Follow us on social media
Showing 3001 words to 6000 words out of 147042 words
Chapter 2 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
sauke a saman kujera ta sake jawo wayarta chart ta shiga ta duba Habib tun 5.40pm ya sauka daga online, sai ta je ta duba Bestie itama tun safe ba ta damu ba sanin tun da suka kusa fara jarabawa Bestie za ta yi wuyar gani.
Sai ta rubuta mata.
"Bestie kina lafiya? Ya karatun? Da wahala ko. Ayya sannu Allah zai ba ki nasara Bestie na"
Ta tura mata kuma ya tafi amma ba ta online tun da bai yi marking sau biyu ba.
Sai ta koma ta duba Mami sai ta ga tana online da sauri ta tura mata.
"Mami na."
Ba daɗewa Mami ta dawo mata da amsa.
"My first Daughter me kike yi da waya da daren nan? Ina mijin ki?
"Mami bai dawo ba"
"Is he Ok?
Mami ta tambaya sai ta amsa mata da lafiya lau ya biya ta gida ne.
"Good, nima ina duba test ɗin ɗalibai ne, gobe zan kira ki. Good night."
"Good night Mami na."
Ta rubuta tana tura baki kamar tana ganin ta.
"Kowa sai ya ce mini wai Good night"
Ta faɗa tana sake tura bakin ta gaba, ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga nan ta koma Tiktok tana ta kalle-kalle amma tana ta duba lokaci har tara ta kusa amma Habib bai dawo ba, kuma bai kira ta ba, ta fita daga wajen da niyar sake kiran shi sai kuma ta koma cikin chart ɗin ta bangaren status, kwatsam ta ga Hamma Sadam ya saka status 4m ago.
Da rawan jiki ta buɗe hotuna ne kuma hotunan ba baƙinta ba ne, duk wani ɗan Nageria dake mu'amala da social media ya san hotunan nan saboda yadda suke trending a duka kafafan sada zumunta tunda satin nan ya fara.
Amma abin da ya ba ta mamaki caption ɗin Hamma Sadam a ƙasan hoton
"Allah ya sanya alheri my Sis Badi'atu"
Baki ta buɗe sannan ta rufe tana sakin wata dariya.
"My Sis? Lalle ne ma to ko a yaushe ta zama sis ɗin ta shi ni ban sani ba?
Ta faɗa a fili tana sake yin dariya hotuna ne ya saka sun fi kala biyar na Amarya Badia'tu da angon ta wato Pre-wedding pictures ne da yan zamani ƴa'ƴan masu kuɗi ke yi in za su yi aure. Hotuna ne fitattu da suke tashe a yanzu bikin sai satin sama ne amma tuni hotuna da katin shagulgula sun watsu a duniya saboda bikin na masu kumbar susa ne da masu mulki da sarauta
Duk in da ka shiga hotunan Amarya da angon ne, sai katin bikin da na Program of events ke yawo a duka manya bloggers ɗin mu na arewa gabaɗaya.
Kallo take yi tana taɓe baki kafin ta ce a fili.
"Allah ya sa ta ma san kana yi Hamma Saddam"
Ta faɗa tana sake yin mirmishin gefen baki, sau ɗaya ta taɓa ganin ta lokacin da Ammah ta matsa mata suka je naɗin sarautan Hamma Lamiɗo a matsayin Yariman Daura. Tun a lokacin ta ga jin kai da isa a wajen wannan yarinyar, ta tabbata tusa kai ne kawai irin na Hamma Saddam ba ma a san yana yi ba. Wata ƙila Hamma Lamiɗo ya yi ma kara shima kuma tana da tabbacin bai san ma yana yi ba. Abin da ya saka na karshe a status ɗin sa katin bikin ne da shagulgulan da za a yi tun satin bikin har zuwa ranar ɗaurin aure.
Ɗaurin aure ne kawai za a yi a masarautar Daura amma sauran shagulgulan duk a garin Abuja za a yi.
Ba ta san ta kwashe da dariya ba sai da ta ga caption ɗin Hamma Sadam a kasan katin
"Family and Friends bikin gidan mu ne fa ya zo. Bikin gidanmu saboda haka ban ɗauke ma kowa ba."
