Follow us on social media

Showing 30001 words to 33000 words out of 140751 words

Chapter 11 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

335

kama shi ya wurga min wayar na dauki abina ina me ninke hijab dina, ganin sa gaske naki kula shi. Sai ya daddume ni ya shiga ™o™arin kwace kuWin ni kuwa naki, gani zai zai cutar da ni na gantsara mishi cizo wanda ya saka shi kara tare da shake min wuya kamar zai kashe ni. Sai da ya ga na fara fita hayacina sannan ya sake ni. Dakyar nake sauke numfashi, sannan ya kwashe kudin ya watsa min dubu biyar yayi gaba abinsa. Hawaye ne ya zuba min in sha Allah na fita na fita kenan. Ina kwance a wurin har aka kira sallah Magariba kafin na lallaba shiga ban daki nayi tsarki na zo nayi alwala na shiga dakin nayi sallah ina zaune. A wurin har aka kira sallah isha na mike na gabatar tare da shafa'i da wutir, sannan na kwanta a wurin, idan na kyale ya Hafiz wata rana zai kashe ni. Kwarai na gano kiyayya a cikin"

idanunshi.

Dama tun can Ya Hafiz bai sona ne? Idan har haka ne tow meye amfanin zaman da shi. Haka na kwana

"washi gari na shirya zuwa gidan suna, sai da na biya gidan Maman Na'ilah na amshi jakar kudin nan, bayan na cire mata itama kudin da ban saj nawa bane, na juya na fita tana ta min godiya, daga nan gidan Aunty Hindatu na fara zuwa ita tana unguwar Federal locals ne, nan na fara zuwa, tana ganina ta fara tambayata. ""Auta lafiya?"" ""Lafiya kenan!"" Na shiga na zauna Mijinta Alhaji Mas'ud ya fito cikin shirin zuwa kasuwa. ""Matar roba kece a gidanmu!""gyada nayi, ""Kiyi hakuri har kika kwanta ban samu zuwa ba na tafi umara ne amma ita wannan matar karfen bata gaya min ba sai da na dawo!"" ""Na gode Angon bogi!"" Murmushi yayi ya ce min. ""Tow ayi min addu'a zan tafi kasuwa!"" ""Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya!"" Muka fada ya fita Aunty Hindatu ta bishi har waje sai da ya fita ta dawo tana kallon yadda nake a takure wuri guda. "" Lafiya Lu'lu'a!? "" Kaina a sunkuye na ce mata. "" Na shirya rabu da shi!"" Wani irin sujada tayi tare da ambaton Allah, ta rike hannuna. "" Da gaske! "" Hawaye na zuba min na ce mata. "" Eh! "" Na gyada kaina ina cizon bakina. Wato ban tab'a jin kwarin gwiwa ba irin na yau sai da ta kira conference call bakiWaya aka hadu ina jin su, tambaya daya suka yi min na shirya rabuwa da Hafiz Ali Umar Jama'are? Na ce musu eh ma shirya. Aunty Hindatu ta gaya musu na zo da kudi, da yadda za ayi da"

"kuWin. Murmushi Ya Ado yayi ya ce shi kenan. "" Baby girl get ready muna bayanki! """

"Haka muka gama muka tafi gidan sunan amma bamu tafi lokaci guda kowa da tafiyarsu, lokacin da"

