Follow us on social media

Showing 120001 words to 123000 words out of 147042 words

Chapter 41 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

daga yanayinta yanzu Ummu za ta zauna ta yi hira har da dariya, ta saki jikinta tana ƙokarin yaƙi da kaddaranta.

Duk da ba ta manta ba amma ta aro jarumta ta yafa ma rayuwarta saboda iyayenta da ƴan'uwanta, tana so ta ga farinciki a fuskokinsu kuma in dai tana son ganin haka sai ta aro ma rayuwarta farinciki, kuma da ta yi hakan ta ga canji Baffa da Ammah sun rage damuwa ganinta cikin farinciki ba abin da ke damunta ko ma yana damunta tana yaƙi da shi. Za ta fito ta yi ta nuna farinciki a fuskarta amma a zuciyarta Ubangiji ne kaɗai ya san irin ciwon da take ciki, sai dai in abin ya taso mata sai dai ta shige ɗaki ta yi ta kuka ba ta yadda ta fito sai ta wanke fuskarta.

Za ta manta amma ba da wuri haka ba domin taɓon da Habib ya yi silan saka mata a cikin zuciyarta ba mai warkewa ba ne da wuri tana tunanin nan da shekara goma wataƙila har abada ma.

A yanzu a ƙalla cikin ta ya kai kimanin wattani bakwai ne, kuma da ita da cikin jikinta duk suna cikin ƙoshin lafiya. Ba abin da za ta ce ma Iyayenta da yan'uwanta sai godiya, domin sun tsaya mata sun kula da lafiyanta da cikin da Habib ya ce ba ya so. Tana zuwa asibiti awo kuma Ummin ikki ke rakata duk lokacin da za ta je, sannan Hamma Abdullahi ke kai su sai dai in baya nan sai su hau kekenapep, su je su dawo kuma komai za a yi na laluranta kafin ma Baffa ya ba da yayyenta sun ba da ta yi komai da shi, cikin ya yi girma tsini gare shi ya yi wani ƙasa, Ummu Salma ta yi baƙi sosai ga kuraje duk sun lalata mata fuska kafafunta sun kumbura gabaɗaya dai hallitan ta ya sauya, jiki duk ya yi wani iri alamun rai na rayuwa tare da kai, Har kuma yau Habib ko wani ahalinsa ba su nemi Ummu ko iyayenta ba, su ma kuma kamar yadda Baffa ya ce ba wanda ya sake neman su, da farko Baffa Umaru ya so ya sake neman su Baffa ya ce har abada kuma shima baya fatan su neme shi nan gaba.

Ammh ba ta barinta ta yi aiki sai dai ita ce ke matsawa sai ta yi aikin tunda a asibiti an ce ta riƙa yawan motsa jikinta girman cikin ya sa kowa ke tunanin namiji za ta haifa, kuma ko a scanning ɗin da ta yi namiji ya nuna amma ita ba ta damu ba ita dai a koda yaushe fatan ta ta sauka lafiya namiji ko mace duk wanda Allah ya bata tana so, domin bayan cikin ba ta da wani abu na rayuwarta da ya yi mata saura, sannan ba ta zuwa ko'ina daga asibiti sai gida ko kwanaki Umma Salamatu ta aurar da Autarta Ammah ta so sai ta je bikin nan wai in ta ga y'anuwa za ta sake sosai ita ko ba ta son zuwa ko'ina ba, ba ta so ta je ana kallonta ana nuna ta cikin tausayi ana cewa Allah Sarki shi ya sa ta ce ba za ta je ba Baffa kuma ya goya mata baya sai dai Ammah ce ta je aka yi biki ta dawo.
Ko a anguwa an gama yawo da maganar an hakura  tunda da dawowar Ummu yanzu wajen wata biyar kenan tuni zukata sun haƙura.

