Follow us on social media
Showing 63001 words to 66000 words out of 147042 words
Chapter 22 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
komai ba Habib ka daina zagin su don Allah."
Ta faɗa kukanta har yana fitar da sauti.
Sai ya kwashe da dariya kafin ya ce"Oh kina jin zafi ne? To na dai na cewa basu da tunani suna da shi, amma dai ba zan fasa faɗa miki kin turo bagidajen tsohon ki wajen iyayena ba kuma ya zo, sannan kuma har ya bar mini saƙo "
"Haba Habib."
Ummu ta sake faɗa cikin kuka tana sakin shessheka domin ji take yi kamar ta shiɗe yadda maganganun Habib suke kassra tunaninta da sauran kuzarinta gabaɗaya.
"Na faɗa wannan bagidajen uban naki ne, wai shi ne yake da zarran zuwa ya faɗa ma Abba cewa in na gaji dake ne na dawo masa dake gida"
Ya gama faɗa yana wata dariya ta reni da wulakanci.
"Shi yana ɗauka ya yi gwanin ta ne, ko kuma me ya ke takama da shi? Lauyan yayanki? Ko mai aikin filin jirgi? Ko mai fama da gwajin kashi da fitsari ko mai aiki da hukumar ruwa? Ko wannan yayan na ki mai bin tsohon ku saro tsoffin injina? Ko kuma wannan yayan naki mai karatun jami'a? Ko wanda ya tafi ƙasar waje da kuɗin tallafi?
"Habibb.."
Ta faɗa muryanta baya fita saboda kuka.
Bai saurareta ba ya cigaba da faɗin.
"Oh na tuna ko yana takama da wannan ɗan da bai haifa ba ne? Lamiɗon da dangin ku ke ji dashi, Yariman Daura ko? Wanda uwarki ke zuwa maula gidan sarki ko? Da shi yake taƙama da har zai zo wajen ƙanin mahaifina ya bar mini wannan saƙon? To in ma gatse yake yi ya yi kuskure, a yau ba sai gobe ba zan cika umarninsa zan mayar masa dake kamar yadda na ɗauko ki daga gidan shi."
"Habib ka bari, ka daina zagin iyayena."
Ummu Salma ta faɗa tana kuka zuciyarta na ƙuna tana wani irin soya da irin wannan cin mutumcin da Habib ya zaunar da ita yana yi ma iyayenta da yan'uwanta.
"Na faɗa ko za ki rama musu ne?
Ya faɗa yana taso mata kamar zai dake ta sai ta yi shuru ban da kuka ba abin da take yi, yi take yi kamar zuciyarta zai fita, wani ɗaci na taso mata ɗacin an ci zarafin iyayenka a gaban idanuwanka amma ba ka da hurumin da za ka hana faruwan haka, miyan bakinta har kafewa ya yi saboda yadda zuciyarta ke tafarfasa.
"Ni ce na yi maka laifi ba iyayena ba. Ni ce baka so ba su ba, to kuma su me suka yi maka da za ka ci zarafin su?
Ummu ta faɗa cikin kuka mai ƙarfin da sautin shi yake fita sosai.
"Ka yi mini abin da za ka yi mini zan jure Habib, ka tozartani iya tozartawa ba zan taba mgana ba, amma ba zan jure jin maganganun cin fuska ko na ɓatanci ga iyayena ba, kar ka sake ban zagi naka iyayen ba kai ma ba ka da hurumin da za ka zagi nawa iyayen."
Tana magana yana mata dariya kamar ya ga wata mahaukaciya.
"Me suka yi mini kike tambaya na?
Tasowa ya yi zuwa gabanta ya durƙusa saitin kunnuwanta ya yi magana.
"Saboda sun haife ki, laifin su kenan a wajena."
Ya faɗa yana yi mata dariya, Ummu na tsiyayan hawaye tana kallon Habib tana jin son ta ji ta tsane shi, tana so ta daina jin ko da ɓurɓushin son shi a cikin zuciyarta amma ina, tunda ba ita ke da alhalin sarrafa zuciyarta ba har yau ba ta daina jin son Habib a ƙasan zuciyarta ba.
