Follow us on social media

Showing 102001 words to 105000 words out of 147042 words

Chapter 35 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

turanci tana jinta tana dariya, Sultan kam a natse shi ya kariso falon yana faɗin.

" Good Afternoon Momi."

"Afternoon My Sultan. How was school?.

Ta faɗaa tana ɗan shafa kan shi. Shi nursery 1, yake shi ne sak Lamiɗo Beena ce ke kama da ita.
Ya amsa mata da lafiya lau da turanci yaro ne ɗan shekara biyar amma yana da tsawo da ɗan kiba shi ya sa sai ka yi zaton shekaransa takwas in ba ka san shekarunsa ba.

Anitha ta fito daga wani korido daga yamma da sauri domin ta na sane da lokacin dawowar yaran tunda alhakin kula da su yana wuyanta ne suna ko ganinta Beena ta ƙwace a hannun uwar ta nufeta ita kuma ta tarbeta tana mata oyoyo.
James cikin ladabi ya gaisar da Balkisu sannan ya  sauke kayan hannunsa ya fice daga falon.
Har Anitha ta ja Beena zuwa cikin ɗakin su Sultan yana bin bayan ta Balkisu ta kira shi yana juyowa ta ce

"Ku sauya kaya ku ci abinci Papa is at home."
Jin ta ce Papa ya sa ya fara tsalle yana murnan Papa ya dawo ya bi bayan Anitha har suka ɓace ma ganin ta, tana tsaye tana kallonsu tana mirmishi,. Ba su san ya dawo ba tunda a jiyan ma cikin dare ya iso gidan kuma ya kwanta yau yana ta barcin gajiya ba su haɗu ba.

Kitchen ta shiga ta iske Debora na ta aikin Dinner tana ganin ta ta rankwafa tana gaisheta ba ta amsa ba ta ce ta haɗa ma Baban su Sultan coffea mai zafi nan da nan ta amsa falo ta fita ta zauna ba daɗewa sai ga shi ta haɗo ta kawo mata a cikin wani karamin fulas fari da karamin mug fari da faranti, Balkisu ta karɓa ta wuce da shi ɗakin Lamiɗo ta iske shi ya sauya kaya zuwa wani wando blue da farar riga mara hannu yana gefen gado yana kunna wayarsa da tafi sati a kashe.
Karamin teburin tangaran ɗin da ke cikin bedroom ɗin ta jawo ta sauke farantin hannunsa.

"Thanks"

Ta ji ya ambata a saman leben shi, halin shi ne duk abin da za ta ba shi ko za ta yi masa zai yi mata godiya wannan daɓi'an shi ne..
Zuba masa ta yi ɗan daidai a mug ɗin sannan ta miƙa masa ya karɓa yana sake yi mata godiya wannan karon da harshen fillanci, duk da ba ta ji amma tana tsinta a bakin shi da bakin yaran tunda yana yi musu magana da fillancin.

Gefen shi ta koma ta zauna shi kuma sai da ya kunna wayar sannan ya kai mug ɗin baki ya kurɓi coffea ɗin. Tun safe bai saka ma cikinsa komai ba rabon sa da wani abu tun jiya da daddaren da ya dawo ya sha tea. Barci ya yini yi na gajiya yanzu haka ma yana jin kamar kasusuwan shi suna naɗe tsabar gajiya.

Sama da wata ɗaya shi ke tuƙi saboda zai bar aiki da kamfanin don kar su bar shi ya tafi haka shi ne sai da suka wahalar da shi, yanzu dai ya samu sun karɓi takardan barin shi aiki sun saka hannu shi ne dalilin dawowar shi gida, nan da wattani biyu zai fara aiki da abon kamfani amma yana da sauran hutu kafin ya kama aiki.
Yana kurban tea din yana ɗan duba saƙonnin dake reto a saman wayarsa.

