Follow us on social media
Showing 54001 words to 57000 words out of 147042 words
Chapter 19 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
faɗa yana kallon ta, sai ta basar da tambayan tana sakin shi wajen Nauwara ta nufa tana gaishe ta.
"Adda Nauwara ina shirin zuwa na gaishe ku ne fa."
"To ai duk ɗaya ne mu ba ga shi mun zo ba."
Ta ba ta amsa suna gaisawa ta jawo Saudat jikinta tana yi mata fillaanci sai ta ba ta amsa itama da fillancin amma ta haɗa da turanci. Ummu ta yi dariya ta ba ta hannu suka tafa lokaci ɗaya tana faɗin.
"Lalle za ku shirya da Amma yanzu."
Suka yi dariya gabaɗayan su Ammi na gefe ta yi karaf ta ce itama ta yi iya fillanci Ummu ta ce ta yi mata ta ji, bayan ta tambaye ta ina su Isma'il? ganin ba ta gansu ba da yaren fillanci sai kawai Ammi ta ma yar mata da amsar tambayanta da turanci.
Da cewa suna gidan wajen Ammah.
"Ke kam Ammi za ki ko shirya da takwaran na ki kuwa ?
Ammi ta tura baki tana rantsuwan ta iya, Saudat na cewa ba ta iya ba sai kawai Ammi ta fara kuka sai da Ummu ta rumgumeta tana lallashinta. Hamma Jibo ne ya ce a waje za su cigaba da tsayuwa sannan Ummu ta tuna da suna waje ne da sauri ta wuce gaba suka bi bayan ta, tana can ƙokarin neman maƙulli Hamma Jibo ya duƙa ya kwaso mata ledojin da ta ajiye a ƙasa.
"Auta Kasuwa kika je ne?
Ya faɗa lokaci ɗaya yana duba ledojin hannunsa
"E Hamma."
Ta faɗa lokacin da ta ɗauko key din tana ƙoƙarin buɗe ɗakin, shi ko jikinsa ne ya yi sanyi har sake leƙa ledojin ya yi ganin abubuwan dake ciki, sai ya sake ɗagowa yana kallon Ummu lokacin da ta buɗe ɗakin tana cewa su shigo, kallon matarsa ya yi itama ta kalle shi domin tana kusa da shi ne ta ga ƙulle ƙullen su manjan da ke ciki da shinkafa da wake da in an haɗa duka ba su wuce tiya ba.
Sai da suka shiga falon suka zauna ita kuma ta kwashi kayanta zuwa kitchen sannan ta kawo musu ruwan a jug na famfo ne da ta siya, Hamma Jibo ya sake shan mamaki a ran shi sai yana tunanin ko dai mijin Ummu ya samu matsala ne a wajen aiki?
Nauwara ma tunanin da take yi a cikin ranta kenan amma ba ta furta ba.
"Anni ni swanwater na ke so na sha ba wannan ba"
Cewar Saudat. Da ya ke da Annni ƴa'ƴan yayyenta suke kiranta a matsayinta na ƙaramar uwa a gare su.
Ammi na jin haka itama ta ce" Anni ni kuma hollandian zan sha."
Ta faɗa da harshen turanci, Ummu ta kasa mgana ta yi wani wiƙi-wiƙi da idanuwana duk Hamma na lura da ita.
"To yanzu dai ba ni dashi ku fara shan wannan sai na fita na siyo muku."
Ummu ta faɗa cikin yaƙe da dariya.
"Haba. Ƙyale su Auta rigima ce"
"Adda ki bari na fita ko megadi na ba ma saƙo ya siya musu."
Hamma Jibo ne ya saka baki ya ce Aa, yaran ma ya yi musu jan ido ya ce su ɗau ruwa su sha in ba za su sha ba su bar shi, dole suka ɗauka suka sha kaɗan Hamma ma ya sha shi da Nauwara, miƙewa ta yi tana faɗin me za su ci ta dafa musu?
Da sauri Hamma Jibo ya ce" Sai da suka ci abinci muka fito fa, Auta ki yi zaman ki kawai."
