Follow us on social media

Showing 99001 words to 102000 words out of 147042 words

Chapter 34 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

nufa daga kudu, sai ka ma lura sosai sannan za ka fahimci akwai ƙofa a wajen tana zuwa ta buɗe a hankali ta shiga, sai ga ta a wani dogon korido tana zuwa karshen koridon sai ga wata ƙofa itama tana buɗewa ta shiga sai ga ta cikin wani falo mai girma da ya ji kayan alfarma sai dai falon ya yi duhu tunda gabaɗaya labulanyan falo da windows ɗin suna rufe ne, ba ka jin motsin komai a falon sai dai na sanyi-sanyi da ƙamshin turaren wuta mai shiga hanci sannan kuma mai sanyaya zuciya.

Daga gabas da falon akwai wata ƙofa ita ta nufa ta ɗan tsaya sannan ta ɗan ƙwanƙwasa shuru ba wani motsi na wani lokaci sannan ta murɗa handel ɗin ta shiga cikin ɗakin.
Bedroom ne shima kamar falon ya yi duhu dum, tunda shima duka windows ɗin a rufe suke sannan labulayan a sake suke.

Tana tafiya takalminta na taka cafet din da ya malale bedroom ɗin idanuwanta na hango masa shi sambal cikin bargo, ba a ganin fuskarsa tunda ya yi kwanciyar gefen dama ne ya danne fuskarsa da filon da ya rumgume a hannun shi da shi.

Har ta iso gaban shi bai sani ba domin barcin sa kawai yake yi, amma fa ko hucin numfashin sa ba ka ji hakan zai alamta maka ko barcinsa cikin natsuwa yake yi
Ta ɗan jima tsaye tana kallon shi, kafin ta ɗan matsa baya ta isa jikin window ɗin ɗakin ta zage labule gefe da gefe sannan ta buɗe glass ɗin haske ya shigo.

Kan drowers ɗin gefen gadon ta ɗau remot ta rage karfin A.C ɗin. Ta rasa yadda aka yi Lamiɗo ke son sanyi haka da yawa daga ɗan shigowarta ɗakin barcinsa sai da ta ji sanyin har kasusuwan jikinta.
Shi fa ko hatta handel ɗin kofar ɗakin shi in ka taɓa sanyi ne ƙalau saboda ko yana nan ko baya nan  ba a kashe A.C ɗakin 24/7 cikin sanyi yake yi, ita ta yi ta cewa sanyin ya yi yawa amma shi haka yake so duk da bai taɓa faɗa mata yana son sanyi ba a zamansu na shidda biyar ta fahimci haka, in ta zo ta ga ya ƙure sanyin za ta ɗauka ta rage ba zai yi mata magana ba amma tana barin wajen zai ƙara karfin gudun sanyi, tun ba ta fahimta ba har ta gane, daga baya sai ta fahimci haka Allah ya yi sa yana son rayuwa cikin sanyi, in ta ma tuna shi da yake rayuwa a saman ruwa ya saba da sanyi ba lalle ya yi masa illa ko cutarwa ba.

Har ta dawo ta zauna a gefen gadon saitin da kafafunsa ke shimfiɗe bai sani ba. Bargon ya ɗan yaye kafarsa doguwa fara sambal mai cike da gargasa mai yawa ta bayyana a waje, ɗan mirmishi ta yi har bakinta na matsowa wayarta ta ajiye a gefenta sannan ta saka taussaun hannayenta ta ɗago kafar tasa ta ɗora a saman cinyarta, lokaci ɗaya tana jan yatsun kafafunsa da suke wasu irin dogaye tafin kafarsa wani irin taushi kamar bai taɓa taka k
Ƙasa ba saboda yadda suke wani ja ja da fari fari kal, haka kumbunansaa kamar kumba bai taɓa fitowa ba tsabar yadda suke tas da su. Har ta gama jan yatsun na shi kuma duka sun yi ƙara, ita haka kurum tana son kafafun Lamiɗo balle ma in ta yi ta jan 'yan yatsunsa suka yi ta ƙaran nan yana saka ta a cikin nishaɗi.
Ɗayan ta jawo daga cikin bargo itama ta ɗaura a saman cinyarta itama kamar ɗayan haka ta yi mata amma ko motsi ma mallakin kafar bai yi ba duk da ta san zuwa yanzu ya san da wanzuwarta a ɗakin tunda ba shi da irin nauyin barcin nan.

