Follow us on social media

Showing 60001 words to 63000 words out of 140751 words

Chapter 21 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

336

ko tayi mishi, yar kwailar nan da suka je ganinta, tayi ta zuba gudu da boya ance saurayi ya zo wurinta. ""Alhaji baki ce kome ba?"" Ta kara fada Hajja a wurinta mace namiji ne, namiji kuma mace, ta juya musu lamarinsu mai sauki ne kusan dabi'ar Fulani da Barebari da nufawa, haka harshensu take taking over na jinsin matukar bada"

yaransu zasu yi maganar ba.

"Akwai wani abu da Hajja da Alhaji ELYakub suka kasa boye shi, kaunar Jikansu da yake bala'in wahalar"

"da su. Domin kaf duniya babu wnada yake juya kakaninsa, kamarshi sauran jikokin basu samu wannan damar ba yo Alhaji ELYakub bai yarda da wasan jika da kaka ba, domin yana da zurfin ilimin addini da na boko, gogaggen dan kasuwa ne, top-notch wanda aka sani a nan kudu da arewa. Mutum ne da yake faWa aji, domin ya bunkasa fiye da kima, hatta Yarbawan lagos suna matukar ganin girmansa, kamar yadda suke ganin girman dan gote. Idan za ayi lissafin attajirai da suka boye kansu ELYakub Kumo yana cikin"

manya na farko.

"Domin yana da hadin gwiwa da bankunar kasar nan, irinsu First bank, UBA, Union Bank, Zenith bank,"

"ya kawo wannan hadin gwiwar? Duk da bankunan ne suka bukaci ala™a da shi ba shi ya bukaci ala™a da su ba, akwai lokacin da idan mutum ya isa wani limit baya bukatar ya tura kansa sai anyi da shi, lokaci yake zuwa ayi da kai. Haka ce ta faru. ""Alhaji baki ce kome ba?"" ""Shi kenan zan gaya mishi shi kenan?"" Gyada kai tayi ta gyara zama ta fara bashi labarin da Malamin ya gaya mata akan Turaki wanda kusan tishi ce ai ya saba jin wannan labarin ba sabo ba ne a wurinsa. Karshe ma ga yadda hiran ta kasance. ""Ita"

"Turaki ta hadu da aljani suka auri juna har suka hayayyafa yaran suna zuwa cikin gidan nan har wurinki,"

"yanzu da ayi kiranye kenan?"" Shiru yayi yana kallon yadda ta damu kuma ya ce mata. ""Gaya min me"

"Malamin ya ce miki."" Gyara zama tayi ta ce mishi. ""Kin san bana bin makamai amma wannan karon nace bari na hada malami guda biyu, tow ita Waya ta Gombe ta ce min babu abinda ya faru, ™addaranta ce har yanzu bata zo gare ta ba. Amma ni ban yarda da ita ba, don bata ce za'ayi aikin kome ba, ta dai ce kome da yake faruwa haka Allah yaso, idan aka yi hakuri ita Turaki zata dawo da kanta, tow na dai bada abin sadaka ya ce ita bata karban Kudi dayawa shi yasa na fahimci karya take yi, tow ita Waya ta kome tace akwai mata aljani suna tare har suna da Yara da shi, ita Turaki ya auri matar aljani ne, shi yasa shi matar aljani ya dauke shi daga wurin mu, idan har muna so ya dawo sai an biya kudin kamar dubu dari hudu da saniya baka wuluk sai a sayi farin kaza, dan taure baki, kaza buja-buja. Jan dawa, bakin dawa, kaura, da"

"fura kwarya goma."""

"""Hajja karya yake shi yake son cin kudinki."" Inji Alhaji ELYakub, shiru tayi tana kallonshi idanunta ne suka"

"shiga cika da kwalla. ""Alhaji ki fahimci yadda nake ji!"" Riko hannunta yayi ya saka nata a cikin hannunsa ya dunkule hannun a hankali yana bugawa yace mata. ""Fadime, ki yarda da maganar wancan malamin farkon shi mutumin kirki ne, shi kuma wannan dan damfara ne, Fadime ina son ki yarda kaf duniya ba mai yi sai Allah. Ni nasan Turaki zai dawo lokaci ne kawai bai yi ba, idan kika ce zaki dawo da shi da karfi zai koma. Kin tuna yadda ya dawo wasu shekaru kafin lamarin ya lalace haka. In sha Allah Turakinki zai dawo gare ki."" Mikewa Ubaid yayi ya basu wuri can wajen gidan ya fita ya damu daya daga cikin kujerun alfarma ya zauna ya zaro wayarshi. Sai da ya cire shi a key ya tsaya yana kallon hotonsu na kuruciya, suna dariya ya danne bayan Turakin. Murmushi yayi sannan ya cigaba da. Lalubar wayar har ya zo kan number shi wanda ya rubuta Introvert. Wayar har ta gama ringing ba a dauka ba, sai can aka turo mishi"

sako da number.