Ummu-Salma tana dariya har sai da ta shaƙe, Hamma Sadam na da abin dariya wai bikin gidan su ne.! Yaushe bikin gidan masu Sarauta da masu mulki ya zama na gidan su? Bikin ɗiyar sarkin Daura ALHAJI Dr. NASIRU MUHAMMAD DAURA ne fa za a yi, za ta auri yaron mai ba ma shugaban ƙasa shawara akan yaɗa labarai, shi ne wai Hamma Sadam ke ta rawan jiki har yana faɗin wai bikin gidan su ne, gaskiya Hamma Sadam akwai tusa kai ba ƙwarjini da gayya ta masa reply akan status ɗin sa na ƙarshe.
"Ka ji Hamman nan, bikin gidanmu ma fa ka ce? Ko dai bikin gidan su Hamma Lamiɗo?
Kamar yana jiran ta sai ga shi ya turo mata da sticker na an ɗaga wani an tika da ƙasa sannan tare da emojin nan na ɓacin rai.
A ƙasa ya haɗo da cewa.
"Bikin gidammu ne Ummu ko ke ba na gidan ku ba ne?
Kai tsaye ta bashi amsa da cewa.
"A'a wallahi ba na gidanmu ba ne Hamma."
Emojin mamaki ya turo kafin ya ce" Ammah na gefe na nuna mata abin da kika ce?
Da sauri ta ce" Rufa mini asiri Hamma bikin gidan mu ne."
Ta rubuta sannan ta tura emojin heart har da na rawa.
"Yauwa yarinya."
Ya rubuto tare da sticker na dariya, saboda haushi ba ta amsa shi ba sai ma ta kashe data ta ajiye wayar, Hamma Sadam na so ya jawo mata masifan Ammah a daren nan ba ta shirya ba, ai tana jin yadda Amma take shirya ma wannan bikin ko ita uwar Amaryan albarka. Wanda take yin abin nan domin shi wataƙila ma ba zuwa zai yi ba, mutumin da an sha yin abubuwa na daɗi da aka sin su bai taɓa zuwa ba, shi bai ɗauki zumunci ma abakin komai ba, ba abin da ya sani sai tuƙin jirgi, kuɗi kawai alhalin ahalinsa suna da tarin dukiyar da har jokokinsa ma ba za su yi talauci ba, tana da tabbacin ko rantsuwa ta yi ba za ta yi kaffara ba, ba zai samu zuwa ɗaurin auran ƙanwarsa ba shi ya sa da bai zo na ta ba, ba ta damu ba Ammah ce ta damu saboda sun yi mgana ya ce mata zai zo, a cewarsa ya ɗauka za su iso bakin gaba ne ana gobe ɗaurin aure sai kuma tafiyar ta su ta sauya tsari shi ya sa bai samu zuwa ba. Duk fa Ammah ce ke ta yawo da wannan mganar shi gogan ba wanda ya ji haka daga bakin shi. To wai wanda ko ɗaurin auran shi bai samu zuwa ba to na waye zai je? Shi ya sa ma wanda ya damu in bai gan shi a sha'aninsa ba, shi ke da kaico shi dai bai ma san kana yi ba, shi fa mutumin nan dabam yake, ɗauka yake kuɗi sune muhimmi a rayuwar nan daga naira ɗaya har miliyan goma zai iya tura maka amma kuma ba zai iya zuwa ya yi maka murna ko jaje ba shi ya sa har gobe bata taɓa saka Hamma Lamiɗo a jerin mutane masu karamci ba, ta fi saka shi a jerin mutane masu girman kai da ɗagawa.
Tana cigaba da cin doughnuts ɗin ta, tana kuma kurɓan tea a lokaci ɗaya amma sai taɓe baki take yi ita kaɗai daga gani hakan yana daga cikin ɗabi'arta.