Gargasan kafarsa guda ɗaya ta ja da ƙarfi har sai da ta tsinke, hakan da ta yi ne ya sa ya ɗan motsa kafarsa guda ɗaya sai ta kalle shi da mirmishi a fuskarta kafin a hankali ta ce.

"Ranka ya daɗe ka tashi haka nan yamma ta yi "

Ta faɗa wani wani irin omo mai cike da aji da sanin ciwon kai
Shuru kamar ma baya jin ta, domin bai kara motsawa ba

"Tun jiya da daddare da ka shigo gidan nan kake barci har wayewar garin yau. Ba ka ci komai ba fa Ranka ya daɗe?

Ta sake faɗa tana ɗan jan gargasan kafarsa guda ɗaya.
Sakwan goma sannan ya iya motsawa daga kwanciyar lokaci ɗaya yana cire filon da ya rufe fuskar shi ya mayar da shi bayan shi, sannan ya miƙe a hankali kamar bayansa ya samu matssala bakinsa na ɗan motsi yana karanta adduar tashi daga barci, lokaci ɗaya kuma yana sauke kafafunsa daga saman cinyarta ya samar musu mazauni a saman lallausan cafet ɗin ɗakin.
Kafin kuma da sauri ya saka hannu yana kare fuskarshi saboda hasken waje ya ɗan shigar masa ido.

"Ni na buɗe windows saboda haske ya shigo kaɗan."

Ta faɗa cikin sautin ta, akwai wuta amma ba ta kunna gulop ba sanin ba ya son haske sosai. 
Miƙewa ta yi ta ɗuka a gaban shi hannu kawai ta ɗan zira kasan gadon sai ga shi ta jawo masa wani ttatausan takalmi na maza zuwa wajen kafafunsa.

Ba musu ya zura dogayen kafafunsa a ciki sannan ya yunkura ya miƙe lokaci ɗaya itama tana miƙewa sai ga ta a gaban shi yar firit.  Kallon shi take yi tana mirmishi a fuskarta shima ya kalleta da idanuwansa masu ɗan girma kaɗan kafin ya ɗan rusuna su, mirmishi ya yi mata amma daga gefe da gefen bakin shi ne kawai ya ɗan motsa.

Muhammad Nasiru Muhammad (Lamiɗo) Sannan kuma Yariman Daura, magajin mai Maimartaba Yarima mai jiran gado.

Wani irin dogon namiji ne faffaɗa, ga tsaho ga jikin murjewa ta cikakkun maza. Lamiɗo na da tsawo sosai domin ko size ɗin takalminsa 45 ne, kuma wannan tsahon na zuru'ar sarkin Jafaru ne, sarki na 11 a tarihin masarautar Daura, shi ne asalin tsatson su har kawo yanzu. Su ke da wannan tsawon kamar ƙiran samudawan farko, sannan suna da girman jiki matansu da mazan su. To Lamiɗo haka yake har ma yafi mahaifinsa Maimartaba Alhaji Dr Nasiru Muhammad Daura cika ido da ƙwarjini. Ahalinsa na Daura ba su da hasken fata sosai amma shi Lamido fari ne jajir, saboda Mami farar bafullatana ce kyakyawa, a wajenta ya ɗauko dogon hanci amma fuskarsa tana da ɗan faɗi ita kuma ta mahaifinsa ce, amma sumar kansa mai santsi da cika ta Mami ce, da yake shi ma'abocin tara suma ne gashi nan sumar ta yi yawa ta kwanta luf tana shan gyara. Sannan bakin sa yana da ɗan faɗi kaɗan zagaye da sajensa da ya zagayo har gemunsa da ya yi ɗan tsawo. Lamiɗo tun yana saurayinsa yana son tara sumar kai da barin gemu har kuma yanzu bai sauka daga kan wannan daɓi'an nasa ba.
Ko a yanzu ma gashi duk ya cika fuskarsa amma duk da haka kyawunsa da cikar zatinsa sun bayyana. Balle ma da ya fara tafiya ya bar gaban Balkisu cikin tafiyarsa ta gif gif ta cikkakun mazan duniya kallo ɗaya za ka yi masa ka shaida Muhammadu ɗan Nasiru da Fatima Sadauki ne, kuma jarumi ne yanayin sa irin na fusattatun maza ne giant masu mazantaka da ke dukan zuciyan duk wanda ya kalle su, jarumatar su ba ya ɓoyuwa, sannan suna iya rike numfashin wanda ya kalle su gaba da gaba na wani lokaci saboda ƙwarjini da haibar da baiwa ce Allah ya ba su, sannan yanayin su komai karatun mutum akan sanin hallayan ɗan adam baka isa ka fahimci yana yin su ba, ko ka ce ga abin da suke so ko ba sa so ba, irin su Lamiɗo sai zama ya haɗaku na shekaru masu yawa shi ne har za ka iya fahimtar lamuran rayuwarsu, amma ba wai don su furta da bakin su ba.

