Follow us on social media

Showing 6001 words to 9000 words out of 140751 words

Chapter 3 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

291

zuciya a kusa.

"Daga wannan ranar ban kara samun matsala da shi ba, ranar bayan kwana biyu na kira Aunty Hindatu"

"na gaishe ta dakyar take amsa min. ""Aunty Hindu!"" ""Kada ki kira ni haka, ki je can ki cigaba da abinda kike yi!"""

"""Ki yi hakuri ba zan kara ba!"" Na fada kamar xan yi kuka. ""Ya isa haka, meke damunki?"" ""Ba kome"

"kawai na kira na gaishe ki ne!"" ""Allah sarki auta ta fara hankali. Ko kina son kudi ne?"" ""Akwai sauran dubu tara ba sai kin turo min ba!"" ""A cikin dubu darin ne ya rage saura tara?"" Shiru nayi ina tuna katobarar da nayi. ""Nayi amfani da shi ne!"" ""Allah ya kyauta, Baban Bauchi ma ya kusan rabon Zakka ai ina ga yana bamu bana umara zamu tafi har dake ko?"" ""Allah ya amince!"" Na fada a hankali domin nasan matukar Ya Hafiz yasan da batun kuma Matarshi ba zata ba, ba zai tab'a barina na leka ko da kofar gida"

ne.

"""Ya kika yi shiru?"""

"""Ba kome kawai ina nazarin yadda zan ga dakin Ka'aba!"""

"Murmushi tayi tana faWin. ""Kin yi waya da Mama ne?"" ""A'a ban yi ba!"" ""Bata jin dadi fa, tana fama da"

"mura."" ""Wayyo Allah Ubangiji ya bata lafiya! Me xan mata Aunty Hindu!"" ""Ki mata farfesu da kayan kamshi!"" Murmushi nayi na ce mata. ""Aunty Hindu ya nusaiba?!"" Dariya tayi tana faWin. ""Tana lafiya ai ta kusan zuwa gida haihuwa!"""

"""Allah ya kawo ta!"" Nusaiba yar aunty Hindu ce da aka yi aurenta, kuma yar dakina ce. Daga haka muka"

"yi sallama, mikewa nayi na nufi kitchen na bude frij na duba nama, zabuwa ce guda biyu ta rage min, ajiyar zuciya na sauke idan na je gidan zan so ganawa da Baban Bauchi. Ko don a tura Mubarak gidan gona kawo min kaji. Murmushi nayi, fitowa nayi na zauna a parlourn. Shigowa Yusrah tayi tana faWin.."

"""Lulu zanci abinci!"" Tashi nayi na nufi kitchen na zuba mata alale da nayi, sannan na fito na ajiye mata, ta"

fara ci ina kallon tv.

"Ni dai shirun Ya Hafiz nasan bata lafiya ba, idan kuwa ta lafiya ce tow zaka samu akwai shirin da yake"

"yi, don haka ina zaune ya shigo da sallama. Kallonshi nayi ina amsa mishi. ""Barka da dawowa, ya kasuwar?"" ""Alhamdulillahi!"" Ya zauna a dame, dakinshi na wuce na ajiye mishi jakarshi, sannan na dawo na hada mishi abinci, koda na kawo na ajiye mishi, kallona yayi ya ce min. ""Luluna ina cikin tashin hankali!"" ""Lafiya?"" Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce min.. ""bari na duba Karima na zo!"" Haka ya tashi tare da Yusrah sun jima kafin suka dawo tare da Matarshi, a lokacin da suka dawo abun ya bani mamaki"

domin dukkansu kuka suke sharshar.

"""Hafiz lafiya?"""

"Girgiza kai yayi yana faWin. ""Lulu ki rufa ki min asiri, Lulu."" Sai hawaye, bakiWaya sai jikina yayi azabar"

