Follow us on social media
Showing 114001 words to 117000 words out of 147042 words
Chapter 39 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar
ba ta sake bari sun haɗu ba amma dai sun sake haɗewa da Balkisu da yaran tunda ko da yaushe suna gidan.
Lamiɗo bai yi ma Ammah maganar Ummu kai tsaye ba ya dai ce ta daina saka damuwa a ranta kar cuta ta kamata ta ce za ta daina in sha Allahu.
Bai kara ganin Ummu Salma ba, sannan bai sake tambayan wani game da ita ba, suma mutanen gidan ba wanda ya yi masa hiran abin da ya dangan ce ta. Suna da kwana goma da zuwa suka tafi Daura.
Daga can Balkisu za ta koma Lagos da yara saboda aikinta da makarantan yara amma shi Lamiɗo zai dawo ta Jimeta kafin ya koma Lagos.
****
*KATSINA STATE, DAURA.*
*MASARAUTAR DAURA.*
Garin Daura karamar hukuma ce da ke cikin Jihar Katsina. Garin yana cikin jihar katsina ne a arewa maso yammacin Nigeria, kuma ya yi iyaka da jamahuriyar Nijar ta wajen Damagaram daga arewa.
Masarautar Daura Jiha ce ta addini, da ta gargajiya a Arewacin Nigeria.
Sannan an kira Masarautar Daura a matsayin ɗaya daga cikin kasashen hausa bakwai, domin itace tare da Biram, Kano,Katsina, Zazzau, Gobir da Rano. Wanda zuriyar ƴa'ƴan Bayajidda suka yi mulki, tare da Daurama da magira,(matarsa ta farko)Jami'ar calfornia's Afircan. American studies na nufin Daura, da kuma Katsina a matsayin tsofaffin kujeru na al'adun musulunci da ilimantarwa.
Akwai al'adan da suke gudanawar a garin Daura bikin hawan sallar gani na ɗaya daga cikin bukukuwan da masu sarauta da dawaki ke kece reni a cikinsa, wanda kuma za a iya cewa ya samo asali ne daga Daura sannan garin ya fice wajen gudanar da wannan al'adan.
**
Tun zamanin sarkin Jafaru ɗan Umaru zuru'an su Lamiɗo ke mulkin Daura sama da shekaru sittin da suka gaba ta.
Mai martaba Sarki Alhaji Dr. Nasiru Daura ya yi hau karagan mulkin Daura shekaru talatin baya sannan shi ne sarki na 42 a lissafin masarautar.
Kuma ya samu nasaran hawa karagan ne bayan rasuwar mahaifinsa tsohon sarki Mai martaba Muhammad Shitu.
Masarautar Daura kayattaciyar masarauta ce mai ɗimbin tarihi.
Lokacin da suka iso filin jirgi na Umaru Musa yar'aduwa da yake an san da zuwan su tuni wasu aminttatun Mai maitarba irin su Waziri da wambai tare da rakiyan dogarai sai ƙanin Lamido Saleem(Sardaunan Daura Hakimin Daura) suka zo tarban su. Shi kaɗai ne ke karatu a Nigeria shi ne kuma ke gida Daura tare da Maimartaba kuma yawancin yana wakilta shi zuwa wajen taro ko wani abu da ya shafi sarauta, mutanen garin Daura suna tunanin Saleem(Hakimin Daura) ne zai gaji Sarki duk da yana da karancin shekaru domin bai wuce 26 ba amma yana da hikima da hangen nesa sannan mai fara'a da son mutane saɓanin Lamido da ba shi da fara'a sosai, sannan ba mazaunin masarauta ba, amma shima an yi shaidarsa da kyakyawan zuciya da son takalawa da matasa, duk da kuma shi ke da Sarautan Yarima Daura mai jiran gado hakan bai hana wasu tunanin Hakimin Daura a matsayin wanda ya cancanta ba, duba da shi jinin Sarauta ne gaba da baya saɓanin Lamiɗo da iya bangaren uba ne sarautarsa take da ƙarfi.
