Follow us on social media

Showing 9001 words to 12000 words out of 147042 words

Chapter 4 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

ya ce yake so ya koma makaranta."

Sai a lokacin ya buɗe idanuwansa kafin ya ce" Gobe kuma? Ya fasa raka ki Dauran ne kuma?.
"Aa bai fasa ba ya ce akwai abin da zai yi ne a can, satin da za mu tafi zai dawo."

Ɗan miƙar da kansa ya yi yana gyara kwanciyarsa kafin ya ce" Allah ya ba da sa'a."
Ta amsa masa da Amin Amin.

"Bayan Umman ikki, sai kuma suwa kika shirya tafiyar da su?

Ya tambayeta yana kallonta, kai tsaye ta ce" Umma A'i tunda na fara yi ma mgana sai ta ce ba ta nan ɗiyar mijinta ta haihu a kano za su tafi, Umma salamatu kuma kasan ba ta son doguwar tafiya. Yanzu daga ni sai Umma Balki, sai Saddam da Ummin ikki."

Kai ya jinjina kafin ya ce"Kun isa ma, Allah ya nuna mana ya sa a yi biki lafiya a gama lafiya."
Ta amsa masa da Amin tana cigaba da faɗa masa sun yi waya da Lamiɗo ya ce Abdulrahaman zai siya musu tiket jirgi za su bi zuwa katsina daga nan motocin gidan Mai martaba sarkin Daura suna jiran su za su ɗauke su zuwa masarauta.

"Allah ya sa albarka."

Ta amsa da Amin kafin ta ce" Baffa ba za ka je ko ɗaurin auran ba?
Kai tsaye ya ce" Zai yi wahala. Ban dai sani ba, bari mu gani."
Tana jin ya ce haka ta san bai yi niyyar zuwa ba.
"Kai Baffa ban san ka da riƙo ba fa. Ai komai ya wuce yanzu mun zama ɗaya silan Lamiɗon mu."

Shuru ya yi na wani lokaci ba tare da ya yi mgana ba. Ya manta sannan ya yafe, kara yake yi ma Fatima, shi ya sa bai cika tusa kansa a wannan bangaren ba.
Janye kafafunsa ya yi daga cinyar Amma ya sauke a ƙasan cafet ɗin da ke ɗakin.
Sannan lokaci ɗaya ya yunƙura ya miƙe zaune yana mai kallon Amma.

"Na san zuwan ba zai gagare ka ba, sai dai in Fatima ce ta ce maka kar ka je ko?
Baffa Mai martaba fa da kansa ya kira ka ya sanar da kai bikin ɗiyarsa me ya sa ba zaka yi masa kara ba! Sannan Gimbiya Shahida ba ka ga yadda ta ke yawan kirana tana tambayana yaushe za mu taho ba, a ƙalla dai sun nuna mana ƙauna hatta Fulani ta kira ni, ta ce ba ta ɗauke mini zuwa wannan bikin ba."

Mirmishin gefen baki ya yi, a cikin ran shi yana faɗin sai yanzu? Da ma ace za su iya mayar da hannun agogo baya wataƙila da sun gyara kuskuren su na baya da Fargar jaji bai kama su a yanzu ba amma a sarari sai ya kalli Amma kafin ya ce" Ni wallahi ban taɓa rike su a raina ba Ammah kin sanni kin san halina. Kawai dai."

"Kawai dai me?

Ta katse shi tana kallon shi sai ya kasa amsa mata, domin ai ta san amsar tambayar nata.

"Fatima ce! Saboda Fatima ce ya sa kake yin wannan baya bayan ko Baffa?
Tafaɗa tana sake matsawa gare shi lokaci ɗaya ta tsare shi da kaifaffun idanuwanta masu sanya shi ya yi laushi bai shirya ba.

"Baffa don Allah kar ka biye ma wannan ƙanwar taka mai zuciyar rashin yafiya, yadda na sanka mai yi ma zumumci hidima ne. Ko saboda Lamiɗon mu ko sabo da shi, kar ka manta har abada Lamiɗo ɗan mu ne."
Ta gama faɗa tana mai riƙo duka hannayensa a cikin nata, ta kuma kafe shi da idanuwanta da ba ya iya mata gaddama in dai ta kafe shi da su.

