Follow us on social media

Showing 132001 words to 135000 words out of 140751 words

Chapter 45 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

297

laifi?"" Jan kumatunsu nayi na ce musu."

"""Break na Wauka."" ""Yaushe zaki dawo?"" ""Mama ta ce zan tafi Bauchi!"" Na fada ina satar kallonshi, ya"

"fada kamar bai da lafiya. ""Eh zata koma Bauchi da zama!"" ""Kakar Bauchi, ki barta kin ji Mom tace tana da"

"kirki, kuma nima ai ta min kirki."" Murmushi Mama tayi tana faWin. ""Tow kishiya amma ba zan bari ki aure min Alhaji ba, domin nima ina da gashi yala-yala irin naki."" Dariya Ilham yayi tana faWin. ""Kaka ai naki yayi fari, ba irin na Aunty Lulu ba ne, ita nata fa ranar donut na ga tayi da shi ko Mom bata donut. Uncle kace kai ma Mom Winka tafi Aunty Lulu gashi, amma tana kama da Mom Winka."" ""Da gaske Bro haka ka fada musu."" Bai ce kome ba, ni ce ma nayi maza na toshe bakinta, na mata rad'a a kunne. ""Bakyau fadar sirrin da kuka yi da wani ko?"" Na fada ina kallon Mama da take kallona. ""Aunty Jasmin ya kwana biyu?"" ""Alhamdulillahi, kin ajiye aiki ko? Brother ma jiya aka sallame shi bai da lafiya!"" Da sauri na d'ago ina kallonshi, ya tara Kaduna, sunkuyar da kai nayi ina kallon kasa na ce mata. ""Allah ya bashi lafiya!"" ""Amin"

"Ya Allah, yaushe zaki koma aikinki?"""

"Gyara zama Mama tayi sannan ta ce mata. ""Ta gama aiki da ku ai, zata koma Bauchi ta cigaba da aikin a"

"can anan ana bibiyar rayuwarta. Sannan su waWanda hotunan ban san ma'anarsu ba, na ji ance kai ne mai gidanta."" Shiru yayi yana kallon hotunan daya na wurin abinci ne, na biyu na Eko hotel ne, na uku dawowarmu daga Japan. Tasowa yayi ya durkusa a gaban ta. Cikin sanyin murya ya dauki hotunan ya ce mata. ""Kasancewarta sakatarinya, ina bukatarta a kusa da ni. Wannan wani kasuwanci muka yi shine sanadin da ta bi ni hotel, wannan gidan abinci ne bata ma ci ba sai tawowa tayi da shi, na uku tafiya ce na kasuwanci. Na rantse miki da wannan rayuwa da mutuwa take hannunsa, sai da tace min ba zata ba, har wata ta ce zata nace a'a. Mama! "" Ya kira sunanta a hankali, cikin rarrashi da niman afwa ya ce mata. "" Ko bayan ranki, Yarki ba zata zubar da mutuncinta ba, ba zata wulakanta tarbiyyar da kika mata ba."

