata jiki, amai kuma da kasala laulayi ne za ta bari in cikin ta ya yi girma watakila ma sai ta haihu ya danganta da yanayin ta.
Ummu Salma na kwance a cikin ɗakinta lamo akan gado tana sauke ajiyar zuciya tana ji daga falon Ammah ana ta yi ma baƙi maraba. Har da Adda Ummu Sulaim, duk tare suka taimaka aka gyara gidan girki dai Ammah ta yi a cewarta Lamiɗo na ganewa in ba ita ta yi mishi abinci ba.
Ga muroyoyin su nan har na Ammah amma ko tarin Hamma Lamiɗo ba ta juyo ba, kuma yana falon tunda ga Ammah can na ta masa maraba kamar ta goyasa.
Da ga cikin ɗakin dai ta ji na matarsa cikin yauki da yanga kamar yadda ta saba tana gaishe da Ammah da su Ummin ikki.
Barci ne ya kwashe ta daga nan ba ta farka ba sai wajen biyar saura shima ɗin ta tashi ne don kanta, Adda