"sanyi bani manta lokacin aurensa da Karima haka ce ta faru yazo yana kuka da tashin hankali, ya Hafiz idan yana cikin tashin hankali bai da nutsuwa, ban san me ya faru ba, amma duk abinda zai girgiza shi yayi kuka nafi shi gudun abun. BakiWaya sai na shiga tashin hankali, yadda yazo ya zauna tare da daura kanshi a kan cinyata, sai jikina ya Wauki rawa, tambayar duniyar nan nayi mishi amma bai ce min cikanki ba sai ce min yake na rufa mishi asiri. ""Na rufa maka asiri me ta faru?"" Kuka Karima ta saka ni ma sai na fashe da kuka, aka rasa me rarrashin wani, har wurin karfe shida sai ga Hajiya, Mahaifiyarshi da kaninsa Tijjani suka zo, nasan a wurina zata sauka duk da bani da wani daraja a wurinta amma nasan wurina ne, shi kuma Tijjani zai sauka a BQ tunda akwai dakuna biyu a bayan. Yadda Hajiya ta ganshi yana kuka yasa ta shiga tashin hankali, nan na kara yarda da cewa ita uwa akan danta ba ruwanta ba abinda ba zata aikata ba. Tana shigowa matar nan ta zube akan gwiwarta, Tirkashi duk abinda zai saka Hajiya Asiya wacce Yaranta suke kiranta da Hajiya, ta saukar da kanta ta roke ka, tow wallahi ba karamin al'amari ba ne, domin nasan Hajiya mace ce mai d'agawa da izza, mace ce mai matukar ji da kanta sannan tana da wani irin girman kai wanda nake da yakinin Ya Hafiz a wurinta ya gada, rike kafana tayi tana faWin. ""Yar nan ki amince ki rufa masa asiri don Allah ki rufa masa asiri wallahi kaf duniya bayan ke babu wanda zai iya rufa masa asiri!"" Duk sai na rude, tun fil azal haka Allah ya halicce ni da saurin rudewa, ko fada ya Hafiz yake take nake shiga tashin hankali, shi yasa bana son abin da zai kawo tashin hankali a tsakaninmu, bakiWaya na shiga tsoro na ce mata. ""Hajiya don Allah tashi ki zauna a sama ni zan sauka! "" Girgiza kai"

"tayi tana kuka. "" Yar nan Hafizu yana cikin tashin hankali kece kawai zaki fitar da shi. "" Wani abu ne me nauyi ya danne min zuciyata, na zuba musu idanu. ""Me kuke so Hajiya?"" ""Me muke so? Tambaya kike me muke so? Bama ki ce zaki rufa mishi asiri ba? Ai na gaya maka Lubnah bata kaunarka, amma ka ki ka yarda gashi tana nunawa kamar abin bai dame ta ba."" Sai ta rufe ni da fada, cikin jin haushi ya mike tare da daka mata tsawa. ""Me kike zo yi? Kin zo ki kara birkita min ita ne? Kin san halin da nake ciki kuwa?"

"Idan kika rud'a min ita ya kike so nayi? Luluna ya isa!"" Ya rungume ni yana shafa kaina. Kallon Hajiyarsu yayi ya nuna mata kofa ba ita ba har Tijjani da Karima. Suna fita ya zauna tare shafa kaina yana faWin. ""Ki"

"yi hakuri, ki yi hakuri."" Me Ya Hafiz yake so a gare ni da yake bani hakuri haka....."

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

UKU

"Bani mantawa shekaru biyar da suka wuce haka ya suka saka ni a gaba da irin wannan niman alfarman,"

"kaina ya daure a lokacin na amince kome ya faru wanda har yau nake ji kamar da ban amince ba, babu abinda zai faru. Koda yake ai zanen ™addarata ce, ""Ya Hafiz me kake bukata?"" Na tambaye shi, sharce hawayensa yayi kafin ya ce min. ""Ba kome pretty!"" Sai naji sunan ya zo min wani irin banbarakwai, saboda rabona da Ya Hafiz ya kira ni da wannan sunan tun farkon aurenmu ludayina yana kan dawwo ba yanzu da nafi kamar da katifa huta ba. ""Hmm me kake bukata?"" Zama yayi ya kwantar da kaina a kafad'arshi, yaushe ya Hafiz ya zama haka? Tow akwai abinda yake bukata. ""Zan gaya miki muje ki yi"

"sallah."" Ya fada yana jan hancinsa. Haka na mike na nufi dakina, shima ya fita zuwa bangaren Karimah."

