Follow us on social media

Showing 99001 words to 102000 words out of 140751 words

Chapter 34 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

310

yi dogon hira tana ce mishi Labubu shi kenan, zata iya catch attention dinsa da duk wani abu da take so tana kiran Labubu, akwai ranar da ta ce mishi me yasa yake son under age, ai karya hakki ne da cutarwa, ya ce mata. ""Granny me yasa Yaranku suke bin maza duk wanda yace yana sonsu zasu bashi kansu, me yasa?"" Sai ta yi shiru. ""Da zinar wuri gara auren wuri! Gara a mata auren da wannan"

"shekarun ta kara samun tarbiyyar Mijinta sama da ta samu tarbiyyar mazan waje."""

"""Kai dai akan Labubu baka ji baka gani!"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Luna ita din wata yanki ce ta"

"rayuwata amma wani ya tafi da ita!"""

........... Wash

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 41"

............. Washi gari.

"Kusan rayuwar Turaki a gida yake yinta, domin tunda ya bar aiki da babban Cibiyar nukiliya ta"

"Germany, ya koma zaman gida ba wai bai da abin yi ba ne, asalima abinda ya tara na wancan aikin bai yin kome da ita, amma yana da wata shago da yake sayar da coffee tun kafin ya dawo rasha da zama, domin a love story din Iyayensa a coffee shop suka hadu haka yasa ya tashi da son bude shagon, idan har zaka ganshi a shagon to kuwa abu me muhimmanci yake kawo shi shagon, sannan shagon yana dauke da baki bakaken fata, wanda ya dauke su aiki, shagon coffee din yana rage mishi abubuwa dayawa, musamman idan ya tuna da yadda ya rasa abinda yake so kawai saboda yanayinsa, a gefen shagon akwai gym da ake yi duk na shi ne. A halin yanzu yana da shaguna manya sosai a cikin Moscow, sai dai idan ka kalle shi zaka iya hango murmushi a kan fuskarsa amma a cikin ransa ba murmushi ba ne, kawai yanayinsa ne haka, duk da kasancewa shi haf Nigeria, yana da wata dabi'a duk inda dan Nigeria yake ya kuma samu wata matsala kafin ka ga wani a wurin turaki ya riga kowa zuwa wurin, ya dibi dalibai maza da mata both Muslim da Christian, domin kuwa abinda ya yarda da shi duk wanda ya zo nan daga gidansu yake ba daga ko ina ba, ya yarda Duk wani dan Nigeria danginsa ne. Sai dai wani lokaci da aka yi wani case na damfara da fashi wani Imyamuri a lokacin ya cire inyamurai a cikin mutanen da yake tallafa wa domin gayen yaso cilla shi cikin matsala, amma bincike irin na kasar suka samu bai da alaka da Yaron. Rayuwarshi babu girman kai, sai dai akwai abinda yayi imani da shi, tsoron mutum duk yadda yake da mutane yana tsoron sharrinsu, sannan idan ka ganshi da matasa tow labarin cigaba ne. A yanzu haka a mutanen da ya diba a nan rasha yan Nigeria ne da zasu yi aiki da shi kuma ya gaya musu gaskiya da albashin da zai basu, dayawa sun yarda domin ita kanta kasar babu wani ma'aikatan gwamnati da basu kuka da ita, gara su yi aiki da kamfaninsa. Rayuwarshi a matsayinsa na wanda ya taso cikin maraici ya saka abubuwa a ransa, ya kuma hakura da abubuwa dayawa don idan ya ce kudi ne ko karfi zai nuna soyayyar da yake kulafuci ba zai samu ba. Shi yasa ya yarda da abinda zuciyarshi take gaya mishi duk abinda ya nima Allah yana bashi sai dai ita da ya nima tace bata bu™atarshi me ya kawo ta kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY? Wannan shine tambayar da suke ta birkita mishi lissafi tun da ya ga sunanta kuma ya kasa yin wani abin arziki, idan kana son mutum kome na rayuwarshi sakawa kake a duniyarka, me yasa ya kasa daina sonta? Me yasa ya kasa ganin laifinta? Saboda ta fito fili ta gaya masa abinda yake ranta da abinda ya ta yanke a ranta. Gaskiyarta da kwarin gwiwarta a lokacin ya hango, ba zai ce ko ta tab'a kallonshi a tsanake amma kuma yaji a ransa tunda ta iya siffanta shi da almajirai ta kalle shi koda kuwa sau daya ne, a hankali ya bude idanunsa da suka yi wani luhu-luhu, ya kafa akan agogon parlourn, karfe uku saura na dare tashi yayi ya nufi dakinsa, koda ya shiga sallah Nafilla yayi sannan ya zauna ya cigaba da addu'a yayi addu'ar idan har Alkhairi ne ya kawo ta kamfanin Allah ya tabbatar idan kuma wani abu ne ya kawo ta Allah ya sa ta bar kamfanin da kafarta ba tare da wani abu ya cutar da ita ba, har kusan asuba, sai da yayi Sallah asuba sannan ya kwanta. Barci ne me nauyi ya dauke shi, amma duk da haka cikin barcin mafarkinta ne wanda tun na wancan fuskar yarinta. Yadda ya ganta ya sa shi farkawa dole ya shiga ban daki yayi wanka, ya kuma fito ya haWa coffee da kanshi, yau kan ma an tashi da niki-nikin sanyi domin ta ko ina ™an™ara ne ke sauka. Bai da yawan cin abinci kasancewar nasu na turawa amma a Nigeria yana son abincin Daddah. Dakin ya shiga ya ji gunjin wayarshi tana niman taimako a dauke ta, jan kujeran da yake aiki yayi ya zauna har wayar ta yanke a karo na biyu, yana kallonta ta kara yankewa a karo na uku ne ya Wauka. ""Hmm!"" ""Amma kana Ina nayi ta kira baka dauka"