*Ya suke?*...........

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA BIYU"

"Daga wannan babu wani sakon, har leka bayan wayar Ubaid yayi ko zai ga sauran sun makale, amma ina"

"iya su kenan kalma biyu, harufa hudu? Wato shi dai ba zai tab'a sauya ba."

Cikin fushi shima ya tura masa da Ash'ar. Tunda ya tura ya kai minti goma a wurin ba reply ai yasan ko

"sama da kasa zasu hadu ba zai dawo mishi da sakon ba, idan yayi sa'a gobe ma da zai kara tura mishi abu daya ne zai sake turo mishi. Sake kiran layin yayi ya danna mishi busy. Takaici ya saka shi wucewa gidan ya samu Hajja da Alhaji ELYakub sun koma hiransu, mika mishi File din yayi ya ce mishi. ""Wannan sune sakon da ya bani, sannan da farko ban fahimci yadda sakon yake ba, sai dazun nan na fahimci sakon."" A hankali ya fara warware mishi bayanin da Turaki ya turo mishi, shiru yayi yana mamakin yadda, kome yake tafiya ba tare da saninsu ba. Sannan wani abin da ya bashi tsoro yadda aka karkata da kuWi ta wani"

hanyar da bai dace ba.

"""An samu masu hannu a cikin lamarin?"" Bude baki Ubaid yayi zai magana aka turo kofar, Alhaji Mudansir"

"ELYakub Kumo ya shigo cikin wata danyen Wagabari dark blue, yayi ya wani irin daukar fatarshi. Sai wani shaki yake kamar dare kwana sha huWu, duk wanda ya ganshi yaga wanda arziki ya zauna mishi, cikin isa"

da kasaita ya samu wuri ya zauna cikin girmamawa ya gaida iyayensa. A hankali ya mai da hankalinsa

"wurin Mahaifinsu da ya ga ya tattara nutsuwarsa ga Ubaidullahi. ""Yanzu ka mai da mishi sakon kace yayi duk abinda yake ganin ya dace, sauran kuma zan dauki mataki in sha Allah ba zan bar kome ya tafi a haka ba."" Wani irin harara Alhaji Mudansir ELYakub ya watsawa Ubaidullahi ya cigaba da sauraren maganarsu da ba fahimtar inda suka nufa yake ba, tunda kusan a dunkule suke maganar. Mikewa yayi don ya fahimci a al'amarin duniyar nan matukar maganar Turaki ne tow dattijon Mahaifinsu baya sauraren kowa kuma baya fahimtar kome idan har da a furta sunan Turaki a gabanshi ko a gefensa."

"""Baffa zan leka kamfani."""

"Kallonshi Hajiya Dadda tayi ta ce mishi. ""Saurin me kike yi da ba zaki zauna ta gama magana ba? Ban"