Ita fa tun wancan satin da ta je gida Ammah ta dame ta da labarin bikin nan na Daura ta ji ba za ta sake komawa ba sai bayan an gama bikin nan, domin hankalin Ammah ba a kwance yake ba yanzu sai ta ga ta je Daura an gama biki lafiya ta dawo tukunna. Baffa dai ba ruwan shi ba lalle ne ma yaje ɗaurin auran ba Ammah kuma ba wanda ya isa ya ce ba za ta je ba ai sai ranar gidan ya kwana ba lafiya. Baffa ma yasan halin kayan shi, shi ya sa ba ya ma gigin shige mata na shi addu'a ne da fatan alheri, domin in dai akan sha'anin abin da ya shafi Hamma Lamiɗo ne ko Baffa bai da ta cewa, da jikinta da zuciyarta take hidimtama wannan bawan Allah da Ubangiji ne ya haɗa wannan ƙaunar da tana tunanin ko su ƴa'ƴan cikinta ba ta nuna musu ƙauna da kula da alamuransu da muhimmanci kamar yadda take kafa-kafa da duk wani al'amarin da ya shafi Hamma Lamiɗo.
Shi ma kuma ba ya iya tsallake umarninta komai tsaurin shi a gare shi. Da Amma kaɗai yake iya doguwar hira cikin nishaɗi, ita ce kawai take iya ganin dariyan shi har da haƙora a waje. In ba za ta manta ba lokacin tana aji biyu a matakin babban sakandiri aka yi bikin Hamma Lamiɗo, auran da a farko cewa ya yi ba ya so tunda haɗin daga kakarsa ce Fulanin Daura, Mai martaba kuma ya ce ba zai matsa masa ba, Mami kuma ta ce ina ruwanta da sha'anin Lamiɗo? A nemi uwar sa Ammah ita ce za ta iya saka baki akan mganar,
Hamma Lamiɗo da bayan gaisuwa magana ta mintina biyar ba ta taɓa haɗa shi da Mami a matsayinta na mahaifiyarsa ba, ko da za su yini waje ɗaya su kwana. Ba ma ita ba, Hamma Lamiɗo zai yi rayuwa da mutum na tsawon kwanaki amma ban da gaisuwa magana ta fatar baki ba zai yarda ta haɗa su ba. In ko ka matsa ka yi hira da shi kai ne da haushi, domin a ginshiƙe zai din ga tafiyar da kai da har sai ka yi zuciya ka ƙyale shi.
Haka ko aka yi tawagar Fulanin Daura har cikin falon Ammah, ta zauna ta roƙe ta da ta sanya baki Lamiɗo ya karɓi auran nan, da suka je suka karɓo masa ƙafa da ƙafa har wajen Mai martaba Sarkin Kano a lokacin Balkisu ba ta daɗe da dawowa daga ƙasar Spain ba, a can ta yi duka karatun ta na likitan ci. Ammah ta yi ma Fulanin Daura alƙawarin za'a yi auran nan kuma maganarta ya tabbata. Tana cema Hamma Lamiɗo in har ya ɗauke ta a matsayin uwa to ya karɓi wannan auran da cewarta da auran ko wata biyu ba a yi ba. Abin mamaki sun rufe shekara da wattani ne da aure matar Hamma Lamiɗo ta haihu, har yau Ummu-Salma na mamakin wannan abu, ka ce ba ka son aure amma kuma ana yi sai shuru, kuma ko zuwa suka yi tare ba mai gane yanayin shi. Ba za ka ce yana son ta ba, ba kuma za ka ce baya son ta ko da wani lokaci yana nan a ginshiƙen sa. Shi fa ba ka iya gane ma yanayinsa kwata-kwata, fuskarsa ba ta bayyana farincikinsa ko bakincikinsa.
Ammah kuma al'amarin ƴa'yanta kuwa sai dai Ummi ikki ta yi gaba ita tana baya, amma in dai lamarin Hamma Lamiɗo ne ba ta jira ba ta kuma sakawa a yi mata, ita ce da kanta take yi masa komai, tun tana ƙarama ta shaida Ammah ta fi hidimtama Hamma Lamiɗo fiye da su ƴa'ƴanta na cikinta tun tana damuwa har ta saduda ta sare. Ta taɓa tambayan Baffa me ya sa Ammah ta fi son Hamma Lamiɗo akan kowa a gidan nan?
"Sabo da shima ɗan ta ne Ummu Salma. Nima ba ki ga ta fi son shi a kaina ba?
