Follow us on social media

Showing 138001 words to 141000 words out of 147042 words

Chapter 47 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

da ke cikinta. Ba ta fatan wata danganta ta sake shiga tsakaninta da Habibu, ba ta ƙaunar sake ganinsa a rayuwanta shi ya sa ta kudirta a ranta cewa za ta yi nesa da rayuwar Habibu da duniyarsa yadda ba zai taɓa cin mata ba har abada. Cikin daman ya ce ya bar mata to babu sauran wani abu da ya rage a tsakaninsu

Tana hawaye wasu na korar wasu, amma tana ji kamar komai na ta na sauyawa. Tabbas dole ne ta manta komai in dai har tana so ta sake cigaba da rayuwa a matsayin Ummu Salma Hadi Baba
Tana kallon gajimare da gizai-gizai tana kuka tana jin ta bar Jimeta har abada sai da ta zo da ziyara amma garin ya bar mata wani wawaken taɓon da ba zai taɓa cikewa ba har gaban abada.

Wataƙila tafiyar Ummu na ɗan lokaci ne, amma Jimeta za ta sake maraba da ita a lokacin da ta yanke dukkan tsammani da samun rayuwa mai inganci.

***
*ANGUWAN DOUGIREI*
JIMETA.
9:50pm

A kayattacen sabon gidan Habib shi ne zaune a saman kujera mai zaman mutum ɗaya kan jikin shi kuma Shamsiya ce a lafe marabanta da tsirara kaɗan ne saboda yanayin ƙaramar rigar dake jikinta da ba ta iya ɓoye sirrukan jikinta ba. shima ɗin ba shi da riga daga shi sai ƙaramin wando amma falon akwai duhu da yake dare ya ɗan fara shiga. Ba kuma don ba wuta ba ne ya sa falon ya yi duhu ba, masu gidan ne suka rage hasken falon suka bar na talabijin ɗin da suke kallo wanda ke ɗan haskaka falon kaɗan-kaɗan.

Hira suke ƙasa-ƙasa ba tare da sun yi wani motsi ba ballatana aji abin da suke furta ma juna, talabijin ɗin ma shi yake ta ɓaɓatu shi kaɗai akan tashar MBC2, su hankulansu na kan junan su lokaci bayan lokaci kuma suna sumbatar bakunan junansu cike da soyayya tare da muradi mai girma.

"Sweety ina son ka, kai ne rayuwata."
Shamsiya ta faɗa cikin irin amo a muryanta.
Kanta na saman kirjinsa yana shafa suman kanta dake tsefe har zuwa ƙasan wuyanta zuwa ƙirjinta tunda rigan mai budaɗɗen wuya ne.

"Nima ina son ki Sweety,da ban same ki ba da na zama mai asara."
Ya faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗago fuskarta ya sumbaci bakinta itama sai ta ba shi dama suka rike kan juna suna masu sumbatar juna kamar za su cinye bakin juna lokaci ɗaya hannayensu na kara kaina a kan jikunna junansu cikin soyayya da muradi mai girma.

Sun daɗe cikin wannan yanayin kafin su saki bakin juna su koma su sake curewa waje ɗaya suna masu sauke ajiyar zuciya a jejjere, Habib ya sake matse Shamsiya dake kan jikinsa kamar ya mayar da ita cikinsa haka yake ji, bai san haka yake son ta ba sai da ya mallaketa bai san bai taɓa son Ummu Salma ba sai da ya auri Shamsiya daga lokacin ya fara ganin tarin bambamcin dake tsakanin su.