"In ka samu natsuwa ka kira Maimartaba da Fulani sun kirani suna tambayana kai, da cewa ba su same ka a waya ba"

Balkisu ta faɗa tana kallon shi. Kamar ba zai yi magana sai kuma ya ce a hankali
"Har su Ammah ban yi magana da su ba."
Sai kuma ya yi shuru ya ɗan ka fasali kafin ya cigaba da faɗin." Zan kira su, "
Sai kuma ya kalleta kafin ya ɗan kurɓi tea ɗin hannun shi
"Ina so ma na je,"
Ta san bai gama maganarsa ba shi ya sa ba ta katse shi ba.

"Na samu sauyin kamfani. "
Numfashi ya fesar a hankali sannan ya a jiye mug ɗin hannunsa a saman teburin gabansa.

"Zan yi hutun 2 month."

Jin ya yi shuru ya sa ta san ya gama magana.
"Ranka ya daɗe dogon hutu haka? Har Daura za mu je?
Ta tambaya cikin fara'a.
Kai ya ɗan daga mata kafin ya ce" In sha Allahu."
"Har da ni za a yi tafiyar?
Ta tambaya
"In za ki je.".
Shima ya ba ta amsa a yanayin maganarsa.
"In ba za mu daɗe ba, zan iya ɗaukan excuse a wajen aiki "
Sai ya jinjina mata kai, ta san halin shi zai ce in da takura ta yi zamanta

"Har da su Sultan?

Bai kalleta ba, amma dai ya ɗan motsa kan shi alamun e, sai ta fara yi masa bayanin sun koma makaranta, amma dai ba matsala in dai ba za su dade ba

"Sai ki dawo tare da su."

Ya furta daga haka kuma ya tsuke bakin shi.
Ma'ana shi yana can ita za ta iya dawowa da yara.
Tana da murna da jin daɗi za su samu tafiya ita da shi da yaran su abin da ba sa samu sai a shekara bai wuce sau ɗaya ba.

Duk da ba hira suke yi ba amma tana tare da shi har aka kira mangariba sannan ta kwaso fulas da mug din zuwa kitchen shi kuma ya sauya kaya zuwa jallabiya ya fita masallaci.
Bai dawo ba sai da ya tsaya ya yi isha'i bayan ya shigo ya ɗan bata lokaci a haraba suna gaisawa da su Baban Adila da Jamess, Lamiɗo kowa ya san shi mutum ne mara ƙyamar mutane duk da yanayin shi, da ya shigo falon ma haka su Sabuwa suka yi layi suna gaishe shi kansu a kasa duk ya amsa musu cikin yanayinsa.
Kafin ya dawo Debora ta shirya tebur da abinci sama da kala uku, Balkisu kuma ta sake wanka ta sauya kaya zuwa material doguwar riga.
Tana fitowa ta iske shi a falo tare da su Sultan suna masa hira Beena na hawa jikinsa tana sauka.

Sultan ko faɗi yake yi Papa zan sha icream, papa zan ci shawarma Papa sai hira yake yi masa shi dai sai ya yi ta uhm kawai yana ɗan mirmishi, Beena kam tana ta wasa da gashin kansa kuma bai hana ta ba.
Balkisu ta kalle su cikin alfahari.

Tare suka yi Dinner jalop rice mai kaza sai kuma mandirice, shi Lamido Jalop din ya ci sai ya sha lemun abarba. Su kuma ita da yaran suka tsakura sauran abincin Beena ma madaran Naan na yara ta sha, Sultan kuma pepe chicken ya ci Bilkisu kum ta ci Mendi rice din da lemu.

Bayan sun gama cin abincin  ba daɗewa Anitha ta zo ta tafi da su domin su yi shirin barci gobe makaranta, suma ba daɗewa suka shige ciki. Debora kuma ta zo ta kwashe komai na saman dining ɗin zuwa kitchen, abincin gabaɗaya ake dafawa su ɗiba na su da na su James ba shamaki, sannan Balkisu ba ta son a gama cin abinci a bar shi a wajen shi ya sa da sun gama take yin saurin kwashe komai zuwa kitchen.



*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t

*16*

*Zone ,3. Jimeta*

BAYAN SATI ƊAYA.