Miƙewa ya yi ya koma in da ya tashi ya zauna lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda har tsohon ki ya bar mini sallahun in na gaji dake ne na dawo masa dake shi bai gaji dake ba, to a matsayin shi na Surukina mahaifin matar da na aura na more albarkatun jikinta ya zame mini kamar wajibi na cika umarninsa."
Kallon ban fahimce ka ba Ummu ke yi masa kamar idanuwanta za su faɗo kasa, ga shi suna masu zubar da hawaye.
Takardan ya jawo a gefen shi ya ɗora saman cinyarsa ya ɗora biron a kai lokaci ɗaya yana faɗin" Zan sake ki kamar yadda mahaifinki ya ɓukata, duk da ya ɗan yi gaggawa, da a ce ya jira da ni da kaina zan sako masa ke ba sai ya wahalar da kansa wajen zuwa ya bar mini saƙo ba."
Ummu Salma ta ji kanta ya sara, har ɗan dake cikinta sai da ta ji ya motsa saboda firgici da tashin hankali.
"Yanzu Habib sakina za ka yi?
Ummu ta tambaya muryanta cikin kuka kamar za ta shiɗe.
"Kina tantama ne? Bari na rubuta na ba ki ki karanta sai ki samu tabbaci "
Kawai sai ta ga ya fara rubutu da sauri ta rarrafa gaban shi cikin kuka tana faɗin" Don Allah Habib ka yi hakuri kar ka sake ni, don Allah ka taimaka mini ka rufa mini asiri ka da ka sake ni."
Take faɗa tana wani irin gunjin kuka, ga ta duke kan gwiyoyinta tana mai zubar da hawaye tana haɗa shi da Allah akan kar ya sake ta.
"Ai abin da tsohon ki ya bukata ne, duk da nima ina da niyyar yin haka amma ba yau ba."
Ya faɗa yana nuna halin ko in kula, yana ma ƙoƙarin cigaba da rubuta abin da ya fara.
Da sauri Ummu ta faɗa kan kafafun Habib ta riƙe shi gam tana wani gunjin kuka.
"Ke miye haka?
Ya faɗa yana fizge kafarsa har tana yin gefe amma ba ta haƙura ba sai da ta sake riƙo kafafunsa da karfi ta rumgume a ƙirjinta lokaci ɗaya tana faɗin.
"Na tuba, don Allah ka yi haƙuri Habib kar ka sake ni."
"Wallahi sai na sake ki, mutuwa ce kawai za ta hana na sake ki, itama sai in yanzu ta zo ta ɗau raina amma in dai ina raye a yau zan yada ƙwallon mangwaro na huta da guda."
Ya gama faɗa yana sake fizge kafafuwanshi ya ɗora saman kujera ya bar Ummu duƙe a gaban shi tana wani irin kuka kamar za ta shiɗe.
"Habib in ka sake ni ina zan je? Wa zai sake kwasa ta? Wa ye zai iya aurena bayan ba ni da komai. Don Allah ka rufa mini asiri kar ka sake ni, kar ka manta da gudan jinin mu dake rayuwa yanzu haka a cikin jikina, kar ka bari ɗan mu ya rayu ba tare da kai ba, ka yi haƙuri don Allah ka rufa mini asiri "
Majina har zuba take yi a ƙasan cafet saboda kukan da Ummu ke rusawa amma ina Habib ba ya sauraranta rubutu kawai yake yi.
"To na ji , wallahi zan yi duk abin da kake so. Na ji zan. Zan zubar da cikin."
Ta faɗa cikin fitan hayyaci, har muryanta na dishewa saboda kuka.
Ganin ya ɗago yana kallon ta, ya sa da sauri ta sake rarrafawa gaban shi tana rawan bakin faɗin " Da gaske na ji zan zubar da cikin in har zan tsira da aurena."
Take faɗa cikin fitan hayyaci, domin ba ta ji ba ta gani, tunanin ta hangenta shi ne in Habib ya sake ta ya gama lalata mata goben ta, ya cuceta ya mai da ita ƙaramar bazawara, sannan tana son shi tana son aurenta za ta yi komai domin ta ga ta tsira da aurenta.
"Kika ce me?
Ya tambaya yana mata wani kallo
"Na ce, e zan zubar da cikin wallahi na yarda."