"Mama da ace Yarki zata yi wani abu da tayi. "" Kallona yayi kafin ya sunkuyar da kai kasa, ya cigaba da cewa."" Allah ya sani ita din Mutuniyar kirki ce, kamila ce, Saliha , mijinta ya dace da mace ta gari. Yaranta zasu yi Alfahari da ita a matsayin Uwa ta gari. Don Allah ki barta anan wallahi ni da kaina zan tayaku kare mutuncinta, kamar yadda xan kare uwar Yaran nan da su Yaran Lubnah ma zan kare mutuncinta."" Ceo yana da hikima,. A yadda yake iya kasuwanci da mu'amala da mutane haka duk wanda ya zauna da shi sai ya fahimci haka. Kaina a sunkuye ina wasa da yatsuna ina jin tsigar jikina yana mikewa, ina ™ara jin wani abu yana tab'a ruhina da zuciyata, d'ago kai nayi ban san yadda aka yi na ji yana bani tausayi ba, a yau na ga yadda damuwa take cike da idanunsa, zuciyata tayi rauni ainun. Kasa jure yadda yake rokon Mama nayi, na riko hannun Yaran muka wuce sama, kafin nayi nisa na tsinci wasu kalmomi da suka fito daga bakinsa. ""Ni maraya ne, amma ina da gata. Na fuskanci cin amana tun ina yaro har zuwa yau da nake gabanki, duk cikin mutanen da suke zagaye da ni daga Kanin Mahaifina, sai Jasminah kanwata sune basu tab'a cutar da ni ba, sai Yar autarki. Ita ce bana gabanta. Tun fil azal haka."" Shiru yayi juyowa nayi ina kallon yadda ya sunkuyar da kai kasa. ""Bana zo nan akan ta koma aiki bane, na zo ne na bata hakuri akan abinda aka fada a kanta. Idan ma ina son lalata ai ba zan yi da ita ba domin ta fito daga gidan da yake da babban zaure, ita din fata ce da yakini."" Murmushi yayi sannan ya ci-gaba da cewa. ""Zata iya rubuta takardan barin aikin na gode da bani aronta."" Yadda Mama ta fahince shi kaf duniya babu wanda ya mishi irin wannan fahimtar. Amma tayi murmushi kafin ta ce mishi."" Zan barta na wani lokaci, na ga kamar kana da bukatar haka, amma ka ji tsoron Allah kada ka kara daukarta zuwa wata duniya, yanxu an daina kiwon dabba mutane ake kiwo, idan har na ga wani abu ba haka ba raina zai b'aci. Duk da ban san sunanka ba, amma kayi wani abu da na kasa fahimta, Auta ta kasa zama ta ga kana rokona. "" D'ago kai yayi yana kallon Mama jinjina kai tayi. Ta ce mishi."" Ban san wacce alaka ce a tdakaninku ba, amma"

"kuma naga ta kasa zama ta wuce sama da Yara, da kace kai Maraya ne ta tsaya cak, nasan wace ce ita. """

"Murmushi tayi ta cigaba da cewa."" Allah ya dafa mana! "" Tayi shiru, tana kallon Ya Ado, gyada mishi kai"

"tayi tana kallon Turaki da yake gabanta, tabbas idan har abinda Ado ya fada mata gaskiya ne, Yaron ya cancanci zama da Lubnah. ""Amma ya batun iyali!"" Shafa kai yayi yana murmushi, kafi ya ce. ""Na so wata yar Bauchi tace bata sona na mata kama da gardawa tun daga lokacin Daddah take karbo maganin aljanu sun aure ni."" Ai kuwa parlourn aka yi ta dariya, Mama ta ce mishi. ""Kuma yanzu baka da wacce tace tana sonka ai kai ba dai budurwa ko?"" Shafa kai yayi ya ce.. ""Mama na baki wuka da Nama ki nimo min wacce zata iya da tsufa."" Rike baki tayi tana faWin, ""ai kuwa zan iya cewa babu wata Y'a a gabana da na baka ita!"" Sosa kai yayi yana faWin. ""Ikon Allah, babu ko kanwar Lubnah ce."" ""Gaskiya bani da ita, Allah ya baka ta gari."" Ta yanke hiran, duk yadda ya so Mama ta yi mishi barin zance akan Lubnah amma fir taki, don shi har yau kallon matar aure yake mata, sai yayi shiru wurin karfe goma suka bar gidan, duk sun fita ina bakin kofar, ina kallonshi. D'ago kai yayi ya kalle ni na dauke kaina, ina jin Jasminah tana"

"cewa. ""Mama gobe ta zo aiki don Allah."" ""Ubangiji ya kai mu gobe lafiya!"""

Bayan tafiyarsu na riga su wucewa dakin Mama na kwanta da tazo dakin sai da tayi sallah shafa'i da

"wutir, bayan ya idar ne ta cigaba da addu'a. Har na fara barci ta ce min. ""Kina son Mai gidanki ne?"" Da wani sauri na tashi zaune ina zare idanu. Kirjina yana bugawa da karfi. Murmushi tayi ta ce min. ""Eh kina son shi Lubnah."" ""A'a wallahi Mama, ni ba wannan a tsakaninmu idan ma ya gaya miki wallahi karya ce."" Hannu ta kai bakina ta rufe. ""Bai gaya min haka ba, amma ni naga haka a tattare da ke, ni Uwa ce kuma dole na fahimci haka amma tunda kin ce bakya sonshi ai shi kenan amma ki sani kafin Azumin baWi ina son ganin mijin aurenki don Allah na baki wannan lokacin ne domin ki samu wanda ya dace da ke, amma ni idan har zaki dauki shawarata wannan mutumin yana bu™atarki sosai. Yana sonki yana kuma girmamaki!"" Murmushi tayi. Sannan ta kwanta kamar nayi kuka haka na ji maganarta taya zata ce yana"

"sona bayan kuwa ba wani mutumci muke ba, haka na kwanta sai na kada barci nayi ta juyi."

