Follow us on social media

Showing 24001 words to 27000 words out of 140751 words

Chapter 9 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

296

zaune ya ce min. ""Uban waye zai miki aikin da kika fara? Kin ga Lubnah bana son iskanci da renin wayo, wallahi zan tattaka ki, zaki fita ko sai na zane ki, ga ki katuwa amma kanki babu ™wa™walwa!"" Ba yau ya saba duka na ba, sannan ba yau ce zai daina ba. Tsoron dukan da yake fadar zai yi yasa na mike ina faWin. ""Kayi hakuri!"" A duk lokacin da yazo ya fara wannan masifar ya tsani yayi"

"magana nayi shiru, idan ban bashi hakuri ba marina zai ta yi. Har sai na bashi hakuri...."

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

TARA

"Haka na fito na karasa aikin, ina kuka na gaji na gaji da abinda yake min, a hankali na gama na koma daki."

"Yanayin ba dad'i, ko nace ni ce bana jin dad'insa. Ana haka bikin yar gidan Aunty Hindatu da aka saka ana d'agawa ya taso saboda mijin ba a kasar yake ba, haka yasa aka saka bikin karshen wata June, tun daga kan kayan da zamu saka da kome Yayuna suka min, har lokacin Mama da Yadiko babu wanda yake shiga"

"harkata tow ba ma damuwa suka yi da ni ba, idan bani na kira ba tow da babu wanda zai kira ni a cikinsu."

"Bikin Maamah yar Aunty Hindatu da za ayi ya saka na dan samu yanci, domin Ya Ado ya kira Ya Hafiz ya"

"gaya masa batun bikin da niman alfarman nazo ayi kome da ni, yadda yasan halin Ya Ado bai da sauki yasa bai yi musu ba, shima Ya Ado zai zo da Yaransa."

*

Yau da wuri Umar ya bar muda lawan kasancewar mashin suke sayarwa shi a bangarenshi amma yana

"aiki da ma'aikatan shige da ficen jahar Bauchi. Yana kokarin hawa motar shi wani magidanci ya ce mishi. ""Malam Umar ko?"" ""Eh nine lafiya?"" ""Hmm dama ina son na tambaye ka ne? Ya kuke da matar Alhaji Hafiz ne?"" ""Eh kanwata ce!"" ""Tow gaskiya ku sayi likkafanin da zaku lullubeta idan ta mutu, ni shawara da zan baka kenan idan kun so ku tsaya mata idan kun so ku barta ta cigaba da mutuwar tsaye!"" Daga"

haka mutumin ya tsare abin hawa ya bar wurin.

"Da wannan tunanin ya iso gida, ya sami Maman Aunty matarshi ya bata labari. ""Ba tuntuni ake gaya"

"muku ba, sau nawa ina baki a gidan nan bayan mun gaisa zasu ce don Allah idan ina da yadda zan yi na kaiwa Lubnah Wauki."""

"Haka suka ta tattaunawa da fadar ko da zasu wani abu su Mama ba zasu bari ba, shi yasa kowa yake"

shakkar shiga rigimar. Haka suka yi ta tattaunawa a tsakanin al'amarin.

*

"Haka bikin ya karaso aka fara hidimar biki babu ji babu gani, kullum xan je kuma Ya Sani shi yake kawo ni"

"har gida, domin Ya Hafiz ya hana ni kwana. Ranar daurin aure ina ta shirin fita da yake ita ranar ta gama wuninta, tunda asuba nake aikin gidana har na gama da wuri Ya Hafiz ya tambayi Karimah ta ce ba zata ba, haka yasa na gama shirina da wuri, wurin karfe tara na fito ba sai ga Karima ba. "" Zan je bikin fa! "" "" Tow don Allah ki hanzarta! "" Na fada ina kallon agogon hannuna. Tunda Karimah ta shiga daki ta manta da ni sai da na kara mata magana wasa wasa bamu bar gidan ba dai karfe biyu da wani abu. Kamar nayi kuka da gayya tayi haka sai dariyar mugunta take min, Ni dai ban kula ta ba. Har muka isa gidan da ya"

cika da mutane.