"san me yake ciwon ranki idan kika zo ki ka ga ana magana akan Turaki sai ki tsirfo da wani hali."" Daga haka bata kara magana ba, ta dauke kamata kamar ba ita tayi maganar ba, kunya ce ta sa shi komawa ya zauna. Burinsa ya fita waje ya jira Ubaid yaji wani abu suke shiryawa. Bai gama wannan nazarin ba sai ga Alhaji Mujitafa, wanda suke kiranshi Auta. Cikin girmamawa ya gaida Iyayen nasu sannan ya kalli Ubaida ya ce mishi. ""Second love, kai ne da sassafen nan?"" Gyada kai yayi yana murmushi ya ce mishi. ""Uncle Auta barka dai."" ""Barka second love, ina wancan Introvert din ya shiga ne? Na kira bai dauka ba."" Kunshe dariya Ubaid yayi yana kallon Uncle Auta da yake ™ara duba wayarshi. ""Duba ai ba zai gaza turo maka sako ba!"" Dubawa yayi yaga sakon. ""Sorry im busy!"" Tsaki yayi ya ce musu. ""Baffa na gaji da halin Turaki."" Make shi Hajiya Dadda tayi cikin wannan rikitaccen hausar nan nata me juya mace namiji , namiji mace ta ce mishi. ""Kin ci gidanku, mara kunya in gaji da halinta, wani hali ne da ita banda halin kwarai, ita yaron nan Turaki mutumin kirki ce, kowa yasan tana da kirki amma bakin halin zeenatu da yayiwa Turaki sharri, ina da tana nan da nata iyalin, wai yaron dan uwanku kenan kuka juya mata baya ke Auta da nake gani a mutumin kirki amma kike cewa kin gaji da halinta. "" Matsawa can yayi yana jin zafin yatsun hannunta. "" Daddah kece kika bawa Turaki dama yayi yadda yake so, Fisabiilillahi me ya nima ya rasa. "" "" Abubuwa dayawa. "" Inji Alhaji ELYakub Kumo ya fada ya ce mishi. "" At teenage ya rasa Uwa da Kannensa, sai Jasminah itama don ba yadda ta iya da shi ne, tunda su biyu suka rage, tunda ta zama yar amshin shatar zeenatu, koda yake uwarta ce ba yadda ta iya amma a gefe guda ina ganin laifinka ne, Mudansir. "" "" Baffa ni kuma?"" Ya nuna kanshi da muryanshi a shake, "" Eh kai;"" shigowa wasu matan alfarma suka yi tare da wani shima babba a cikin gidan. "" Daddy! "" Ta kira sunansa. Kallonta yayi yana mai mika mata hannu ta zauna a kusa da shi, tana kallon Alhaji ELYakub Kumo ta ce mishi. ""Baffa ina kwana?"" "" Lafiya lau Fadima."" ""Barka da safiya Kawu?"" "" Barka dai Munir!"" Shigowar wata hamshiyar mace parlourn cikin wani uban ado kamar zata biki da daya daga cikin yan matan nan da suka je salon, nunawa yarinayr wurin zama daya yarinyar tayi. "" Badar ga wuri! "" Wani yatsina fuska tayi, tana kallon"

gefen da mahaifiyarta ta zauna. Itama nan ta zauna.

"Kallon zuri'arshi yayi babu bare a cikinsu dukkansu ahalin Kumo ne, kuma masu hannun jari a"

"kamfanin KUMO properties nigeria agency, kamfani ce fa take sayan duk wani kadara da gwamnati zata"

"yi gwanjonsa, kamfani ne da banku suke binta, ba iya nan ba akwai wasu iyalan nan, domin kuwa lissafin a bayyane take."

Su waye KUMO properties nigeria agency?

"Alhaji ELYakub Kumo, dan asalin Gombe ne da ya fito daga garin kumo, ba fulatani ne da ya gaji arziki"

"daga iyaye da kakanni domin su ke da sarautar Sarkin Fulani Kumo anan lagos sarautar ce da ita ta Sarkin Fulanin lagos., dogaye ne masu matsakaicin jiki yayinda matan cikinsu suka kasance sirara iyayen suka"

kasance yan chubbys.

"Alhaji ELYakub yana mata daya Hajiya Fadime, wacce suke kiranta da Daddah. Ita ta haifi Yara shida"

maza uku mata uku.

"Marigayi Alhaji Haris shi ya fara bada shawarar kafa kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma"

"har yanzu sana'arsu ta gado sayar da shanu da madara basu fada ba domin bude wani kamfani aka yi na sayar da madarar shanu da namar shanu. Kasancewar Alhaji ELYakub da girmansa ya fada harkan boko, domin lokacin da ya auri Dadda bai gama secondry School ba, tun yana Yaro dan shekaru goma sha uku yake kad'a shanu daga Gombe to lagos, a cikin gwangwaro. Haka yasa wani bayarabe ya bashi shawara ya fara karatu domin Allah ya mishi baiwar iya sarrafa kudi, gashi tun yana wannan shekarun turanci ya"

zauna akan harshensa.

