ENGLISH DESCRIPTION
TA ME GARI
Some people are feared because they are cruel. Others are feared because no one can predict what they will do next.
Dije is a fearless village girl with a sharp mind, endless mischief, and a talent for turning every insult into unforgettable revenge. When two highly educated young doctors from the city arrive in her village, they make one mistake that changes everything.
What they believe is a terrifying spirit is actually an intelligent young girl determined to teach them a lesson they will never forget.
But what happens when Dije is taken from her peaceful village to live in the very house of the people who despise her?
Will she survive the humiliation and cruelty waiting for her in the city?
Or will she unleash the kind of revenge no one sees coming?
Filled with laughter, emotional twists, family drama, romance, unforgettable revenge, and powerful life lessons, TA ME GARI is a captivating novel that will keep you turning pages long into the night.
If you love African romance, Hausa novels, village to city stories, enemies to family drama, emotional suspense, comedy, and unforgettable female protagonists, this is one story you cannot afford to miss.
Enter Dije's world. Just remember, anyone who underestimates TA ME GARI will regret it.
HAUSA DESCRIPTION
TA ME GARI
Akwai yaran da ake tsoro saboda mugunta. Akwai kuma wadanda ake tsoro saboda rashin sanin makamar su.
Dije, yarinya ce daga kauye mai cike da wayo, barkwanci, da muguwar dabara. Duk wanda ya raina ta, sai ya dandana sakamakon abin da ya aikata. Lokacin da wasu samarin birni masu ilimi suka zo kauyen su, sun yi kuskuren da ba za su taba mantawa da shi ba. Daga wannan rana rayuwarsu ta juye gaba daya.
Abin da suka dauka aljana ce, ashe yarinya ce mai cike da dabaru. Amma me zai faru idan aka kwaso wannan yarinya daga kauye aka kai ta gidan wadanda ta raina kuma suka tsane ta?
Shin Dije za ta iya jure zalunci da cin mutunci a birni?
Ko kuwa za ta mayar da martani ta hanyar da babu wanda ya taba zato?
A tsakanin dariya, hawaye, soyayya, ramuwar gayya, sirrika, da rikice rikicen iyali, wata tafiya ce za ta bayyana cewa ba kowane mutum da ake raina yake da saukin karya ba.
TA ME GARI labari ne mai ban dariya, cike da soyayya, tausayi, rikici, darussa, da abubuwan da za su sa ka kasa daina karantawa har zuwa shafi na karshe.
Idan kana neman Hausa novel mai soyayya, barkwanci, ban tausayi, ramuwar gayya, rayuwar kauye da birni, da labarin da zai sa ka yi dariya sannan ya taba zuciyarka, to wannan littafi naka ne.