Komai na bukatar haihuwa Mami ta siya mata kaya masu kyau da yarari, domin ta ce duk abin da Ummu za ta haifa ita ce uwarsa da ubansa. Wasu kayan ma duk yan waje ne Mami ta siya mata kwanaki ma da suka je London ta siyo mata wasu kayan yara masu kyau sannan itama ta zo mata da dogayen riguna masu kyau sama da kala biyar tunda yanzu su take sawa kayanta duk sun yi mata kaɗan, balle ma tunda ta dawo gida ta daina amfani da kayan lefen Habibu kayanta tun na gida take sawa kuma yanzu ba sa shiganta sai dogayen rigunan da Mami ta siya mata take bumjumawa a cikin gida sannan atamfan wajen Hamma Lamiɗo da Ammah ta ba ta ta raba shi uku duk ta yi zannuwa faya tana ɗaurawa a gida biyun kuma suna cikin ɗan kit ɗin kayan haihuwan da Mami ta yo mata.

Ba mai zuwa wajenta sai Baɗɗo Shamsiya ma ta ja baya da ita ba ta san dalili ba. Sun daina waya kamar yadda suke a baya sannan tun bayan dawowanta gida sau uku ta zo, na ukun ma cingham da minti ta kawo mata wai an saka ranar aurenta ta daɗe tana faman mamaki, ita dai kamar yadda Shamsiyan ta faɗa mata gidan su ba ka yin aure sai ka yi Degree ka yi bautar ƙasa kuma haka ne tunda duk yayyen Shamsiyan ba wacce ta yi aure tana cikin karatu sai da suka gama, amma za ki iya ɗora karatunki na gaba a gidan mijin ki,  amma sai ga shi ita tana aji uku ne ma a lokacin amma za ta yi aure sannan ƙarin mamakinta ba ta san Bestie na da wani saurayi ba, saboda dokar gidan su amma sai ga shi ta kawo mata mintin saka rana, sannan ita ko a labari ba ta taba faɗa mata ta samu miji ba, da Ummun Salma ta yi mata ƙorafin  ta samu miji amma tana ƙawarta na kusa da ita ba ta sani ba?

Sai ta ce ta yi hakuri ganin tana cikin damuwa shi ya sa ba ta faɗa mata ba, kuma ba su daɗe da haɗuwa da mutumin ba.

Har tambayanta ta yi ya aka yi mahaifinta ya amince ta yi aure ba ta gama makaranta ba.? Sai da Shamsiyar ta yi wata bazawaarar dariya kafin ta ce dangin mahaifiyarta ne suka shige mata gaba, sannan shima mahaifin na su yana sonta saboda maraicinta shi ya sa ya yi mata abin da take so. Ummu ta yi mata fatan alheri  da cewa ta bi dai a hankali domin yanzu maza ba a gane musu sai ka shiga kuma zence ya sha bambam.

"Bestie ki kwantar da hankalinki. Sweety yana sona, ni ce kusan rayuwarsa nima kuma shi ne rayuwata. Kuma ki cire ma kanki tunanin wai don ke ba ki yi sa'ar aure ba ki yi tunanin koma ba zai yi sa'a ba. Ke dai kawai ba ki yi dace ba ki bar shi a haka amma ni na san abin da na zaɓa ina mai bakin tabbacin na yi kyakyawan zaɓi kuma na yi dace.".

Kalamanta su ɗan yi ma Ummu tsauri amma ba ta nuna mata ba, ta yi mata fatan alheri da ta tambayan ta yaushe ne lokacin bikin! Sai ta ce ba a saka date ba amma in an sanya za ta faɗa mata har Ummu ta yi fatan cewa Allah ya sa lokacin ta haihu yadda za ta samu zuwa, domin ko ta daina fita ba za ta ƙi zuwa bikin Shamsiya da Baɗɗo ba su ne suka yi mata komai a nata bikin da Habib.