"ba?"" Kurban tea din yayi ya ce mishi. ""Ina kallon wayar!"" Shiru Uncle Auta yayi kafin ya danna mishi"

"Ash'aria, murmushi yayi kafin ya ce mishi. ""Me kake yi da cv din har yau baka turo an ga wadanda suka yi"

"qualified ba?"""

"Shiru yayi kamar bai da ta cewa har Uncle Auta ya kara fusata. ""Dan iska mai zubin yan daudu ina"

"magana kana min yanga."" ""Da kaina zan musu interviews!"" ""Da gaske? Zaka zo kenan?"" ""Ina tunanin haka."" ""Baffa ya sani ne?"" Shiru yayi yana kallon coffee din ya ce mishi. ""No zasu ta jirana, i don't like su ta jirana."" Murmushi Uncle Auta yayi yana faWin. ""Akwai abinda zai dawo da kai ne?"" Shiru yayi yana zoben azurfan hannunsa ya sake wata karamar murmushi ya ce mishi. ""Uncle akwai abinda kake gudun na gani ne idan na zo?"" ""Kai tafi can uban me zan boye maka!"" Anan ya shiga bashi labarin yadda suka yi fa Granny, sannan ya sake murmushi yana kallon dakin yana son dakin, ya ajiye dakin nan a matsayin dakin da zai fara honeymoon idan har Allah ya bashi damar yin aure. Can ya ce . ""Uncle Auta, a mutanen da ka diba aiki har da, manta kawai."" Shiru Uncle Auta yayi kafin ya ce mishi. "" Kana nufin akwai wani abu ne?"" Daha kasar zuciyarshi ya furta wata kalma da ya kusan saka shi jin kunya. ""Uncle idan na dawo na hadu da ita fa?"" Sai kuma ya ce . "" Ba haka nake nufi ba!"" "" Har yanzu baka hakura da Lubabatu ne? Anya ba aljana ba ce kuwa ka hadu da ita?"" Tsaki yayi ya share zancen ya ce mishi."" Batun ghost worker's?"" ""Ba shi nake magana na Turaki magana nake akan har yanzu!"" Kashe wayar yayi, sake kiranshi Uncle Auta yayi yaki Wauka, y kira yafi sau goma amma bai dauka ba, bayan wani lokaci Datti ya kira dauka yayi ya saka a kunnensa. ""Mujitafa ya ce zaka zo haka ne?"" Shiru yayi ya fara kame-kame, ""wato"" ""ban sanka da magana biyu ba, kuma ya ce kai zaka yiwa sabin ma'aikata interviews tabbas muna"

"bukatar kazo don Allah, kazo don Allah muna bu™atarka!"" Wani irin shiru yayi yana sauke numfashi."