Shamsiya sonta yake yi da dukkan zuciyarsa zai iya zama da ita na har abada in dai tana tare da shi ba tare da ya takura mata ba. A farkon auren shi da Ummu Salma shi kan shi ya ɗauka yana daga cikin harijan maza ma su yawan buƙata domin yadda yake hakarta kamar Allah ya aikosa sai da ya auri Shamsiya ya ƙaryata haka, yau kimanin sati uku da auran su amma komai na rayuwarsa ya sauya. In dai zai ganta ga ta gashi ko ba za su yi wani abu ba farinciki ya ishe shi, sonta ne ke masa nauyi a zuciyarsa ba sha'awanta ba shi ya sa ko bayan faman da ya yi kafin ya mayar da ita cikakkiyar mace bai wuce sau uku zuwa huɗu suka marabanci juna ba tsausayinta yake ji ba ya so ya ba ta wahala, ita kaɗai ne ya ke jin daɗin yin wasanni da ita aamm a lokacin Ummu Salma wannan ba ya yi masa shi dai kawai sha'awanta ne ke azalzalansa so kawai ya ke yi ya marabance ta domin kauda wannan kaifin sha'awan a zuciyarsa wani abu kamar asiri in yanzu zai gama to yana sake kallonta zai ji yana son ƙari, har yanzu in ya kwanta barci ko in ya kaɗaice tana yawan faɗowa tunaninsa ko da ya saketa ba wai wannan ƙishiruwan sha'awan nata da yake ji ya gushe daga zuciyarsa da gangan jikinsa ba ne, kawai ya rabu da ita ne saboda lokaci ya yi amma karya yake yi har gobe akwai sauran abin mamora a jikin Ummu Salma.

"Sweety'
Kamar daga sama ya ji Shamsiya na kira sunan shi ya faɗa dogon tunani sannan ne fa ya yi saurin dawowa cikin hayyacinsa.

"Naam Sweety me ya faru?
Ya faɗa yana mai kallon fuskarta ta cikin duhun ɗakin.
Baki ta tura masa kafin ta ce" Gani a tare dakai tunanin me za ka yi kuma?
Sumbatar bakinta ya yi yana yi mata mirmishi kafin ya ce" Ai ke ce tunanina kuma ga ki a tare da ni Sweety na"
Itama sai ta sake sumbatar bakin shi tana yi masa wani irin kallo.

"I love you mai tsada na."
"Love you too madara ta."
Ya mayar mata da martaninta yana mai shafa bayanta zuwa ƙugunta.

"Ko tunanin tsohuwar matarka kake yi ne?
Ta faɗa tana masa dariya.
Fuska ya haɗa kafin ya ce" Kin fara ko?
Ɗan gemunsa ta ja kafin ta ce" Ai kun yi zaman aure ba laifi ba ne in ka tuna good memories ɗin ku tare da juna."
Hannunta ya ture daga fuskarsa.
Sannan ya kalleta yana faɗin" In ina tare dake ina mantawa da kaina ne Sweety,  ki sani ko da tana nan ke ce tunanina bayan ba ta ma ke ce tunanina, ni na ma manta da ita ko tana ma wani hali oho."
Ya faɗa cikin alhini da amon tausayi.
Shamsiya ta kwashe da dariya har tana sarƙewa sai da ya riƙa bubbuga bayanta yana yi mata sannu.

"Kin gani ko? Ki yi a hankali kin ji ko?
Yake faɗa yana ɗan shafa bayanta har da ma kirjinta.
Amma duk da haka ba ta daina dariyan da ta fara ba.

"Me ya saka ki dariya!
Ya tambaya shima yana ɗan taya ta dariyan kaɗan.

"Ummu Salma na tuna, baiwar Allah har gobe tana tsananin son ka."
Sai ta sake kecewa da dariya.
Shima dariyan ya ɗan saki kafin ya ce" To ai yanzu dolenta za ta cire ni a zuciyanta domin ta fahimci ba a hallice ni don ita ba, an hallice ni don ke ce kawai. Ke kaɗai ba ki da abokiyar tarayya."
Ya gama faɗa yana sumbatar saman sumar kanta.

"Abin da ke bani dariya in na tuna, ta zo gidammu ana jibi bikin mu ta ga hotunan auran mu amma wai ta kasa gasgata gaskiya ne, ta yarda da ni ta aminta da soyayyar da take yi maka a wautar ta tana tunanin wata rana za ka dawo gare ta? Ka daɗe kana ce mini yarinyar nan ba ta da tunani ban taɓa yarda ba sai ranar."

Ta gama faɗa tana sake kwashewa da wata dariyan daga gani tana cikin nishaɗi da labarin da take bayarwa.
Nan fa ta cigaba da faɗin maganganu marasa daɗi a kan Ummu Salma labarin zuwanta gidansu da duk abin da ya kwana kullum sai ta tuna ta yi dariya kamar ya zama abun tunawarta ta yi nishaɗi.