*FARGAR JAJI SECOND PROMO.*
KU BIYA #800 A MADADIN 1K, TURA TA WANNAN ACCT ƊIN.
9069067488.
JAMILA UMAR OPAY.
08032773332.
09069067488.
VALID 24HOURS.
MUN GODE.
*Janafty*
*FARGAR JAJI.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*
"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"
*FARGAR JAJI SECOND PROMO.*
KU BIYA #800 A MADADIN 1K, TURA TA WANNAN ACCT ƊIN.
9069067488.
JAMILA UMAR OPAY.
08032773332.
09069067488.
VALID 2HOURS.
MUN GODE.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L6zUax648eTERbvw8Bqyie?mode=gi_t
*18*
A mota ɗaya Lamiɗo da Saleem suke cikin wata baƙar Hilux, tana daga cikin motocin Mai martaba. saboda Lamiɗo ne, ya sa a motocin alfarma ake zuwa tarbansa in dai ya zo Daura. Ba sai Mai martaba Sarki ya yi magana ba kowa ya shaida yadda yake son Lamiɗo ba ga iya ahalin masarauta ba har jama'an gari saboda yadda yake yawan zencen sa ko yana nan ko ba ya nan.
"Ranka ya daɗe barka da zuwa Garin Daura."
Saleem ya faɗa yana mai kallon yayan na shi wanda tunda suka shiga mota suka fara tafiya bai yi maagana ba.
Balkisu da yara suna motar gaban su tare da hadiman Mai martaba.
"Saleem"
Ya kira sunan shi cikin yanayin maganarsa.
"Ranka ya daɗe an iso lafiya?
Saleem ya sake faɗa, sanye yake cikin rawaninsa tsaf ya fito a Hakimin Daura kuma Sardauna.
"Mun same ku lafiya? Ya makaranta?
Lamiɗo ya faɗa yana kallon shi.
"Lafiya lau. Allah ya taimake ka. Allah ya kara maka lafiya da arziƙi Allah ya tsare mana kai Yarima."
Saleem ya gama faɗa har yana jinjina masa hannu.
Mirmishi ya yi har sai da fuskar ta nuna kafin ya jinjina kai.
"Ka san ba na so ko?
"Tuba na ke, a gafarce ni ranka ya daɗe"
Lamiɗo ya yi wani mirmishi mai tsada kafin ya ce" Hakimin Daura"
"Naam Allah ya taimake ka."
Saleem ya faɗa har yana ɗan rusunawa cikin girmamawa.
Kafaɗansa Lamiɗo ya dafa yana sake kallon shi.
"Sardaunan Daura."
Ya sake faɗa a hankali kamar ba ya son magana. Ko direba da Wambai dake gaban motan ba za su iya cewa ga abin da Lamiɗo yake faɗi ba.
"Allah ya ja da zamanin Yarima."
"Ka daina mu'amalanta na kamar sauran mutane."
"Tuba na ke yi ranka ya daɗe."
"Am your brother, mu yi mu'amala kamar yan'uwan juna."
"A yi mimi afuwa. Tuba na ke yi Ranka ya daɗe."
Ya sake faɗa yana mirmishi ba zai dai bari ba kenan.
Lamiɗo ya ɗan sake dukan kafaɗansa ba tare da ya sake magana ba
"Allah ya taimake ka. Tuba na ke yi. Tuba na ke Yariman Daura. Yarima mai jiran gado"
Ya san ba ya son wannan kirarin shi kuma yana yi masa ne saboda ya yi magana. Ba uwa ɗaya suke ba, ba kuma su san juna a shekarun baya ba amma yanzu da suka san shi a matsayin ɗan'uwa na jini suna son shi, musamman ma Saleem ɗin jin Lamiɗo yake yi kamar uwa ɗaya uba ɗaya saboda kyawawan hallayansa duk da ba ya da yawan magana da son hayaniya akwai kyakyawan alaqar Yaya ga ƙaninsa a tsakanin su, suna waya sannan in dai ya zo garin kuma Saleem na nan a lokacin har ya koma duk in za su je suna tare.