***

"Daga Bauchi aka yi ta kiran Ya Ado, da cewa ai su Baban Jama'are da Baba Malam sun zo lagos, amma ba"

"a kuma jin labarinsu ba, wannan abin bai yiwa kowa dad'i ba. A wurina cewa nayi Allah yasa su fada hannun yan yankan kai, domin idan sun zo babu alkhairi a zuwan nasu, haka akayi ya bin office din Yan sanda ana niman, dama kuma akwai wata hukumar da gwamnatin lagos ta ware na musamman idan aka kama mabarata ana tara su sannan a saka su a babbar mota ya kawo su arewa, Goggo Alti ce ta d'agawa Rufa'i da Ya ado hankali akan Babansu mara mutuncin tsoho, ni ko a jikina. Haka ayi ta nimansu har inda ake tara mabarata a can aka same su sun sha uban azaba ba uwar azaba ba. Haka aka kai Baba Malam asibiti shima saboda muran da ta kama shi, Baban Jama'are kan da sauki sai kin yar kunyar da take damunsa ya kasa sake jiki da kowa, gidan wani abokin Ya Ado can ya kai su da yake akwai BQ, anan suka zauna don kwanan Baba Malam daya aka sallame shi. Haka suka daurawa kowa dawainiyya da jigila, idan suka zo asibiti dakyar suke komawa masaukina. Yadiko kuwa ta wanke Baban Jama'are da cewa.. ""Ba fa dole aka ce sai kun zo ba, fisabiilillahi kun zo kuna daurawa mutane dawainiyya, yaji da na iyalinsa"

"ko yaji da na mahaifinsa, wannan ba yi bane"""

Tunda tayi magana sai suka dauke kafa da zuwa asibiti irin sun yi zuciyar nan. Ranar wata juma'a

"muka tawo gaida Abba, da sauki ma dai ya amsa min sama-sama, sai dai wani abu da ya dake ni zuwan Doctor Ahmad da kayan dubayya, yadda yake ta kallona da jana da hira, amma naki sakewa da shi, duk abinda yake faruwa a kan idanun Abba, da yake mun zo bayan an sauko juma'a shima Ahmad ya shigo, wurin karfe hudu sai gasu Baban Jama'are, ko basu gane ni bane, da suka shigo suka gaida Baba da jiki nida su Adil muka gaishe su, sai sake Baba Malam yayi yana faWin."" Wannan ba luba ba ce?"" "" Ita ce Baba wani abu ne?"" "" Ita ce dai da gaske?"" Ganin yadda suke ta mamakin ganina sai Yadiko ta ce min. "" Zo ki kai wannan abin waje ki zubar ki ta addu'a ido guba ne."" Haka na fita jiki a mace. Rufa'i da Ya Ado suka shigo lokacin na fita kenan muka hadu a hanya. "" Ya ka mai damu gida!"" ""Ok! "" Yana shiga ya ga su Baban Jama'are, nan ya sha jinin jikinsa. Haka na zubar tare da dawowa dakin. "" Akan me zata koma? Ita tace muku zata ko?"" Inji Yadiko,Gabana ne ya fadi lokacin da na shiga ina jin maganar da take a hasale. ""Yadiko ai Abba ya sallama min Lubnah kaf duniya babu me iko da ita sama da ni, idan shi Hafiz din jahili ne ai ni ba jahili ba ne, aure fa babu shi ko ina zasu sai su je, ke muje gida ga wannan idan ya muku zaku iya tafiya idan kun ga bai muku ba, ku cigaba da xama amma ba gidan Abokina ba domin ina jin kunyar"

"shi."""

