Follow us on social media

Showing 69001 words to 72000 words out of 140751 words

Chapter 24 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

322

kuka hadu ta yi amfani da wannan turaren, ta haka zaka kara rabata da nutsuwarta. Amma"

kada ka sake wani ya shiga tsakaninku..........

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 26"

"""Ga wannan zoben ka saka a hannunka, akwai lokacin da zakai ka gare ta. A ranar ka hadu da ita kada ka"

"sake wani ya shiga cikin lamarin ka daidaici lokaci domin sa'arka zata fara idan har bukatar ya biya zoben zata haske idan kuma ka bari tayi baki bukatar ta lalace. Idan kuka hadu ba zata tab'a bijire maka ba, duk abinda kake so da ita zata maka, koda kuwa cewa kayi ya kashe kanta ko wani nata ne kuwa. "" Jinjina kai yayi yana kallon Malam irin kallon rashin yarda nan, Malamin ya janyo wata kwanon sha ya ce mishi. "" Nasan baka yarda ba. Amma bude wannan abin zaka yarda da ni, ba yau nake maka aiki ba hatta rashin fadar da ta kasa yi mune muke danne bakinta, mun yi haka ne don ka dangwali arziki son ranka. "" Hannunsa yana rawa ya bude kwanon, sai ga Lulu zaune akan abin sallah. Ya cigaba da cewa. ""Ka rufe!"" Ba musu ya rufe, ya kuma ce mishi. ""Bude!"" Mama ce take zuba abinci a takeaway ana fita da shi sadaka. ""Kai din banza kasan har rago aka yanka domin kawai ka nisanci yarta, ita fa a tsaye take ko ta mutu ko tayi rai ita Yarta kawai take son tayi farin ciki."" ""Malam yanzu me ake so?"" Kallonshi Malamin yayi yana shafa gemunsa cikin son abin duniya ya ce mishi. ""Mahaifyarka ta san abinda take biya, ni bana yanke"

"kudi amma ana bani kudi me nauyi ne, sannan babban abinda yake lalata min aikina wasi-wasi."""

"Jin haka yasa Hafiz nutsuwa domin yana jin haka a ransa, haka suka bada kusan dubu hamsin,"

"sannan suka fito daga gidan Hajiya Asiyah tana gaya mishi yadda zai yi, haka dai suka bar unguwar suka wuce gida, bai kwana ba ya dawo Bauchi, bai shigo ba sai karfe tara na dare, kin isa gidansa yayi ya wuce bayan gari a can ya kwana yana sheke ayarsa, washi gari ya isa gida yana muzurai, sai dai ganin wani bako a gidan ya bashi mamaki, sai yayi kamar bai damu ba, bayan ya huta bakon ya tafi sai ga Karimah, ta tsaya mishi a tsaye. ""Waye wancan mutumin?"" ""Ai dan uwana ne?"" ""Kamar ya dan uwanki ne?"" Ganin zai bata mata lokaci ta juya ta bar dakin, shi kuwa zuciya ta kwashe shi ya bita dakin ya ga gadon a wargaje. Yaransa ma gasu nan suna ta barci har lokacin basu farka ba, ga bra dinta da pant dinta a kasa, ba kawai sai Malam Hafiz ya rufe ta da mugun duka ba, kamar dai kashe ta. Dakyar ta kwace ta fita kamar mahaukaciya haka ta bar gidan, ya kama Yaran ya musu wanka. Ya kira Hajiya ya gaya mata, ta ce maza ya sake ta. Ya shirya ya tafi gembu ya aure yar dan uwanta, ya ce mata tayi hakuri zai kira Baban ya gaya mishi yadda suka yi, ai kuwa haka aka yi ya kira shi ya gaya masa, karya da gaskiya Baban Bauchi ya"

"tausaya masa tare da cewa yayi hakuri kada ya sake ta,ya zo maza."