"Kusan fulanin zamanin da akwai zuciya haka yasa yana dawowa ya fara makaranta, shekara daya yayi"

"a primary ya tafi secondry School, yana da shekaru ashirin cib ya gama secondry School, a wannan shekarar aka auren mishi yar baffansa Daddah. Zamansu yayi albarka domin kuwa kuwa an haifi Harisu"

"wanda shine Babba,sai Mudansir, Khaulatu, Sameerah, sai Ramatu kafin Uncle Auta wato Mujitafa."

"Kamar yadda suke su shidan haka kowane a wurin halinsa daban, Alhaji ELYakub ya gina kansa da"

"matsayin da yake ta hanyar sana'ar sayar da shanu daga Gombe zuwa Lagos, kafin wani abu ya faru a gabansa, wani mutum ne ake bi bashin banki, su kuma banki suka zo kwace kadarorin mutumin lokacin duniya tana kwance, a take suka fara kwashe kayan sanin cewa suna tare da bayaraben for while sai ya tambayi kudin da ake bin mutum banki ta fada mishi, cikin ikon Allah sai ya gwada biya, tare da maida wa mutumin kayanshi idan Allah ya hore mishi ya biya shi. Shi dai da farko bai dauki haka a matsayin"

wani babban al'amari ba.

Bayan an bashi shawarar ya dawo Lagos da zama ai zai fi yana sakawa ana kawo mishi dabbobin

"daga arewa, ace duk bayan sati biyu yana hanyar Lagos, a lokacin ya haWa degree dinsa na daya zuwa na"

"biyu, ga shi idan ya ce yana da iyali ™aryata shi ake domin a lokacin ya cika shekaru talatin a duniya, haka"

"ya nime gida a alaba rago, ya kawo Daddah da Yaranta, dama can ko a Gombe Yaran suna karatu domin"

"Daddah tana haihuwar kunika ne, yaran kusan kansu daya idan ka cire Harisu da ya fi su tsawo, tunda"

"suka dawo Lagos sai rayuwarsu ta kara inganta, idan aka samu jajjirtaccen namiji akan ilimin Yaransa, tow bakiWaya dauke kome yake yi, haka Alhaji ELYakub ya kasance, ya tsayawa Yaransa musamman harisu da ya kasance mai zuciyar neman na kai, domin shi ya fara bada shawarar Daddah ta fara sayar da fura da nono lokacin bai wuce shekarun sha biyar a duniya ba, da ya gama secondry yana jami'a shi ya fara gayawa Mahaifinsu madadin kudin da yake biyawa mutanen da suka shiga matsala da banki yayi Register da lasin domin ya fara sayan kadarorin mutane, idan ka biya kudinsu ka dauki kayanka, a yanzu an cigaba, shi anan kasar turawa da yake karatu haka suke yi, domin shi a can Rasha ta tafi karatunsa bayanshi babu wnada ya samu wannan damar domin sun dauki irin rayuwar karya da son a san su din wasu ne, Uncle Auta ne kaWai yayi karatu har zuwa Nijar, da yake shi din na. Musamman ne, Allah ya haWa jininsa da dan uwansa Harisu, Haris yana da abokai guda biyu, Jibrin Mahaifin Ubaid, sai Abbas, abokai uku nan sun taso cike da kaunar juna da adalci idan ka cire Uncle Auta a cikinsu wnada ya"

kasance Yaro ne.

"Jibrin Mahaifin Ubaid, dan Kanwar Alhaji ELYakub ne, ya dauko shi ya kawo shi gidansa tun suna Yara,"

"shi kuma Abbas dan abokin Alhaji ELYakub ne, mahaifinsa ya rasu Maraya ne, wanda dangin mahaifinsa suka kwashe dukiyarsa suka watsar da shi. Haka Alhaji ELYakub ya haWa su da nashi."

"Lokacin da suka dawo gidan ba karamin wulakanci suke sha da Mudansir ba, domin kiri-kiri yake nuna"

"musu sun zo cin arzikinsu ne, Jibrin yana da zuciya sosai haka yasa ya daina zama a gidan, don yana jami'ar Lagos a can yake karatu yake zaune sai weekend da yake shigowa, Abbas dai yake nanike Mudansir idan Harisu baya nan, domin yana da bala'in kwadayi da son abin duniya."