"Fashewa da kuka Baba Malam yayi yana fadawa Abba ai yana gani amma ya kasa magana. ""Yadiko ki"

"taya yarki da addu'a nan fa sati biyu zasu tafi jarabawa, zata fara aiki."" addu'a sosai tayi sannan muka bar Asibitin, ashe basu tafi ba kuma Rufa'i yayi musu bayani da inda zasu je su hau motar Yola amma suka ki, karshe a masallacin asibitin suka kwana. Duk yadda suka so ganina don su kunna min wuta Allah ya taimakawa Ya Ado ya hanani kara zuwa asibitin wannan abin ya dame su, suka yi ta kunnawa Abba magana da tashin hankalin da sai da jininsa ya sauka har ya fara alamar zai suma, aka kore su. Wannan"

abin ba wai iya su kaWai ya shafa ba domin Baba Malam ya kira mutanen Jama'are ya gaya musu.

"Kusan tun da muka rabu da Ya Hafiz ban kara jin shi ba, ina zaune yau Lahadi, aka kira ni dauka nayi, na"

"saka a kunnena.. ""Kina nufin don kin zo lagos kin kin sabe wannan tsutsar jikin naki, zai saka na manta da cewa ke Matata ce? Ki ji da kyau ke Matata ce ni Hafiz Umar Jama'are ban sake ki ba, ki gama haukarki ina nan ina jiranki. "" Ji nayi kai na ya sara, na kasa amsa mishi wani tsawa ya daka min sai da naji kamar guduma ya buga ya kara buga min tsada idanuna jajur ga wani tsoron da ya cika min rai na ce mishi. ""Meye nayi maka ne?"" Aikuwa ya shiga zagina da cin mutuncina da zarafina yana gaya min matu™ar ban je na ga Baban Jama'are ba sai ya bani mamaki ya kara da cewa.. ""Zan miki abinda kaf duniya babu wanda zai yarda ni nayi miki, nafi ki sanin Lagos idan ban saka an dauko min ke nayi yadda nake so da ke"

ba shege nake.....

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 42"

*Traumatic yana da alaka da abinda ya samu mutum na tsawon lokaci ko kuma na tun daga Yarantar

"mutum ba wai ina son nunawa mutane cewa Lubnah bata da yadda zata yi ba ne, akan Hafiz Lubnah"

"bata da karfin da zata iya karban kanta ba wai ta gaza ba ne, ko yaro ne aka fuskaci domestic violence"

"haka zai taso a kangare na taSa jin wani karatun malamin addinin Muslunci da Yaron ya turawa malamin cewa saboda abinda Babansu yake yiwa Uwarsa yake jin kamar ya kashe shi. Na ga a wani blog na Garkuwar Arewa da wata yarinyar ta turo cewa saboda wannan domestic violence ta kasa bawa duk wani d'a namiji, ba ita aka yiwa ba mahaifiyarta Ubanta yake cutarwa amma tana ganin idan ta hadu da namiji irin Ubanta ne! I don't mean to push Lubnah amma akwai irin masu halin da take ciki! Please be"

patient with the story Nagode sosai*

"Mikewa nayi na ji kamar cikina ya tsarga. Ya cigaba da gaya min duk maganar da ta fito bakinsa, ji nayi"

