Follow us on social media

Showing 27001 words to 30000 words out of 147042 words

Chapter 10 - FARGAR JAJI Soyayya Ta Koma Cin Amana by Jamila Umar

ce kin ga wasa a magana ta ne Ummu-Salma."

Ya faɗa cikin ta da jijiyan wuya, Ummu ta firgita domin ba ta taɓa jin Habib ya yi mata tsawa irin na yau ba har ta fara hawaye.

"Ba wasa na ke yi ba. Mene ne matsayar ki?

Kanta dake girgizawa tana kwance amma ta kasa mgana saboda kuka ne ya taho mata zuciyarta na wani rawa rawa na ganin ko jin abin da ba ta taba tunanin gani ko ji daga bakin Habib ba.

"Amsa za ki ba ni da bakin ki ba kai za ki dinga kaɗa mini ba malama."

Ya sake faɗa lokaci ɗaya yana mai ɗora kafarsa a jikin gado ya ɗan duƙo yana mai kallon Ummu da ta fara rawan sanyi haƙoranta  na haɗuwa gap! gap!.

Mirmishi ya yi, mirmishin da iyakarsa fatar bakinsa kafin ya ce" Ko mutuwa za ki yi sai kin faɗa mini matsayar ki."

Da ƙyar Ummu ta iya miƙewa zaune tana mai kallon Habib tana hawaye.

"Me kika yanke?

Ya sake tambayanta wannan karon ya ɗan ɗaga murya.

"Me ya sa kake son sai na zubar da ciki Habib?
Me ya sa? Lafiyata kalau, ba ni da wata damuwa cikin nan kuma na sunna ne to me zai saka ka ce sai na zubar da shi?

Kallonta yake yi amma bai yi mgana ba, ita kuma tana kallon shi hawaye na gudu bisa kumatun ta mamaki take yi? Mamakin Habib? Mamakin me ya sauya shi cikin lokaci ƙanƙani haka.

"Kawai ina so ki zubar da shi ne."

"Saboda mene?

Ummu ta katse shi da sauri cikin kuka.

Sai ya yi shuru bai yi mgana ba amma yana ta kaɗa kafa.

"Ba zan zubar da cikin ba, sai ka ba ni ƙwaƙwaran dalilin da zan gamsu da ya cancanta da na zubar ɗin sai na bi abin da kake so."

Kallonta ya ke yi cikin mamaki, bai ɗauka  Ummu za ta ba shi matsala ba ya yi tunanin yadda take son shi komai ya ce ta yi, za ta yi ba tare da ta yi masa gaddama ba amma ya ga alamun sai ya fito mata a Habib ɗin sa sannan za ta fahimci ba da wasa yake yi ba.


"In kuma ban faɗa miki dalilin ba fa??

Ummu tana mai kallon shi hawaye na zuba ta ce" Ba zan bi Umarninka na saɓa ma Allah ba Habib. Ina son cikina kuma zan rene shi har ya fito Duniya. Ba zan yi ma Ubangiji butulci da kyautar da ya yi mini ba, ya tsamo ni a cikin dubu ya ba ni sai na yi masa butulci a wajen kashe rai?

"Ai bai za ma rai ba malama. Babu zunubi in  an zubar da shi yanzu."

Ya katse ta a fusace, Ummu ba ta san tana da ƙarfi ba sai da ta gan ta a tsaye a kan kafafunta.

"Ai daga gudan jinin ne ake busa masa rai. Ka ga ko shima zunubi ne."

Ummu ta faɗa kai tsaye tana mai share hawayenta.

"Ban san dalilin ka ba, ko ma mene ne dalilin ka na tsayar da shawaran cewa ba zan zubar da cikin nan ba Habib."

"Ko da na ce ba yanzu na shirya zama uba ba.?

Habib ya katse Ummu lokaci ɗaya yana yi mata wani kallo.

Cikin mamaki ta ke kallon shi, amma ta kasa mgana saboda bakinta ya yi mata nauyi.

"Ko da na ce miki ba ke nake so ki zama uwar ƴa'ƴana ba?"

