Follow us on social media

Showing 105001 words to 108000 words out of 140751 words

Chapter 36 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

313

amai. Da gudu nayi watsi da takarduna, na nufi yarinyar da kowa ya kama gabanshi tana niman faduwa, na rungume ta ta baya na shiga matse cikinta tare da buga bayan da kaina sau biyu nayi mata na ukun sai ga amai da kwallon abin ya fado, zubewa muka yi dukkan mu, domin ta suma ne, da sauri na kara gyara mata kwanciya a jikina masu kula da su, suka shiga ihu, ""ban ruwa!"" Ka fada musu, mika min suka yi na"

"kunsa a bakina na watsa mata sau uku sai gashi ta fara ajiyar zuciya. Nima ajiyar zuciyar nake saukewa,"

"na tashi duk kayana yayi kura, ashe labarin abinda ya faru har an isar ciki, tallafo yarinyar nayi na zauna"

"da ita a kujeran da na tashi. ""Sannu daga yau kada ki kara cin abu a tsaye, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce yana daga kyauwun dan uwanku ya ci abu cikin nutsuwa, haka zai kiyayye daga sharrin shaidan da sauran abokan halitta, idan zaki ci abu ki daina zuwa gaban jama'a kin ji, ki samu can gefe guda ki ci, mutane ba kowa bane normal wani yana da evil eyes, evil tongue, da bad mouth. Kada ki sake tsaya a gaban mutane kin ji."" Gyada min kai tayi na mike tare da kallon masu kula da su. ""Iyayen Yaran nan sun yarda da ku, suka baku amanarsu, sannan sun amince da nagartakun suka bar Yaransu a wurinku, ku kula da aikinku kowacce addini da kabila ta yarda da gaskiya da rikon amana, please ku taya su kula da Yaransu. Allah ya bamu sa'a."" Lokacin da na juya na ga bakiWaya mutanen da suka fito sun koma ciki abinsu, ajiyar zuciya na sauke na tattara takarduna, sannan na nufi ciki don sai yanzu na tuna da an kira ni fa, ina shiga cikin hall din naga wasu daga cikin staff din sai kallona suke irin kallon wulakancin nan, kofofi uku ne, kuma dukkansu an rubuta interview, wurin matan na isa na ce musu. "" Don Allah a wacce kofa aka kira sunana? "" Ina ga wannan ba wani abu ba ne da na fada da zafi, amma daya daga cikin matar ta ce min. "" Kin ajiye mu ne mu ji ko an kira sunanki?"" Kalaman Ya ado ya dawo min na kada na bari a wulakanta ni, kuma kada na wulakanta kowa, murmushi nayi nace mata. "" Sorry! "" Daga nan na wuce na zauna har wurin karfe biyu bakiWaya suka fito mazan suka tafi sallah wasu daga cikin wadanda suka zo interviews din suma sun fito, haka nima na fita nayi sallah, ashe sun rigani dawowa, ina zuwa kuma suka fito wai ashe an yi ta kiran sunana, bana nan. Sai nayi kamar na kunyata Ya Ado ne, haka na tattara kayana wani mutum ya ce min. ""Mrs Jama'are!"" Wani irin kwallar farin ciki ne ya cika min idanu, na juya ya ce min.."" ana kiranki! "" Gyada kai nayi na bi bayansa, wani hadadden office ne, muka bi stair aka kai ni, kusan tattaunawa ake suke suna faWin "" a cikin mutane dari da wani abu bakiWaya mutane sha bakwai ne suka tsallake!"" ""Sha takwas dai Uncle Auta, sha takwai kamar ya?"" Shigowar da nayi yasa suka zuba min idanu, murmushi Macen cikinsu tayi duk da bata kai su shekaru ba, amma da alamar suna ji da ita ga Yaranta s gefe, d'aga min hannu daya wacce na taimaka yayi na mata murmushi. ""Mom ita ce ta ceto rayuwata!"" Mikewa uwar tayi ta mika min hannu. ""Na gode da abinda kika yi, yau kamfani tana alfahari da ke da kuma irin wannan ceto ran da kika yi, min gode."" Gyada kai nayi ban iya amsawa ba. ""Me yasa kika yi missing interview din?"" Wani can na gefenta ya tambaye ni, cikin girmamawa na ce mishi. ""Na farko na tsaya ceton Rayuwarta ne, saboda yar adam ce kuma hakki ne a kaina na tsaya na taimaka mata, na biyu idan da na tafi na barta wani abu ya same ta har abada ba"

