Follow us on social media

Showing 111001 words to 114000 words out of 147042 words

Chapter 38 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

ko da mintina goma ba ne, Mamin ma kwata kwata ba ta yi ta kansu, ko su Sultan a matsayin jikokinta ba ta taɓa ganin ta ja su jikinta ba. Tun lamarin na ba ta mamaki har yanzu daga baya ya zame mata jiki. Ta riƙe Ammah a matsayin uwar mijinta da Baffa a matsayin uban mijinta, sannan ta riƙe Maimartaba a matsayin uba sannan ta riƙe Gimbiya Shahida a matsayin uwa Fulani Daura kuma a matsayin kaka.
Mami kuma sai ta saka ta a cikin sahun wasu makusanta Lamiɗonta.

Tashi ta yi tana yanga kamar yadda ta saba ta karisa kujeran da yake zaune ta zauna kusa da shi, kanta ta ɗora saman kafaɗan shi tana sauke numfashi jikinta da gashin kanta suna fitar da wani sihirtattacen ƙamshi mai daɗi.

Ya ɗan motsa amma bai buɗe idanuwansa ba tun da ya san ita ce, hannunta ta tusa cikin yatsun hannunsa guda ɗaya ta jimƙe shima sai ya taya ta suka jimƙe yatsun hannunsu a tare, mirmishi ta yi har yana fidda sauti kafin ta sake lafewa daga gefen kirjinsa.
Sun fi minti goma a haka sai ita ce ma ake jin sauka da hawan numfashinta amma shi ba ko a jin motsin na shi numfashin, in za su kai gobe a haka ba zai ce mata komai ba.

Ta san shi ta san waye Lamiɗo, ko mai za ta yi ba zai taba cewa aa ba, mutum ne mai girmama zamannsu mai daraja aure da sauke haƙƙoƙi.
Ta tuna bayan haihuwan Beena ta faɗa masa ta yi planning tunda ta samu haihuwan a jere da juna, ko faɗa bai yi mata ba ko irin ya ce me ya sa ba ta faɗa masa ba. Shi ba wanda ya isa ya gane ya ji daɗi abu ko bai ji daɗi ba fuskarsa ta iya shanye komai ba ta kuma bayyana abin da ke fuskarsa. Hausawa na cewa wai labarin zuciya a tambayi fuska to shi Lamiɗo labarin zuciyarsa sai dai a tambayi bakinsa, domin komai bin kwafkwafin ka ba ka isa ka fahimci abin da ke cikin zuciyarsa ba.

"Ranka ya daɗe."

Ta kira shi kamar yadda ta saba kiran shi.
Bai amsa ba kuma bai buɗe idanuwansa ba, ta ɗan ɗago ta kalle shi ta san ba zai yi magana ba amma tana da tabbacin yana jin ta.

"Ashe kuma abin da ya faru da Autan Ammah kenan?

Ta faɗa lokaçi ɗaya tana ɗan wasa da gargasa hannun shi, da hannunta guda ɗaya.
Shuru na wani lokaci sannan ya buɗe idanuwansa da suka ɗan ƙanƙance sun ɗan kuma sauya launi.
Kallon shi ta yi, shima sai ya kalleta yadda ya kalletan ne ya sa ta san bai san komai ba.

"Ba ka sani ba?

Ta faɗa cikin sanyin murya lokaci ɗaya tana goga masa gashin kanta samana kirjinsa cikin wani salo.
Bai yi magana ba amma ta ga ya ɗan jinjina mata kai alamun bai sani ba.
Sa sauri ta tashi daga kan kirjinsa tana fuskanshi.

"Jiya da na ganta wani iri na tambayeta ko ba ta da lafiya ne? shi ne fa Ammah ke ba ni labari."
Ya yi mata kuri da ido yana son jin ƙarshen maganar..ita kuma sai ta yi shuru tana nazarin shi, yana so ya ce mata me Ammah ta ce? Amma kuma bakin shi ya gaza furtawa.