Ko Baɗɗo da ta zo Ummu ta faɗa mata an sanya ma Shamsiya ranar aure sai da itama mamaki ya kamata har sai da ta maganta da cewa ita da ta ce a dokar gidansu sai ka gama Jami'a za ka yi aure, nan fa Ummu ta karanta mata abin da ta ce mata bayan itama ta yi mata wannan tambayar.

"Tab. Ni ko ta ba ni mamaki duk yadda kuke bai kamata a ce sai dai ta zo kawo miki minti ba."
A lokacin Ummu shuru ta yi ba ta yi magana ba, Baɗɗo ta yi ta faɗa tana cewa Shamsiyar ta sauya tunda Ummun ta dawo gida.

"Ko saboda yanzu kin yi aure kin fito shi ya sa ta ja baya dake?
"Kin san tana makaranta, ba ta samun lokaci."
Daƙyar Ummu ta samu Baɗɗo ta bar maganar saboda kar Ammah ta ji daman da ta ce mata an sanya ma Shamsiyar ranar aure ga ma mintin da ta kawo mata nan ta nuna mata taɓe baki ta yi ta ce shi ya kawo ta kenan? Domin ita Ammah ta ce tun maganganun da ta ji tana yi yarinyar ta fita zuciyarta.
Ita kanta Ummun ta san alaqar su da Shamsiya ta ja baya kuma kamar Shamsiyan ne ke gudunta tunda ita tana kiranta amna ba ta ɗauka, sai a yi kwana huɗu sama da sati sannan za ta kirata da cewa karatu ya yi zafi shi ya sa ba ta samun lokaci itama daga baya da ta ga haka sai ta kama kanta amma ranar ta yi kuka, yau ace mutane sun fara gudunka saboda kaddara ta faɗa maka, tana tuna a baya yadda kowa ke haba haba da ita saboda tana gidan mijinta yanzu kuma duk abin da take tunanin ta samu sai da Habib ya dawo da ita baya ba ta da komai a rayuwarta in ta tuna yadda rayuwarta ta sauya lokaci ɗaya sai ta yi kuka sosai, har kuma yau yana nan a cikin zuciyarta duk da tana ta addu'an Allah ya cire mata tunanin shi da soyayyarsa a cikin zuciyanta. Tana ta samun sauƙi amma kuma bai fita duka ba, ta dai dangana ta kuma aminta da cewa wataƙila Habib ya yi nisan da ba zai taɓa dawo gare ta ba.

In ta kalli kanta a madubi da katon ciki, mara duk ta yi baƙi fuska ta lalace komai dai na ta ya sauya sai ta yi ta zubar ƙwalla. Tabbas ta rasa komai Duk wani abun sha'awa da namiji zai gani a jikin mace ya yaso ta, ta rasa shi. Da gaske Habib ya lalata mata gobenta wataƙila ma har da jibinta. Ya raba ta da martabamta na har abada. Ba za ta taɓa komawa Ummun Salman baya ba, ko shekaru tun tura ta na nan a yadda Habib ya sako ta. Sai dai za ta haihu kuma za ta shayar da abin da za ta haifa komai na jikinta zai saki to wani kuma taƙama gare ta? Ba ta da komai sai godiyar Allah da imani kawai.
In tana kuka sai ta yi hamdala ta ce Ya Allah Ummu Salma ta gode,  domin ya barta da rai da lafiya ya kuma ba ta iyaye masu jajircewa yau da babu su ba ta san wani hali za ta shiga ba wata kila da ta kashe kanta cikin ƙunci da baƙin ciki.

***

Hamma Saddam ya sake zuwa gida sun ɗan smu misSemister break, dawowar shi ne ya matsa ma Ummu sai da ta amince ya buɗe mata WhatsApp, ganin ya nace ne ya sa ta ce ya buɗe mata da sabuwar lambar nata.

Nan take ko ya buɗe mata ya kuma yi adding ɗinta a family group ɗin su, tunda ya buɗe mata ba ta ma shiga saboda yanzu ta saba da rayuwarta ba waya. Ba ta da lambobin kowa sai na yan'uwanta.