A lokacin dariya ta yi, kuma gaskiya ya faɗa ko Baffa bai isa ya ce wani abu akan Hamma Lamiɗo ba, ko yana nan ko baya nan Ammah mai tsaya ma yau ɗin sa ne har da jiyansa ma sannan za ta tsaya ma gobensa ma. Ba ta san Habib ya dawo ba domin ba ta ji motsin ko shigowar motarsa haraban gidan ba hankalin ta na kan Tv tana hakaito soyayyar Ammah ga Hamma Lamiɗo gefe ɗaya tana kallon drama ɗin Rayya da Avm Adnan, haka kurum take son film ɗin sabo da su, soyayyarsu na matukar birge ta Kamar ita da Noorin ta.
Su suka sanya ta mantawa da Komai ta ma yar da hankalinta kan kallon gabaɗaya.
Kamar daga sama ta ji ana murza ƙofa alamun an saka key za a buɗe, ƙurama ƙofar ido ta yi ba ta yi ko motsi ba. Ya saba ina tana dirin shigowar motarsa ta ke kamewa a tsakiyar falo yana shigowa za ta tafi da gudu ta naɗe a jikin shi, shi kuma kamar ko yaushe ya fara juyi da ita a tsakiyar falon cikin soyayya da muradi.
Amma yau sai ta ji kasala ya rufe ta ta kasa tashi, ko mararin ganin shi a lokacin ba ta ji ba wataƙila da ba ta gan shi ba ne ya sake ta ba ta dai sani ba. Tana nan zaune ya shigo falon ɗauke da karamar jakarsa ya ɗan jiƙe domin ga alamun yayyafi nan a jikin baƙaken suit ɗin da ke jikinsa.
Wataƙila ya ɗauka ba ta falon ne, shi ya sa ya tuɓe takalmansa ya ƙariso ciki sai dai me! Sai ya gan ta zaune tana mai kallon shi da manyan idanuwan ta.
Waro ido ya yi kafin ya ce.
"Baby da man kina jina?
Ya faɗa yana mai sauke jakar hannunsa a saman kujera mai zaman mutum ukun dake kusa da shi, ware ma ta hannuwa ya yi lokaci ɗaya yana sake faɗin.
"Baby na i miss you."
Ya faɗa yana yi mata murmishi, wannan murmishin na shi mai tsada da ya kan narkar ma ta da zuciya a lokuta da dama in ya kalle ta ya yi mata.
Maƙe kafaɗa ta yi, lokaci ɗaya tana tura baki , sannan ta kauda kanta alamun ta yi fushi, yana ganin haka ya yi saurin isowa kujeran da takwle zaune yana faɗin.
"Baby am sorry, kin ji ni shuru ko?
Ta ƙi yarda ta kalle shi, ganin haka yasa ya ɗauke Bowl ɗin dakw gaban ta da mug ɗin tea ya ɗora bisa table ɗin gaban su da karfin sa ya saka hannu yana ƙokarin juyo da fuskarta ta ki ba shi damar haka.
"Baby ni ne fa? Noori ɗin ki ne yau ba ki son kallon fuskar shi?
Ya faɗa yana kawo mata hannu zai taɓa fuskarta da sauri ta bige hannun shi, cikin shagwaɓa ta ce.
"Noori ka san zan damu ko?
Ta faɗa tana mai kallonsa lokaci ɗaya hawaye suna cika kwarmin idanuwanta ba ta da wuyar kuka abu kaɗan sai ya saka ta kuka ko kallo ta ke yi ɗan emotion kaɗan sai ta fara hawaye, yanzu ɗin ma ji kawai ta yi tana so ta yi kuka.
Jin muryar ta na rawa ga shi idanuwanta da jwalla ya sa ya ruɗe ya tarairayo ta da hijabin jikinta ya ɗora ta bisa cinyarsa yana tallabe da fuskarta da tafukan hannayensa duka biyu
"Ni ne ko? Sorry Baby Gwaggo ce t kira ni kuma na manta waya ta a mota na saka ta chaji, lokacin da na fito na ga kiran ki sai ban kira ba, tun da lokacin ina kan hanyar dawowa ne"
Ya faɗa yana mai kallon ta itama shi ta ƙura masa ido, tana sake runtse ido sai kawai hawaye suka zubo mata sharr a saman kumatun ta.