"muka isa gidan kowacce daban daban ya shiga. Anan muka samu ana ta liyyafar, ina isowa Ya Tahir ya riko hannuna ya kai ni wurin abokansa abin mamaki har da Ya Hafiz a wurin wato don jaraba ya biyo ni, irin kallon da yake min na tuhuma da zargi yasa ni dauke kai, babyn aka kawo min Ya Tahir ya ce min. ""Ga takwara na miki!"" Kurawa yarinyar idanu nayi hawaye na zuba taruwa a idanuna, na d'ago kai ina kallonshi hawaye na zuba min, wannan na gudu wannan na koro wannan, kasa magana nayi ina kallonshi. ""Takwara na miki!"" A hankali nake shashekar kuka ina me rungume yarinayr har cikin raina nake jin kaunar yarinyar. Haka Yan uwana suka taru ana ta taya ni murna ban haihu ba amma yan uwana sun min kara domin duk abinda ya dace nayi sai gashi sun yi min kome har da kayan barkatu. Soyayyar da yan uwana suke min ya wuce tunanin mutum. Haka na tashi na tafi wurin uwar jaririyan nayi ta kuka, ita kan dariya tayi min. ""Lulu Allah ya sani nafi ki farin cikin saka sunan Yarinyar nan, kuma taki ce har abada!"" Haka nayi ta kuka a wurin kukan da na kasa yi shine nake yi ina yi ina kallon yarinyar, yadda nake kuka Aunty Hindatu ta ce a kyale ni, nayi kukan dama tun tuni ake son nayi ban yi ba, sai nayi har kaina ya fara ciwo, suka kai ni dakin Ya Tahir na kwanta, barci ya dauke ni mai karfi. Sai wurin karfe biyu na farka zan yi sallah na ga bakona, ita mai jegon ta bani sabon pant da ledar pad, na gyara jikina na fita wurin yan uwa da ake ta hidimar bikin sunan, Aunty Hindatu bata gayawa sauran dangi ba, iyamu yan daki daya da dakin Yadiko aka san da zancen. Wurin karfe shida nayi sallama na wuce gidan Aunty Hindatu. Itama can ta dawo, ta fito min da kaya kala uku domin gobe da sassafe zan wuce Kaduna wurin"

Ya Almu.

Hafiz

"Karfe takwas ya dawo, koda ya shigo ya g kofar dakin Lubnah a rufe tsaki yayi, yana tambayar Karimah."

"""Yarinyar nan bata dawo ba ne?"" ""Ba ka bani sandar kiwonta ba fa!"" ""Ikon Allah!"" Ya ce daga nan bai"

"kara magana ba, haka har zuwa karfe tara na dawo babu labarin Lubnah, bai damu ba yasan yadda zai ji"

da ita gobe.. don haka yake shirya yadda zai cika Baban Bauchi.

**

Washi gari.

"Asalin tashar Kaduna aka kai ni, wanda yake hanyar Jos, daga nan Aunty Hindatu bata bar wurin ba sai"

"da ta ga motar ya tashi, sannan ta dawo gida."

"Dama wayata na bari a wurinta, ta bani wani tsohon wayarta da layin duk tsoho ne, amma tana amfani"

da shi. Haka yasa na kwantar da hankalina don ko na tafi da wayar Ya Hafiz zai iya amfani da kiran na dawo.

"Karfe biyar biyu na rana na iso Kaduna, Ya Almu yazo ya dauke ni. ""Auta sannu da ™o™ari, sannu"

"Ubangiji yasa karshen wahalarki kenan!"" ""Amin Ya Allah!"" Na fada a hankali, muka wuce gidansu da yake base na Sojojin sama."

"Muna isa Matarshi Aunt Saliha,ta tarbe ni. Ina zata saka ni ina zata ajiye ni. Don farin ciki da jin dadi."

"Haka nayi ta jin kamar alfarma aka min. Nayi wanka aka bani abinci naci kaWan, sai kuma na fara jin kamar nayi wani kuskure. Wurin karfe uku Aunty Hindatu ta kira shi tana gaya mishi yadda Ya Hafiz ya rikice yana bin gida gida yana niman inda nake. Shiru nayi da Ya Almu yake gaya min yadda hankalin Ya Hafiz ya tashi ya rasa yadda zai cusa ranshi har Jama'are aka bincika ko ina can. Gashi yau aka yi wani hatsari a hanyar Jama'aren hankalinsa yayi mugun tashi. Sai jikina ya fara rawa na kasa zama ko na zauna zan tashi tsaye. Rike hannuna Aunty Saliha tayi tana faWin. ""Ki saka a ranki, zaki iya yaki da kanki idan kika koma kofar da zaki sake samu ki gudu ma ba zaki samu ba, ki nutsu ki gaya Allah kukanki, Hafiz ba shi bane karshen rayuwarki, kina da naki rayuwar ki sa ranki, zaki rayu!"" Kuka na saka mata har ina shashekar kuka. ""Zan koma kawai ya sake ni."" ""Yes muna tare dake, shi zai bukaci haka a yanzu kuwa kina komawa daga shi har su Abba ba zasu baki damar kare kanki ba, ina magana a matsayin daya daga cikin matan da suke ya™i da matan da suke da irin matsalolinki ne, kada soyayyar da kike ji yayi tasiri a ranki, kwarai zaki koma amma dole muna bu™atar nutsuwarki."" Dakyar ta shawo kaina nayi hakuri tare da rarrashina muka bar zancen Ya Hafiz ba a kara zancensa ba, kawai so suke nayi farin ciki. Kuma na yarda amma na kasa farin cikin. Yaron mai sunan Abba ana kiranshi Zunnur, ya dawo daga wurin Yayarta shi Waya Allah ya basu har yanzu dai basu kara sun wani ba koda yake yan boko ne Original masu"