Ummu Salma na zaune a tsakar gida a saman kujera yar tsugunno da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safiyar ranar talata.
Farin wake ne a cikin wani farantin silba tana gyarawa Ammah kuma na daga cikin kitchen tana ɗora sanwa amma jefi-jefi tana yi ma Ummu hira wacce ta yi shuru kamar ruwa ya cinye ta. Ammah ce ke ta maganarta ita kaɗai. Baffa baya nan tun jiya suka tafi ibadan shi da Hamma Abdullahi.
Gidan sai ya rage daga Ammah sai Ummu Salma, Saddam ma ya koma makaranta shekaranjiya.

Gajiya da kwanciya ya sa take ɗan fitowa tsakar gida ko za ta samu abin da za ta iya taimaka ma Ammah da shi amma ba ta barinta ta yi komai sai ta ce ai Likita ya bata hutu, ita kuma ta bata tabbacin ta warke, jiya ne ma Hamma Abdurrahaman  ya zo ya ji suna wannan takaddaman, shi ya yi ma Ammah magana ya ce aikin da za ta yi daga zaune ta riƙa bata saboda ta riƙa ɗan motsa jikinta hakan ma lafiya ce ga abin da ke cikinta shi ya sa yau ɗin Ammah har ta amince ta bata wake ta ce ta gyara mata.

"Saura fa kwana biyu zuwan su Lamiɗo Auta, daga yau sai gobe jibi ne ya ce mini za su taho."
Ummu ta yi shuru hankalinta na kan waken da take gyarawa amma kuma hankalinta da tunanin ba ya wajen ta tafi duniyar tunanin rayuwarta.

Yau wajen kwana uku kenan Ammah ta kasa zaune ta kasa tsaye murnanta ya kasa ɓoyuwa tunda Hamma Lamiɗo ya kira ta ya ce za su zo shi da matarsa da yara ranar al'amis kuma za su ɗan kwana biyu ta kasa sukuni tun jiya ta tura matan su Hamma Abdullahi su Adda Suwaiba da Adda Ummu Sulaim suka je gidan shi dake anguwan Jambutu Haske suka gyara suka yi share-share. Sannan yau da safen nan ta ji Ammah na waya da Hamma Abdullahi tana tunasar da shi Hamma Lamiɗo ya ce ya ɗauki motarsa ya kai ta wanki sannan a ɗan duba ta tunda ta yi wattani a ajiye ba a hauta ba, tana can gidan lullube a cikin tamfol.

Alhalin ba Ammah ya bama saƙo ba da kan shi ya kira Hamma Abdullahin ya faɗa masa, shi ma jiya ne kafin su wuce da Baffa yake mata maganar shi ne yau ta kira shi tana sake tunasar da shi har da cewa in ba za su dawo ba ne ya kira Abdularrahaman shi ya je ya ɗau motar ita dai maganarta kar shalelenta ya iso garin nan ba a yi masa abin da yake so ba.

"Da man Kabiru ya faɗa mini zuwan nan da ya yi kwanaki Lamiɗo ya samu sauyin wajen aiki yanzu zai dinga samun hutun sosai tunda ya sauya wajen aiki."
Ammah ta sake faɗa tana daga cikin kitchen.

Ummu Salma dai na jin ta amma har a lokacin ba ta yi magana ba, tunani take yi in da ace tana da in da za ta je ta ɓoye ma ganin Hamma Lamiɗo da matarsa za ta je, har sai sun tafi sannan ta dawo, tana jin kunya da nauyin su zo su ganta a haka,  su ga yadda rayuwarta ta dawo baya, yanzu kunyar mutane take ji da Ammah tayi baƙi ko tana falo za ta shige ciki tana jin nauyin haɗa idanuwana da Jama'a ko yayyenta kunyar haɗa idanuwana take yi da su, tana ganin kamar ita ba ta da sa'ar rayuwa ta tafi gidan aure amma ga shi ta dawo musu ba ma ita kaɗai ba tare da nauyin cikin jikinta. Duk da Ammah ta ce ba ta faɗa masa ba amma in ya zo ya gan ta ko bai ta tambaya ba Ammah za ta iya faɗa masa dalilin zamanta a gida tunda shi tambaya ba ɗabi'ansa ba ne ko zai shekara yana ganinta ba zai damu da ya tambayi dalilin zamanta ba.