Shuru ya yi kawai yana kallon sa ya ɗan kwantar da kansa a jikin kujeren motar. idanuwansa na lumshewa lokaci ɗaya yana kallon hanyar da suke wucewa zuwa Daura, yana jin wani alfahari na samun Lamiɗo a matsayin ɗan'uwa.
Shi ko Lamiɗo hanya yake kallo iska na ɗan shigarsa, wani natsuwa ya je ji na kama sa a duk lokacin da ya zo Daura. Ba domin ba ya son duk abin da ya shafi sha'anin Sarauta ba da ace shi ba ɗan kowa ba ne to da ya ji daɗin rayuwarsa a Daura. Ya yi rayuwa a Jimeta amma yadda yake son yanayin garin Daura da jama'ar cikinta na musamman ne, a cikin zuciyarsa komai na garin ya yi masa damuwarsa ɗaya abubuwan sarautan nan mai hana kunnuwan mutum su huta, in ya je Daura har ya koma cikin ganin jama'a yake yi, in kuma za a yi taron Fada Mai martaba sai ya matsa masa ya je, kafin a gama zaman fada ya shiga mummunan takura a rayuwarsa.
Shi ba ya son hayaniya, ba ya son magana ya fi daraja ya ji duniyar ma ta yi tsit gabaɗaya.
Amma in dai yana amsa sunan Muhammad Nasiru(Yariman Daura) ba zai iya guje ma abubuwan da suka shafi sarauta ba a baya ya yi haka amma jini da sarauta suna cikin jinin jikinsa ne ko ba a Daura ba shi ɗin kasaitattace ne.
Har suka iso garin Daura magana ba ta sake haɗa shi da ɗan'uwansa ba shima kuma kanin na shi ya san waye shi bai takura masa ba shima a cikin motan lamo ya yi kamar baya ciki.
Motocin da su Bilkisu ke ciki kofar shashen cikin gida ta nufa, su kuma direct motar su fada ta nufa, tuni bushe-bushe da kaɗe-kaɗe suka cika fada na zuwan Yariman Daura.
Motarsu ko gama fakin ba ta yi ba dogarai suka yi caa,tuni yar natsuwanr da ya fara samu ta yi ta kanta ga hayaniyar mutane ga busa wanda ya ke sake bashi tabbacin ya shigo garin Daura rayuwarsa ta sauya ya tashi daga Muhammad matuƙin jirgin ruwa ya koma Muhammad Nasiru(Lamiɗo) mai sarautan Yarima mai jiran gado duk da dai shi kam ya san ba wani gadon da ya je jira ba zai iya yin wata sarauta ba domin ba zai iya ba.
A guje dogarai suka buɗe musu ƙofofin motar shi da Saleem, da yake a tawagan da suke je ɗauko shi har da masu kakin masarauta.
Tun kafin ya fito daga motar dogarai suka zube a kasa suna faman kawo gaisuwa..
Daga lokacin ya ji kamar ana sauya shi komai na shi ya sauyawa kamar ba shi ba.
Shi ya sa aka ce in dai kai jinin sarauta ne, duk in da ka shiga ba zaka ɓuya ba.
Tuni Lamido ya rikiɗe ya fito a Yariman Daura sak.
Kafafunsa farare masu cike da gargasa ya fara sawowa waje masu ɗauke da takalma rufaffu bakake na fatar damisa masu kyau, sannan gangar jikinsa ta fito. Dogon Yarima mai ƙwarjini da Haiba. Haka wani dogari ke faɗi kamar zai saka kansa a kasa saboda girmamawa.