"Wanka za ka yi ranka ya daɗe?

Balkisu ta faɗa tana mai kallon bayan shi.
"E.."
Ya amsa mata cikin dakakkiyar muryansa amma cikin sanyin amo a karon farko sannan ya tura ƙofar tiolet ɗin ya shige ya rufo.

  Numfashi ta fesar tana mai sake bin bayan shi da kallo bayan ya shige. Sanye yake da bakin wando wanda iyakarsa gwiwan kafafunsa sannan jikinsa wata farar riga ce mai dogon hannu tana da botira a gaba amma bai saka boturan ba, ƙirjinsa mai cike da gargasa ya bayyana a waje kuma tasan ma dalilin da yasa ya yi saurin barin in da take tsaye saboda haka ne.
Tunda take ba ta taɓa ganin namiji mai kunya irin mijinta Lamiɗo ba

Yau shekaran su shidda da auren su tare da albarkan ya'ya biyu amma bai taɓa yarda ta gan shi daga sama har ƙasa naked ba, itama za ta yi rantsuwa bai taɓa kallonta haka ba. Da farko ta ɗauka ko ba ya son ta ne yasa yake yin haka sai da zaman su ya mika ta fahimci haka Allah ya yi shi, yana jin kunyar tsaraici shi ya sa ko kayan barci baya sakawa masu sharara, in zai kwanta sai ya saka dogon wando, da riga mai dogon hannu ya rufe jikinsa ba ya so ya fidda wani tsaraici na jikinsa duk ko da ita ɗin matarsa ce, yana jin nauyi da kunyar ta gan shi a haka, shima bai iya mata dogon kallon matukar ta fidda masa tsiraici, domin akwai wani lokacin tana da cikin Sultan suna gudanar da Sunna ta kudiri niyyar sai ta ga abin da Allah ya hallata mata. Ita da mijinta amma ace ba ta san girman shi ba, sai da ta bari sun natsa cikin harkan sannan ta kunna hasken ɗakin, ranar ta ga abin mamaki da saurin gaske ya faɗa gefenta cikin zafin nama ya jawo bargon dake gefe ya rufe jikinsa, sannan ya juya mata baya cikin wani sauti amon murya ya ce itama ta rufe jikinta. Ta daɗe lamarin yana ba ta mamaki kuma ta ji haushi har sai da ta yi masa magana da cewa ita fa matarsa ce halaliyarsa amma yana jin kunyar ta ga jikinsa, ko shima ya ga jikinta. Har ta gama maganganunta bai ce mata komai ba, bai ma sake tayar da maganar ba sai da ya tafi ne ya tura mata da saƙon cewa ta yi haƙuri daga haka bai ce komai ba kuma bai sauya ba, dole ita ta bi shi a yadda yake tunda haka Allah ya hallice shi, hallayan shi ne a haka kuma ba zai iya canza kan shi ba.