Ta faɗa hawaye na kwaranyo mata yadda ya ga ta ruɗe ne tana roƙon shi har tana cewa ta yarda za ta zubar da ciki ya sanya shi nishaɗi ya kwashe da wata dariyan jin daɗi.
"Na yarda ko yanzu ne ma mu je a zubar amma don Allah kar ka sake ni "
Ta sake faɗa tana haɗe hannayenta waje ɗaya alamun roƙo.
"Yarinya kin makara."
Ya faɗa yana dariya sannan ya cigaba da rubutun sa.
"Wataƙila da wata ɗaya kafin yanzu ne kika ce mini haka da zan iya sauraran ki, amma yanzu lokaci ya kure miki, da man ai na sha faɗa miki sai kin yi nadama, a ranar da nadamar ba za ta yi miki amfani ba lokacin da na ke bin ki, kina mini yadda kike so ai ba ki yi tunanin rana irin ta yau za ta zo ba, duk ɗaukan maganganuna kike yi a wasa?
Ummu ta kasa magana ban da kuka ba ta komai.
Ɗagowa ya yi yana kallon ta kafin ya cigaba da faɗin" Ni yanzu ban damu da ki zubar da cikin jikin ki , ko ki zubar ba ko ki haife shi duk wannan ya rage na ki, dake da cikin duka bana so, ba na kuma buƙatar ku a cikin rayuwata "
Ya ƙarishe faɗa yana nuna ta da yatsa daga sama har ƙasa cikin ƙyama.
Ummu ta gigice ta sake fashewa da kuka tana faɗin" To ba ka ce jikina kake so ba? To ai ga jikin nawa ai ba na hana ko?
Ta faɗa tana yi kamar za ta haura a saman kujeran da yake zaune.
"Ke kar ki hauro mini nan"
Ya faɗa yana zare mata ido.
"To to na zauna "
Ta faɗa lokaci ɗaya tana zaman dirshan a gaban shi yanayinta kawai za ka gani ka fahimci ta rasa natsuwarta ba ta ma san abin da take yi ba, ballantana abin da take furtawa.
Ganin ta cikin wannan yanayin yafi masa komai daɗi, nishaɗi da farinciki yake ji da man ya ce sai ta yi nadama to kaɗan ta gani.
"Ai ni gama moran duk wani albarkatun jikin ki, babu wani sauran maiƙon da ya rage da ban gama lashewa ba."
Ya faɗa yana dariya ƙasa-ƙasa har yana kashe mata ido ɗaya.
Ummu na kuka tana kallon Habib kamar zai yi mata gafara tana rokon shi Allah da Annabinsa kar ya sake ta, amma ina bai ƙara sauraran ta sai da ya gama rubuta abin da ya yi niyya sannan ya miƙa mata , ta kasa karɓa lokaci ɗaya tana girgiza kanta cikin kuka.
"Karɓi mana "
Ya faɗa yana mai sake miƙa mata takardan.
"Don Allah Habib. Kar ka. Sa ke ni."
Ta ƙarishe faɗa kamar za ta shiɗe domin har numfashinta ya fara ɗaukewa.
"Ai na ma riga na sake ki Ummu Salma."
Zuciyarta ta tsinke, idanuwanta suka fara rawa, hannaunta ɗaya ya kama ya tusa mata takardan lokaci ɗaya yana faɗin" Tunda dare ya yi na yi miki alfarman ki kwana amma gobe da safe ki tattara kayanki ki koma gidan ku, kayan ɗaki kuma suma ki zo ki kwashe kafin masu gidan su bukaci dakin su."
Yana gama faɗin haka ya kwashi takardansa da biron sa ya wuce yana sake faɗin" Alhamdulillah."
Har yana wani harba ƙafafuwansa, Ummu ta bi shi da kallo cikin zubar ƙwalla takardan ta matse a hannunta tana sakin kuka da ƙarfin iyawanta, kuka ta fashe da shi da duka muryanta da ubangiji ya ba ta, kanta a ƙasa kamar tana sujudda take rusa kuka kamar ranta zai fita Habib ya gama tozarta, irin tozarcin da bata taɓa jin labarin an yi ma wata mace ba, Habib ya sake ta da ƙaramin ciki bayan ya gama lalata mata rayuwa ya mayar da ita ƙaramar bazawara, ya kunya ta iyayenta ya cutar da ita sannan ya cutar da zuciyan ta.