"Dad ni egg zan ci "
Ammi ta faɗa kamar za ta yi kuka wannan karon Nauwara ce ta balla mata harara kafin ta ce" Ba shi kike taso kika bari a gidan Ammah ba? Zan zane ki fa"
Ta faɗa mata cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana hararanta Ummu duk ta zama wata iri sai yaƙe take yi amma da ka ganta tana cikin damuwa.
"Auta taho nan ki zauna kusa da ni."
Ya faɗa mata yana mai nuna mata kusa dashi jikinta a sanyaye ta zo ta zauna kusa da shi kanta a ƙasa.
"Auta me ke faruwa ne?
Ya tambaya yana kallon ta, sai ta ɗago tana kallon shi cikin yaƙe kafin ta ce" Me ka gani Hamma? Lafiya ta lau na yi ta zazzaɓi kwana biyu ne "
"Haka Ammah ta ce sannu?
Nauwara ta faɗa tana kallon ta, Amma ta faɗa mata Ummu na da ciki shi ke ɗan ba ta wahala wataƙila shi ya sa duk ta rame.
Hamma Jibo ya yi shuru yana kallonta ya kasa magana.
"Hamma ba fa komai Allah."
Ummu ta sake faɗa tana faɗaɗa mirmishinta wanda ba ta san bai boye damuwarta ba.
"Megidan na ki ba shi da aiki ne yanzu?
Cikin mamaki ta ce" Yana aiki me ka gani Hamma?
"Na ga kin siyo abinci Auta."
Ya faɗa kai tsaye yana kallon ta cikin nazarin ta. Sai ta kasa mgana, kanta na ƙasa amma hawaye take yi ganin haka ya sa Hamma Jibo ya ce Nauwara ta kwashi yaran su shiga ciki zai yi magana da Ummu Salma. Da sauri ta bi umarnin sa ta kwashi yaran suka shiga bedroom ɗin Ummu suka zauna.
"Auta ki faɗa mini abin da ke faruwa ni fa ɗan'uwan ki ne, zan yi komai domin ganin kin yi farinciki."
Kalamansa sake sake ruguza rauninta ta sake fashe masa da kuka, kanta ya dafa yana ɗan bubbugawa alamun lallashi, sai da ta yi kukan ta ya ishe ta sannan ta warware masa komai amma shima ta ɓoye masa abubuwa da yawa kamar yadda ta ɓoye ma su Baffa, sai dai ta bayyana masa ita ke ciyar da kanta tunda har ya gannin ma idanuwansa ƙarya ba na ta ba ne. Har da haɗa sun da aka yi waje ɗaya kamar an samu masalaha duk ta sanar da shi.
Hamma jibo ya ji wani abu ya kama shi na tausayin ƙanwarsa da jin haushin Habib cikin faɗa ya ce" Kuma kike zaune yunwa za ta kashe ki Ummu ga su Baffa a kusa?
Tana kuka ta ce" Hamma ina son aurena sannan ina son iyayena ba na so na saka su cikin damuwa."
"Ai cutar da kanki da kike yi shi ne zai saka su a damuwa Auta."
Ya faɗa yana kallon ta, tana hawaye ta ce" Ka yi hakuri Hamma."
Kanta ya jawo a saman kafaɗanta yana lallashin ta.
"Ya nuna ba ya jin maganar na gaba da shi tunda an masa mgana ya nuna ya ji amma bai ji ba, sakarai ne shi? Ta ina aka taɓa haka? Kawai sai ya ce sai kin zubar da ciki saboda ba shi da tunani?
Ya cigaba da faɗa Ummu na ta kuka tana faɗin Hamma ka yi haƙuri.
"Ya zama dole su Baffa su sake sanin halin da ake ciki."
Ya faɗa yana sakin ta lokaci ɗaya yana ƙokarin ɗauko wayarsa.
"In ba haka ba wata rana zaki mutu ba a sani ba, kin ga yadda kika rame? Kuma kina da juna biyu in wani abu ya same ki fa?
Da sauri Ummu ta sauko ƙasa ta duƙa tana faɗin" Don Allah Hamma ka yi haƙuri, kar ka sanar ma da su Baffa ba na so hankulansu ya sake tashi."