"Tun ranar da Mama ta ce tana son ganin Turaki, Ya ado ya zauna ya mata bayani da rokon da Alhaji"

"ELYakub ya roko da kada ya nuna mishi Lubnah bata da aure yin haka zai haifar da daukar kome fa zafi, a haka ya dauka tana da auren in sha Allah akwai jarabawar da yake akan Bilal din yayi nasara da kanshi zai nima mishi auren Lubnah, sai dai a yanzu baya son ya san cewa bata da aure ne. Tun ranar da ya ga CV dinta yake ta fada mishi ta dawo aiki, amma kasancewar shi mai takatsantsa a rayuwarshi yasa yaki nuna ita ce daga Alhaji ELYakub sai kawunsa suka san ita ce, shi yasa da girmamawa suke kara bibiyar lamarin. Duk sun san bata da aure shi Waya suka bari a baya. Murmushi Mama tayi ba mamaki Addu'arta ne Allah ya amsa ya bata mijin maraniya, mijinta ita Waya mijin da kafin a ce wata ta samu irinsa zata wahala, murmushi Mama tayi tare da sujada Allah ya bashi ikon cinye jarabawar da Alhaji ELYakub ya ke mishi."

"Sai ga Mama ta kasa barci juyi kadan ta kalli Autarta tausayi da soyayya take ji akanta, kamar ta mai da"

"ta ciki, tasan rokon da yake mata ba rokon ta koma aiki ba, ja'iri miskilin banza."

***

"A bangaren Turaki kwana yayi yana juyi, karshe sai da ya tafi sallah dare, a jingine da gadon yayi barci."

"Yana me jin kamar gari ya waye ya ganshi a office duk baya jin dadi amma haka bai haka shi jin wannan karsashin ba, washi gari da safe da wuri ya tashi likitan yazo ya mishi allura da bashi magani ya sha ya"

"shirya sai da ya ga Yaran Jasminah sun tafi makaranta sannan ya tattara ya wuce office, shi da Taj."

"Idanunsa a lumshe yana jin Taj yayi horn, ajiyar zuciya ya sauke domin yasan ita ce kawai Taj zai yiwa Horn haka, tsayawa yayi."

Duk da saurin da nake domin garin nan bai rabuwa da ruwan sama. Don hadari ne a narke a sama Taj

"yayi min horn, na san shi da ogansa ne sai na Wan matsa gefe har ya tsaya. Sauke glass yayi ya ce min. ""Shigo mana!"" Shiga nayi ina faWin. ""Amma kun yi sauri ko?"" Gyada kai yayi yana faWin., ""short cut na bi."" ""Ayya!"" Muka cigaba da tafiya, ""Baki san Oga bai da lafiya ba ne?"" Juyawa nayi na kalle shi tare da cewa. ""Ya jiki?"" Banza yayi min wannan mutumin anya aljanu basu kanshi. Haka muka isa kamfanin zan dauki jakarshi ya dauke abinsa, sake baki nayi ina kallon ya cigaba da tafiya a hankali ba bi shi da idanun, sai nake ganin kamar na san wani da yake irin wannan tafiya da jimawa, juya kaina nayi tare da son tuno a ina nasan me irin wannan tafiyar? Ganin zan bawa kaina wahala amma kuma ina fara tafiya, naji gabana yana wani irin bugawa d'ago kai nayi ina kallonshi ya juyo yana kallona. Nima shi nake kallo, akwai wani alaka da ya tab'a faruwa a tsakaninmu da shi ne? A ina na tab'a ganinshi, zuciyata tana wani irin bugawa, idanunshi cikin nawa. Sunkuyar da kai nayi tare da rike jakata da kyau. Jikina yana rawa, wani irin kuka nake son nayi wanda ban san dalilin ba, kuka ne wanda nake ji kamar nayi kewar wani ko wata a"

"rayuwata da jima, nayi kewar wanda ban sani ba waye shi hawaye suka shiga zubo min da gudu........."