Hafiz

"""Hajiya ni ban kirawo ki nan, ki kara min matsala ba. Kin san irin halin da nake ciki? Yarinyar nan lallabata"

"zan yi na rufawa kaina asiri, idan ba haka ba wallahi sai dai na kare a gidan Yari, kin san ban ajiye ba ban bada ajiya ba, sannan shi wancan Mijinki ba shi ne da shi. Don Allah ki ajiye kiyayyar da kike mata, nima hakuri nake da ita kada ki sake ki kara mata wani maganar banza!"" Cikin kaskantar da kai ta ce mishi. "" Ya kake so nayi? Kasan bana son ganka cikin tashin hankali, amma ka gaya min yadda zan bita, ai duk abinda kace shi za ayi Alhaji karami!"" Zama yayi da kyau ya ce musu. "" Nan da sati idan ta amince zan sayar da gidan nan, abinda ya rage zan sayi wani karami a tudun salamanu, bana son danginta da ita"

"kanta su san abin da yake faruwa, ina son kafin haka na tafi Umara da ita, domin yadda kome zai tafi. """

""" Umara kuma? Taya Umara kuma? "" Inji Karimcy, kallon an kusan fita Masallaci yayi ya ce mata. """

"Wani sati zamu tafi na gama shirina, zaki bi Hajiya da Yara zuwa Jama'are! "" Ya fada yana fita daga part din, tabbas yayi shirme, amma yasan idan har ya samu hadin kan Lulu kome zai tafi yadda ya tsara."

"Lokacin da ya koma, tana zaune akan abin sallah, hannunsa dauke da wata cadi yayi shiru cikin"

"doguwar rigan jikinshi. Ya yi jugum kamar wanda yake ciwo, a yau daya na hango ramar da yayi kafin ya kalle ni cikin karfin hali ya ce min. "" Kin idar ne? "" Gyada mishi kai nayi ina kallonshi, domin duk ya bani tausayi sai na rasa me ke min dad'i na matsa kusa da shi na, daura kaina a kan gwiwarshi, shiru yayi kafin ya ce min. ""Allah ya jarabce ni a kwanakin nan, duk yadda nake son nayi ™o™arin dauke kaina amma na kasa."" Shiru yayi yana jan numfashi, ya kwantar da kanshi a jikin kujera yana haki. "" Ya Hafiz me kake"

"bukata? Ya Hafiz baka yarda xan iya kome akanka ba ne??"""

"Girgiza kai yayi yana faWin, ""Lubnah ba zaki iya ba, ni da nasan ba zaki iya tunda kwanankin baya yan"

"uwanki sun bukaci mu rabu gara kawai na sallame ki, na kare rayuwata a gidan Yari, domin nasan karshe na a gidan Yari zan gama rayuwata!"" Na kaWu da jin zai kare rayuwarsa a gidan Yari, haka yasa na shiga"

damuwa nayi ta rarrashinsa da mishi alkawarin duk abinda yake so ya gaya min xan mishi.

Haka muka cigaba da zama har aka yi sallah isha ya tafi masallaci.

Hafiz

"Fitar da yayi ba masallaci ya nufa ba, bangaren su Hajiya ya nufa, ya zauna domin sallah dai baya yinta,"

"kome za ayi sai dai a yi amma idan akan sallah ne ba zai tab'a yin ta ba. Haka ya zauna ya yi shiru Hajiyarsa ta ce mishi. "" Hafizu ka barmu cikin duhu meke faruwa ne? "" Shafa kanshi yayi kafin ya ce mata. "" Ba kome. "" "" Wani irin ba kome? Me ya faru? "" "" Wato Hajiya Yan uwan Lubnah suna son su raba mu. "" Nan ya kwashe kome ya gaya mata, shiru yayi yana kallonsu. "" Yanzu saboda haka ne ya dauko ni? "" Girgiza kai yayi yana lashe busashen lips dinsa yana kallon kasa. "" Ba saboda shi ba ne. "" A hankali yayi shiru ba zai tab'a fada ba, ko zai mutu ne domin bai yarda da Hajiyarsu da Tijjani ba, kai hatta Karima bai"

"yarda da ita ba, shi a duniya yafi yarda da Lubnah akan kowa."

"Ana idar da sallah ya mike zai fita Karima ta ce mishi. ""Bamu ci abincin dare ba!"" ""Baki da hannu ne,"

"kin manta halin da nake ciki ne? Ita kanta ta rude balle ni ta san me zata dafa, ki shiga ki dafa muku. "" Ya fita daga parlourn."