Ya faɗa yana mai kafe ta da idanuwansa sannan lokaci ɗaya yana takawa zuwa gaban Ummu-Salma da ta kasa mgana sai kallon Habib ta ke yi, domin sai ta ke ganin kamar a mafarki komai ke faruwa.

"Ko da na ce miki ban taɓa son ki ba, ba ke ba ce matar da na shirya ki zamo uwar ƴa'yana ba, a hakan za ki yarda ki haifi cikin da ni ba zan amsa sunan uban shi ba?

Ummu ta ji wani jiri ya kwashe ta, ba domin ta yi saurin jingina da wardrope ɗin da ke gefenta ba da sai ta faɗi saboda yadda kalaman Habib suka ruguza duka saurin kuzarinta. Kan ta ta ji ya sake sara mata har wani duhu-duhu take gani, jikinta na rawa kamar ana mata kiɗan mazari, kallon Habib ta ke yi kamar tana tunanin in ta buɗe ido za ta ga komai da ya ke faruwa ba gaskiya ba ne. Sai dai ta runtse ido ta sake budewa still Habib ta ke gani a gabanta yana sake jadadda mata bai taɓa son ta ba.

"Kin shirya ma hakan!?

Ta kasa mgana hawaye ne kawai ke yi mata ambaliya, duhu duhu ma take iya ganin Habib tsabar yadda ta ji kamar ba a duniya take ba.

"To ki sani in dai kin ƙi bin umarni na , kin yi taurin kai to ina so ki san wasu abubuwa guda uku."

Har wajen fuskarta ya kawo kansa sannan ya nuna ta yatsa kafin ya cigaba da faɗin.

"Ki sani wannan cikin ba ni da danganta da shi, tun da kika ƙi bin mganata to ki je na bar miki. Na biyu kuma da man na faɗa miki sai kin yi nadaman jayayya da ni Ummu-Salma. Na uku kuma ba zan ce miki komai ba amma zan sanar da ke daga yau kin fara bankwana da farinciki, kin ƙulla ƙawance da baƙin ciki da tashin hankali a rayuwarki, sannan kin fara rasa komai tun daga yau ɗin nan, kin rasa ni Ummu Salma. Watakila da kin bi umarnina da kin tsira da wani abun tun da kuma kika zaɓi taurin kai mu zuba mu gani."

Yana gama faɗin haka ya juya zai bar ɗakin cikin ƙaraji da ihu Ummu ta ce.

"To ka san ba ka sona me ya sa ka aure ni Habib?.

Ta faɗa tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.
Kuka take yi da dukkan muryanta da iya ƙarfinta.

Juyowa ya yi ya kalleta kafin ya ɗan cije baki kafin ya yi mgana Ummu ta zuɓe a kasa a kan gwiwoyinta tana sake faɗin.

"Me ya sa Habib? Me ya sa haka? Me ya sa ka je ka nemi aurena a hannun iyayena in dai har ka san ba ka taɓa sona ba? Sannan ka san ba ka san haihuwa da ni me ya sa ka yi mini cikin?

Kuka take kamar ranta zai fita amma bai sa Habib ya ji tausayin Ummu ba, bala'in jin haushin ta ya ke ji, domin taurin kanta adadin ɓacin ran masoyiyar shi, shi kuma duk abin da zai ɓata mata rai yana gudun shi.

"Za ki san dalilin anan kusa."

Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin har yana bango ƙofa yana jin ƙaran Ummu da sanda ta sake fashewa da kuka mai cike da sauti.

Falo ya fito ya kasa zaune ya kasa tsaye me ya sa Ummu za ta yi masa haka? Bai taɓa tunanin za ta ba shi matsala haka ba, ƙaran shigowan saƙo daga wayarsa ne ya dakatar da shi daga tunanin mafitan da ya ke yi.

"Ya ake ciki? Ta amince?

Wannan lambar dai da ya yi ma saving da M.S ita ne aka sake turo masa saƙo da ita.

Jikinsa na rawa shima ya ma yar da amsa.

"Ba ta amince ba."