"*DIJAH BORNO, Zully da Naj, ayi hakuri sai yanzu ku yi maneji yau na ci uwar sabada da aiki ne.*"

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 58"

"Zuba min idanu yayi ganin har zuwa lokacin ina tsaye. ""Taj ka shigo da ita ta daina wannan shirmen!"" Ya"

"fada yana me nufar cikin kamfanin, zuwan Taj ya tsaya a gefena."" Me ya faru kuma?"" Da sauri na goge hawayen da yake ta zuba na ce mlshi. "" Ba kome"" muka shiga cikin kamfanin, a tunanina yadda ya je har gidan mu yayi bikona. Zai zama me yawan min uzuri, sai dai wannan me shafar aljanun ba haka yake ba, an jima zai birkice an jima zai dawo kamar bashi ba, tun da na fahimci yana da matsalar ™wa™walwa, wanda yake birkita mishi lissafi. Sai na mishi uzuri domin irin wannan halinsa ba iya ni kaWai ba kowa ma tsoronsa yake, a cikin wata biyu da nayi ya kori mutane a cikinsu kuwa har da shugabar gudanarwa na kamfanin sai ya fara bani tsoro. Shugaban gudanarwa, kwashe wasu abubuwan yayi fa akan lallai sai na zo office dinsa nayi wasu cike-cike. Gudun matsala na tafi nayi, sai da na je na ga mutumin bai da kirki sam, domin na fara aikin kenan ya taso ya fara ™o™arin yi min iskanci, kamar wanda aka jefo shi ya daki kofar sai da ta buWe. Ganin yadda razana domin nima na dauki wani bokitin zuba datti, ina ™o™arin kare kaina, sai gashi nan ya zo. Ajiyar zuciya na sauke me nauyi, tare da sake bokitin a kasa. ""Na kore ka!"" Ya fada yana me juyawa na rufa mishi ba, sai da muka isa office Winsa ya zuba min idanu. Ya rasa me yasa kome yake zuwa a haka, na farko ba shigar banza take ba, na biyu bata cika shiga harkan kowa ba abinda yake gabanta ya ishe ta, amma ya rasa me yasa kome yake zuwa kamar an tsara shine. ""Da ba gaya min ba haka zaki zauna ya wulakanta ki?"" Kaina a kasa, na ce mishi. ""Allah ya fishi."" ""Abinda nake son na fahimta kenan, je ki."" Haka na juya na fita, haka muka cigaba da aikin da dad'i ba dad'i ga Airah da ta"

"saka ni gaba duk abinda zan yi ban iya ba, kai da ta ishe ni ce mata nayi. ""Ki fita harkata tunda bana shiga"

"rayuwarki, ban ga dalilin da zaki shiga rayuwata ba."" Iya wannan na gaya mata na cigaba da abinda yake"

"gabana, wani abin da yake ™ara bani mamaki, duk yadda za a kai mishi magana baya bi ta kai."

"Ranar wata juma'a, ina zaune ciwon ciki ya dame ni. BakiWaya na kasa sakewa dan abu kaWan haushi"

"yake ba ni. Fitowa yayi ya ga na kifa kaina da table din, fita yayi can bayan minti goma sai ga Jasminah. Office dinta muka je, ta haWa ruwan dumi a gora, saboda na gaya mata gaskiya abinda yake damuna, ina kwance ta kawo min tare da cewa. ""Dan saka akan maranki zaki ji sauki!"" Haka nayi ta sakawa ina murzawa har barci yayi gaba da ni, hayaniyar Ubaid na ji yasa na bude idanuna a tsaye yake a kaina.. ""zaki yi danasanin show up da kika yi a wannan lokacin, idan har ba da wata manufa kike bibiyar Turaki ba ki ajiye aikin ki kama gabanki."" Murmushi nayi na ce mishi. ""Ban san me kake nufi ba, ban san me"

"yasa kake bibiyata da fitina ba, ka yi tunani idan kanwarka ce fa.?"""