"Za ka je ko Baffa?

Ta faɗa har tana kasa-ƙasa da murya.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce" Za mu je, zan yi ma Abdullahi(Baba) mgana."
"Baffa ka yi ma Abdurrahaman mgana ku zo tare da shi."
Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce" Shike nan. Da ma kin sani kin yi ma Abdullahi(Baba) mgana ko da matarsa sai ku tafi."
Baki ta riƙe bakin ta ce" Na sha'afa wallahi bari zan yi masa mgana na ji."

"To Amman Lamiɗo."

Tana dariya ta ce"Kai kuma Baffan Lamiɗo ba."
Yana y'ar dariya ya ce" Na bar miki, duka matsayin tuntuni. Wannan Lamiɗon naki ai sai ke. Ni fa cikin satin nan da ya doka mini kira cikin dare sai da ya sa jinina ya hau na ɗauka ba lafiya ba ina ɗaukan kiran cikin damuwa na ce" Lamiɗo lafiya cikin daren nan?
Buɗar bakinsa sai ce mini ya yi" Baffa me ya sa kake tambaya? Ai da man wannan ne lokacin da na ke kiran ku a waya"
Ja'irin yaron nan ko a jikinsa bai ma damu da ɗaga mini hankalin da ya yi ba, muna gama gaisawa ya kashe wayarsa shi ya sa ma ko zan je ba saboda Lamiɗo ba ne sai saboda zumunci da girman mahaifinsa , amma shi Lamiɗo da na samu zuwa da kar na samu zuwa duka ɗaya ne a wajen sa."

Amma na dariya Baffa na taya ta, ya ci gaba da faɗin" Ta bakin Fatima ta ce ba zan iya da ɗan Ammah ba shegen faɗin rai. Ta manta jinin dake gudana a jikinshi."
Amma na gimtse dariyanta lokaci ɗaya tana faɗin" Ni fa bana ganin duk abin da ake faɗa akan Lamiɗo, a wajena yafi kowa sauƙin kai."

"Uhm da yake ɗan gaban goshin ki ne ai ba kya ganin laifinsa. Gaskiya Fatima ne ke kika bata Lamiɗo ya saba da komai ya yi dai-dai ne a wajen ki."

Amma ta dariya ta ce" to ba ta bar mini ɗan ba, babu kuma ruwanta da ni balle rayuwar ɗa na."

"Allah ya ba da sa'a."

Baffa ya faɗa Amma ta amsa da Amin..

"To iyalan na Lamiɗon za su taho bikin dai ko? Domin shi gogan na san ba zai samu zuwa ba."

Amma ta ce" Gaskiya ya ce mini da wuya ya zo suna can ko wata ƙasa ne ma, sunan da wuyar faɗa Baffa, amma ita Balkisu ya ce za su taho tare da yaran gabaɗaya tun da sun samu hutun makaranta."
Baffa ya jinjina kai kafin ya ce" Hakan ma ya wadatar. Allah ya nuna mana lokacin."
Ta amsa da Amin suna cigaba da tattaunawa har sha biyu saura na dare sannnan suka yi shirin kwanciya sai bayan sun kwanta ne Amma ta ce.

"Baffa ka yi mgana da Ummu ne a kwanaki nan?

Baffa na daga kwance ya ce" Jiya ta kira ni da safe mun gaisa. Tana lafiya ita da mijinta, shima yau da safe sai da ya kira ni muka gaisa."

Amma ta yi kyafci kafin ta ce" Habibu dai ya kira ni da safe amma Ummu ba ta kira ni ba."

"To ai kin yi mata faɗa zuwan ta na karshe shi ya sa ba ta kira ki ba."

Baffa ya faɗa yana dariya Amma ta kalle shi tana cigaba da faɗin" Au har ta faɗa maka? Munasiran yarinya."
"Ki rage yi ma uwata faɗa, kar ki manta ta girma yanzu matar aure ce."
"Ai ko duniya ta haifa sai na ci mata in ta yi mini ba dai-dai ba."

'"To me ta yi miki kuma?