Ta yi nisa cikin tunanin ta ba ta ma san Ammah ta fito tana yi mata magana ba, sai da ta ji ta taɓa ta sannan ta yi firgigit ta dawo hayyacinta.

"Ammah kina magana ne?

Ta faɗa tana kallonta lokaci daya tana koƙarin shanye hawayen da suka cika mata kwarmin idanuwanta.

"Auta"

Ammah ta kira ta, sai ta sunkunyar da kanta tana jin kamar ta kace da kuka.

"Ba an hana ki shiga zurfin tunani ba, sai yaushe ne za ki saduda ki fahimci duk abin da Ubangiji ya yi daidai ne? Sai yaushe za ki dogara da Allah ki san cewa Habibu ya shuɗe daga rayuwarki Ummu Salma.?
Ammah ta gama faɗa tana tsaye tana kallon Ummu wacce har ta fara tsiyayan hawaye a saman ƙuncinta

"Wallahi in na ga kina kuka da damuwa kan wannan yaron haushinki na ke ji, bai ma kamata kina yi masa kuka ba, an san da damuwa amma haƙuri ake yi tunda damuwa da kukan ba zai sauya komai ba. To gwara a yi hakurin yafi alheri in kika yi hakuri wata rana za ki ci riban haƙurin ki Auta."

Ummu Salma ta rushe da kukan da take ta riƙewa. Ammah ta duka a gabanta lokaci ɗaya tana dafa kanta.
"Ki yi hakuri Auta kin ji ko?
Sai Ummu ta gyaɗa mata kai amma kukanta ya kasa tsayawa.
"Mu kan mu muna cikin damuwar abin da ya faru, amma yanzu mu damuwarmu taki ce Auta. In ba ki kwantar da hankalin ki ba, muma hankalin mu ba zai kwanta ba. Samun kwanciyar hankalinki shine farincikin mu da mu da yan'uwanki  gabaɗaya, tunda dai ba mu isa mu sauya abin da ya faru ba, to gwara mu taru mu yi haƙuri gabaɗaya mu fauwalla ma Allah duka lamuranmu da sannun komai zai wuce sannan kuma zai yi miki sakayya in sha Allahu "

Duk wannan dogon nasihan da Ammah ke yi mata ba ta ji ba kuka kawai take yi har da gunji.

"Yanzu shike nan Habib ya rabu da ni har abada Ammah?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana kallon Ammah idanuwanta suna masu zubar da ƙwalla.
"Shike nan Habib ya rabu da ni. Shike nan ya gama da ni Ammah?
Amma ta yi kasaƙe tana kallonta cikin takaicinta. Ba ta son ta yi ta ma yaro magana yana yi mata taurin kai.

"Ammah ina son Habib. Ina son na sake rayuwar aure da shi. Wallahi ina son shi, na kasa mantawa da shi sai na ke ganin kamar tunda ya rabu da ni har abada ba zan sake farinciki ba Ammah."

Ta ƙarishe faɗa tana mai sakin wani marayan kuka mai fitowa da shessheƙa
Ammah da takaici ya ƙume ta, ture ta ta yi kafin da sauri ta miƙe tana faɗin" Ke kam dai an yi sakara Ummu, wallahi in da kin san yadda na tsani sunan yaron nan da baki yi gangancin ambaton shi a gabana ba. Haba don Allah yaron da ya yi miki wulakanci ya tozarta ki kike ikirarin har yanzu kina so saboda ba ki da zuciya Auta?
Ta faɗa lokaci ɗaya tana balla mata harara.
Ummu ta danne kukanta sanin halin Ammah yadda ta fusata sai ta iya kai mata duka ma in ba ta yi wasa ba.