"Muna shiga cikin gidan Aunty Hindatu ta watsa min harara tana faWin. ""Wai ke me yasa baki kome da"

"jikinki? Kullum zaki zo sai kin makara."" Zan amsa caran Karima ta ce musu..""jiki duk tarin kitse taya zata"

"yi sauri? Ai kun san Habibi yana kokari ko?"" Wani hade rai Aunty Innah tayi tana kallonta cikin haWe giran"

"sama da kasa ta ce mata..""An kasa dake ne?"" Da sauri na cewa Aunty Innah..""Inna uwa maba da mama bata yi karya ba, jikin nan damuna yake ni kaina da ina da hanyar rage shi da na rage, gaskiya ta fada!"" Duk da na gama aikin gidan da wuri ita ta makarar da mu. A hankali na wuce bayan na fadi haka na barta nan kunya da yadda sauran yan uwana da yan uwan Ya Hafiz suka mata ca, Mama tana jin su bata amsa ba amma kuma zuwa yanzu ta fara jin kamar akwai abinda suke ™o™arin aikatawa. Dakin Aunty Hindatu nayi na zauna can kuryan gadonta. Shigowa Aunty Nana tayi ta ce min. ""Ke kullum aka yi magana sai ki nuna babu kome, Alhamdulillahi tunda ba kome amma ki sani Ubangiji yana madakata!"" Ta fada min tana wani dauke kai Aunty Nana Yayar Ya Hafiz ce, kuma na hannun damanta uwa uba Karima kanwar Mijinta ne, murmushi nayi na de mata. ""Kiyi hakuri wallahi ni ce na makarar damu kamar yadda ta faWa!"" Na fada mata kamar xan yi kuka. Tsaki tayi ta bar dakin Yaya Asabe da take alolan a ban daki ta fito tana faWin.."" Lubabatu ba zaki daina cutar da kanki ba?"" Washe mata hakori nayi ina faWin "" ba kome fa"" ""da kome mana, na akanki aka fara aure ne Lubabatu meke faruwa a gidanki"" dariya na fara mata, dariya irin wanda kana gani kasan ba lafiya ba, na ce mata..""ba kome wallahi!"" Shiru tayi tana kallon yadda na koma na yi shiru. Ina murmushi. Ina zaune Aunty Hindatu ta kawo min kayan anko dinmu da su, na saka na fito Was da ni. Kowacce ta saka sarkan gwal dinta ni dai bani da shi sai wata fashion da na saka Aunty Munah ta ce min. ""Lulu ina gwal Winki?"" Da yake iya mune a dakin. Zare idanun nayi ina kallonsu. ""Ina gwal Winki?"" Aunty Innah ta kara jefa min tambayar bakina yana rawa nace musu. ""Na sayar da shi?!"" Wani katon salati suka saka tare da zaro idanu. ""Karya kike munafuka gaya min gaskiya ko naci ubanki ina kika kai sarkokin gwal Winki!"" Shiru nayi naki magana, shigowar Yadiko dakin ta ji suna sake tambaya ta ina na kai sarkan gwala-gwalai na. ""Na sayar nace!"" ""Me kika yi da shi Lubabatuna."" ""Inji Goggo alti Yayarsu Baba mace ce mai fahimta da sanin ya kamata, tana da zurfin ilimin addini sosai. Ta ce gaya min. ""Gaya min ina kika kai sarkokin gwal Winki!"" Jikina ne ya dauki rawa. Nace musu. ""Goggo na sayar!"" Wani irin mari Mama ta kifa min sai da na ga haske, na rintsa idanuna bakina yana rawa nace mata. ""Na sayar da su!"" Shiru dakin ya Wauka haka aka bar zancen amma ran Mama ya b'aci. ""Kome kin sayar gidanki, kin sayar kome kin sayar shi yasa kudin Umaranki na shekara biyu na ce kada a baki don baki da hankali!"" Ni dai ban ce musu kome ba. Bayan mun gama muka fito waje, muka bar Goggo Alti da Goggo Uwani sai Yadiko da Mama.. ""Salamatu ina jan hankalinki da ki tashi akan Yarki, wallahi yarinyar nan tana bukatar"

"wani a tare da ita, ni dai bana zargi amma yarinyar ko baki kika mata iya ka kenan."""

"Haka muka sha hidimar bikin sannan aka shiga hadadar kai Amarya dama ban saka kaina ba, haka na"

shirya muka tattaro muka dawo gida ashe akwai buhun bala'in da yake jirana. Tunda muka shiga gidan Ya Hafiz yake Bala'i da fada zagi da cin mutuncina har sai da nayi kuka.

"""Ke gaki mai yan uwa har zasu tsare ta da magana suna gaya mata abinda ransu yaso, don na rufa miki"

"asiri na zauna dake haka na kuma zauna da wannan fuskar naki mai kama da ta giwar zasu zagar min Mata wallahi sai na sake ki,.na rantse da Allah idan na sake ki ba zaki tab'a samun wanda zai aure ki ba wallahi billahi azmin, wannan tarin jikin naki mugu da shi kamar kashi."""