"zan yafewa kaina ba, koda ace ban samu aikin nan ba, ba laifi amma nayi sa'ar ceton Rayuwarta. """

""" Bayan nan an kara kiranki bakya nan ina kika je? "" Ya kara cilla mun tambayar. "" Ibada na tafi, koda"

"na dawo na samu an tashi, duk abinda ake nima a duniyar nan, anan zamu barshi, can ne dolenmu don na rasa wannan damar ba wani abu bane, babbar damar da zan rasa shine rasa sallah nan."""

""" Kina magana da kawazuci, me yasa kika ajiye son kika dauki kawazuci?"" Yar dariya nayi, yadda"

"suka kalle ni sai na rufe bakina, kaina a kasa kafin na ce mishi. "" Duk wata mace a duniyar nan idan har ta isa mace uwa ce, ko ta haifa ko kada ta haife ita din uwa ce, idan har da rayuwa ta bamu abinda muke so,"

"zan ji ciwon idan aka ce Y'ata ce a cikin wannan yanayin, akwai abinda dukiya baya iya siyansa a cikinsu"

"kuwa har da Yara, kawazuci ba iya mutane ke raye akanshi ba hatta dabbobi suna da ita. """

"Jinjina kai yayi ya kara da cewa. "" Yanzu idan kamfanin nan tana cikin wani irin yanayi kuma lokancin"

"sallah yayi zaki iya tsallakewa ki yi sallah!"" Kallon kasa nayi nace mishi. ""Ba mamaki wanda ya tsaya har kamfanin ya iso wannan matakin bata raye, yau ya tara amma baya nan balle ya ga yadda yake tafiya, an tambayi wani daha cikin magabata me tafi yin addu'a a kai game da Lokaci, ya ce Allah ya bashi aron numfashi ya kara ganin wata lokacin da zai ibada, kamfani bata kai ibadana muhimmanci ba, zan bawa kamfani lokacina amma banda ta ibada ta."" Daga haka suka yi shiru basu kara magana ba, Nima kuma ban ce uffan ba, ina tsaye a wurin karar shigar sakon da aka musu na d'ago kai ina kallonsu, daya babban cikinsu ya ce min. ""Mrs Jama'are, idan aka baki damar aiki da kamfanin nan me kike ganin zaki yi har ya kai ga nasara."" Jan iskar bakina nayi na ce mishi. "" Na karancin hadahadar kasuwanci a degree na farko, na kara yin master a tallace-tallace, idan har akwai abinda xan yi shine zan tsara yadda kamfanin nan zata fito idanun duniya. Zan mai da hankalina wurin daidaita kamfanin izuwa ga sauran takwarorinta na"

"duniya, sannan zan bawa aikina muhimmanci sama da kome da kowa na kamfanin. """

""" Mrs Jama'are idan kamfanin ta dauko karyewa, nasan kin san aikin kamfanin me kike ganin zaki mata"

"kada ta karye?"" Lashe bakina, na sauke ajiyar zuciya kafin na ce."" A matsayina na karamar ma'aikaciya kuma wacce take da ilmin tsara tallace tallace, shine zan fara duba yadda zan janyo hankalin masu zuba hannun jari, daga gida zuwa kasashen ketare, aanan kuma zan yi ™o™arin rufe duk wata kofa da zata janyo min karyewa a cikin kuwa shine zan zubar da ma'aikata, ba zan debi sabbin ma'aikata ba, tsofin zan kara basu horo sannan na kara inganta ilimin su yadda zasu fuskanci yanayin da ake ciki, za a rage wasu abubuwan da ake yiwa ma'aikata idan kamfani ta farfaWo sai a kara musu, wannan tsarin economic"

"ne ta kowacce kamfani da kuma manyan ma'aikatun duniya."""