"Uhm labarin fa ba daɗi ga tausayi yaron nan ya zalunci Autar Ammah"
Ta faɗa tana matse hannunta cikin na shii.
Idanuwansa ya ke buɗewa a kanta, zuciyarsa har wani tsalle ta yi amma bai nuna ba, yana nan a yanayin shi tun farko.
Ita kuma Bilkisu ba ta fahimci ya matsu ya ji labarin ba sai ta cigaba da faɗin" Ta rame fa duk ta yi wani iri. Ai ka ganta ko?
Ta gama faɗa da sigan tambaya.

Ya yi shuru kawai yana kallon ta.
"Ko ba ka gan ta ba?
Ta sake tambaya tana kallon shi, sai da ta ja yatsunsa sannan ya ɗan lumshe ido ya buɗe lokaci ɗaya yana mai jinjina mata kai alamun e ya gan ta.

"To ba ka ga ta rame ba? Duk ta yi fari ashe ma da ciki ya sake ta."
Hannunta dake cikin na shi ya matse har sai da ta ɗan kalle shi lokaci ɗaya kuma ya zare hannun shi ya yi shuru ba tare da ya yi magana ba.

Bilkisu kuma ta shiga ba shi labarin da Ammah ta ba ta ganin kamar Lamiɗon ya tattara hankalin shi a kanta.
Har ta gama bai ce komai ba amma hankalinshi da natauwarshi yana kanta ya yi mata kuri yana kallonta kuma yana sauraranta.

"Ammah ta ce hankula sun tashi sun shiga damuwa amma dai yanzu da sauƙi tunda an kwarari wata biyu cikin na uku. Ummu Salman ce sai a hankali har yanzu ba ta daina yan koke koke ba.".

Ta gama ba shi labarin kuma ya saurare ta amma bai ce mata komai ba.

"Wai ko Ammah ba ta faɗa maka ba?
Ta sake tambayan shi.
Sai wannan karon ya yi magana
"Ba ta faɗa ba."
Kawai ya iya cewa sannan lokaci ɗaya ya miƙe yana kallonta kafin ya ce" zan yi wanka"

Da ga haka ya wuce ta ya fara tafiya a hankali cikin takunsa har ya shige tiolet ta bishi da kallo, ko maganar ta dame shi ne ko ba ta dame shi ba, ba za ta iya sani ba. Amnma ta yi mamakin yadda bai sani ba ko Ammah ba ta faɗa masa ba ta yi tunanin amininshi KB zai faɗa masa, ta wani fannin kuma ba ta yi mamaki ba sanin halin mijin nata, ba ko da yaushe kake samunsa ba. Za ka iya tura masa saƙo sama da wattani bai gani ba, kuma sanda aka yi abun yana can wajen aiki ba lalle ya sani ba, ita dai ta tausaya ma Ummu Salma, ƙaramar yarinya ta haɗu da jarabawa, ita fa ta ga ƙokarin su Ammah yadda suka yi ma Ummu auren wuri haka a lokacin ta yi ta ce ma Lamido ta yi ƙarama da aure bai ce mata komai ba, ga shi nan ya sake ta ya wulakanta ta da ƙananun shekarunta.
Ta shi ta yi ta ɗau wayarta ta bar ɗakin domin ta san in gogan ya fito ya iske ta ba zai ji daɗin shiryawa ba, shi ya sa ta bar masa ɗakin ta koma ɗayan bedroom ɗin ta ɗan kwanta.

Shi ko bai wani daɗe ba ya fito daga wankan, sai da ya tabbatar da Balkisu ba ta ɗakin sannan ya saki jikinsa da ga shi sai towel ɗaure a kugunsa ya fito ba ya ɓata lokaci wajen shiryawa yanzu ma cikin lokaci ya shirya ya saka farar shadda gezner ɗinkin zamani riga da wando, rigar yau har ta fi sauka masa saboda yau jumma'a za su je masallaci tare da su Baffa, wani nishaɗi yake ji tun safe na tunowa da rayuwar baya amma labarin da Balkisu ta bashi ya ɗan hanashi sukuni.
Taje kansa ya yi da gemunsa da yake tunanin yau zai je gyaran fuska a rage masa gashin fuska. Turare ya fesa kaɗan saboda shi ba ya son kamshin turare ya yi masa karfi da yawa yanzu kan shi zai fara ciwo, ko Balkisu ta cika turare har kansa yake hawa in kuma ya shaƙa da yawa haka zai yini da ciwon kai, bai taɓa ce mata ta daina sawa ba, saboda shi a tunanin shi saboda abin da ba ya so shi kaɗai ba zai tauye mata haƙkinta tunda ita tana so ba.