Tsayawa ya yi yana kallon ta cikin mamakin ta.
"Hamma ina son na tsira da aurena ba abin da ya rage mini a yanzu. Don Allah kar ka bari su Baffa su san abin da ke faruwa."
Ya rasa yadda zai yi da ita ganin tana ta kuka shi ya sa sai ya mayar da wayar shi aljihu yana faɗin" To na ji ya isa."
Ya saka hannu ya ɗago ta yana share mata hawaye miƙewa ya yi yana ce mata bari ya je ya dawo.
"Hamma."
"Zan dawo yanzu."
Yana gama faɗin haka ya fice, nan ta zauna tana kuka Nauwara ta fito ta same ta, tana kuka ba ta tambayi ba'asi ba ta zauna tana ta lallashinta Ammi ta yi barci Saudat ne idanuwanta biyu da ya ke akwai wutar nepa sai Nauwara ta kunna mata cartoon zaman shuru suka yi Ummu ta daina kukan amma ba ta daina ajiyar zuciya ba.
Ba daɗewa sai ga Hamma Jibo ya dawo Allah sarki ɗan'uwa. Kayan abinci ne ya siyo mata mai yawa kuma shi ya dinga ɗauka yana shiga mata da shi cikin store, Ummu ta yi hawaye ta yi kuka tana yi masa godiya ba abin da bai siya mata ba har kayan tea sannan ya tura mata 100k ya ce ta riƙe a hannunta. Ba su daɗe ba ya ce su tashi su tafi da alƙawarin zai faɗa ma Baffa halin da take ciki amma ba zai bari a kashe mata aure ba, sai dai za a sake kiran Habibu a ji dalilin shi na yi mata horan yunwa.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t
*09*
Suna tafe a mota za su koma gidan Ammah, Nauwara ta fahimci mijinta na cikin damuwa tun fitowan su daga gidan Ummu fuskar shi ta nuna damuwar da yake ciki, ta fahimci akwai matsala amma ba ta so ta yi shisshigi tunda bai sanar da ita komai ba. Ga kukan da Ummu Salma ta yi ta yi, sannan ga kayan abincin da ya siya mata shima wani alama ne da cewa wani abu na faruwa.
Hannunta ta ɗora saman hannunsa dake saman sitiyari, ta riƙe ta ɗan matsa da ya sa ya kalleta lokaci ɗaya yana ma yar da hankalin shi kan tukinsa su Saudat na baya suna ta wasa ba su ma fahimci abin da ke faruwa a gaban motan ba.
"Ina fatan ba wata matsala ba ne game da Auta ba ko?
Nauwara ta faɗa cikin kwantar da kai tare da kulawa ga mijinta Jibril Hadi Baba.
Kai ya gyaɗa mata kafin ya sauke ajiyar zuciya.
"In sha Allahu komai zai yi dai dai."
"Allah ya sa. In sha Allahu."
Ta amsa masa cikin jinjina masa kai lokaci ɗaya tana yi masa mirmishi, shima sai ya mayar mata da martanin mirmishin nata, amma gabaɗaya baya cikin natsuwarsa halin da ya iske Ummu Salma a ciki ya gama ta yar masa da hankali shi ya sa suna komawa gida sun ci sa'a Baffa ya dawo lokacin ɗakinsa kawai ya shiga Nauwara kuma da yara suka ya da zango a falon Ammah in da suka iske su Hassan da Hussaini na ta wassani isma'il ne ma ya yi barci.
Baffa ya razana da labarin da Hamma Jibo ya sanar da shi, ya yi masa zuru yana kallon sa cikin ɗimuwa da mamakin labarin da ya ba shi, wai Ummu na yini da yunwa saboda ba abinci ya tuna yadda store ɗin su yake rumbatsa da kayan abinci wani ba ya karewa ake sake kawo wasu, Baffa ba zai iya kirga shekarun da ya ɗauka bai siya hatsi ba, haihuwa ce ta yi masa rana har da ma waɗanda bai haifa ba suna yi masa, amma a ce ɗiyarsa na aure a garin nan amma tana kwana da yunwa saboda son rai da mugunta da zalunci irin na Habibu.