""" Kina nufin a watsar da tsarin diban ma'aikata kenan? Idan haka ne kuwa har dake a cikin haka ya"

"miki?"" Gabana ne ya fadi shi kenan nayiwa kaina, sai nayi murmushi na ce mishi."" Haka ma ba laifi bane, kowacce kamfani tana kokarin ceto rayuwarta ne. Idan har aka duba masalahar kamfanin babu amfanin"

"diban ma'aikata, idan kuma kamfanin tana da bu™atar haka ai ba laifi bane. """

""" Mrs Jama'are ko dai zaki gare muradinki ne? "" Inji matar, murmushi nayi mata nace mata. "" Ko daya ni"

"ina da nawa ra'ayin ba wai aikin kamfani nake da buri ba, amma a tambayar da aka min dole na bada amsa."" Cidar d garin ya fara alamar za ayi ruwa yasa na kalli agogon hannuna. ""Shi kenan zaki iya tafiya!"""

"""Na gode!"" Na fita ai nasan ba wani batun daukar aiki, ya xan yi da Ya Ado?"

"Ruwan da aka fara yasa da na sauko kasa ba tsaya ina kallon waje kamar yadda kowa ya tsaya, matan"

nan sai gulma suke.

"Bayan fitar ta ya juyo kujeran, yana ta rubuce-rubuce. ""Bro yarinyar tayi tana da kwarin gwiwa!"" Inji"

"Jasminah, ""Kuma da alamu zata yi abinda ya dace, shi dai bai ce kome ba, "" can dai Uncle Auta ya ce mishi. "" Sunan yarinyar kamar yaso na taSa jin sa a wani wuri?"" "" Usman Umar Jama'are, Baristan nan!"" Inji Ubaid, "" wow dole ta samu confidence, irin wannan ake bukata asalin kwarin gwiwa na gani a cikin kalmanta!"" Shi dai shiru yayi can Uncle Auta ya ce mishi. "" Ni kuwa yarinyar ta min, tana da nutswa da hankali!"" "" Oo Uncle Auta fell in love daga kallo daya."" Buga table din yayi ya ce musu."" Bata min ba ta cika surutu, mai surutu baya abinda ya dace!"" Daga haka ya bar office din yana mai riko hannun Yaran.."" Uncle BT amma tana da kirki, me yasa ba zaka dauke ta ba. Ina sonta."" "" Princess idan aka kawo ta kamfani ba zata yi aikin da ya dace ba zata yi ta hira da mutane ne."" "" Uncle BT yana da kirki Please!"" Dan durkusawa yayi yana kallon yarinyar da take murza idanunta. "" Uncle tana da kirki she is a good person!"" Taya zai gaya mata bata da kirki, bayan ta ceto rayuwarta. "" Princess kada ki damu da irinsu."" Idanunta ne suka cika da kwalla, har suka zubo mata ta ce mishi.""please!"" "" Ok ok bar kukan haka kin ji! "" Gyada kai tayi tana murmushi, haka suka fito sai lokacin ya hango tana fita daga kamfanin a hankali tana tafiya ruwa na zuba kaWan kaWan, bodyguard dinsa ne suka fito da lema suka saka mishi bayan ya dauki Yarinyar, suka bude motar ya sakata, ya daura mata belt sannan ya shiga suka tashi motar, a hankali"

suka bar kamfanin a bakin gate suka tsaya sakamakon wata motar da ta danno kai.

"A hankali nake tafiya har na samu wani abin hawa na gaya mishi inda zai ajiye ni, ya ce na shiga, sai dai"

"cikin ikon Allah motar taki tashi dole na sauka na cigaba da tafiya nayi tafiya sosai, kafin na nufi garej, kamar ance na d'ago kaina daga lemar na hango ya Hafiz ban san lokacin da na sake lemar na fara ja da baya ba, murmushi ya sake yana kallona, daidai sake wata irin ruwa mai karfin gaske shaaa, karafuna ne suka dauka rawa, na ji kamar cikina ya hautsine, wani irin abu na ji ya tsaya min a wuyana. Na fara ja da baya, yana bina ina ja da baya yana bina, ga titin ba motar da suke wucewa, hawaye ne ya fara zubo min. Karar horn na ji na kalli wurin, na hango motar kamfanin ce, wani irin kuka ne ya kwace min ganin yadda suka wuce. ""Ba fa mai taimakonki, kaf duniya babu sai ni, ni kaWai ne last hope dinki!"" Yadda yake tawowa ban san me ya tare ni ba, haka na zube yayi kaina zai damke ni, na kare kaina tare da fasa wata irin kara tare da kiran sunan Allah, na rufe idanuna hannuna biyu na saka ina mai kare kaina, wani irin"

"kara naji wanda ban san yadda akayi na bude idanuna ba, sai ganin............."