Shi ya sa ko ba ya son abu ba ya faɗa, gani yake yi kamar son kai ne. In kuma yana son abu shima ba ya faɗa gani yake yi don shi kaɗai yana son abu kaza kamar ya shiga haƙƙi ne ya ce kowa sai ya so abinda yake so ko ya zama irin sa ba.
Sai ita Bilkisun ce da kanta ta gano ba ya son mu'amala da turaruka tunda in ya yi birthday tana siya masa a matsayin gift zai karɓa amma sai shekara ta sake zagayowa bai taɓa amfani da shi ba, uban turarukan dake ɗakin shi kamar za a buɗe shago amma baya amfani da su tun daga lokacin ta fahimci bai cika son ƙamshi ba, ita kuma gata tana son ƙamshi tana mu'amala da turare sosai in ka yi mata kyautar turare ba ta mantawa.

Ba ta daina amfani da shi ba amma in suna tare sai ta yi amfani da mai sauƙin ƙamshi, ita fa koda yaushe jikinta a cikin ƙamshi yake duk bayan wata ɗaya tana zuwa a yi mata gyaran jiki na skin care. Shi ya sa fatar ta kamar ta turawa wajen taushi da santsi sannan ba aikin da take yi, daga zuwa asibiti ta duba patients shike nan ta dawo gida ta kwanta.
Sannan gaba da baya tana cikin jin daɗin rayuwa.

Kan kujeran da ya tashi ya koma ya zauna da wayarsa a hannu ƙiran samsumg ita ce wayar da yake amfani da ita na Family, shi in ba zai yi kira ko an kira shi ba sai ta yi kwanaki bai yi amfani da ita ba, a wajen aiki kuma suna da wayoyin aiki shi ya sa.

Yana so ya tambayi wani labarin abin abin da ya faru amma ba zai iya ba.
WhatsApp ya buɗe ya shiga, 24/7 datar shi tana buɗe ne tun a can ma wajen aiki suna da wifi a Lagos ma haka. Ta kwana a kunne saƙonni su yi ta shigowa amma sai a fi wata bai duba ba. Tun ballatana in yana wajen aiki bai cika duba wayar ba.
Wasu saƙonnin ma sun fi wata biyu bai duba ba.
Ya ga saƙon Mahma tana tambayan lafiyan shi?
Giransa guda ɗaya ya sosa da hannu ɗaya yana jin nauyi , bai kyauta ba ya kamata ya kira Mahma.

Har da saƙon Maimartaba yana faɗin sun ji shuru kwana biyu ba a samun wayarsa Fulani ta damu.
Bai amsa ma wannan ba tunda lokacin da ya koma Lagos ya yi magana da su gabaɗaya.
Ƙasa ƙasa ya yi ta yi, can ne ya gano group ɗin Ammah da Baffa ya dai san an buɗe amma bai taɓa bibiya ba sai yau ya shiga ya ɗan duba saƙonni.

Ya ga Date ɗin da Hamma Jibo ya sanar da labarin da Balkisu take faɗa masa an kwarari wata biyu cikin na uku ma.
Sake sosa giran shi ya yi, haka ne ƙololuwar nuna damuwarsa, tunani yake yi ko shi ya sa daga Baffa har Ammah duk suka rame masa a ido, bai yi magana ba ne amma a zuciyarsa sai da ya ce duk sun rame amma sai ya danganta haka da ɗan daɗewar da ya yi bai gan su ba.

Fita ya yi daga group ɗin, ya je ya nemo KB da sunan shi ke a matsayin Friend a wayar Lamiɗon.
Sai ya ga ma ya yi masa mgana.

"Amini mutanen Jimeta."

Haka ya rubuta masa dubawa ya yi sai ya ga yana online.

Rubutu ya fara yi na wani lokaci kamar zai rubuta wani abu ashe kalma ɗaya ne ya rubuta.

"Amini."
Ya ɗan ja fasali kamar yana ganin sa.