"Innalillahi wa'inna alaihirraju'un."
Baffa ya samu kan shi da furtawa saboda hankalin shi ya tashi matuƙa.
"Baffa wallahi hankalina ya tashi da yadda na ga Auta. Ba zan ɓoye maka ba sam ban ji daɗin ganin ta ba, tunda na baro gidan ta na ke cikin damuwa. Baffa Auta ta sauya tana neman mutuwa a cikin gidan nan ba wanda ya sani."
Ya karishe faɗa kamar ya yi kuka, da man shi yana da tausayi da rauni.
"Baffa ina tambayanta sai kawai ta fashe mini kuka, Baffa ka ga yadda Auta ke kuka, kamar ran ta zai fita amma a haka roƙona take yi kar na faɗa muku wai ba ta so hankalin ku ya tashi ni kuma na ce sai na sanar daku domin dole ne a yi wani abu tun kafin Auta ta samu wata matsalan a dawo ana wallahi tallahi Baffa."
Ya dire maaganarsa yana shafa naman goshin sa cikin damuwa.
"Gwara da ba ka rufe ni ba Jibo. Ai wannan ba mganar da za a yi shuru ba ne. Tunda tun farko mun sako waliyin shi a ciki nan aka kira shi ya ce ya bar mganar in sha Allahu ashe yaudaran mu ya yi, ya koma ya sauya wani tsarin to Jibo horon yunwa fa? Kashe mana Auta yake son yi ko mene ne manufarsa?
Baffa ya faɗa yana kallon Hamma Jibo cikin damuwa muraranta da ya bayyana a saman fuskar shi.
"Mene ne mafita Baffa?
Baffa ya yi shuru yana tunani kafin ya ce" Wannan karon ba zan jira ma Baffan ku Umaru ya zo ba, zan kira shi na ce ya tura mini lambar shi waliyin Habibun zan kira shi na ce masa ina son mu haɗu ni da kaina zan warware masa komai sannan na faɗa masa ya sanar da ɗan shi in har ba ya son Ummu ne ya dawo mini da ita gida ni ina da abincin da zan ciyar da ita ba wai ya gagare ni ba ne"
Yadda Baffa ke magana kaɗai ya isa ka fahimci ya kai makura a takaicin Habibu, ba abin da ya fi ƙona masa rai a ciki irin horan yunwa ga ciki a jikinta amma ya barta tana wahala saboda wata manufarsa ta banza da wofi. To shi ba zai ɗauka ka ba, ba a dole ya sako masa yarsa in ba zai iya rike amana kamar yadda ya ɗau yaƙini ba.
"Baffa na lura Auta na son mijinta. Kar a yi gaggawan raba su a tsaya dai a sake samun masalaha."
Baffa ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce" To son banza Jibo? Me son ya tsinana mata balle mu iyayenta! Kuma ni na ma fara tamtama in har yanzu yaron nan Habibu na son Auta. Domin mai son ka zai so haɗa zuru'a da kai, sannan ba zai taba wulaƙanta ka ba, ballanta har yana da shi da gangan ya yi maka horo da yunwa."
"Haka ne Baffa"
Hamma Jibo ya faɗa cikin gamsuwa da mganar Baffa amma yadda Ummu ke kuka har yanzu hoton ya kasa ɓace masa.
"Ko tana son shi, in shi ya nuna baya ra'ayin ta ai dole ta haƙura."
Hamma Jibo ya yi shuru duk jikinsa ya yi sanyi. Nan take Baffa ya kira ɗan'uwansa Baffa Umaru bayan sun gaisa ya ce masa yana son ya tura masa lambar waliyin Habibu mijin Auta Ummu Salama.
"Hadi lafiya kuwa?
Baffa Umru ya tambaya daga can bangaren cikin mamaki, domin shi a tunanin shi an samu masalaha tsakanin Auta da mijinta tun bayan zaman da suka yi.
"Zan sanar da kai daga baya. Yanzu dai ka turo mini lambar ina jira.'