hakoran Abcd.

Sai dare da na shimfida hakarkarina na kwanta sai wasu abubuwan suka yi ta dawo min.

***

*Mafari tushen kome*

2015- June/July

JIBWIS Bauchi state.

"Yau ake bikin Yaye mu, kasancewar mun gama Jss3, zamu faWa aji hudu na Senior secondry School. Wani"

abu guda uku yake tattare da wannan ranar yanayi uku yanayin da ba zan iya mantawa da shi ba.

"Sunana Lubabatu Usman Umar Jama'are, wacce ake kira Lubnah Shehu Usman Jama'are, Abbanmu"

"haifaffen garin Jama'are ne na jahar Bauchi. Iyayena bakiWayansu yan Jama'are ne, a unguwar kofar Fada. Gidansu Abba yana da tarihi domin suna cikin Kingmaker idan za ayi nadin sarauta a fada. Yan uwa da sauran dangi suna can."

Abba wanda shine da na biyu a cikin gidansu Alhaji Umar Madaki yana cikin amintattun sarki kuma

"wanda ake damawa dasu a fadar, wato Kakanmu wanda muke kira da Baba Malam. Abba da Mama auren zumunta ne aka musu har zuwa yau Mama bata taSa yaji ko wani abu ba, haka Yadiko wacce itama bata taSa yaji ba itama yar kanwar Hajiyarsu Abba ne, Abba yayi karatun boko tun daga barewa College zuwa ABU zaria, akan ce kowani mutum da inda bakin rabonsa yake shi Abba ya karanci hada makamashi ne, amma yana gama bautar ™asa ya kama kasuwanci, dama tun yana aji uku aka mishi aure da Mama, tana shiga ta haife Ya Ado, bata rufe shekara ba ta haifi Aunty Hindatu, sannan ta haifi Ya Umar, shima shekararsa daya da rabi ta haifi Aunty Innah, sai a lokacin Abba ya auro Yadiko sanin cewa dukkansu yan uwan juna ne sai suka zubar da kishi suka rungumi juna, itama Yadiko ta haifi Ya Tahir, bai"

cika shekara ba aka. haifi Aunty Munah wato aunty Maimunatu.

"A lokacin Baba Ali yana tare da Matarshi Hajiya Asiya yar garin Gyembu, wacce suka haihu tare da"

"Yadiko tana goyon Ya Hafiz, kwatsam Abba ya tattara iyalinsa ya dawo Bauchi saboda ya samu aiki kuma ga kasuwanci, sai abin ya zo mishi da sauki ga aiki ga kasuwanci, Hajiya ganin yadda Abba yake ta gaba, abin ya d'aga mata hankali domin Baba Ali malamin secondry School ne, sai ta rena mishi tana ganin kamar gazawarsa ce ta haifar masa rashin arzikin har dan uwansa ya fishi, Bayan Baba Ali akwai Goggo Larai da Goggo Uwani, sai goggo talatuwa, su biyu maza sai Babarsu Goggo Alti. Abba wanda ake kiranshi Baban Bauchi bai taba zama ya manta yan uwansa ba, domin ko zuwan shi aikin hajji tare da"

"Baba Malam da Goggo Alti suka je, lokacin duniya na kwance........"