"Yaron da tunda ya sake ki bai sake waiwayoki ba, ba ruwan shi da ke ballatana yadda kike rayuwa, cikin dake jikin ki ma bai damu da shi ba ballatana ke, amma saboda wawanci ke kina nan kina kuka kina cewa wai kina son shi, to Allah ya tsine ma wannan son Ummu ba shi da albarka tunda bai tsinana miki komai ba sai tozarci da wulakanci"

Yadda Ammah ta harzuƙa tana ta faɗa ne yasa Ummu tana hawaye ta ce" Ki yi haƙuri Ammah."
"Ke kika sani wannan kuma ruwanki ne, ki yi hakuri ki rumgumi kaddaranki, ki sani yanzu rayuwarki ta sauya ki rika tuna Habibu a matsayin wani darasi ne wanda ya shuɗe daga rayuwarki, sannan ki riƙa tuna ba ke kaɗai ba ce nan da wani lokaci za ki zama uwa. Abu na ƙarshe kuma ki zauna ki yi ta kuka da damuwa kar ki yi farinciki a kan wanda har abada bai san kina yi ba sannan bai damu da rayuwarki ta cigaba ko ta tsaya ba. "

Ammah ta gama faɗa tana barin wajen zuwa kitchen ta bar Ummu na kuka wurjajan lokaci ɗaya tana faɗin" Ki yi haƙuri Ammah."
Ammah na jinta ta yi mata banza takaici duk ya kumeta, tana jin baƙin ciki in ta ga Ummu Salma na kuka saboda wannan yaron mara mutumci, wanda bai san kana yi ba har da cewa wai tana son shi, Allah ya tsine ma wannan soyayyar domin su kansu iyayenta bata amfanesu da komai ba.

Nan Ummu ta bar ma Ammah gyaran wakenta ta shige ɗaki ta kwanta a saman gado ta cigaba da rusan kuka kamar ranta zai fita kowa yaƙi ya fahimceta, kowa ya kasa gane yanayinta.
Ko za ta manta da komai ba yanzu ba,  wataƙila sai an ɗauki wani lokaci su yi mata uziri su gane yanayinta har gobe mafarkin Habib take yi sannan tana begensa ba laifinta ba ne laifin zuciyarta ne da ta kasa tsanar shi har yanzu.

Ranar yini ta yi kuka fuskar duk ta yi ja, idanuwana sun tasa Ammah ba ta sake bi ta kanta ba ko abincin da ta shigo mata da shi cewa ta yi in ta gama dama ta tashi ta ci in ba ta ga dama ba ta cigaba da kuka saboda wanda bai san tana yi ba, ba ta sake bi ta kanta ba ballanta ta lallasheta. Ita ce don kanta ta haƙura da kukan ta sauko ta ci abinci jin cikinta na ta murɗawa, su Baffa ba su dawo a ranar ba sai washegari da rana, Ammah kuma ba ta sake mata magana ba, tun bayan gaisuwan safe, itama sai ta kama kanta ta daina kuka amma a ƙasan zuciyanta dankare take da damuwa.
Da ta je gaishe da Baffa idanuwanta ya kalla kawai ya fahimci ta yi kuka.
"Auta har yanzu dai ba ki daina koke-koken nan ba?
Sai ta kasa yi masa musu, tunda gaskiya ya faɗa shuru ta yi kanta na ƙasa tana wasa da gefen hijabin jikinta

"Har yaushe ne za ki kai kina wannan kukan Auta? Kuka fa ba zai yi miki magani ba sannan ba zai taɓa dawo miki da abin da kika rasa ba. Hakuri da tawakwalli shi ne mafita ki samar ma da kanki lafiya ki bar zuciyarki ta huta sai gangar jiki ta amshi canjin ki Auta. Juna biyu kike da shi halin da kike ciki zai iya shafar abin da ke cikin ki, in hakan ta faru kuma kema kina cikin matsala, faruwan haka kuma daidai yake da muma kin saka mu cikin damuwa Auta"

Tunda Baffa ya fara magana ta fara hawaye.
"Ki yi hakuri Auta ki yi tawakalli. Ubangiji yana sane dake, shi ya haɗa ki da Habibu a karon farko, kuma da saninsa ya raba ku, in kina yin haka sai ki yi masa bultulci, ki sani in kika yi hakuri Ubangiji mai rahama ne mai jinƙai, watakila ya yi ma rayuwarki wani kyakyawan canji anan gaba. Canjin da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login