"Haka ya tattara yaran ya wuce dutsen tanshi, ya samu Yadiko da mai aikinsu suna ta aiki, yadda ya"

"shigo gidan hankali a tashe ga yaran a hargitse, yadda ya zauna gaban Baban Bauchi yana rusa kuka yaran na taya tashi, duk sai Baban Bauchi yaji wani abu na damunshi don haka ya ce mishi. ""Ka nimo auren ko yar waye, in sha Allah zan tsaya maka ita kuma babu amfanin zama da mace irinta, abin tausayi Allah ya jarabce ka da rashin mata na gari."" Haka yayi ta rarrashinsa tare da cewa ya bar Yaran a gidan Yadiko ta kula da su, ai daga waje ta ce mishi. ""Gara tun wuri ku nima musu wurin zama amma ni ba zan yi renon yarana da jikokina na kara da na shi, dama ace Yaran Lubnah ce zan karba."" Kiri-kiri ta ce ba zata amsa ba. Haka ya batawa Abba rai ya kira Munah don ya lura sun fi jin maganar Yaransu akan maganarshi. Haka yasa shi gayawa Munah, kiri-kiri ta gaya mishi ai suna tare da uwarsu abin sai ya fusata Abba. Dakyar Yadiko ta rike Yaran zuwa washi gari ya wuce da su Jamaare, daga can ya wuce"

Gembu.

"Kwanaki biyar yayi ya dawo, sannan ya gayawa Abba, aka saka karshen wata za a tafi gembu a nima"

masa auren.

***

Lubnah

"Duk ranar Lahadi ina da dabi'ar wanki da guga, duk da cewa kuwa ana mana wankin ne. Haka na hada"

"kayana na goge su gugar ma kaiwa ake. Monday ya kama Yau da wuri na fita domin muna da test, ina shiga makarantar. Ban san waye shi ba ni dai naga yana ta bina a mota har na shiga department dinmu, wurin karfe daya muka fito. Masallaci muka wuce nayi alwala na gabatar da sallah, sannan na tafi"

"cafeteria, na sayi ruwa na wuce hanyar Library. ""Excuse me?"" Aka fada ta gefena, juyawa nayi na kalle"

"shi, gabana yana faduwa. ""Sannu ko!"" Ya kara ce min. Ni dai ban amsa mishi ba, da za a lura da ni ba"

"karamin rawa jikina yake ba, kallona yayi a tsanake ganin yadda nake raba idanu yasa shi ce min. ""Sunana Rafiq"" kafin ya cigaba da magana na ga wasu yan iskan abokai masu kama da yan kwaya, da"

wani irin sauri na bar wurin na bar wurin suka ta min dariya.

"Ya Ado ya zo daukana na nufi motarshi, sai ga gaye nan, ya tare ni ai kuwa Ya Ado ya fito yana ganinsa"

"ya ce mishi. Barista Yar uwarka ce."" Kallonsa ya Ado yayi da kyau. Ya ce min."" Shiga mota ina zuwa!"" Haka na wuce motar na zauna ya ce mishi. ""Ita ce autarmu, don't mess wrong person, kada ka kuma shiga rayuwarta, kasan har yanzu akwai sauran case dinmu, idan karatu ka zaba tow idan kuma zamu koma kotu ne mai sauki ne. Domin na kare ta babu abinda ba zan aikata ba na gaya maka."" Daga haka ya dawo motar muka bar makarantar. "" Tun yaushe ya fara damunki?"" "" Yau!"" Na bashi amsar a sanyayye, "" baya jin magana iyayensa na kokari amma yana janyo musu magana, ina fatan bai miki wani"

"abu ba."" "" Ni tsoro ya bani;"" na fada ina kallon gefen hanya."

"Murmushi yayi ya ce min. "" Ba abinda zai miki, na gargade shi."" "" Allah yasa ya ji!"" "" Yana son gobensa zai"

"matu™ar wahala bai kiyaye ba, yasan idan na kure mishi gudu sai ya rasa inda zai boya. Da haka muka isa gidan, ya bawa Aunty Zakiyah labarin abinda ya faru tayi ta dariya tana faWin..""idan ubansa ya ji sai ya kusan mutuwa yadda yazo akan case Win kudirat ai kasan basu ji da dad'i a hannunka ba, gaskiya SAN kana vocalno."" Wuce ta yayi yana faWin. ""Ke kuwa kina aman kankara!"" Jin zasu sake layi na wuce sama da sauri Princess tana bani labarin Auntynsu me eyelashes, ko baka da niyyar dariya lamarin Auntynsu"

"nan sai ka dara, yadda Princess take takaicin Eyelashes din nan."

****

KUMO FAMILY Mansion .