"Baby ki daina kuka mana. Bana so kin sani."
Ya sake faɗa bayan ya saka tafin hannunsa yana share mata hawaye.
Buɗe idanuwanta ta yi tana kallon shi, gashin idanuwan ta duka biyu ya sumbata kafin ya ɗago yana faɗin.
"Gudu na yi ta yi a mota fa Baby."
"Ba na hana ka ba."
Ta faɗa cikin wata irin shagwaɓaɓbiyar murya.
"Kin hana ni Baby."
Ya ba ta amsa shima cikin ƙaramar murya, lokaci ɗaya yana kwantar da kan shi a saman kirjin ta hannayensa kuma ya tusa su ta ƙasa hijabinta yana shafa mararta zuwa ƙirjin ta banƙarewa ta yi shi kuma sai ya ji daɗin haka zare mata hijabin jikin ta ya yi ya tsaya yana kallon kirjin ta.
Ganin haka ya sa kunya ya kamata sai ta faɗa kan kirjinsa tana masa kukan shagwaɓa.
"Noori ka bari."
"Me zan bari Baby?
"Uhm"
Ya faɗa yana shinshinar wuyanta cikin lokaci ya fara birkicewa, yana bin sasaan jikinta da wasanni ta kasa mgana sannan ta kasa hana shi, duk da yau ɗin tana jin gajiya a jikinta amma Habib ya sabar mata da komai, ƙa'ida ne in ya dawo kafin ya yi wanka ya ci abinci sai ya riban ce ta, kuma a daran ma ba zai bar ta ba kafin asuba ya yi sau uku ko sui huɗu, haka ma bayan asuba, tun Ummu-Salma na ɗaukan hakan a matsayin amarci a farkon auran su har yanzu ta daina ɗauka haka. Sai ta bar shi a matsayin mijinta Habib na daga cikin mabukatan maza ma su yawan buƙata.
A farko-farkon auran su ta sha tambayan ta kanta da man wanne ne daɗin auran? Ba hutu sam, lokacin ba ta yi kiban amarci ba sai rama saboda kwazzaban Habib saboda ba ta cikin jinsin mata fitannanu, amma saboda Habib ta koya, har in bai neme ta ba sai ta ji ta a takure, da farko ta ɗauka illa ne hakan sai da ta ga wani rubutu a faceebook wanda ke nuni da cewa yawan mu'amalar aure ga mace nuna soyayya ce makura daga mijinta shike nan ta daina fargaba ta saki jikinta duk lokacin da Habib ya marabanceta za ta ba shi cikakken goyon baya, amma tunda ta yi ɓarin cikinta wattani biyu baya da suka wuce ta daina jin shauƙin abin, kwana biyu kamar lamarin ya yi sauƙi yanzu kuma ya dawo mata, sai ta rika jin ta gaji sannan ba ta son a sakar mata wata gajiyan bayan wacce take muƙurƙusan kashin ta a lokacin, sai dai ta kasa mgana ta na ji tana gani Habib ya ɗaga ta sama yana nishi zuwa bedroom ɗin su, kan gado suka faɗa ya cigaba da abin da ya fara.
Ta yi ƙokarin ta bashi dukkan haɗin kai har ya samu natsuwa, bayan ya shiga wanka ko ɗan yatsan ta ba ta iya motsawa tsabar yadda take jin jikinta a mace. Tana kwance ta rufe rabin jikinta da blanket saboda Habib ya yi fatali da kayan jikinta tun a farkon yaƙin. Tana kwance ya fito ɗaure da towel a ƙugun shi karamin kuma yana goge ruwan da ke gashin kansa.
Tana daga kwance take ƙare ma Habib kallo, in dai ana neman cikar zati da mazantaka Habib ya kai a namiji, fari ne tas shima sannan dogo amma ba shi da tsaho sosai yana da faɗin jiki daga sama kaɗan kyakyawa asalin bafullatanin Yola ne na uwa da na uba, hancinsa har baka sumar kansa tana nannaɗe irin ta fulani, ko ta ko'ina Habib ya kai za kuma a nuna shi daga