"Me ya faru..?

Ya sake rubutawa ya tura masa sai kuma ya dakata kawai yana kallon wayar.

"Naam Amini ya gajiya! Ya baƙun ta?

"Me ne ya faru kuma!?
A ina?

Duk wayar na hannunsa saƙonnin suna ture juna suka shigo
Sai ya fara rubutu sai ya goge ya yi ya kai sau uku sannan ya samu ya rubuta.

"Ummu Salama."

"Me ya samu Ummun?
Hamma Kabiru ya turo masa cikin mamaki.
Haushin chart ɗin Lamiɗo yake ji magana ba magana ba ya rabata ya ɓata maka lokaci.

Kawai sai ya kira shi Video call kamar ba zai ɗauka ba sai dai ya ɗaga kiran.
Hamma Kabiru ya bayyana a cikin lap na asibitinsu yana sanye da suit da farar rigar lapcot ɗin sa. A jikin lapcop din an rubuta sunan shi..
Kabiru Hadi Baba.

"Amini wai me ya faru da Ummun ne?

Ya faɗa yana kallonsa, shuru ya yi masa yana kallonsa sanin halin shi ya sa ya ce" Wai ko maganar abin da ya faru da sakinta da ɗan iskan yaron nan ya yi?
Sai da ya ɗan lumshe idanuwansa sannan ya ɗan gyaɗa masa.
"Kai ai an kwana biyu Amini, lokacin kana can wajen aiki shi ya sa ban faɗa maka."
Nan shima ya shiga sanar da shi duk abin da ya faru

"Amini na so Baffa ya cire hannunsa mu kai yaron nan kotu amma kasan dai halin Baffa, Ammah ma ta goya masa baya. Ya sako yarinya ga shi ya barta da wahalan ciki tunda ya sake ta an ce ba ta kara lafiya ba, kullum kuka da rashin cin abinci, ita a damuwa su Baffa ma cikin damuwa. Amini da a ce su Baffa sun matsa ma Ummu Salma ta cigaba da karatunta da yanzu duk wannan abubuwan da suka faru wallahi ba su faru ba."

Ya karishe faɗa yana jin haushi in ya tuna cin mutumcin da Habib ya yi musu.
Shuru kawai Lamiɗo ya yi yana jinsa ba tare da ya yi magana ba.

"Wai yaron nan ne zai ce shi ba son Ummu yake yi ba auren sha'awa ya yi da ita yanzu kuma tunda ya gama moranta bari ya yada ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda"
Lamiɗo ya sake sosa giran shi na dama wannan karon kansa ya duƙar ƙasa bai kuma yi magana ba

"Ya ce ba ya son cikin jikinta tunda ya ce ta zubar ba ta zubar ba. Baffa kuma ya ce ta haifa su suna so kuma za su riƙe, ka ji halin da ake ciki ni tun zuwan da na yi ma ban koma ba, ga tausayi in ka ganta amma haushinta zai sa in kana kusa da ita ka yi mata dukan tsiya"
Lamiɗo ya ɗago yana kallon shi.
"Me ya sa?
Ya tambaya a hankali kamar ba ya son magana.

"To Abdulrrahaman na faɗa mini har yanzu tana son wannan shegen bayan ya gama tozarta ta, saki uku fa ya yi mata Amini bayan ya haɗo ta maganganun cin mutumci, shi ne har yanzu take so? Wallahi da ina garin nan sai na taka wuyanta tunda ita shashasha ce."

Sai da Lamiɗo ya motsa bakinsa ya ɗan murmusa.
Amma dai bai yi magana ba shi kuma Hamma Kabiru ya shiga faɗa ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba, shi dai kawai su Baffa yake ba ma laifi da ba su yi ma Ummu aure ba da duk haka bai faru ba ya manta da zanen kaddaran bawa ba ka iya guje masa.

Gajiya Lamiɗo ya yi ya motsa bakinsa ya katse Hamma Kabiru sanin halin shi in ya fara kawo hujjojinsa sai fa kowa ya fahimce sa.
"Ammah ta damu ko?
Shi ya sa ta rame ita da Baffa."
Ya tambaya ɗaya bayan ɗaya.
"Ai damuwa ta zama dole Amini, gwara ma Baffa ana iya gane damuwarsa Ammah ce sai dai ta kunshe ita kaɗai."