In ta ma duba chart ɗin sai dai ko Baɗɗo in ta yi mata magana sai Shamsiya da yanzu a chart ɗin suna ɗan gaisawa jefi jefi, sai Hamma Abdulrahim tun da shi yana can wata ƙasar suna yawan magana da su Hamma Jibo suna ɗan jan ta da mgana.
Hamma Kabiru da ta yi masa sallama sai da ya yi sati sannan ya buɗe.

Kuma bayan ya amsa sallaman ta gaishe shi ya ga saƙon amma bai sake yi mata magana ba itama ba ta sake bi ta kansa ba sanin halin shi
Sun zo shi da matarshi da yaran shi suka yi sati suka koma, Hamma jibo ma da Hamma Mustpaha sun sake dawowa har Hamma Lamiɗo ya zo shi kaɗai kuma bai kwana ba a ranar ya wuce Daura da kuma zai wuce bai sake biyowa ta nan ba, Ammah ke ta faɗin yanzu ya sauya ma'aikata ba zai riƙa daɗewa ba a gan shi ba sanda ya zo ma Ummu na asibiti ta je awo ita da Ummin ikki sai da suka dawo suka ga Ammah da kuɗi sabbin yan dubu dubu ta ce ba daɗewa da fitan Lamiɗo ya wuce Daura duba kakarsa Fulani ba ta ji daɗi ba.

Akwai wata class mate ɗin su ita da Shamsiya da suka yi Ahmadu Ribaɗo tun primary har sakandiri duk da dai ba sa wani yi da Ummu amma suna ɗan gaisawa a chart sannan lokacin tana group ɗin su na makaranta da wancan layin suna ɗan magana, shi ne da ta ga ba ta ganin Ummu a online da wancan lambar kuma ta yi ta kiran wayar a kashe sai ta yi ma Shamsiya magana. Ita kuma sai ta ce mata Ummu ta sauya layi ne sannan kuma ta ba ta sabon layin na ta, sai dai kawai ta ga Madina Jafar ta yi mata magana suka gaisa ta kuma ce Shamsiya ce ta ba ta sabuwar lambarta.

Ba tare da izinin Ummu Salma ba Madina ta saka ta a cikin group ɗinsu na makaranta da sabuwar lambarta tunda su Madinan su ne ke jagoranta group ɗin, ba ta ma sani ba domin ta yi kwana biyu ba ta hau ba, ba kuma don ba data ba kawai dai wayar ce ta fita daga zuciyanta. Data sai tana yin expering a wayarta yayyenta da sun ga ba ta online za su saka mata kati ma ya fi na dubu biyar a wayarta ba wanda take kira da shi.

Sai can da ta hau ne ta ga ta saka ta, tsoro take ji kar ya zo sun samu labarin abin da ya faru da ita, ba ta son ta zama abin dariya a wajen ƙawaye kamar za ta yi left sai kuma ta fasa lura da cewa kamar ba su sani ba, tunda Madina na yawan tambayanta ya Oga sai ta ce yana lafiya. Shi ya sa ta ɗan saki jikinta suke ɗan gaisawa kuma ba ta yi left a group ɗin ba.

Ranar da daddare ta kunna data suka yi video call da Hamma Abdulrahim har da Ammah da Baffa ma duk sun yi magana da shi ya zama kamar ɗan turawa saboda zaman turai yana ta murna shekara mai zuwa zai dawo gida ya gama karatunsa na likitan ci gabaɗaya.

Ta ga Baɗɗo ta yi mata saƙo da Madina amma ba ta duba ba sai da safe.
Baɗɗo lafiyanta ta tambaya ta ce tana lafiya saƙon Madina ne ya ɗan ba ta mamaki.

"Ya shirye shiryen biki?