"A harabar gidan da aka kawata shi da kayan bud'e baki, aka hadu duk da layya ta kusa amma a duk sati"

"Alhaji ELYakub yana da dabi'ar azumi da mazan gidan, idan aka sha ruwa aka yi sallah za a zo kofar harabar Alhaji ELYakub a sha ruwa kafin lokacin isha yayi a kara zama tattauna akan abinda ya shafi"

"family din na alkhairi da sharri, cigaba da koma baya."

"Da sallama wani dogon matashi, hannunsa rike da wata yar yarinya kyakywa, ga gefe guda"

"Matarshi tana dauke da wata baby, da sallama suka zauna domin aka haduwa maza da mata ne, cikin girmamawa ya ce. ""Alhaji Baffa Barka da shan ruwa ya ibada."" ""Alhamdulillahi Khamis ya aikin da can Kano?"" ""Lafiya lau.""Ya fada yana shafa kai Alhaji ELYakub ya kalli matar da take dan takure tana gaida iyayensu, duk da itama kusan har cousin din Abbas ce, Baban Khamis din, amma rayuwar aurenta ba sauki. "" Annah! "" Juyawa tayi tana murmushi ta ce mishi. "" Baffa ya jikin girma? "" Murmushi yayi ya ce mata. "" Alhamdulillahi ya can Kanon da fatan babu matsala ko? "" "" Eh ba matsalar kome!"" "" Masha Allah!"

""" Ya furta haka suka sha ruwa ana kiran sallah isha mazan suka tafi masallaci matan suka kafa dandalin"

"hira, har mazan suka dawo aka cigaba da hiran. Bayan hira yayi tsawo sai lokacin Uncle Auta da Ubaid"

"suka iso da iyalansu. Su kan basu cikin estate din don sun ce ba zasu zauna ba sai ranar da Turaki ya dawo ta ce zai zauna a estate din zasu dawo idan ya ki kuwa dama unguwarsu daya Lekki gidansu ma na kusa da juna. Kuma irin hauka da hayaniyar da ake a KFM basu cikinsa basu sani ba sai sun zo ne a basu labari. Nan hira ya kara dinkewa bayan an yi gaishe gaishe, daga Ubaid da Auta babu wnada ya zo da"

iyalinsa domin sun fahimci yadda ake rena musu mata.

"Gyada zama Alhaji Abbas yayi karkace kai cikin iya makirci ya ce. ""Baffa idan baka manta ba, akwai"

"al™awarin da Marigayi ya kulla a tsakaninmu."" Gyara zaman glass dinsa Alhaji ELYakub yayi yana saurarensa. Ya cigaba da cewa., ""marigayi ya ce idan har ni ko Jibirin dayanmu ya haifi y'a mace yana kamawa Turaki!"" Murmushi Alhaji ELYakub yayi yana kallon Abbas, ya ce mishi. ""Tabbas anyi baka wani zuwanmu Gombe ko? Sai dai a lokacin ba cewa yayi dole ayi auren ba idan Turaki yana ra'ayin yaran sai a"

"kulla zumunci idan bai ra'ayi ai baa yi namiji auren dole."""

""" Mujitafa amma ai ya dace Turaki ya ajiye iyalin haka indai ba maganar da ake ta yaWawa na cewa"

"yana homo ba! "" Inji Hajiya Khaulatu, lumshe idanu Alhaji ELYakub yayi da karfi, ya jima kafin ya bude kanshi a sunkuye.. cikin dattako ya ce musu. "" Ba zan yiwa Bilal Turaki dole ba, idan ma ya ga dama ya rayu babu mace ba sabon abu bane, domin akwai bayin Allah da suka koma ga Allah babu abinda ya dame su da mace. "" Haka suka yi shiru ya kalli Hajiya Khaulatu ya ce mata. "" Kika ce ana zarginshi ko?"" ""A'a baffa!"" Dakatar da ita yayi ya nuna mata hanya ta bar wurin ya kuma rantse ya baya bukatarta a wurin shan ruwansa. Karshe haka aka tashi abin bai yi dad'i ba, a hanya Uncle Auta da Ubaid suka kira shi, sai da aka yi kira biyar a na shida ya dauka. ""What?"" Wani Uban Ash'aria Ubaid ya watsa mishi, amma ba kula shi ba, sai da Ubaid yayi mishi mugun zagi da cin mutumci kafin ya ce mishi. ""Ubana da yake gefenka yana godiya!"" Bakin ciki yasa, Ubaid sake tsaki ya ce mishi. ""Dan kutumar uba, shege dan"

"daudu. Kuma auren dole za a maka idan baka zo naija ba."""