"Parlourn Lubnah ya isa ya zauna yana kallon tv, sannan yana jin motsinta a kitchen. Yasan zata yi wani"

"abu amma shi abinda yake bukata yafi karfin abinda zai ci,. Shiru shiru bata fito ba, sai ya fara tari kamar wanda ya kware."

"Haka yasa na ji tarinsa na fito da sauri ina faWin,"" sannu Yaya kwarewa ka yi? Bari na kawo maka ruwa!"

""" Na koma kitchen na kawo mishi ruwa da sauri na bashi ya sha yana sauke wata irin ajiyar zuciya da nishi mai karfi, sai da ya tsinkar min da zuciya. Daura kanshi yayi akan kirjina yana ajiyar zuciya. ""Luluna ina cikin tashin hankali, mutuncina da kimata zata zube. "" "" Ya Hafiz meke faruwa ne? Idan Baban Bauchi yaji ranshi zai b'aci"" a wani zabure ya mike zaune yana kamkame ni,"" don Allah kada ki gaya mishi, Innalillahi wainnalihir rajoun, don Allah ki rufa min asiri wallahi idan ya ji zuciyata zata buga. "" Kamar"

"yaro me tsoro haka ya koma min, ina son Ya Hafiz son da bana yiwa kaina. Shima kuma yasan haka ina"

"sonshi so na hakika, don haka ya kara gigicewa yana mata gungun kamar mai cutar farfadiya. Shafa"

bayanshi nake ina bashi hakuri da rarrashinsa.

""" Ya Hafiz meke faruwa? "" Shakuwa ya fara tare da buga kirjinsa, haka yasa na mike tare da kawo mishi"

"ruwan da na ajiye a saman Centre table, na bashi ya sha. Jin kauri a kitchen yasa na wuce da sauri na sauke jallop din taliya da kifin da nayi na zubawa Hajiya sannan na zuba mishi na zuba nasu karima da Yaranta sai na Tijjani, na saka a katon tire, na fita da shi zuwa bangaren Karimah, koda na isa na samu suna ta hiran halin da Ya Hafiz yake ciki suna jajjantawa. "" Yanzu idan har bai yi wani abu ba zai iya fuskantar fushin hukuma kenan Hajiya? "" "" Eh kai Yar nan, kuma kin ga ai fushin hukuma babban tashin hankali ne domin ba mamaki su wuce da shi gidan Yari! "" Wato sune suke magana amma ni ce hantar cikina yake kad'awa, ""Allah ya kyauta in sha Allah haka ba zai yiwu ba!"" Na fada musu ina ajiye musu abincinsu. ""Zai yiwu kai tunda baki haihu da shi ba, taya zaki fahimci halin da yake ciki, idan kika tuna halin da Uban Yaranki zai shiga kome kika mallaka zaku kashe shi a nan wurin, ki sani ba zance zan rabaki da Hafiz ba. Amma ina ganin lokaci yayi da ya kamata Hafiz ya hakura da ke domin ke ba matar rufin asiri ba ne? Tunda har ta kai ya saka wannan gidan a kasuwa."" Dafe kirjina nayi cikin wani irin bugawa da yake kamar zuciyata zata dirko daga kirjina, ""haba Hajiya me yasa zaki gaya mata? Me yasa zaki bari ta sani? Idan wani abu ne na amince zan fuskanci hukuma akan laifina gara na fusk."" Rufe mishi baki nayi"

"ina girgiza kai. "" A'a don Allah kada ka ce haka, ba zaka sayar da gidan nan ba! """

""" Au ka ji ba, saboda gidanta ne, gidan da Ubanta ya saya maku, da ace gidanka ne wani ya isa ya hana"

"ne? "" Maganganun Hajiya suka kara birkita min ™wa™walwa sai kaina ya fara juyawa, na fita da gudu na"

nufi dakina.

"Bayan fitar Lulu suka kwashe da dariya, Hafiz ya ce ""mahaukaciyar banza yanzu zata dauko jikinta yana"

"rawa. Amma kun taimaka min."" Tijjani da ya cika bakinsa da abinci ya ce musu. ""Amma maganar gaskiya, ya kamata ka kyale yarinyar nan, iya adalci ta maka tayi maka kome, idan ka cigaba da abinda kuke akwai lokacin da kome zai lalace wallahi."" ""Dalla yi min shiru, ba gara shi ba kai ina sai dai na rike ka na rike matarka."" Inji Hajiya, ""Kyale shi Hajiya ai yadda Lubnah take kaf duniya babu me iya juya ta sama da ni, sannan idan kana ganin zata iya rayuwa babu ni zan gaya mata a gabanka zaka ji me xata ce, kuyi shiru"

"gata nan zuwa!"""