Sanye yake da wani baƙin yadi mai ɗan santsi ɗinkin riga da wando amma tazarce, sai ya ɗauki jaket baƙa na saƙin sarauta a jiki ya ɗora a sama. Kansa da hula baƙa ta dara shigar bakake ya yi daga samansa har ƙasa, ya rage gashin fuskarsa sai haibansa ta sake fitowa amma suman kansa na nan domin hulan ma a saman sumar ta zauna sannan gefe da gefen wajen kunnuwan shi kana ganin suman da ya tara da ɗan yawa.
"Barka da zuwa Yariman Daura. Sauka lafiya Namijin fama. Sauka lafiya Yariman matasa. Farin Yarima kake dogo ɗan Nasiru jikan Shitu, barka da zuwa shalelen Masarautan Daura. Barka da zuwa kasaitattacen Yariman Daura. Jama'ar Daura na yi ma dogon Yarima barka da zuwa."
Hannu kawai yake ɗaga musu ba ya magana fuskar nan ta sa ta sake ginshiƙewa saboda jinin mulki ne ya motsa a cikin jininsa.
"Takawarka lafiya ɗan sarki jikan sarki. Angon Balkisu Baban Muhammadu, takawarka lafiya Amintattace, takawarka lafiya mai alheri takawarka lafiya Yarima Allah ya ƙara tsawon kwana Allah ya tsare gaban ka da bayan ka."
"Barka da isowa Hakimin Daura takawar ka lafiya Sardaunan Daura."
Suke ta faɗa kamar za su shiɗe suna mai ƙanƙantar da kan su. Hannu kawai ya ɗaga musu ya wuce tawagan suka bi bayan shi zuwa fadar Sarki Mai martaba Alhaji Dr Nasiru Daura in da yake gudanar da zaman fada a daidai lokacin.
"An gaishe ku. Yariman Daura ya amsa muku."
"An gaishe ku. Hakimin Daura ya gaishe ku."
Haka shugaban dogarai yake ta faɗa. Da irin takunsa na jaruman maza gif! Gif suka shiga fada, suna shigowa suka duƙa gaban Mai martaba da ke zaune kan wata kyakyawan karaga cikin naɗi idanuwansa ne kawai a ake gani su kuma su Wambai suka jeru cikin masu zaman fadan da suka sha rawani.
"Allah ya ja zamanin ka na kawo Yarima gida kamar yadda ka bukaci na jagoran ci haka."
Saleem ya faɗa cikin ɗan rusunawa.
Jinjina kai Mai martaba ya yi alamun gamsuwa, ko da ba a ganinsa fuskar sa amma kowa ya shaida yau yana cikin farinciki.
"Sarki ya gode ma Hakimin Daura. Allah ya ja zamanin Sardaunan Daura."
Lamido ne ya ɗan rankwafa cikin yanayin maganarsa ya ce.
"Allah ya tamaimaki Mai martaba fata duk mun same ku lafiya?
Maimartaba ya sake jinjina kai.
Dogarai suka ɗauka.
"Sarki ya gaisheka Yarima, sannan yana yi maka maraba da sauka a masarautar Daura."
"Na gode. Allah ya kara yawan rai da lafiya mai ɗorewa."
Lamiɗo ya faɗa yana ɗan jinjina kansa.
"Amin Yarima. Allah ya ja zamanin ka, Mai martaba ya amsa."
Ɗaya bayan ɗaya Lamido ya juya yana kai gaisuwa ga walikan fada suna amsawa da an gaishe da Yariman Daura barka da sauka,
Duk da haka fuskar nan ta shi ta nan a ginshiƙe cikin irin yanayin sa.
Yarima ya amsa, Yarima na godiya.
Wani dogari ke ta amsawa.
Ba su daɗe a fadan ba Mai Martaba ya ba da Umarnin Hakimin Daura ya raka Yarima zuwa bangarensa domin ya huta.
Bangaren Yarima in da yake sauka in ya zo Daura. Shashe ne mai girma a cikin masarautan.
Har kofar shashin Saleem ya raka shi.
"A fito lafiya Ranka ya daɗe."