"Lokacin da Harisu ya dawo sai gashi tare da wata yar kasar habasha, amma haifaffiyar kasar rasha, mai"

"suna Annah. Kasancewar Alhaji ELYakub bai hana kowa yadda yake so ba, haka ya amince da abinda dansa yake so, amma da sharadin idan ya gama ya samu lokaci zai aura mishi yar dangi, bai ki ba shima Harisu ya gayawa Annah tana sonshi, haka yasa ta amince, Ubanta mai kudin gaske ne a rasha da Habasha, don kusan da yardan Iyayenta suka tawo gani take idan Harisu ya dawo ba zai tab'a aurenta ba, Annah ba fara bace asalin kalar fatarta na an Ethiopia ne, shi harisu ne ma Faris sosai domin shi ya dauko fatar Daddah don ita farin fatarta har wani jajja ya™e. Irin tarban da suka yi Annah yasa abin ya bawa yan uwan Harisu haushi, amma Jibirn ya goya mishi baya, satin su biyu suka tafi har can rasha aka basu auren Annah, sai dai tunda aka yi Auren yan uwansa suka tsangwami Annah saboda ita bata sallah, haka yana basu haushi bayan sun manta cewa Addini ya bawa maza musulmai damar auren auren Ahalul kitab."

"Wani ikon Allah annah tana shigowa sai ciki, wannan cikin ya saka mata kwadayin abubuwa musamman fura da nono, sai tuwon dawa, wanda kusan abincin Alhaji ELYakub ne, haka suka hadu suka yi renon"

"cikin har ta haifi danta, namiji Masha Allah."

"Lokacin da sako ya isawa danginta, sun zo domin farin ciki. Ranar suna ta ce ta bar addininta na"

"Kirista ta koma addinin Muslunci, yaro ya ci suna Bilal wanda Jibirin ya ci Turaki domin a lokacin sunan yaron aka kara bunkasa kamfanin KUMO properties nigeria agency, aka kara fadadda shi, a lokacin Jarin Alhaji ELYakub yayi kasa, sai da Annah wacce sunanta ya koma Nana Aishatu, ta tafi har rasha ta nimo kudi, a wurin mahaifinta iya mata uku ya haifa. Annah Aisha ita ce Babba haka yasa da tazo da bukatarta basu hanata ba, ita ce mutum na farko da ta fara saka hannun jari a Kamfanin, kafin Bilal ya cika shekara"

biyu a duniya Kamfanin KUMO properties nigeria agency yayi wani irin bun™asa.

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 23"

"Irin bun™asa da ba a tab'a kawowa ba, kasancewar ko a can rasha ita take ji da kamfanin mahaifinta, sai"

"Harisu ya ce a bata wani bangare na kasuwanci a kamfanin yadda zata iya jagoranta, duk abinda zai yi sai ya fara da iyayensu sannan ya kawowa abokinsa Jibrin shi yake bashi shawara. Rike kamfanin da Annah A'ishah tayi ya kai kamfanin wata irin matakin nasara, a lokacin ta samu cikinta na biyu, tana kuma jagorantar kamfanin, kafin ta haihu bankin First suka fara kulla Yarjejeniyar kasuwanci, wnada idan aka samu matsala na bashi su zasu fara tuntuba, domin babu kamfanin a kasar nan sai su ne suka fara jagorantar shi. Shekarar Turaki biyu da wata goma aka haifa mishi Yakub wanda suka kiranshi da Baffa,"

wani irin kaunar Yaran suke kamar su boye su.

"Daddah kuwa soyayyar duniya ta daurawa Turaki, sonshi take kusan tun yaye ta rike musu da taki"

"basu. Sai a lokacin Mudansir ya koma makaranta, suma matan da suka fara maganar karatu Alhaji ELYakub ya ce sai dai su yi aikin mazansu. Khaulatu dama suna soyayya da Abbas, Sameerah kuma tana tare da wani dan Kano da yake nan Lagos, ELYakub yaso Jibrin ya auri Ramatu amma yaki domin ya riga Harisu aure, matar ce dai take Gombe, itama tana da Yaro Ubaid wanda kusan wata uku ne tsakaninsu"

da Bilal Turaki.

"Ita Khaulatu tana cikin wani gidan da Alhaji ELYakub ya basu ita da Abbas, haka tayi ta fama itama"

"dai ta koma boko damuwarsu shine matsayin da Aisha da harisu suke kai su samu, sai dai irin wannan matsayin ana samun shi ne ta hanyar da ta halatta, haka suka sakawa ransu kyashi da hassada, wanda yasa suka kasa gaba suka kasa baya. Abin haka yayi ta tafiya har zuwa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login