"Wawancin iyayenta na gani, suka barta da cikin jikinta alhalin wanda ya yi cikin ya ce ba ya so, to mene ne amfanin haihuwar da za ta yi?
Ta faɗa tana kallon shi, sai ya ɗan juya mata ido alamun bai sani ba.

"Ni dai har abada ba za ka kawo mini jinin da ba nawa a gidana ba, ba mu yi wannan alƙawarin ba."

"Ba ma zan kawo ba? Me zan yi da abin da ta haifa! Ke da za ki yi ta haifa mana yara?
Ya gama faɗa yana ɗan jan hancinta mirmishi ta sakar masa har tana sumbatar gefen kumatunsa.

"Da gaske na ke yi na bar ma Ummu Salma da iyayenta wannan cikin har abada ba ni da alaqa da shi"
Ta jinjina kai cikin farinciki.

"Wayyo ta ba ni tausayi, "
Ta sake faɗa tana sake saka dariya.
"Lokacin har wani ɗaga kafaɗa take yi. Bestie Allah kuma ya ba ku miji wanda ya fi Noori na ma komai da komai."
Ta gama faɗa tana kwaikwayon muryan Ummu Salma daga shi har ita sai da suka sake tsintsirewa da dariya.

"Ko haihu ta yanzu? Domin ganina da ita na karshe na ga cikin ya yi kasa. Ko da yake ina ruwanmu ko Sweety?
Ta tambaya tana kallon shi.

"To ai ke ce ke ɗauko maganarta. Ni tuni na gama da babinta."
"Labarinta na sanya ni nishaɗi ne."
Ta sake faɗa tana dariya.
"Na san zuwa yanzu kowa ya san na aure ka, na san na sha tsinuwa wajen yan'uwanta barin ma uwarta din nan bafullatanar banza, da wannan yayanta na ta lauya masifaffe da shegiyar ƙawar nan nata Baɗdo ba ta da mutumci, ka ga saƙon cin mutumcin da ta turamini ranar biki! Wai duk abin da ya samu Yar uwanta ni da kai Ubangiji ba zai ƙyale mu ba to ina ruwan mu? Daman ai aro na ba ta kai kuma na zo na karɓi kaya na sai aka ga laifina Sweety?

"Bai kamata a ga laifnki ba, ai su ba su nan abin da ya faru ba ne."
Ya faɗa cikin sanyin murya.
"Ko da Ummu Salma ta riga ni haɗuwa da kai. Amma ai ni ka zaɓa sama da ita ko?
Ta sake tambayan shi tana ɗan kallom shi.

"Tabbas."

Ya faɗa abin da ya faru a lokacin yana dawowa masa.
"Wallahi tun a ganin farkon da na fara yi maka kishi da hassada suka kume ni, a raina ina faɗin me ya sa sai Ummu ce za ta fara haɗuwa dakai? Ranar na koma gida da baƙinciki ina ganin kai ne irin namijin da nake burin aure ban taɓa tunanin za ka kawo kanka gare ni ba wallahi tallahi da ka makara ba ka zo ba, ni da kaina zan neme ka na yi maka tallar kaina sannan na sanar dakai na fi Ummu Salma bukatar ka a rayuwata."

Ta gama faɗa cikin wani yanayi kamar ta yi kuka.
"Sweety wallahi ina sonka."
Sake rumgumeta ya yi a jikinsa yana faɗin" Na sani, nima ai kinsan ina son ki! In kika yi duba da tsawon lokacin soyayyarmu da yadda na cika alƙawarin kema za ki san bayan ke ba na son kowa a duniyar nan a matsayin matar auran da zan zauna da ita. Na fuskancin komai saboda na mallake ki "
Ta sake ƙamƙame shi tana faɗin" Na sani Sweety na sani wallahi."
Sumbatar sumar kanta ya yi kafin ya ce" Ki bar tuna duk abin da ya wuce, rayuwarmu ce yanzu kawai a gabanmu Sweety, mu zauna mu gina sabuwar rayuwa wacce za ta yaɗu zuwa nan da wani lokaci kaɗan. Can wait na ga ranar da za ki haifa mini ɗa ko ƴa daga mahaifarki."
Ya faɗa yana kai hannunsa ƙasan maranta ita kuma sai ta noƙe wai tana jin kunya.