Kai ya jinjina masa kafin su rabu shi ya juya shi kuma ya shige ciki tuni falon ya cika da hadimai mata wasu na jera abinci wasu na shigowa da shi.
"Barka da sauka Yarima. Barka da isowa ranka ya daɗe."
Magajiyar hadiman Fada ta faɗa cikin ladabi bayan ta zube kasa, haka ma sauran hadimai mata suka yi suna mai zubewa a gaban shi.
"Yauwa na same ku lafiya?
Ya faɗa a iya fatar bakinsa sannan ya shige wani korido.
Ba wacce ta sake motsi sai da ya nisa da in da suke sannan Magajiyar hadimai ta miƙe tana ba su umarnin su yi sauri su jera komai Yarima ya shigo.
Dattijuwa ce ita ce shugaban hadimai mata na gidan Sarki gabaɗaya, sannan amintataciya ce a wajen Uwargidan Maimartaba Gimbiya Shahida da umarninta ne ta ce ta yi jagoranci a tanadar ma Yarima da iyalansa duk abin da za su nema.
Cikin lokaci suka gama shirya komai suka bar shashen gabaɗaya.
Shi ko Lamiɗo ɗakin shi na musamman ya shige ya yi wanka ya ɗan kwanta. Shashen na da girma ga dakunan barci ne ba adadi shi ya sa har ya yi barcinsa ya samu natsuwa ya tashi kafin La'asar bai ji ko motsin Balkisu da yara ba suna wani shashe a cikin bangaren na dabam ita da su Sabuwa.
Alwala ya yi ya fita sanye da jallabiya fara wannan karon sai ya dora rigar sarauta mai ruwan zuma haka ma hulan kansa ta sakin gidan sarauta ne haka ma takalmin kafarsa na irin takalman da yayan sarakunan kan saka ne, ga kaya nan birjit a cikin clothset dinsa na bangaren gidan Sarki sai wanda ya zaba sai saka.
Yana fita suka haɗe da Saleem shima da shirin zuwa masallacin.
"Barka da fitowa Ranka ya daɗe."
Lamido bai yi magana ba amma ya jinjina kai.
Yana daga cikin shaidar da ya samu, Lamido mutum ne mai daraja lokacin salla bai taba zuwa garin Daura ya yi fashin salla cikin jam'i ba.
Tare suka yi salla da Mai martaba a sahun gaba sai karamin kanin su Mujahid(Amir) ɗan shekara goma sha shidda , Mai martaba ransa fes ga shi zagaye da yaran shi maza yamma da kudu.
Bayan an idar da salla limamin masallacin ya yi ɗan tunsarwa akan zumunci da falalar nasu sada shi, daga nan Lamido da Saleem suka koma bangaren shi duk da jama'a na son ganin shi amma Hakimin Daura ya ce Yarima na hutawa ne sai zuwa gobe.
Tare suka ci abinci a bangaren Lamiɗo kamar yadda suke yi in ya zo garin tare da Mujaheed da suka taho tare da shi, ita Balkisu sun riga sun ci na su abincin tuni har an raka ta shashen ɗakunan matan gidan daga ƙarshe ta ci burgi a bangaren Fulanin Daura.
Bayan sun gama cin abincin sun ɗan natsa Lamido ya sauya kaya farar shadda har da babban riga, kayan da in ba a Daura ba, ba ya mu'alama da su.
Da rakiyar Salem da Muhajeed ya fara isa bangaren Uwar gidan Mai martaba yar kuma tsohon wazirin Daura.
Gimbiya Shahida, ita ce mahaifiyar Saleem kuma ita ce Fulani ta aura ma Mai martaba lokacin yana tare da Fatima.
Gimbiya Shahida ya'yanta huɗu ne uku mata namiji ɗaya. Sakeena ce babba tana auran jakadan nageria a England.