Ya tura ba daɗewa sai ga shi an dawo masa da amsa.

"Duk da ka faɗa mata cewa ba ka taɓa son ta ba?
Shi ya sa ba za ka so haɗa zuru'a da ita ba?

"Na faɗa mata."

"Me ya kamata ka yi a yanzu?

"Na kasa samun mafita."

"Ka sake ta Habib."

Shuru ya yi kafin ya rubuta amsa.

"Zan sake ta. Amma sai na nuna mata kuskurenta sai na saka ta yi nadaman sanina a rayuwarta. Sai na saka ta ji dama ba ta yi mini gaddama ba tun fari. Sannan daga karshe na yi mata sakin wulaƙanci da ƙasƙancin da ba ma ita ba dangin ta ma  ba za su taɓa mantawa da ni ba"

"Good Job.. Cikin jikin ta fa?

"Zai fita ko tana so ko ba ta so."

"Ka aiwatar da hakan da gaggawa domin ka san ba mu da lokaci"

"Ki yarda da ni."

"Na daɗe da Aminta da kai Masoyi na"

Saƙon ƙarshe ya saka shi farinciki har sai da ya murmusa, wayarsa ya ma yar cikin aljihun wandon jikin shi, ya fara safa da marwa yana tunanin yadda zai yi sanadiyar zubar cikin jikin Ummu Salma ko ta karfin tsiya, yana jiyo kukanta a cikin ɗaki amma ko a jikinsa tunanimsa kawai ta ina zai samar masa da kansa mafitar zubar da cikin nan? Domin bai shirya ba, kuma ba akan Ummu Salma ba.

Abin da bai sani ba, wannan gudun jinin sai an busa masa rai kuma sai ya shaƙi iskar duniya, duk abin da zai yi Ubangiji ya riga da ya gama na shi.


*Janafty*
*FARGAR JAJI.*

*Wattpad:JamilaUmar315*
*Arewabooks:JamilaUmarJanafty*

"To Hajiya Hauwa'u Inuwa Aminu (Anty Hairi) with love and gratitude"


https://chat.whatsapp.com/LsC7Rjmei7J6Hd11e95nNS?mode=gi_t

*05*

Ummu-Salma ta sha jin wata hausa a bakin hausawa. Da sukan ce wai yadda na ga rana haka na dare,  ta ɗauka wata mgana ce kawai ta shaɗi faɗi, wacce ba ta da tushe ballanta makama, ita a da in aka ce mutum ya kwana bai yi barci sai ta yi ta mamakin me zai hana shi barci? ta ɗauka sai in an yi maka mutuwa ta uwa ko ta uba, ko ciwo ita bai hana ta barci. Sannan Ammah da Baffa duk suna raye kuma duka yayyenta ba wanda ta taɓa rasawa. Sannan tun tasowarta take cikin farinciki da gata. Har haɗuwarta da Habib da yadda ya shafe wattani takwas ya na nuna mata fassaran so da ƙauna a baki da aikace.

Ba ta taɓa riskan kanta a yanayin da ta kwana a ciki ba ranar. Har aka kira sallar asuba idanuwanta biyu suna kuma masu zubar da ƙwalla ko sun gaji sun haƙura da zubar ƙwalla ba a ɗaukan lokaci za su dawo suna kwarara kamar an buɗe famfo.

Tunanin ta guda ɗaya ne, yanzu duk wannan soyayya da ƙaunar da Habib ya nuna mata duk na ƙarya ce? In tana so ta aminta da mganar shi sai ta ji ta kasa ta fi gasgata da gaske Habib na son ta ɓacin rai ne ya sa ya faɗi wannan mganar, amma in yana son ta me ya sa ba ya son haɗa zuru'a da ita? Ta kwana a ƙasan cafet jingine da wardrope ba ta damu da komai ba, ita kawai fatan ta, ta buɗe ido ta ga komai a mafarki ne in kuma da gaske ne to ya kasance Habib ya zo ya ɗuka yana ba ta haƙuri ya ce duka mganganun da ya faɗa ba gaskiya ba ne, sai hakan bai faru ba har garin Allah ya waye ba ta sake ganin Habib ba, ba a ɗakin barcin su ya kwana ba sannan ko da ta rarrafa ta fita da safe ta iske shi ya bar gidan. Kukan da ta kwana yi ya taimaka wajen sake sakar mata zazzaɓi mai zafi, tana kwance tana hawaye in ta gaji ta yi kuka salla ne kawai ke ta yar da ita tun jiya ta kasa saka komai a cikin ta sai dare da ta ga za ta mutu ta sulala indomie da ruwan tea ta ci shima ɗin bai zauna ba ta amayar da shi, ruwan zafin ta sake sha shi ne ya samu zama a cikinta.