"Ke ce na zaɓa ki zama uwa ga ƴa'ƴana. Kuma ba zan sauya miki ba."
Gabaɗaya ya gama kashe mata zuciya da kalamansa. Sai ta sake narke masa cikin shagwaɓa shi kuma yana biye mata sun daɗe a haka domin da ya ce su je ɗaki su kwanta sai taƙi karshenta a saman jikinsa ta yi barci ta bar shi da sake shuga tunani mai zurfi.

Tabbas a ganin farko da ya yi ma Ummu Salma ya ji yana son ta amma lokacin da ya haɗa idanuwansa da na Shamsiya sai ya fahimci ashe ba so ya ke yi ma Ummu ba sha'awanta yake yi, in yana tare da ita burinsa kawai  jikinta ne a gabansa amma in yana tare da Shamsiya burinsa kawai ya dauwama tare da ita ko da ba za ta amfanesa da komai ba, tun bai fahimci karatun ba har dai ya fahimta ba shi da mafita illa ba ma zuciyansa abinda take so sai kuma aka yi saa itama shi take so, kawai sai suka jone suka kuma tsara komai. A lokacin a gida ba za a aurar da Shamsiya ba sannan shi kuma yana son auran Ummu Salma saboda ya cire wannan kwaɗayim nata a zuciyarsa shi ya sa ya yi ma Shamsiya alƙawarin zai yi auren shekara ɗaya ya sake ta sannan ya zo su yi aure daga baya ta aminta amma babu sharaɗin haihuwa, kaddara ce ta gifta har wannan cikin ya zama rai a cikin Ummu Salma amma ba shirin su ba ne, bai samu matsala a bangaren iyayen Shamsiya ba saboda dangin mahaifiyarta sun tankwasa mahaifinta, kuma gidan yan boko ne ba wani damuwa aka yi da dogon bincike ba tunda aka fahimci shima yana da iliminsa da aikinsa sannan ko da aka ce ya saki matarsa ta farko ba wanda ya yi bincike mai tsanani akan haka, kuma a cikin ahalin Shamsiya ba wanda ya san shi a matsayin mijin kawarta, shi kawai a san shi ne a matsayin mijinta na yanzu. Ya so ya samu matsala da Alhaji Sheriff shi ne ya ce ba zai sake zuwa ya nema masa aure ba, amma Baba Usman da su Gwaggo duk ya siye su da kyauttuka tuni suka manta da komai, shi ma dai Alhaji Sheriff ɗin da magiyan Habib ɗin da Baba Usman da Gwaggo ya amince ya je ya nema masa auran Shamsiya har aka ba shi amma da sharaɗin in wani abu ya biyo baya kar ya saka shi a ciki.

Shi kuma ya amince a tunaninsa me zai biyo baya? Masoyiyarsa fa ya aura, yana tunanin dukkan wani buri na shi zai cika, ya gama samun farinciki bayan ya watsa farimcikin wata,bai san cewa watakila farincikin na shi na lokaci kaɗan ba ne, ƙila nan gaba kaɗan Fargar jaji zai kama shi ya fara nadaman abin da ya aikata nadama mara amfani alhalin kuma lokaci ya sare masa.

****
*NDC QUATERS KADUNA NAGERIA.*

*BAYAN SHEKARU BIYU.*

"A Yau na koya mana yadda za mu sarrafa shinkafar mu zuwa chinese rice, za ki yin ta da kowani shinkafa amma ta kasance mai kyau ce saboda gudun caɓewa. Uwargida da Amarya har da ma ƴan'mata tare da zawarawa duk a yi pratical ma'ana gwaji domin da gwaji ne ake ƙwarewa ni ce dai taku ɗin nan HANAN DELICIOUS sai mun sake haɗuwa daku a wani sabon video na gode kar ku manta ku yi like in yau kika fara kallon videos ɗina to kar ki manta ki bibiya duka shafukana a Facebook Hanan B Jimeta a Youtube channel ɗina za ku kama ni a Hanan Delicious, in kuma a instergram ne za ku iya kama ni a Hanan B Jimeta, in kuma a Tiktok ne za ku iya kama ni a Hanan Delicious domin samun kayattacen videos ɗina akan girke girke masu  kayatarwa tare da snacks na zamani domin jin daɗin ku. "

"Mahmah..."