(Alhamdulillahi na gode sosai wannan wurin nasan sai an ji kamar a cije ni kuma duk wnada ya zagi

hafiz shi da kanshi)

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 45"

"Kamar yadda aka ce mata suna suka tara, haka ma Maza sun kashi gida daban daban, domin ni dai ban"

"tab'a ganin irin wannan mutumin ba, hannun da ya Hafiz ya kai zai damko ni ita aka murder a baya sai da tayi wata irin ™ara, kafin ni da shi mu farfaWo, bawan Allah nan ya kara sake mishi naushi. Sai na kasa fahimtar tsoron waye zan ji a tsakaninsu Hafiz ne ko wannan mutumin da sauri na kara kifa kaina kasa ina wani irin kuka, ji nayi an lullube ni da abu, an d'aga ni. Muryan mace na ji tana faWin.. ""Sannu muje mota, ai ke ma'aikaciyarmu ce, Sir ba zai bari wani abu ya same ma'aikancinsa ba."" Haka ta saka ni a"

"motar sannan ta koma ta dauko min lemana da tarkace na, a hankali na kalli inda Ya Hafiz yake kwance,"

"mutumin ya murde hannunsa. Sai zabga mishi naushi yake irin na b'acin ran nan, barin wurin muka yi, na"

"kifa kaina a kan cinyata, idanuna rufe. ""Wacece unguwa kike?"" A hankali na gaya musu ma cigaba da kuka."

---

"A can kuwa Garej Mr Turaki bai yi niyyar shiga al'amarin ba, tunawa da yadda aka yiwa Mrs Thomas yasa"

"shi kiran security na kamfanin kafin ya fita da sauri duk da kiyayyarshi da sanyi kuwa, amma ta gane ta ne da lemarta. Sannan Ilham ta kara ce mishi, ga wacce ta taimake ta. Haka yasa shi tsayar da motar, umarni ya bawa Tajudeen akan ya kira sauran security din domin ya tuna abinda ya faru da wancan matar haka yasa shi sauka ya samu Hafiz. Ba zai ce ya yake ji ba, domin abu ne me sauki da mutum zai"

"bada labarin yadda ya ji shi, wani babban al'amari ne da Allah kaWai yasan yadda abin ya™e."

Yadda ya dage da dukkan zuciyarshi yake kai mishi duka zaka rantse da Allah irin yasan Mafarin