"""Kanwata Allah ya mata tsari da irin rayuwarki, bari na gaya miki kowa yasan kina juya mishi tunani ne,"

"lokacin da ya so ki, ai cewa kika yi ba zaki auri mai zubin Gardawa ba, yau kin san waye shi shine bari ki kashe aurenki!"" Ji nayi zuciyata tayi wani irin bugawa kamar nayi kuka. ""Ban fahimci me kake nufi ba?"" Na tambaye shi a rud'e. ""Ubaid me kake aikatawa ne haka?"" ""Bari na gaya mata Jasminah ta sani ba ita Waya ba ce kowa ma yasan yadda take juya mishi tunani, Malamin da ya dauke ku Physic daga 1-2 kika ce kin samu wanda ya fi shi kudi shine wannan, mayyar kudi, kudin wancan mijin naki ya kare ne?"" Tass na wanke shi da mari wanda yayi daidai da shigowarsa, shima ya d'aga hannunshi, amma ya rike hannun yana faWin. ""Me ka zo yi a kamfanina? Ba nace kada na kara ganinka ba?"" Ya janyo shi waje. Murmushi yayi ya ce mishi. ""Wallahi tunda ta mare ni sai ka Sattar da ita."" ""Idan ka fasa ka rena wanda ya halicce ka, tab'ata daidai yake da. Nihla!"" Wani naushi ya kaiwa Bilal shi kuwa ya kauce fada ya rutsa a tsakaninsu, kamar Yara dambe. Zama nayi dirshan nayi na zubawa kasa idanu, sai a lokacin abubuwan da suke ya faruwa ya dawo kaina, jin ihun Jasminah ya sani fitowa kamar wacce ruwa ya yiwa duka, na kai hannu a hankali dafa kafad'arshi na ce mishi. ""Ka bar fadar nan don Allah!"" Sake Ubaid yayi shi kuwa ya kai mishi naushi, ai kuwa akan fuskarshi ya same shi, sai da glass dinsa ya fadi, zai rama na shiga tsakaninsu tare da tallafo fuskarshi.. ""kalle ni ya isa haka, ni ce matsalarka? Ka yi hakuri zan bar aikin ka ji ka yi hakuri kada ka kara fada a kaina don Allah!"" Na mika mishi glass dinsa ina kallon yadda yake jin kamar zai tashi sama. ""Muje ka saka maka magani!"" Jasminah ta ja hannunsa har office ni kuma na hada kayana, na bar office din ina fitowa na ga yadda ake kallona. Sai naji wani irin abu ya tsaya min a rai,na iso gida na samu Mama sai lokacin na fashe da mata da kuka, na zauna a gabanta ina kuka kamar raina zai fita, rike hannuna tayi tana faWin. ""Me ya faru?"" ""Mama dama shine Malamin da ya tab'a cewa yana sona a Bauchi? Mama me yasa ya boye min? Mama me yasa yake faWa da kowa a kaina? Mama me yasa"

"na kasa tuna shi sai yanzu?"""

"Murmushi tayi ta ce min. ""Yana sonki ne shi yasa yake faWa akanki, yana sonki ne yasa ya zame miki"

"izuwa yana sonki ne yasa yake bayyanawa duniya akanki zai tari aradu da fadin kai, yana sonki ne yasa yake faWa da kowa yake yaki da kowa saboda kada ya rasa ki, a yanzu da bai san kina da aure ko baki da aure ba, ya iya kare kimarki ki yi lissafin idan aka ce yasan baki auren kowa akanki. Tow ba makawa sai"

"yadda karfinsa ya ™are, shi wannan da gaske yake sonki ba cutar dake zai yi ba. """

""" Yan uwansa basu sona!"" Na fada ina kuka,"" akan me zasu su so ki?"""

"""Mama ya fi karfina, Mama danginsa wasu irin dangine, na masifa Mama ba zan iya bude mishi"

"zuciyata ba, Mama ban tab'a sonshi ba tun farko a yau ma ina kara fada kamar farko bana sonshi."" Murmushi Mama tayi ta ce min. ""Nasan ai zuciyarki a rufe take shi yasa kika ki yarda ko kalli kowani mutum da sunan soyayya, amma ba zan boye miki ba, kina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login