Yadda ya bar ta da ajiyan da daddare haka ya sake dawowa ya iske ta kwance a falo tana rawan sanyi. Yadda bai ce mata sannu ba itama ta yi alƙawarin ba za ta sake yi masa mgana ba sai shi da kan shi ya gano ya yi mata laifi ya ba ta haƙuri, tunanin Ummu-Salma Habib na son ta kuma zai dawo gare ta domin ya ba ta hakuri su daidaita kansu har a wannan lokacin yardan da ta yi ma Habib bai samu nakasu ba.

Tsayin kwana biyu ba ta da lafiya sannan ta warware tun da ta na shan pracetamol amai kuma da man laulayi ne ba shi da magani, a kuma kwanakin nan magana ta fatar baki ba ta sake haɗa Ummu da Habib ba, ya sauya akalan zaman su gabaɗaya. Ba ta sanin fitan shi ba ta sanin dawowar shi, sannan ya daina kwana ɗaki ɗaya da ita, ya koma yana kwana a ɗayan bedroom ɗin da daman na shi yawancin ma kayan sa suna ciki ne, kawai shi ya ce ya fi son na ta ne saboda yana da tiolet a cikin ɗakin saɓanin ɗayan sai an fito yana tsakiya shi ya raba bedrooms ɗin su guda biyu.

Da ta ji sauƙi ta fara yin abinci ta jera a saman dinning da beakfast kamar yadda ta saba sai dai yadda ta ijiye haka take ɗauka, sun kwashe sama da sati a haka tun Ummu na tunanin nadamar Habib har ta fara sarewa, ta dawo tana gaishe shi in sun haɗu da safe amma bai taɓa amsata ba, yadda ya ke yi ma a cikin gidan kamar bai taɓa sanin ta ba. Saboda in ya dawo ba ya neman ta ballanta ya san a wani hali take ciki, abin da ya faɗa ne yake aiwatar wa da man  ya ce sai ta yi nadaman ƙin bin umarninsa tun kuma tafiya ba ta yi nisa ba Ummu ta fara nadama sai dai ba ta jin za ta iya zubar da cikin jikinta, abin da ke damunta ta kasa jin haushi Habib a cikin zuciyarta da duk da irin yadda zaman auran su ya sauya. Ta kwana kuka ta yini kuka duk ta rame ta lalace ta kuma ta kasa tattauna mganar da kowa, tunanin ta da hangen ta Habib zai dawo ya ba ta hakuri ba za ta yi saurin fallasa sirrin auran ta ba, sannan tana son shi har gobe Habib na nan da wannan matsayin a cikin zuciyarta ta kasa jin haushin shi ko kaɗan a cikin zuciyarta.

Da a ce wani ɗan'uwanta zai gan ta a yanayin da ta ke ciki sai ya yi gaggawan tambayan ta ko wani abu na damun ta ne, saboda yadda
Ummu-Salma ta koma, ta sake yin fari ta ɗashe ga shi tana laulayi mai zafi ba ta iya cin komai sai ruwan lipton in dai ta ci abinci sai ta amayar da shi, yini take yi a kwance kamar ruwa amma babu ruwan Habib, tana jin shi zai shigo da daddare sosai tun da zaman su ya sauya sai ya kai sha ɗaya na dare a waje bai dawo ba in ko ya dawo yana ɗayan ɗakin sai dai ta ji shi yana ta waya ba kuma za ta iya gane da wanda yake yin wayar ba. Wani lokacin sai in ta ji zai fita ne da sassafe sai ta rarrafa ta fita falo in ya fito ta gaishe shi amma bai taɓa amsawa ba har ya saka kai ya fita ba zai sake kallon ta ba.