"A hankali na shigo parlourn ba kome a tare da ni, suka zuba min idanu. "" Ya Hafiz ko zaka zo! "" Shiru"

"yayi kafin ya mike yana dafe kirjinsa da yake nuna min alamar yana mishi ciwo. "" Don Allah riki ni, jiri nake ji."" Haka na matsa jikinshi, muka fito har zuwa parlourna, ya zauna a dogon kujera ya kishingida yana lumshe idanunshi. Dakin na wuce na dauko kwatin yan kunayena,. Na ajiye mishi sannan na koma gefe na zauna. ""Ban san me ya faru ba, amma ga shi ka. Biya abinda ake binka."" Kallona yayi kafin ya dauke kai yana dafe kirjinsa. ""Lubnah bar dukiyarki kada yan uwanki su ji, su kara himmar raba mu, ki barshi kawai Allah yana nan."" ""Kudin ne ba zai iya ba?"" Hawaye ne ya zubo mishi ya ce min. ""Wato wani ™addara ne ya fada min, a shagon Baban Bauchi. Gashi saura kwana uku na hada kudin."" ""Baban Bauchi"

"bai sani ba ne?"" Dafe kanshi yayi da hannu bibbiyu yana nishi. Ban san lokacin da na kara rudewa ba, na"

"riko hannunshi tare da janyo shi jikina ina tab'a shi. ""Ya Hafiz ko mu tafi asibiti ne? Innalillahi wainnalihir"

"rajoun! Ya Hafiz lafiya?"" Yadda ya mike min kamar gawa yasa na kara kidimewa, garin juyawa na ci tuntube da center table din parlona, ban damu da zafin ba amma har cikin raina na ji ciwon sai dai halin da Ya Hafiz yake ciki yasa na manta da ciwon da naci, sai na kasa gane kukan da xan yi na ciwon ne ko kuma na halin da ya Hafiz yake ciki ne? BakiWaya na shiga tashin hankali, ban san adadin soyayyar da nake yiwa ya Hafiz ba, haka yasa na kara birkice na rungume shi, ina kuka sosai, domin zuciyata ta karye ainun. Bana son naga abinda zai d'aga mishi hankali, a daren muka kai shi asibitin ni'ima aka bashi kulawar da ta dace har da karin ruwa, Tijjani muka bari a can asibitin muka dawo gida, Hajiya sai kuka take, tana shashekar duk sai naji na damu da kai, dakyar muka dawo tambari inda Unguwar yake, na tura kan motata zuwa cikin gidan, dama motar da yake hawa tawa ce, tunda ya sayar da tashi kwanakin"

baya ya dauki tawa yana amfani da shi.

"Koda muka fito Hajiyarsu ta ce min. ""Lubabatu dama nace ko."" kallonta nayi ina son naji me zata ce,"

"sai ta ce min. ""Dama kada ki gayawa Iyayenki halin da ake ciki domin idan kika gaya musu abin ba zai yi dadi ba, idan babanku na Jama'are yayi cewa ga abinda ya faru. Ki zama mace mai rufawa Mijinta asiri haka zai saka Allah ya rufa miki ta yadda baki zata ba."" Gyada kai nayi ina faWin.. ""in sha Allah Hajiyarmu!"" Na fita daga motar na nufi cikin gidan, na rufe bangarena parlourn na zauna nayi ta tunani kafin na shiga na kwanta, karfe biyu da arba'in da biyar na farka sallah dare, ina yi ina gayawa Allah kuka"

"ta da matsalata, nayi tawassali da sunayen Allah tsarkaka, Allah ba zai tab'a wulakantamu ba."

"Ina zaune har aka yi sallah asuba, sannan na yi raka'atu fijir, ina idarwa na daura da sallah asuba,"

"sannan na fita na fere doya na daura a wuta, sannan na daura ruwan tea, a hankali nake bin kome ina lissafin yadda xan shawo kan matsalar ya Hafiz, wurin karfe bakwai sai ga Tijjani yazo daukar mota zai je

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login