Ammah ta miƙe daga kwancen da take tana faɗin" Zuwa fa ta yi ina mata hiran bikin nan na Daura ta yi banza da ni, shi ne na danƙwashe ta yarinyar nan ta fara mini kukan shagwaɓa wai ita ina ruwanta da bikin da zan ce sai ta saka baki a hiran? Ka ji fa shi ne na fattatake ta na ce kar ta dawo mini gida ta ce wai gidan ai na Baffa ne, na ce ta ci ubanta Baffan ma a ƙarƙashina yake ballanta ita "

Kafin ta gama bashi labarin ya fara dariya, Ammah dai ba za ta sauya ba, in tana faɗa da yara sai ka ce ba ita ta haife su ba musamman ma ita da Autar ta Ummi, ba sa zama a inuwa ɗaya yanzu nan lafiya anjuma za a ji su suna tafka tsiya ta fattateketa a gidan tun kafin ta yi aure gidan Ummin ikki take zuwa ta yi ma Amman ya ji sai in ta gaji da kanta take dawowa, ita fa Ammah ba ga ya'yanta ba ko na yan'uwa ne ba ta da sauƙi, jikoki kan sun san sauran in ƴa'yan su Jibo suka zo hutu sun ma san hali ba ruwanta da wasan jika da kaka yanzu sai ta ji ƙaniyar mutum, ba a yi mata wargi in aka dame ta ta kira uban ko uwar ta ce su zo su tattara ƴayan su ta gaji, ita da gidan Baffa ba za a bar ta sake ba. Babar ɗiyar Jibo Sauda wancan hutun da suka zo kafin su koma ta ci dundun Ammah, saboda ba ta jin mgana ga son jiki ita kuma Ammah ba ta shiri da yaro mara kunya da son jiki yanzu za ku samu matsala,  ba su gama cinye hutun ba ta kira Jibo ta ce ya zo ɗauki sangartatun ya'yan shi ba za ta iya ba sun dame ta. Da yake shi ne babba kuma yana aiki ne Airport na Abuja can yake zaune da iyalansa.

Baffa ne mai wasa da jikokinsa da ƴa'ƴan sa amma ban da Ammah kana yi mata wasan za ta ma yar da shi na faɗa, ƴaƴan lamido ne kawai jokokin gata a wajenta in suka zo ta rasa ina za ta saka su kamar yadda take yi ma ubansu hidima suma haka take yi musu.

Hatta matar Lamiɗo hidima Ammah ke yi mata, ita kuma sanin Amma ce komai na mijin nata sai ta riƙe ta gam, domin yadda take yi ma Amma hidima da kuɗinta ko Mami da ta kawo Hamma Lamiɗo duniya ba ta yi mata haka, to ina ma ta ga fuska Mami ko a fili ko a sarari ba ta taɓa nuna Lamiɗo ɗan ta ba ne, Islam da Faruk sune duniya ta shaida ƴa'ƴanta. Shima bai taɓa nuna wata a matsayin uwa ba bayan Ammah ba

Sannan matar Hamma Lamiɗo  ita ɗin yar masu kuɗi ce ɗiyar sarauta ce domin babanta shi ne Sarkin Kano na yanzu, ita kuma likitar mata ne mai zaman kanta, shi ya sa ko su matan Yaya Jibo ba su isa su haɗa kan su da Balkisu ba,  ita ɗin ta musamman ce a wajen Ammah kamar yadda mijin nata yake gangariyan na musamman a wajen Amma.

"Ummu ta raina ni Baffa."

"Ba ruwana ina shiga zan ji kunya ke da Autar ki."

Da sauri Amma ta ce" Ba Auta ta ba ce, Autar Umman ikki ne."

Baffa ya sake yin wata dariyan kafin ya ce" Har da ke me, ni na ɗauka har da ita za ki tafi bikin. Na tabbata Habibu ba zai hana ta zuwa ba."

Da sauri Amma ta ce" Wallahi ba zan je da ita ba, kawai ta kunya ta ni, ka manta zuwan da na yi da  ita naɗin Sarautan Lamiɗo nan fa na faɗa maka abin da ta yi mini sai da na yi nadamar zuwa da ita, tana ta taɓe taben fuska suna jan ta da mgana sai ta ga dama take amsawa, sannan ta maƙale mini  ta ƙi zuwa ko'ina sai na yi mgana sai ta tura baki ta ce ba ta san kowa ba, wallahi ban ji daɗin zuwan da na yi da ita da man na ce har abada sai dai in ita ta kai kanta ba dai ni ba."