"Mahmah.."

Ta ji ana kiranta daga falo, ta kuma san yanzu za ta shigo kitchen ɗin in kuma ta shigo za ta ɓata mata Video ya sa da sauri ta ce.

"Bissallam. Sai mun sake haɗuwa. Bye."
sannan da sauri ta matsa wajen ringligt ɗin da ta ɗaura a wayarta ƙiran iphone 15 ta  yi saving ɗin Video ɗin dai dai lokacin da ƙaramar yarinyar ta ƙariso cikin kitchen ɗin.

"Mahmah."

Aka sake faɗa cikin murya irin ta yara masu shagwaɓa.
Da sauri ta baro in da take tsaye sanye da abaya baƙa ta yi rolling ɗin mayafin J.c mai ruwan madara kyakyawan farar fuskarta da dogon hancinta ta yi kyau sosai.

Sama ta ɗaga yarinya tana faɗin
"Waye ya taɓa mini Hanan ɗina?
Ta faɗa tana share mata idanuwanta ganin hawaye.
Dakyar ta lallaɓata ta yi barci sannan ta zo ta fara Video ɗin nan, da ta kwana biyu ba ta ɗora komai a shafukanta ba  Hannan da man akwai rigima balle kuma ba ta da lafiya tana ɗan zazzabi ga zawon haƙori na can gefe da suke fitowa shi ya sa rigimanta ya ƙaru kuma rigiman saboda ta san sun kwanta tare kuma ta farka ba ta ganta a gefenta ba shine ta taso tana kuka.

Sanye take da bulawus ta yara mai kyau, kanta kuma kitson kalaba ne an kama da band ga ta dai yarinya yar kimanin shekaru biyu amma tana da suma kai da gashi ga ta fara jajir da ita amma ko kusa ba ta kama da Ummu Salma, kamaninta da komai kamanin mahaifinta ta ɗauko, wanda kullum in Ummu ta kalleta sai ta ji baƙin ciki, ba ta so ta sake cin karo da mai irin fuskar wannan mutimin ba, amma sai ga shi tilon yar da ta haifa ta ɗauko kamaninsa

"Mahma"

Ta sake faɗa tana sake lafewa a jikin uwar ta ta,.
"Gani nan kukan na mene ne? Ko yunwa kike ji ne?
Sai ta gyaɗa kanta.
"Tea Mahma."
Ta ce tea za ta sha, nan da nan Ummu ta saɓa ta a baya tana faɗin" Hau bombu yanzu na haɗa miki tea ɗin ki sha."

Nan da nan ko ta lafe a bayanta ita kuma da haka ta yi amfani ta saka ruwan zafi a wata butar a kitchen ɗin tunda suna da wuta su da sai su yi sati ba a ɗauke musu wuta ba koma an ɗauke akwai solar ba ka gane ma akwai wutar ko babu.
Tana cikin tattara kayan video ɗin ta Basira ta shigo Kitchen ɗin.

"Ya Ummu da kan ki kika goya wannan yar rigimar!"

Ta faɗa tana dariya Ummu ta juya tana kallon Basira yar matashiya ce ko za ta girmeta bai wuce da shekaru biyu ba, itama kaddaran aure ne ya faɗa mata suka rabu da mijin watanni kaɗan da auran su, ita ce wacce Mami ta sake ɗaukowa daga can garin su Daddy ɗanmarke bayan sun mayar da Baraka an yi mata aure.

"Ba ruwan ku a ciki Basira."

Ummu ta faɗa tana sake zumkuɗa Hannan a bayanta.

"Yi kwanciyarki Hanan kar ki biye ta Basira."
Saboda suna yin ta Hanan kiyuwa da rigima Basira kuma faɗa ta yi ta janta tana saka ta kuka amma bai hana anjuma Hanan ɗin taje wajenta da zanin goyo tana faɗin bombu.

Hanan na son goyo sosai ko domin da aka haifeta ta sha goyo ne? Lokacin Baraka nan nan ko da yaushe tana bayanta Mami ma in tana gida za ta goya ta haka ma Islam har Faruku rigima yake yi a lokacin sai an goya masa shima.

"Ke sauko ki kyale Ya Ummu ta huta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login