"kamar ana kunce min duk wani abu da yake kaina ya ce min, ""kina son Iyayenki kuwa? Shi kenan sai ki tuna kamar yadda rayuwarmu take baya yadda kowa yayi shiru akanki yanzu ma bata sauya ba, ki gane mana ina sonki, i a son ganin kukanki na ga kina kuka yana min dad'i sannan idan kika sake wani ya min magana akanki hmmmm abinda zai fi haka muni, don haka ki zuba idanun zuwa na sannan ki gayawa Adamu ya kula min da mahaifina."" Wurgi nayi da wayar na koma can kuryar dakin na zauna Kamar marainiya, ko kara wayar tayi sai na zabura, wani irin tsoro ya kama ni. Haka na wuni a dakin har dare ban fita ba, sallah ne kaWai nayi dakyar, ba sai ga zazzaSi ya rufe ni ba, kwanciya nayi a dakin har Ya Ado da Aunty Zakiyah suka zo duba ni ban gaya musu ba. Wayata da take can a yashe Aunty Zakiyah ta dauka tana kallon Ya Ado, duba wayar tayi tana faWin.. ""Lafiya wayarki a can!"" Da sauri na amshi wayar na kashe, na koma na kwanta. Kusan haka suka gama maganarsu suka fita, kwana biyu wayata a kashe idan Mama ko Aunty Hindatu zata yi magana da ni sai dai a wayar Ya Ado ko Aunty Zakiyah, nan Mama ta sha jinin jikinta, ta cewa Ya Ado ya amshi wayata ya bincika, itama zata taya ni da addu'a, Ya Ado ya amshi wayata ya kuma saka ni a gaba da fada har sai da Aunty Zakiyah ta ce ya kyale ni ya daina min faWa, kafin na samu ya hakura washi gari sai gashi yazo yana rarrashina, sannan ban san me yayi ba. Sai ya ce min. ""Daya layin na turawa su Mama wannan Mtn din ba a iya kiranki ba sai dai idan kece zaki kira, sannan wannan ko Rufa'i ban yarda ki bashi ba, idan Hafiz ya kira ki, ki gaya min ki bude baki ki gaya min."" A Bauchi kuwa Mama sai da ta saka aka rufe shagunan da Ya Hafiz yake, duk yadda aka kai da bata hakuri fir taki, shi kuwa kamar zai yi hauka. Da ta gaya mishi zata iya kome akan Lubabatu bai yarda ba, sai da ta saka aka dauke shi a kai aka kai shi office din Yan sanda aka rubuta yarjejeniyar ya fita a harkata tunda abin ya koma yar haka, bata kyale shi ba sai da ta ce ua kyale su Sani su kula da shagon Abba, domin ba ™aramin mamaki suka sha ba jin yadda kusan tun kafin a kwantar da Abba ba a kuma zuwa sari ba, kayan da yake store ya kare tass, ina kudin? Sai shiru karshe da aka kira shi ya zo, ai kuwa ya gudu aka nemi shi sama da kasa babu shi, babu labarinsa. Abin bai yiwa kowa dad'i ba, sannan kudaden da Abban yake da su ba zasu kai ayi sabon sari ba, haka yasa dole aka fara hada abinda ya sawwaka, aka gayawa Mama tace musu. ""Ina ruwana yana da gidaje da filaye ku sayar ai bance ya dauko na shi ya cuce shi ba, balle"

"ace a tare zamu raba zunubi ba."" Fir Mama taki ta kuma gayawa Yadiko."

***

Turaki.

"Duk yadda yaso kaucewa dawowa haka yayi ta ji zuciyarsa na fisgarshi, duk da yana ™aryata kanshi da"

"cewa zai dawo ne ba wai don ya ganta ba, asalima don kada a samu matsala zai saka a tura ta tsohon kamfani. Amma kuma da wata bangare na zuciyarshi ya tuna mishi cewa akwai Khamis akan mata ko taure ya sallama mishi, sai ya ji ranshi ya Saci, yanzu idan yayi wani abu za iya d'agota, duk da file dinta ya shigo ta email address kamfanin ne, ba ta hannun Uncle Auta ba, duk yadda yaso ya kaucewa haka amma zuciyarsa ™ara tunzura shi take, sai dai duk yadda ta tunzura shi idan ya tuna tana da aure sai jikinshi ya kara sanyi, wani hanzari ba gudu ba, idan kuma mijinta ya mara hanyar samun aikin fa? ""Tsuk!"" Ya sake wata guntuwar tsaki yana kallon waje, ta parlourn.. ""Bilyl"" kallon Granny yayi tasha rigan sanyi. Murmushi yana kad'a kafarshi. ""Bilyl ko baka da lafiya ne?"" Kallonta yayi irin kallon mamakin nan, zama tayi tana kara bude mishi kalmar rashin lafiya da take nufi. ""Ina nufin ko baka da karfin maza ne!"" Bai cika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login