Baffa dai na ta dariya bai yi mgana ba.

"Ka san ta da shegen iyayin tsiya, ba ta da wayewa a wajen shiga mutane. In da Baɗɗo ta fita kenan da ba domin makarantar ta ba da tare da Baɗɗo zan tafi"

Baffa ya gyaɗa kai amma bai yi mgana ba.

"Ka dinga yi mata faɗa Baffa in kana so mu shirya da Auta nan ta ka."

"Zan yi mata"

Ya faɗa yana riƙo hannun Ammah, sai ta kalle shi, shima ita yake kallo waiwayi ya fara mata sai ta fara dariya tana  kiran sunan shi.

"Baffa..!!!

*****

Jalingo Street.

Taa ƙasa faɗa ma Habib canje-canjen da ta ke ji a jikin ta. Tsoron ta kar ta sanya masa rai akan cikin kuma su je a yi gwaji a ga ba shi ba ne, kuma sun yi mgana da Sisna da ta nemi shawaranta sai ta ce kar ta faɗa masa amma ga shawara mai zai hana ta yi gwajin da PT ta fara gani in tabbas akwai cikin?

Sai ta aminta da shawaran Baɗɗo, ita ta bar ma alhakin siyo mata PT ɗin da alƙawarin in za ta zo gidan sai ta taho mata da shi, haka kuma aka yi ranar wata Jumma'a daga makarantar da take karatu wato State polytechnic Yola(SPY JIMETA)  ta hayo abin hawa zuwa gidan Ummu.
Tare suka yi gwajin har tsinke biyu amma sai ya nuna babu cikin shike nan murnan Ummu ya koma ciki.

"SisNa kar ki wani damu, soon in sha Allahu za mu samu wani Baby kin ji ko?

Baɗɗo ta faɗa cikin sigan lallashi ganin Ummu ta ɗaga hankalinta.

"To amma yanayin da na ke ji a jikina fa SisNa?

Baɗɗo ta ce" Wata ƙila gajiya ce kawai ba wani abu ba."
Ummu dai duk da ba haka ta so ba amma hakan nan ta haƙura ta cigaba da karɓan lallashi daga wajen yaruwata Aisha(Baɗɗo) wata ƙawarta kwara ɗaya da dangatakar jini bai haɗa su ba amma amincin Amma da Ummi ikki shi ya haifar da wannan kyakyawan dangantar dake tsakaninta da Baɗɗo a yau.

Ba sa iya ɓoye ma juna komai, tun suna yara tare suka taso, duk da Ummu ta ɗan girme ma Baɗɗon da shekara ɗaya, amma yadda suka taso suka ga aminci mai ƙarfi a tsakanin iyayensu suma haka suka samar da na su misalin aminci a tsakanin su, duk da ita Ummu tana da wata ƙawar da suke kusanci sosai Shamsiya(Bestie) ita makaranta ce ta haɗa su tun da ga primary har gama babban sakandiri, a yayin da ita Baɗɗo ba ta da wata ƙawa Aminiya kamar Ummu Salma

Tare suka yi girkin dare, don Ummu ta hana Baɗɗo tafiya da ta matsa ma sai ta kira Habib a waya ta kai masa ƙaran ta shi kuma ya ce a ba ma Baɗɗo wayar ya yi mata magana da cewa ta tsaya har ya dawo su ci abiinci sai ya ma yar da ita gida tun da itama duk suna cikin garin Jimeta ne a wata anguwa mai suna Nasarawo.

Baɗɗo ba ta da yadda za ta yi dole ta zauna da man in dai ta zo gidan Habib da Ummu ke ma yar da ita gida wata rana kuma shi kaɗai, ta daɗe tana yi ma Ummu murna da farincikin samun gwarzo irin Habib, ta daɗe tana sha'awar irama ta yi aure ta tafiyar da mijinta da gidanta kamar da Ummu ke tafiyar da na ta gidan abin sha'awa abin birgewa, sannan abin da ke ƙara sa take ganin girman Habib girmama duk wani ahalin Ummu, son duk wanda take so shi ya sa ita da Shamsiya Habib ke yi musu hidima da jikinsa da aljihunsa saboda kawai sune makusantan Ummu na sosai ɗin da ba wanda ya san tsakanin su.