"Nan ma din bai bashi amsa ba sai da yaji Ubaid ya sauke ajiyar zuciya ya ce mishi. ""Ka gama?"" Wani"

"uban ashar ya danna mishi, Uncle Auta ya ce mishi. ""Ubaid ya isa haka, Son ka dawo haka?!"" ""Tow Uncle!"" Ya amsa mishi yana sauke numfashi, ""shege waye ya sani ko iskanci kake da wannan ajiyar zuciyar!"" Uncle Ubaid da dama can ya saba da wannan halin nasu. ""Ya isa Son kyale shi haka yaushe zaka dawo Boy!?"" Sai da yayi shiru kamar ba zai magana ba ya ce mishi. "" In sha Allah soon! "" Cikin takaici Ubaid ya ce mishi. "" Soon da baturen da ya kirkiro sun ci kaniyarsu!"" Katse wayar yayi dan ya gaji da"

hayaniyar Ubaid ya ishe shi......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 27"

"""Wai kai kan yaushe zaku girma ne?"" Cikin takaici Ubaid ya kauda kanshi yana huci, har suka iso"

"unguwarsu, sai da ya ga tsaya Uncle Auta ya shiga gidansa sannan ya juya zuwa gidanshi da yake kusa da na Turaki, kallon yadda aka kunna haske gidan yake shi bai tab'a kwana ya wuni ba tare da yasan me yake faruwa a rayuwar gidan ba, don haka yana shiga cikin gidanshi, ya nufi cikin gidan. Matarshi da take ta zaman jiran shi. Mikewa tayi tana faWin.. ""Daddyn Nihla barka da dawowa?"" ""Yawwa Fahimah."" Ya"

"fada yana nufar dakinsa, haka ta bishi kamar ta sani ta ce mishi. ""Key zaka Wauka?"" Bai juya ba ya gyad'a"

"mata kai. ""Dazun an kawo sako yana store."" Juyawa yayi yana kallonta. ""An kawo sako kika ce?"" ""Eh"" ta"

"fada tana matsa mishi a hanya, ta taka a hankali har dakin da aka ajiye sakon, daga rubutun da yake jikin ledar kwalin zuwa girman kwallin yasa shi juyawa ya fita, gidan ya shiga ya samu ko ina fesa. Gwanin ban sha'awa. Ciro wayarshi yayi ya saka a kunne. Yana kira da shi. Rejected din kiran aka yi, sannan ya turo mishi. ""Sorry Man im busy!"" Me Turaki yake haka da yake da muhimmanci sama da shi? Idanunsa ne cika cika da kwalla. *Ba kome nake bukata ba sai lokacinka nake bukata Please ka saurare ni dan"

"uwanka* kusan minti talatin yana jiran sakon, amma babu alamar haka."

"Sai da ya gama zamanshi har ya mike zai fita sako ya shigo mishi. *Captain Ubaidullahi am sorry, bani"

"da lokaci ne! Zan kira ka gobe sai ka sakawa princess naji muryanta.* Rintsa idanunshi yayi yana tuno wani babban al'amari da ya shiga tsakaninsu lokacin da ya dace ya yarda da shi amma ya juya mishi baya, ya bada shaidar da bata dace ba akanshi, yasan ya rusa yarda da take tsakaninsu, amma ba yana nufin haka ya raba su bane asalima yayi haka ne don Turakin ba wai don kanshi ba. Amma tun daga lokacin ya"

lura da Turaki yana gudunsa. Wannan yafi kowa yi mishi ciwo a ce Amininka yana gudunka.

"Haka ya nufi gida zuciyarsa ba dad'i, ya wuce dakinsa ya kwanta ko kayan jikinsa bai iya cirewa ba,"

"haka ya kwanta ringigine yana kallon sama, yana ji kamar kome ya dawo da baya ya goge kuskuren da ya aikata. Amma ina kome ya tafi fiye da yadda ba zato, anyi amfani da amintarsu an lalata alakarsu. A hankali ya kwana rabi barci rabi nazarin tsakaninsu, kuma yasan threating dinsa aka yi har yayi magana"

"idan ba haka ba, tow da ba zai tab'a bude bakinsa ba."