Koda ta ɗago daga durkushen da ta yi ruwan hawaye da majina ya gama jiƙa cafet ɗin gabanta sannan fuskarta har ta jirkice tsabar kuka da tashin hankali, a hankali ta miƙe tana jin jiri na ɗiban ta, kanta na sara mata da ƙarfi, cikinta ya cure waje ɗaya daƙyar ta iya jan kafafunta tana dafe bango ta koma ɗakinta tana matsanacin kuka takardan sakin na matse a hannunta ta kasa dubawa, ba ta son gani ba ta son ganin wannan baƙin rubutun Habib a gare ta, kukan ta kawai take yi da karfi ba ma tunanin ta yi shi a cikin zuciyarta, yi take yi tana shessheƙa, tana fidda sauti ga majina na shatata, ga ruwan hawaye kafin kace me gaban riganta ya jiƙe da hawaye, fuskarta ta kumbura saboda kuka idanuwanta sun tasa sun yi jajir kamar gawarshi, daga karshe ma da ta gaji da kukan dole ta haƙura ta koma ajiyar zuciya tana faman sauke numfashi a jejjere kamar wacce ta yi gudun tsere tana zaune a ƙasan tayels a gefen gado kanta na gefen gadon ta ɗora saman hannayenta lokaci ɗaya hawaye na kwaranya har a saman hannayen ta amma ta daina kuka da sauti sai dai a cikin zuciyanta take jin wani ɗaci da raɗaɗin da ba za ta iya misalta yanayin ba.
Takardan sakin na jimƙe a hannunta ganin zufan hannunta ya fara jiƙa takardan ya sa ta ɗan ɗage zanin gado ta tura takardan ta koma ta kwantar da kanta tana ta tsiyayan hawaye yadda ta ga rana haka ta ga dare barci ko ɓarawo bai sace ta ba a cikin kunnuwanta aka fara kiran sallan asuba, duk kuma tana zaunen har wasu masallatan suja tayar da salla amma ta ƙasa tashi saboda kuka ga jikinta duk ya yi tsami kanta saboda ciwo ba ta ma san ma ɗago shi, sannan ga idanuwanta sun kumbura sumtum ko iya buɗe su ma ba ta yi, ko'ina na jikinta ya yi tsami saboda kwanan da ta yi a zaune cikin yanayi mara daɗi, da rarrafe kamar yar koyo ta shiga tiolet ta kama ruwa sannan ta wanke fuskarta da ruwan zafi ta ɗauro alwala haka ta fito da rarrafe nan domin ba za ta iya tashi ba ji take yi kamar kafafunta ba za su iya ɗaukan gangan jikinta ba.
Salla ma a zaunen ta yi, ta daina zubar ƙwalla amma raɗaɗin dake cikin zuciyarta kaɗai ya isa ya yi ajalinta. Domin zuciyarta wani zafi take yi ga wani abu mai ɗaci da ya tokare mata a ƙirji tun jiya ya kasa wuce miyan bakinta ya daɗe da kafewa sannan bakin nata ya yi ɗaci kamar maɗaciya, sannan ga ciwon kai mai tsanani yunwa take ji amma a bakinta ba ta bukatar cin komai maranta ya cure waje ɗaya da ya haifar ma gangan jikinta rawa, bayan ta idar da sallan ta kura ma waje ɗaya ido tana ma rasa abin da take tunani, yanzu fa wata sabuwar rayuwa ce ta tunkaro ta bayan barin ta gida na wattani takwas a matsayin matar aure yanzu kuma za ta koma gida a matsayin bazawara har da ƙaramin yaron ciki, yanzu a wannan kadamin wa za ta kira? Ina za ta nufa? Rayuwarta ta gama lalacewa ba ta da sauran wani abu na mamora a tare da ita.
Tuna gargaɗin da Habib ya yi mata ajiya ne ya sa ta rarrafa ta ɗauko wayarta dake saman side drower ɗin gadon. Gwara ta bar gidan tun kafin ya fahimci ba ta tafi ba ya yi mata wulaƙanci, agogon wayarta ta duba sai ta ga shidda ne da mintina biyu na safe wataƙila Baffa na masallaci sai ta kira wayar Ammah amma tana ta ringing ba ta ɗauka ba ta kira ta kamar sau uku amma shuru, sai ta mayar da akalan kiran zuwa ga Baffa, domin nan duniya su ne kaɗai ne suka rage ba za su guje ta ba, amma ta rasa komai na ta. zuciyarta na sake yin duhu in ta tuna yadda Habib ya zaunar da ita yana cin zarafin iyayenta da ƴan 'uwanta.