Sai bai matsa masa ba ya amsa masa da to zai tura masa, suna yanke wayar mintina biyar tsakani ya turo masa lambar, Hamma Jibo ya ba ma wayar ta sa ya ciro masa lambar ya saka a cikin wayar sannan ya ce ya kira ya ba shi zai yi mgana da shi.
Kira ɗaya ba ta ko daɗe tana kara ba Alhaji Sheriff ya ɗaga wayar da sallama Baffa ya amsa bayan gaisuwa sai Baffa ya gabatar da kansa.
"Sunana Alhaji Hadi Baba ni ne mahaifin Ummu Salma, matar yaron wajen ku Habibu."
Nan da Alhaji Sherif ya washe baki kamar yana ganin shi, suka sake gaisawa tunda ba su da lambar juna, daman da Baffa Umaru ne suke magana tun neman auren.
"Alhaji lafiya kuwa? Ina fatan ba wata matsala ce ta sake tasowa daga bangaren yaran ba?
Alhaji Sheriff ya tambaya daga can bangaren, domin ya ji mamakin kiran na sirikin Habibu a wannan lokacin.
"Lafiya lau, in ba damuwa adireshin gidan ka za ka turo mini zan zo har gida da safe na same ka, akwai mganganun da za mu tattauna ne."
Baffa ya faɗa cikin dattaƙon sa.
"Haba Alhaji ai ba sai ka zo ba. Ni zan zo na same ka a gobe da safen in sha Allahu."
Amma Baffa ya ce aa shi ya yi niyar zuwa saboda haka ya bar shi kawai ya zo, dole ya amince suna gama waya da Baffa nan take ya tura masa adireshin gidan shi da ke At Unit cikin gari, ya yi zuru shi kaɗai yana tunanin me kuma ya sake faruwa? Amma jikinsa ya ba shi koma me zai kawo surukin Habibu wajen sa to ba zuwan lafiya ba ne, in ko haka ne Habibu ya gama kunyata shi da girman shi.
Bangaren Baffa kuma, da shi da Hamma Jibo suka shirya za su je gidan Alhaji Sheriif da safe Baffa ya ce kar Hamma Jibo ya sanar ma da Ammah komai sai zuwa nan gaba har sua ga abin da zai je ya dawo. Shi ya sa ya yi shuru bai faɗa mata ba shima Baffa ko a fuska bai nuna mata wani abu ba, tausayin Ummu ya dame shi
shi ya sa ko a waya ya kasa kiran ta, baya so ya ji muryanta sai ta saka shi kuka.
Ammah ko ba ta san abin da ke faruwa ba, da ta tambayi Nauwara yadda suka baro Ummu sai ta ce tana nan lafiya Hamma Jibo ma haka ya ce mata su Saudat kuma Allah ya sa yan surutun ba sa kusa da ta ce ta ga Anni na kuka kamar Allah ya rufe mata baki ita da Ammi ba su yi surutun ba.
Baffa kwana ya yi bai yi barci ba. Ba kan Ummu farau zawarci ba ya san shi take tsoro, shi ko da ya bar yarsa ta mutu a gidan wanda ba shi da asara gwara duniya ta zage shi , zai ajiye wani fillanci ya tsaya mata. Shi me ye bai gani ba? Nan ƙanwarsa Fatima ta dawo masa da yaro a cikin jinin haihuwa da takardan saki kuma ya karɓeta ya riƙe ta gam, to ba wani sabon abu ba ne in Ummu ta dawo masa da ciki gida, a wannan karon ma godiya zai yi ma Allah ya karba duka kaddaransa, daga karshe da ya gaji da juye juye sai ya tashi ya shiga tiolet ya ɗauro alwala ya yi nafilfilu, tare da addu'o'i ma su yawa akan in har babu alheri a auren Auta da mijinta Allah ya sauƙaƙa mata kaddaranta.
Da Ammah ta farka ta gan shi yana ta salla, sai itama ta mike ta shiga tiolet ta ɗauro alwala ta zo ta jera a gefen shi, ta tayar da salla ba su suka koma suka kwanta ba sai wajen uku na dare, asuba na yi Baffa ya ta da Ammah shi kuma ya yi alwala zuwa masallaci.
Nauwara da yara suna bangaren