Gadon ta ɗan kakkabe tana ninke farin bargon. Gabaɗaya ɗakin kalan baki da fari ne Lamiɗo na son abu fari kuma yana son baki ko kayan shi rabi farare ne rabin su kuma baƙaƙe ne, bayan ta gyara gadon ta ninke bargon ta ɗan saka shi a gefen gadon ya ɗan ba da styel, itama sai ta koma ta zauna tana ɗan mirmishi.
Tana son mjinta tana son Lamiɗo, lokacin da mahaifinta ya kirata akan Lamiɗo ta ji wani iri, da jin labarin Baban shi ne ya yi gadon Sarauta, mahaifiyar shi ba yar kowa ba ce. Bata taɓa tunanin haka za ta ga Lamiɗo ba, sai da ya zo haɗuwar su ta farko anan ta fahimci ko a cikin maza shi na dabam ne, ko ita da take jinin sarauta gaba da baya tunda kakanta na bangaren uwa ya yi sarautan Kano, to ba za ta nuna ma Lamido iko da sarauta ba, tafiyar shi, maganar shi, yanayin tsarin rayuwarsa kaf kamar wanda aka haifa a gidan sarauta ya kuma girma acan, sai ga shi ta ji labarin shi bai ma zauna a Daura ba sai da ya girma ya zo. Kenan duk wani abu na hallayar shi ko yanayinsa halitar shi ce haka Allah ya yi shi.

Ba auren soyayya suka yi ba kakar sa Fulanin Daura ce ta zo ta nema masa auran ta, saboda kyayawan alaqan da ke tsakanin masarautun ba jayayya aka amince, kuma daman a zamanin da muke ciki ƴa'ƴan sarakuna sai ƴaƴan sarakuna ƴan'uwansu ko kuma ƴaƴan masu riƙe da madakan ikon a kasar gabaɗaya. Shi ya sa sai haɗin ya yi daidai duk da ana ta cewa mahaifiyar Lamiɗo ba ƴar sarauta ba ce wataƙika ba zai yi gadon Sarauta ba amma kwarjinsa da tasirinsa bai gushe ba. Balkisu ma tun a ganin farko da ta yi masa ta ce ya yi mata tana son shi. Duk a tunanin ta wannan shuru shurun na shi, da wannan ji da kan duk zai sauke su bayan aure. Itama jinin sarauta ne tana ji da takama da girman kai amna haɗuwarta da Lamiɗo sai ta sara ta kuma jinjina masa ta san ita ba ta yi komai ba. Bayan auren su babu abin da ya sauya Balkisu ta yi tunanin za su yi soyayya ta kwatance a yanayin yadda take, yar gayu wayayyiya mai ilimi. Amma sai ta ga sabanin haka, shi fa ba ka iya gane yanayin da yake ciki yana son abu ko ba ya so duk ba ka isa ka gane ba. Ta sha wahala sosai kafin ta fahimci Mijin data aura, komai in za ta yi masa ko ya yi masa ko bai yi masa ba, ba zai taɓa magana ba in ya yi masa ba zai nuna alamu ba, in ma bai yi masa ba, ba zai nuna ba.

SSai da ta yi ta karatun nazarin hallayan Lamiɗo sannan ta fahimce shi, shekaran su shidda da aure ba ta taɓa jin ya ce yana son ta ba, sunan ta ma bai wuce sau goma ya taɓa kira ba, in ma magana ta kama sa dole sai dai ya yi maganarsa kawai kai tsaye, da yawan lukata baya gida in ya kirata a waya suna gaisawa ya tambayi yara bai kara cewa komai sai dai in ita ce ta dauko masa hira. In ya dawo za su zauna a gida ɗaya amma bayan gaisuwan safe in dai ba itace ta yi masa magana ba za su iya yini su kwana ba su sake yi ma juna magana ba. Zai iya yini a bangarensa bai fito ba, wani lokacin sai dare in ya fito cin abinci tare da yara. Tunda duk da yanayin shi yana son yara yana wasa da su Sultan, suma ɗin akwai lokacin haka in yana son kaɗaici ma ba zai fito daga bangarensa ba yana son shuru fiye da komai a rayuwansa.