****
*6:13am*
Shidda da mintina sha uku Baffa da Hamma Saddam suka shigo gidan daga masallaci, jiya da yamma Saddam ya dawo daga makaranta can Bauchi. sun gama jarabawa za su yi hutun sati uku kafin su koma.
Ɗakinsa ya wuce shi kuma Baffa ya ƙarisa cikin gida, ɗakinsa ya wuce kai tsaye yana shiga ya iske Ammah na zaune saman darduma da casbaha a hannunta bakinta na motsi, yana takawa zuwa gefen gado wayarsa dake cikin aljihun rigan jikinsa ta ɗau ruruwan kira, bai duba ba sai da ya zauna sannan ya fiddo wayar yana duba sunan mai kiran..
"Auta."
Ya faɗa a sarari cikin mamaki, Ammah na lazimi sai da ta kalle shi cikin mamaki.
"Auta kuma! Ummu Salma?
Amma ta faɗa cikin ƙarin mamakin gabanta na faɗuwa, shima ita yake kallo amma sai ya aro jarumta a matsayin shi na namiji.
"Bari na ji Allah ya sa lafiya."
Ya faɗa shima cikin ƙarfin hali, kafin ya ɗaga kiran ma ya katse hannunsa na rawa yana ƙokarin sake kiran ta sai ga kiranta ya sake shigowa da sauri ya ɗaga kiran yana mai kiran sunan ta.
"Auta"
Ya faɗa yana jin bugawar zuciyarsa na ƙaruwa da sauri da sauri.
Ummu Salma daga can bangaren jin muryan Baffa ya sa rauninta ya karu, hawaye ya kece mata mai hade da kuka Baffa sai jin sautin kukan kawai ya yi ta cikin wayar.
"Ummu Salma."
Baffa ya faɗa cikin tashin hankali, Ammah na jin yadda ya kira sunanta cikin sauri ya sa ta bar saman darduman ta dawo gefensa ta zauna ta kafe shi da idanuwanta cikin damuwa tana faɗin.
"Baffa me ya faru da Auta?
Ta faɗa tana jin jikinta na yin wani sanyi, haka kurum take jin faɗuwar gaba tun jiya da man kawai Autan ke faɗo mata arai ta so ma kiranta sai ta ga dare ya yi tana shirin da man yau ta kirata a waya ta ji lafiyan ta ne.
Baffa ya kasa mgana jin yadda Ummu ke rusa masa kuka a waya gabaɗaya jikinsa ya gama yin sanyi amma sai ya yi jarumta komai ya faru daga gare ka ne Ya Ubangijin mu.
"Ki bar kukan nan ki yi mini bayanin abin da ya faru Auta."
Ya faɗa cikin lallashi a muryan sa Amma ta sake tsurewa a cikin zuciyanta tana maimaita kalmar kukan da ta ji Baffa ya ambata.
"Baffa."
Ummu Salma ta kira sunan Baffa muryanta a shaƙe da ƙyar ma take fita.
"Naam Auta me ya faru ne?
Ya faɗa cikin sauri domin ya kosa ya ji abin da ya faru duk da yana zargin wani abu amma bai yanke hukunci ba.
"Baffa."
Ta sake kiran sunan shi cikin matsannacin kuka duk ta ruɗar da Baffa, ga Ammah ma a gefen shi kamar za ta kwace wayan idanuwanta kawai ya kalla ya ga tsoro da firgici a cikin su.
"Na'am ina jin ki Auta, ki daina kuka maza ki sanar da ni abin da ke faruwa bar kuka Auta kin ji ko?
Ya ƙarishe faɗa muryansa na karyewa shima jin irin kukan da Ummu Salma ke yi a waya kamar ranta zai fita.
"Baffa Habib."
"Me ya samu Habib ɗin?
Baffa ya katse da sauri kafin zullumi ya kashe