Ta yi mamakin tambayan cikin mamaki itama ta mayar mata da tambayar shirye shiryen me?
Madinan ba ta online itama daga nan ta sauka ba ta sake hawa ba sai bayan kwana biyu.

"Bikin Bestie ki mana, ba farkon watan gobe ba ne ko an ɗaga ne?

Sakon da ta ga Madina ta tura mata kenan a gabanin tambayar da ta yi mata tun ranar.
Mamaki ya kamata,yanzu har bikin Shamsiya ya zo amma ba ta sani ba, wayance ma Madina ta yi da cewa ba ta gane tambayar ba. Ta so ta yi ma Shamsiyar magana sai kuma ta fasa a zuciyarta ta ce za ta tsaya ta ga ni shin Shamsiya za ta faɗa mata, in ba ta faɗa mata ba sai ta samu tabbacin zarginta na cewa ta ja baya da ita tunda ta zama bazawara sannan ba ta son yadda ta zama cukus ta je bikinta to in har hakane itama ba cewa ta yi za ta je ba Allah ya sa a yi lafiya a gama lafiya.

Abin ya dame ta amma ba ta faɗa ma kowa ba ta yi shuru da bakinta sai dai har watan ta gangara Shamsiya ba ta yi mata maganar ba ranar har ce mata ta yi har yanzu ba a saka date ba tace mata ba a saka ba, ai ta ce in har sun saka za ta yi mata mgana.
Tun daga ranar ta yi ma kanta alƙawarin ba za ta sake yi mata magana ba, in ma har an yi bikin ne ba ta fada mata ba, ba za ta zargeta ba sai dai ta yi kudirin za ta kirata a waya ta yi mata fatan alheri. Amma fa zuciyarta ta yi mata nauyi yau wai Bestie ce ke gudunta to waye ya yi saura yanzu da ba zai guje ta ba.
Har Ammah ta ɗan fahimci tana cikin damuwa har sai da ta yi magana amma ta ce mata ba komai.

****
Thursday.

A farkon watan da cikinta ya shiga wata na takwas ta koma awo, ranar Ummin ikki ba ta nan ta je Mubi Baɗɗo ce za ta raka ta ita kuma an kira ta suna da test a makaranta sai ta tafi. Baffa ya ce Ammah ta rakata ta ce ba za ta je ba, da man shima ya san ba zuwan za ta yi ba saboda kawaici maganar cikin dake jikin Ummu ba ta yadda a yi maganar da ita in dai tana wajen saboda kawaici.

Ummu Salma Ita kaɗai ta je da aka yi mata awon sai da likitan ta sake yi mata faɗa kan yanayin kwanciyar da take yi, na ringigine da man wancan awon da suka zo da Ummin ikki sun ce kwanciyar jaririn jikinta ya jirkita kuma a wattanin cikinta ya kamata a ce kanshi ya dawo kasa, da yana kasan ne daga baya ne ya jikirta. Kuma ta ce saboda yanayin kwanciyar da take yi ne.

"Dr to yanzu ya zan yi?
Ta tambaya cikin damuwa, ba ta san wani abu ya samu cikin jikinta. Saboda shi ta rasa komai na ta

"Kar ki damu in dai kika kiyaye irin kwanciyar da mai ciki bai kamata ta yi ba zai komai daidai in sha Allahu."

Ta faɗa mata ta daina kwanciyar ringigine gwara ma na gefe da gefe saboda lafiyan abin da ke cikinta.
Sannan sun ba ta yanzu bayan sati biyu za ta dinga zuwa awo tunda ta kusa haihuwa. saɓanin da sati uku ne.

Da za ta dawo Kekenapep ta hau ta dawo da gida, haka ma ta hau da za ta je Hamma Abdullahi ba mota a hannun shi sai mashin, ita kuma ba za ta iya hawa mashin a yanayin ta ba.

Ta dawo gida wajen sha biyu na rana ta samu Ammah har ta gama abincin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login