"Karfe shida na safe ya wuce dakin motsa jiki, ya jima yana motsa jikinsa sannan ya dawo yayi wanka ya"

"shirya ya samu Amirah tana abin karyawa tana juyawa ta kawo mishi parlourn Wan rungume ta yayi yana sumbatar goshinta. ""Morning beauty"" ""Morning my star!"" ""Ina Nihla?"" ""Tana barci haka ya cigaba da karyawa wayarsa ce tayi ™ara yana dubawa ya ga Introvert. "" Assalamualaikum! "" "" Amin waalaikumunsalam! Barka da safiya."" Daga can ya ce mishi. "" Yawwa ina princess? Ina Mamana? Ina abar kauna?"" Tashi yayi yana hadiye abin bakinsa ya ce mishi."" Tana dakinsu bari na duba ta. Haurawa sama yayi da gudu ya same ta tana juyi, shafa kanta yayi ya ce mata. ""Honey tashi da Appa!"" Ya saka mata wayar a kunne, nan ya shiga mata waka ta fara dariya alamar tana nemansa a zahiri, yadda take raba idanu tana wangale yan hakoranta kwaya hudu zai tabbatar maka tayiwa Introvert din mugun sani, irin sanin da ko shi Ubaid da yake Mahaifinta bata mishi wannan sanin ba, yadda take dariya har da tashi ta"

"zauna, zaka girmama shakuwar da yake tsakaninsu."

"Sun jima sai da Uban ya cire wayar ya ce mishi.. ""Malam zan tafi aiki? Ka kira Amirah ta bata wayar."""

"Ya fada yana gyara daukar ta. Ya fito da ita yana faWin.. ""Amirah zo ki amshi yarinyar nan ta cika pamper dinta da kashi sai tsami yake."" Ya dauki abinda zai Wauka suka cigaba da wayar shi tunda ya raba wayar"

"da yarinyar tuni ya ja bakinsa ya tsuke, bayan ko minti biyar ba a yi da raba shi da yarinyar ba, sai shine"

"yake ta zuba a kofar gate ya hango Uncle Auta yana jiranshi, zuwa yayi ya dauke shi. Sannan ya kai shi inda yake aikinsa sannan ya ajiye shi kafin shi ya wuce KUMO properties nigeria agency. Yana shiga yayi parking, office din da yake na shi ya isa ya fara abinda ya kawo shi domin bayan nan yana da kasuwancin da suke yi tare da Mr Turaki. Shigowa aka yi tare da banko kofar, bai d'ago kai ba don yasan cikin marasa kunyar Jikokin Alhaji ELYakub Kumo ne. ""Kai matsayici taya Turaki da baya kasar nan ya san me ke tafiya a kamfanin nan? Sannan maganar haraji!"" ""Khamis Mudansir ELYakub Kumo Please zaka iya fita daga office dina?"" ""Lallai ne ka samu wuri, daga kai har Mrs Thomas zaku yi bayani!"" Y cigaba da ihu da fada da jidali, kamar zai daki Ubaid, shigowa Alhaji Mudansir ELYakub Kumo yayi ya kifa mishi mari sai da ya zauna a kujerar da yake kallon na Ubaid, wannan abin bai saka Ubaid d'aga kai ya san suna wurin ba, ""Dad!"" Sake kifa mishi mari yayi yana faWin.."" Ka yi hauka ne? "" Ya fada cikin zafin rai. Shigowa Alhaji ELYakub yayi yana kallon Ubaid da yake aikinsa kamar babu mutane a dakin ya ce. "" Da fatan dai lafiya ko?"" Murmushi yayi ya ce mishi."" Alhamdulillahi Alhaji barka da safiya. "" "" Barka dai ya me ake tattarawa ne? "" "" Alhaji takardun tax din nan ne nake haWawa, domin CEO ya ce a shigar da kome kafin karshen shekarar nan, ""da kyau!"" Inji Alhaji ELYakub, yana murmushi, ""Mudansir ya ake ciki batun bayanin kenan?"" ""Ni da Abbas mun sakar musu da kuWinsu na 2019-2020."" Alhaji Mudansir ya fada yana kallon Ubaid yana son ta hango yadda zai dauki maganar, murmushi Ubaid din yayi ya ce mishi. ""Sir kudi ya fita ranar biyar ga watan Mayun 2019 daga office dinka, amma bai shiga asusun ofishin haraji na jaha ba, 2020 May 10 ya fita amma bai shiga ba, ga shaidar da office din haraji suka turo haka yana nufin suna bin na tsawon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login