Bangaren abinci kuma sai da Ammah ta taimaka mata ta ɗan ba ta satar amsa, duk da ba ita ke yin abincin ba sai dai ta ba da umarnin a dafa masa. Lamiɗo na cin tuwo amma ba ya shan duk wata miya mai yauƙi, ba ya son yaji ba ya son mai ya yi yawa. Ba ya cin naman jan akuya sai kaza ko kifi, kuma ba ya cin shinkafa tsura ko wani abu sai da miya, miyar ko wata iri amma ban da miyar yauƙi, yana son ganye sosai. Da Balkisu ba ta sani ba ta yi ba shi miyar yauƙi sannan ita tana son cin yaji. Gashi dai ba ya so amma ba zai taɓa magana ba, sai dai ta ga baya ci da yawa sai dai ma wani lokacin ya yi ta cin abun gaya ba miya, in ta yi masa mgana sai dai kawai ya yi mata shuru, Ammah ce ta taimaketa anan ne ta san ba ya shan miyan yauki. Shi fa in dai shi zai fada maka abin da yake so da bakinsa to ba za ka taɓa sani ba. Tuni Balkisu ta sauke jin kai da sarauta ta fara karantan mijinta domin ta san cewa ba irin mijin kowa ba ne, Lamiɗo mijin Balkisu na dabam ne a cikin maza.

Da haka ta samu ta karance shi tsab har suke zaune lafiya cikin mutumtawa. Ko bai furta da bakin shi yana son ta ba, tana ganin haka a aikace. Ba ta damu ba ta amince da na shi salon nuna son ne a haka bai taɓa danne mata hakkinta na aure ba, tana daga cikin sahun gaba a matan da suka yi sa'an aure, ta samu miji na nunawa sa'a ga shi gwarZo kuma jarumin namiji mai iyawa da duka bukatunta, farkon auren su sai ta zauna jiran sai ya zo gareta ta yi ta cutuwa shi kuma ko yana son abu ba ya nema. Ba ma ka gane yana so ko ba ya so. Shi ya sa da ta fahimce shi ta riƙa ba da kai bori ya hau abin mamaki kuma sai ya fi ta ma rawan jiki da son nuna jin daɗinsa, tun daga lokacin ba ruwanta in tana bukatarsa za ta je gare sa shi kuma a kowani hali yake ciki bai taɓa tankwafar da bukatarta ba sai ya tabbatar da ta samu gamsuwa ɗari bisa ɗari.

Ta yi nisa cikin tunaninta ba ta ji karan buɗe kofar toilet ba sai dai kawai ta gan shi ya fito sanye da rigan wanka baka, gaban rigan ta ɗan buɗe, ganin ta a zaune kuma sun haɗa ido.  Da sauri ya juya baya lokaci ɗaya yana jan rigar wankan ya rufe ƙirjinsa.

"Me za ka ci na sa Debora ta dafa maka."
Ta faɗa cikin harshen turanci lokaci ɗaya tana mikewa tsaye.

"Anything is ok. Buh zan fara da Coffea mai zafi."
Shima ya mayar mata da martanin maganarta cikin harshen turancu muryansa mai kama da ta jaruman maza.

"Okay"

Ta faɗa, bai ma jira ta fice ba shi ya fara shigewa cikin clothset ɗin sa, domin ya sauya kaya. Ita kuma sai ta fice tana zuwa main falo su Sultan na shigowa falon James na bin bayansu ɗauke da jakunkunansu da basket ɗin su na makaranta
Suna ganinta Beena yarinya yar shekara uku
Yar ajin Baby class dabar dabar da lukutun jikinta na yara ƴan hutu ta nufe ta da gudu da karamar muryanta tana kiran sunanta

"Momi."

Da sauri ta tarbeta ta ɗaga ta sama tana nishi, tunda Beena akwai jiki kamar kazar turawa.
"My Beena."
Ta faɗa tana jan kumatun ta, ita kuma ta tsinke da magana tana fada mata ta ci egg a makaranta da plantain, da muryansu ta yara da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login