Duniyar duk ta yi mata ƙunci ba abin da ke yi mata daɗi, kowa sai ya ji ta ɗif kamar ba ta nan Ammah duk rashin nuna kulawanta ga Ummu sai da ta kira ta, an ci sa'a ma ranar wayar na kusa da ita domin kwana biyu nan sai a hankali ko iya amfani da wayar ba ta yi saboda kasala da zazzaɓin da ta ke fama da shi.

"Ummu kwana biyu daga ke har megidan na ki mun ji ku shuru ina fatan dai kuna lafiya?

Haka Ammah ta faɗa bayan Ummu ta ɗaga wayar. Lokacin da ta amsa mata da lafiya sai da ta danne bakin ta saboda kuka take yi hawaye sun kece mata amma ta kasa iya faɗa ma Ammah wani abu. Tunanin ta Habib zai dawo zai yi nadama sannan zaman auren su zai gyaru bai kamata ta yi gaggawan fallasa sirrin gidan auran ta ba shi ya sa ta daure ta ce ma Ammah zazzaɓi suka yi ta yi ita da Habib kwana biyu shi ya sa a ka ji su shuru amma duk sun samu sauƙi.
Ammah ta yi fatan ƙara samun sauƙin su sannan suka yi sallama to shi ma Baffa haka ya kira ta yana tambayan ko tana lafiya.

"Lafiya ta ƙalau Baffa."

Ta ba shi amsa da fillanci, shima ba ta faɗa masa komai ba sannan ba ta bar shi ya fahimci wani abu ba. Mami ma da ta ji ta shuru sai da ta kira ta, itama ce ma ta ta yi zazzaɓi suka yi ta fama da shi a kwana biyu nan. Baɗɗo ma sai da ta kira ta, ta ce a online kwana biyu ba ta ga ta hau ba itama dai ƙaryan ta yi mata na zazzaɓin sai ta ce satin nan za su gama jarabawa za ta zo ta duba ta daga haka suka rabu. Abin da ya ba ta mamaki yadda Bestie ba ta kira ta ba sai da ta kunna Data sai ta ga ta yi mata mgana ta faɗa mata za ta kashe wayarta sai dai lokaci bayan lokaci za ta dinga kunnawa har su gama jarabawa, shi ya sa ba ta san ta yi kwana biyu ba ta online ba. Sannan dalilin da ya sa ba ta kira ta ba kenan.

Sun shafe wajen sati uku a haka ita da Habib ba abin da ya canza, ba ta sake tsinkewa da lamarin Habib ba sai da ta kama shi yana saka mata wani abu a cikin zoɓon da ke cikin frezer ɗin ta. Abin da bai sani ba ita yanzu ko ruwa ba ta sha ya zauna mata ballanta wani zoɓo tun wanda ta haɗa ne kafin zaman su ya lalace ta ma manta da shi. Da daddare cikin ta na ta juya mata saboda yunwa domin yini ta yi ba ta ci abinci ba, ba ta san shigowar Habib gidan ba tun da ta samu barci ya ɗauke ta sai a lokacin ta farka da agogon wayarta ta yi amfani ta duba lokaci. Ƙarfe 2:43am na dare, tana fitowa sai ta ga kitchen da ɗan hasken fitila ita da farko ma ta tsorata shi ya sa ta yi tsam, ta fara takawa salaf-salaf ta leƙa kitchen ɗin tun da ƙofar a buɗe ne daidai ya na saka wani abu a cikin zoɓon da ba za ta iya tantance mene ne ba, amma koma mene ne ba abu ba ne mai kyau tana da tabbacin haka, ba abin da zai ta da mutum cikin dare yana zuba wani abu a cikin abin sha kuma ace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login