Bayan sun gama girkin Baɗɗo ta gyara gidan tas ta goge ta saka turaren wuta yana tashin ƙamshi, Ummu ta matsa mata sai da ta yi wanka kaya ma ta dage sai ta saka nata taƙi, a cewarta na ta ba su yi datti ba tun da ta ƙwabe su da za su fara girki ta saka wata doguwar rigar Ummu sauƙaƙƙa ta zaman gida. Bayan sun yi sallar mangriba ne Ummu ta yi wanka ta ci ado suka zauna a falo suna kallo suna hira a cikin hiran ne Baɗɗo ke faɗa ma Ummu ranar litini su Ummin ikki da Amma za su wuce Daura.

"Au da man  tare da Ummin ikki Ammah za ta tafi?

Ummu ta tambaya Baɗɗo ta gyaɗa kai mata kafin ta ce" Ke ma ai kin sani, suna nan suna shiri."
Baɗɗo da Ummu suka kwashe da dariya har suna tafawa.

"To su Daura za su je ko Abuja? Tun da na ga duka events ɗin na su a Abuja za su yi ɗaurin aure ne kawai a garin Daura fa."

Ummu ta tambaya tana  kallon Baɗɗo da dariya a bakin ta.

"To ni ina zan sani, kullum dai dai sai Ammah ta kira Ummi a shige ciki a daɗe ana tattaunawa."

A tare ma wannan karon suka kwashe da dariya kafin Ummu ta ce" Wa ya ga su Ammah a tawagan uwar Amarya."
"Sai ki iya ganin su."
Suka sake yin dariya nan Ummu ta fara ba ma Baɗɗo labarin karon su da Amma zuwanta gida na karshe.

"Sisna haka fa Ammah ta fitike ta in da take shiga ba ta nan take fita ba wai kawai saboda tana labarin bikin Daura ban tanka ba, shike nan fa ta fara faɗa daga ƙarshe  ta ce na bar mata gida tun da ba gidana ba ne, ki ji ƙarfin hali."

Ummu ta ƙarishe faɗa tana, riƙe haba da sigar mamaki.

"Amma hoo. Ammah drama Queen."

Baɗɗo ta faɗa tana dariya.

"Ba wanda Amma ta ƙyale. Hamma Lamiɗo ne kawai ban taɓa ganin ta yi ma faɗa ba."

"Ke ko wannan ai ɗan gaban goshi ne."

Ummu ta taɓe baki kafin ta ce" Ai ni tun da gabda bikina ya taɓa kiran wayar Amma na ɗauka ya ji ni ce, ina fa mgana ya yi banza da ni daga karshe sai ce mini ya yi wai shi ba ya mgana da mara son makaranta .
Ummu ta karishe faɗa hawaye na cika ƙwarmin idanuwanta in ta tuna da cin mutumcin da Hamma Lamiɗo ya yi mata sai ta yi hawaye.

"To ke me ya kai ki ɗaga kiran sa? Mutumin da sai ya gan ka ya nuna bai san ka ba, ka gaishe shi yana ji sai ya ga dama zai amsa sai ka ce jinin sarauta hauka ne."

Baɗɗo ta faɗa cikin jin takaici domin itama ya taɓa yi mata wulakanci zuwan farko da ya kawo ma Amma matarsa, sai ya kawo ta wajen Ummin ikki, ta shigo falon tana gaishe shi ya yi kamar bai ji ba sai da Ummi ta ce Baɗɗo na gaishe ka sannan hankalinsa na kan wayarsa ya amsa a ɗakune kamar mai ciwon baki da " lafiya" Wannan abin ya yi mata ciwo tana uwar ɗakin Ummin ta ji yana cewa bai gane ta ba lamarin Hamma Lamiɗo bayan jinin sarauta har da wulakanci da ɗagawa ma a cikin shi.

"Ban san shi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login