"lamarin ne, amma ina shi zuciyarshi abinda ya bashi ita din mace ce me rauni kuma tana bukatar taimakon shi, fisge shi Ubaid yayi yana faWin. ""T meye haka? Me yayi maka? Haba da girmanka?"" Huci yake yana nunawa security Hafiz. ""Ku tabbatar kun hada shi da yan sanda."" Sannan ya juya ya bar wurin ranshi yana soya, ko ruwan da ake yi bai dame shi ba, tunda Ya shiga motar yake jin wani irin zafi. Har suka isa Mansion na Kumo bai magana ba, yana zaune shiru towel Jasminah ta lullube shi da shi tana faWin. ""Sanyi zai kama ka!"" Komawa gefensa Alhaji ELYakub yayi ya zauna yana press din hannunsa a hankali, alamar yana calming dinsa da ya huce wani irin zuciya ce me cike da kishi, dafe kanshi yayi ga hannunsa da ya ji ciwo yayi ja saboda naushin fuskar Hafiz kawai,"" Me ya faru da ita?"" Daddah ta tambaye su hankalinta a tashe, "" Fada yayi da wani!"" Uncle Auta ya fada yana kallonshi. "" Fada!!!"" Duk suka hada baki, domin abin da mamaki Daddah ta ce. ""Wai yaushe ma taso ne?"" ""Muma ganinsa muka yi dazun!"" Ubaid ya bata amsa, cike da mamaki Alhaji ELYakub yake kallonshi. "" Kuna nufin bai gaya muku zai shigo ba?"" Alhaji ELYakub ya tambaye su cike da mamaki, shigowa Alhaji Abbas kumo yayi yana faWin.."" Amma wannan wacce irin abin kunya ne Bilal ya aikata? Duk an dauki videon ana yaWawa a duniya. Baffa ya kamata ka yi wani abu, taya zai shirya interviews without our knewing, ba laifi sai ya je ya kama fada da yan iska idan wani abu ya same shi fa? Ya yake tunanin al'amarin zai kasance ga masu saka hannun jari."" Mikewa yayi bai karasa jin mai yake faWa ba yayi waje abinsa, "" Turaki! "" Ina tuni ya bar cikin gidan abinsa. Shi dansa ne zai saka shi gaba yana mishi ihu, ko dansa da yake abinda yaso baya mishi ihu, "" Bilal listn to me!"" Kwace rikon da Ubaid yayi mishi yayi yana kallonshi. "" Ni Yaro ne?"" Ya tambayi Ubaid, girgiza mishi kai yayi yana faWin."" Muje na sauke ka a gida."" Haka ya shiga motar yana shiga ya fara jera atishawa, yana yi yana karawa. Har suka iso gida, kusan sanyi ya gama kama shi."

"Wanda ya haWa har da zazzaSi me karfi, tare da mura. Karshe sai da Uncle Auta ya haWa da kiran likitan family din ya mishi allura. Alhaji ELYakub ya zo shima hankalin Familynshi ya tashi sosai saboda sun san yana da irin wannan ciwon wannan wani abu daya da suke son kara amfani da shi, ba kome bane sai"

"maganar fadar da aka yi. Hajiya Khaulatu da tazo ta ganshi, ba ta bar gidan ba sai da ta san yadda ta"

"samu Alhaji ELYakub ta ce mishi. ""Tunda babu wanda zai zauna da shi Badr ta zauna da shi mana, zai so"

"ya bukaci wani abu idan ya farka."" Uncle Auta yasan manufar yar uwarsa, amma idan yayi magana, zata ce yana hana su samun kusanci da Turaki, haka yasa shi zuba mata idanu, Mahaifinsu kuwa ya amince,"

haka ta fita tare da kiran Badr tazo gidan tayi jinyar Turaki.

Shi kan tunda aka saka mishi ruwa da allurai ya cigaba da barci.

***

"Har gida suka kawo ni, kuma har lokacin ban daina kuka ba, domin na razana ba wai Hafiz ba, ganin"

"yadda mutumin nan yake dukar Hafiz sai ya bani tsoro matar ta ce min. ""Mun iso nan ne ko?"" A hankali na fito ta rako ni har kofar gidan sai da ta ga shigana sannan suka bar kofar gidan. Tunda na ga motar Ya Ado, kukan da nake ya karu, ban san yadda aka yi ba sai naji kamar an cire min duk wani tsoron Ya Hafiz dake ji, naji a raina idan na kara ganinsa sai dai wani ba shi ba. Haka na shiga parlourn na tsaya daga bakin kofar, zuba min idanu suka yi ganin yadda nake kuka. Tasowa Aunty Zakiyah tayi ta nufo ni. ""Hafiz ko?"" Cikin shashekar kuka na ce mata. ""Eh!"" Haka ta wuce da ni dakin kasa ta haWa min ruwa nayi"

"wanka , ina fitowa ta bani magani na sha da tea me zafi na kwanta, karfe shida saura na tashi. Nayi sallah la'asar da ta kwace min, da sallah Magariba, ina zaune a wurin Ya Ado ya shigo. ""Ya interview din?"" Kallonshi nayi idanuna cike da kwalla. ""Kayi hakuri nayi missing dinsa, ban samu yi ba."" Zama yayi s stool yana kallona. ""Hafiz ya bi ki can ko?"" Hawaye ne suka zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login