Shuru ya yi, Ammah tana cikin damuwa duk ta rame baiwar Allah. Ko saboda Ammah da yana nan aka yi haka sai ya saka an yi ma yaron nan ladabi tun da ya saka Ammah damuwa ita da Baffa.
Lamido gajiya ya yi da tsarin Kabiru ya kashe wayarsa ya ce zai je gida za su je masallacin jumma'a da su Baffa, amma ya ce in ya dawo gida za su yi magana.

Hula ya baƙa saka da wani rufaffen takalmi mai rufewa.
Har ɗaki ya bi Balkisu sai ya isketa ta yi barci har bargon ya ɗan gyara mata sannan ya fita. A falo ya iske su Sultan suka naɗe shi suna kiran sunan shi, kaya ya ce Anitha ta sauya musu tare da su zai fita ba daɗewa aka shirya su Sultan ma kamar ubansa farar shadda ya saka har da hula Beena kuma wata riga ce yar kanti a jikinta pick colour ga takalminta na mata cover mai kalan pick, gashin kanta an kama mata da kananun ribbors masu kala-kala.

Ganin ba a saka mata hula ko hijabi ba ya sa ya ce Anitha ta nema mata hula saboda Ammah za ta yi magana ko Baffa in su ka ganta ba ɗankwali ko hijabi.
Shi ya tuka su zuwa gidan Baffa, Ammah na ganinsa da yara ta tarbesu. Sultan da Beena sun saba da kakarsu suka make suna kiranta da Ammah. Ita kuma ta rumgume su tana murna.
Da su kaɗai Ammah ke wasan jika da kaka domin tana ta ce ma Sultan ya yo wanka yana so ya kwace ma Baffa gwammati a wajenta ko? Baffa ma da ya fito cikin manyan kaya ya ce ina ai ba wanda ya isa ya ture gwamnatinsa.

Ummu na cikin ɗaki tana jin su amma ba ta fito ba.
Tana jin zuwan su Hamma Abdulrrahaman da tafiya su masallaci su huɗu har da Hamma Abdullahi.
Sultan ma sun tafi da shi Beena kawai aka bar ma Ammah tana ta fama da ita, yarinya akwai shagwaɓa ta ce wannan za ta ci sai an bata ta ce wannan Ammah kuma ba ta gajiya.
Kafin su dawo Ummu ta fito ta shigar da ruwa ɗakinta karma ta nema daga baya, ba ta kaunar ma su sake haɗuwa har sai sun tafi.

Nan gida suka dawo a falon Ammah suka ci abincin suna ta hira duk da shi ɗan kasaitar ba a jin muryansa sai dai ta su Hamma Abdulrrahman.
Sai can yamma suka watse, Allah ya taimaketa har suka bar gidan ba ta fito ba kuma ba wanda ya neme ta sai Baffa shima sai bayan ya dawo sallan mangariba ya zo ya duba ta.

Kusan satin su Lamido ɗaya a jimeta suna hutawa. Kullum sai ya zo gidan Ammah shi da yara Balkisu kuma bai wuce sau uku ta zo ba, tana gida tana hutawa amma dai ta leka gidajensu Hamma Abdullahi Lamiɗon ma Ammah ta tura su tare da matarsa ta shi gidan Ummin ikki sun gaishe ta.
Ranar da suka yi sati suka tafi Jalingo gidan Hamma Kabiru kwanan su biyu suka dawo daga nan Ammah ta ce ya kamata su je Mubi ana ta tambayan shi tunda ya daɗe bai je ba, suka shirya tafiyan da Hamma Abdullahi da matarsa sai shi Hamma Lamiɗo da iyalan na shi a helux ɗin Lamiɗo suka tafi suka yini suka dawo. An ce Hamma Lamiɗo ya yi ta rabon kuɗi ga su Baffa Umaru da iyalansu har gidajen su Umma Balki duk ya je haka Hamma Abdullahi ya zo yana faɗa, shi daman mai  wuyar Ammah ta yi magana ko bai yi ra'ayi ba zai je.

Ummu dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login