Tana can tare da iyalanta(ita ce kuma ke da sarautan Magiyar Gah mata na garin Daura)
Sai Munnira(Magajiyar Hah matan garin Daura) auren zumunci aka yi mata tana auren yaron Hajiya kilishi yayar Mai matarba Sarki Nasiru. Sai Saleem Hakimin Daura, sai auta Badi'atu wacce ba ta daɗe da yin aure ba.
Ba su wani jima a shaahenta ba bayan gaisuwa da yi masa maraba ya yi mata sallama sai kuma bangaren Gimbiya Hadiza wacce ke bin ta.
Ita kuma ya'yanta uku. Ita ɗin jikar sarkin Kano ce.
Hajiya Sadiya(Bata tuman Daura) tana auren yaron Wambai ne, suna kasar portugal da zama.
Sai Hajiya Zainab(magajiyar Jah mata)
Tana aure anan cikin garin Daura, sai Hajiya Safiyya(Yakumon Daura) tana aure a masarautar Gusau. Itama bayan gaisuwa suka bar nan zuwa shashen mai bi mata.
Gimbiya Maimuna ɗiyar marigayi sarkin katsina da ya rasu.
Ya'yanta uku
Yazeed(ɗan ruwatan Daura hakimin Babban mutum) yana can kasar waje yana karatu. Sai Sagir(ɗan burum ɗin Daura) shima yana can kasar wajen yana karatun lauya. Sai Auta Hafsat tana sakandiri.
Sai shashen ta karshe Gimbiya Amratu.
Ita kuma kakanta ƙani yake wajen marigayi Mai martaba Sarki Muhammad shitu kenan kakkani suka haɗa da Mai martaba sarki na yanzu, ita ɗin yar Daura ce kuma yar masarauta.
Yaranta biyu ƙanana ne Mujaheed(Amir) da Mujadala(Amira)
Nan ma gaishe ta suka yi suka fice, lamarin mulki da saurata sai wanda aka haifa a cikin shi ko gaisuwan ma ba wani mai yawa ba ne, shike nan an yi an gama.
Daga nan sai suka ci burki suma a katon bangaren yar Sarki jikan Sarki, matar Sarki sannan uwar Sarki.
Hajiya Raƙayya(Fulani Daura).
Fulani na da mayan ya'ya mata amma namijinta kwara ɗaya ne Mai martaba Muhammad Nasiru Daura, duk da a wancan lokacin maigidanta Marigayi mai martaba tsohon Sarki yana da wata matar kafin ita mai suna Hajiya Rakiya.
Tana da ɗa namiji babba amma an haife shi ba shi da lafiya daga karshe ma ya rasu bayan mahaifiyarsa ta rasu ba daɗewa.
Akwai yaranta biyu yayyen Mai martaba ne da Fulanin Daura ta riƙe su.
Hajiya Kilishi ita ce babba kuma tana da sarautan(Magajiyar garin Daura) Tana kuma auren shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin katsina ne.
Sai Hajiya Balaraba(Magajiyar zama Daura) Tana auren wani babban general ne a hafsan sojan ƙasa tana zaune a garin Abuja da iyalanta.
Sai ya'yan Fulani ƙannen Mai martaba mata
Wacce ke bi ma Mai martaba Hajiya Zaliha wacce Lamiɗo ke kira da Mahma ita ce(Magajiyar sanda mata)
Kuma tana auren madakin masarautar Zazzau ne tana can garin Zariya.
Ita ce kamar 5 and 6 na Mai martaba Sarki komai zai yi sai ya yi shawara da ita ga shi ba ta taɓa haihuwa ba shi ya sa take son Lamiɗo kamar ran ta.
Sai mai bi mata, Hajiya Zeenatu(Magajiyar Gabas)
Tana auren shugaban yan sandan na ƙasa gabaɗaya.
Sai Hajiya Zannura,(Magajiyar Yamma)
Tana auren ɗan sarkin Katsina. Sai ta ƙarshe Hajiya Binta(Magajiyar sha wata Daura)
Tana auren ɗan sarkin muslmin garin sokoto ne