*Wannan book din paid na kudi*

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500*

"*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105"

ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita*

Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

SHA BIYU

"Shekara na dawowa ya biyawa Baban Jama'are, da Goggo Uwani da Goggo Takatuwa, suka tafi a lokacin"

"ta Kano ake tafiya haka yasa a can suka tashi. Ko a Bauchi unguwar da Abba ya fara zama a ibrahim bako, haka ya zauna a lokacin yana aiki a ma'aikatan albarkatun kasa, sai da suka shafe shekaru goma sha biyar, lokacin an haifi Ya Almu da Ya Abba su kan tagwaye ne, Yadiko ta haife su Ya Almus shine Babba, Sai Aunty Raliyah tana aure a Jos, sai kuma Ya sani,da dan lokaci ya ja sannan aka haife ni, na samu gata a wurin Yayuna. Dakinmu bakiWaya mu Biyar ne, Ya Ado, Aunty Hindatu Ya Umaru, Aunty Innah nice na biyar, dakin Yadiko kuwa akwia, Ya Tahir, Aunty Munah, Ya Almu da Abba, sai aunty Raliyah da Sani,"

bakiWaya gidanmu Allah ya albarkaci iyayenmu da mu biyar ne.

"Haka muka taso cikin wani irin so da gata, ni dai ban san sanadin da Ya Hafiz ya dawo gidanmu ba,"

"amma ma taso na ganshi a cikin gidanmu, kuma abin al'ajabi a dakinku, wato Ya Hafiz kyakkyawa ne tun ina Yarinyar na yi crushing dinsa, kuma bana kaunar na ga wata ta kula shi, Ya Hafiz bai da yawan magana, duk da lokacin da na fara wayo yayuna mata Aunty Raliya ce bata yi aure ba, domin duk yaran"

gidanmu suna fara jami'a a gida ne su karasa a gidan mazajensu.

"Haka yasa ita Aunty Raliya ba a Bauchi take karatu ba, a BUK ta karanci karatun jarida. Tana cikin"

"karatun ta hadu da Alhaji Bilya suka yi aure, ni sai bana ce ba amma a wannan lokacin muka fara"

"shakuwa dabYa Hafiz, domin kuwa an hanani zuwa bikin nayi ta rigima har na hakura. Idan na ce muku"

"mun shaku tow ina nufin mun yi wani irin shakuwa da duk wanda ya ga yadda muke sai ya ji sha'awarmu, da farko Yayuna maza suna zuwa shagunan Abba, amma daga baya suka shiga barin shagunan daya bayan Waya. Na farko yar rigima ake tsakaninsu a shagon daga baya sai su bar zuwa shagon kuma dama kowannensu yana da abin yi, Ya Ado dama lauya ne, tuni ya samu aiki a Abuja ya koma abinsa sannan ya"

haWa da kasuwanci domin abin ya same musu jiki.

"Ya Umar shima yana aiki da ma'aikatan shige da fice a nan Bauchi, kuma yana da wani shago da suke"

"shigo da mashina, sai Ya Tahir, malamin makaranta ne Tatari Ali Polytehnin, yana sana'ar fitar da tsabar abinci. Ya Almu da Ya Abba, shi Almu sojan sama ne yana garin Kaduna, sai ya Abba da yake sojan kasa yana Maiduguri. Ya Sani dai ya gama karatu yana da shagon da yake kula da su na sayar da generator, Yayuna mata kuwa Aunty Hindatu tana aiki a babban Kotun majastir na nan Bauchi ita ce magatakarda."

"Sai Aunty Innah tana aiki a babban asibitin Bauchi babban nurse. Domin degree biyu gare ta, MBS."

"Duk yan gidanmu babu cimma zaune, kowa akan kafarshi yake Abba ya ji haushina yadda duk Yayuna"

"suka ki zama a tare da shi, don haka ya kama Ya Hafiz ya daura shi akan kasuwancinsa, ban ce muna da kudi ba, amma muna da wani irin rufin asiri da duk wanda ya ganmu tow ya san mun fi karfin a wulakanta mu, wannan lokacin ni daya ce mace sai yar rikon gidanmu Jalilah yar gidan Goggo talatuwa,"

Babanta Yayan Yadiko ne.

"Abban ya Hafiz wato baban Jama'are ya hadu da hatsari wanda yayi sanadin da ya rasa ™afarsa daya,"

"haka yasa ya daina aiki Abba ya bude masa shago aka zuba kayan kudi, Hajiya Asiyah idan mace muku matar nan ayin kyau domin kaf yan gidan wato iyayenmu babu wacce ta kamo ta kyau, bafilatana ne amma irin masu burin nan. Duk da yan Gyembu ne sai dai mazauna Jama'are ne, yadda yayi burin Baban Jama'are ya kasance abin bai zo mata yadda yake ba, amma tayi making wasu abubuwan wanda daga cikinsu wofatar da Ya Hafiz, wanda haka yasa Abba ya dauke shi, Ya Hafiz ko nace yan gidansu basu son karatu, both mazan da matan. Da yake Allah yana yankarsu da tsada dakyar yan matan suka gama"

"secondry School, su kuma mazan dama watsarwa suke su kama abinda zasu iya."

"Shagon da Abba ya budewa Baban Jama'are kuwa, Yaran da Uwar ne suka ruguza kome, Abba ya kara"

"cika shagon suka sake lalatawa, ganin za ayi na uku Baban Jama'are ya ce a barshi haka shi dai zai koma noma, haka da yayi ya b'atawa Hajiya Asiya rai, Baban Jama'are mutumin kirki ne, haka yasa koda ya koma noman rani da damina, idan. Amfani yayi haka zai cika ya kawowa dan uwansa, shi kuma Abba sai ya mishi hanya yana cire amfanin gona ya haWa shi da masu saya har da saya mishi motar da zata na"

"wannan jigilar da shi, da yake yana da kafar roba da yake amfani da shi, Allah ya dafa masa kuma ya"

"tsaya da kafarshi amma a haka Hajiya Asiya gani take bai kai Abba ba, shi kuma haka bai dame shi ba."

Domin mutum ne mai yarda da Allah.

"Ya Hafiz shine Babba, Aunty Nana Asma'u ita ce take binsa Sai Ahmad Tijjani, yake bin Aunty Nana, sai"

"Babangida, yake bin Tijjani, sai Yahanasu, kafin Firdausi. Ita Aunty Nana tana auren wani dan siyasa a can azare, sai Yahanasu itama wani dan abokin Abba take aure suna River State, sai Firdausi da take tsalle tsalle taki zaman auren domin Allah ya mata ruwan kyau."

"Ya Hafiz yadda bai samu soyayyar mahaifiyarsa ba domin kuwa bata janyo shi a jiki ba, sai da ya zama"

"mutum, nan ta fara nunawa ita fa danta ne, babu wanda ya damu shima a lokacin bai da uwa sama da Mama da Yadiko, domin yana da gaskiya da rikon amana, duk inda Abba yake shiga Ya Hafiz ya sani duk inda Abba yake niman kudi Ya Hafiz ya sani. Kome na Abba ya sani kuma haka yasa shi kara samun yarda har da na dangi domin idan ba Abba bane ya ce yayi wani abu ba zai tab'a yi ba. Shima Abba yana ganin"

"kamar dan uwansa ne a tare da shi, domin kaf halin Baban Jama'are Ya Hafiz ya kwashe bai bar kome ba."

*

"Haka na taso da wani mahaukaciyar kaunar Ya Hafiz da fari ni doguwa ce, sannan a yanayin yan gidanmu"

"bamu da irin jikin nan da zaka ga mutum kato, a'a muna da yanayi jikin fulanin Jama'are, sannan"

"gidanmu yanayin kowa daban, yanayin dakin Mama mu fatarmu tana da dan duhu, yayinda dakin Yadiko Fatarsu take da haske, haka yasa idan ka gan mu zaka yi ta mamakin yanayinmu."

Wannan shine labarin dangina da gidanmu.

2015-

June/July.

"A karo na uku na lashe musabakar Alqur'ani, na fara shiga tun ina jss 1, sannan wancan satin mun Quiz"

"and prize, na kasa a garin Abuja wanda na wakilci makarantarmu, tare da rakiyar Yayuna. Allah ya zuba min rawan kai surutu uwa Uba tsokana da son ayi da ni, gashi yau mun yi bye bye da Jss3."

"A lokacin ina fama da tashen balaga, wayyo kusan kwaila da rawan kai, haka muka shiga makaranta"

"mu hudu team dinmu, nice a gabansu na juya ina kallonsu ina musu bayanin yadda Abuja yake, sai ji nayi kamar nayi kawo da mutum. Na tafi kamar xan fadi, na ji an tare ni. Da yanayin wata gaurayayyen hausa"

"mai mix da fulatancin da ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login