"""Kayi hakuri!"""

"""Hakurin Uban me kike ba ni? Bayan kaf duniya babu mummuna irinki, ga baki ga muni ga munin hali da"

"na halitta, ina kallonki gani nake kamar zan mutu don takaici!"""

"Kaina a sunkuye ya gama zagina na ce kuma ce mishi. ""Kayi hakuri na gode sosai, Allah ya baka"

"hakuri."""

"""Don na rufa miki asiri ina zauna dake zaki ci mutumcin matata!"" ""Kayi hakuri ba zan kara ba!"""

"""Kina nan tibi-tibi sai kace aladiya!"" ""Na gode sosai!"""

"""In ba don ina kunya Mama da Baban Bauchi ba wallahi da na sake ki, domin ya gaya min duk ranar da"

"na sake ki sai dai ki nime wani uban ba dai shi ba."". ""Kayi hakuri ba zan kara ba."""

"Na fito ina murmushi, abubuwa dayawa sun boya a bayan murmushi na, kuka da ihu sun boya a bayan"

"fuskana, amma haka na share na manta da kamar ba ayi ba. A tunani na zancen ya kare, sai dai a wurin Karamcy bai kare ba, domin kuwa bori ta saka mishi a kan sai ya min duka shine zata huce. Ya rasa yadda zai yi da ita kuma yasan matu™ar ta fara fushin nan zai zame mishi tashin hankali, don haka ya fito ya tsaya bakin kofar dakina yana faWin. ""Ke Jaka fito ki bata hakuri!"" Wani hakuri kuma? Kawai daurewa"

nayi na fito waje ya ce min muje ki durkusa ki bata hakuri..

"""Ni dai gaskiya ba zan durkusa ba domin hakuri kan xan mata amma ban da durkusawa."" Dama kamar"

jira yake kawai ya rufe ni da duka. Duka sosai sai da makota Baban Na'ilah da Na'ima tare da basu Boy suka shigo gidan dakyar ai kwace ni a hannunsa. Tunda na shiga dakina na rufe na kwana ina kuka.

"Washi gari naki fitowa na daura abin karyawa haka ya gama barazanarshi ya fita, yana fita nima na dauki"

"hanya na nufi gidan. Ashe ina fita Karimah ta kira shi ta gaya masa gani nan na fita. Idan nace ban daku ba nayi karya, haka yasa na kwaso jiki na kawo ™ara, sai dai ban kai ga isa gidan ba Ya Hafiz ya kira Baba ya gaya mishi karya da gaskiya, ina isa gida Mama da Yadiko suka fatattake ni, akan na koma, don ba zan kashe musu aure ba, Baba yace musu duk wacce na zauna a wurinta a bakin aurenta, wannan ya bawa Ya Hafiz lasisin mai da ni jakarshi da zaran nayi laifi zai rufe ni da duka, wanda ya cusa min tsoro da"

"tashin hankali, wannan dukar da zalinci yasa ni jin dole na rayu ko don na rabu da Ya Hafiz, na gaji."

"Kaf yayuna aka rasa wanda zai tsaya min, Maman Na'ilah kaWai ta bani shawarar na fara niman zabin"

"Allah, idan da alkhairi a zamanmu Allah ya shiga lamarin idan babu shawara daya ne, na kai shi kotu a raba auren domin idan aka cigaba da irin wannan zaman karshe daya zai iya rasa rayuwarsa. Haka na dukufa da azumi da addu'a sallah dare da sadaka. Sai da na shafe wata hudu cib har zuwa lokacin ba wai ina da nutsuwa bane, sai dai na ji n koma baya na saurari karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i, duk da zuciyata bata yarda da abinda nake nufi ba, amma ni a kaina na gaji, ni a karan kaina ina son na rabu da shi, ina son na bashi iska ko zai gane yadda nake ji, duk wannan lokacin Ya Hafiz bai tab'a nuna yayi nadamar abinda yake aikatawa ba, kai hatta Yaransa suka yi kuka da ni zai min dukar da dai na tsani kaina. Duk wannan abin da yake faruwa kowa yana jin takaici amma ba yadda suka iya tunda ni ban ga hanyar fita ba, bani da wata madogara, sannan ba ni da wata makama, haka yasa na zubawa sarautar"

Allah idanu.

"A cikin wannan ukubar na samu Maman Na'ilah da Na'ima na ce mata.. ""Don Allah ina son kudin nan"

"zan samu, idan ba xan samu ba ki barshi kawai!"" ""In sha Allah zaki samu yanzu ma kuwa!"" Mikewa tayi ta shiga can cikin dakinta, ta janyo abu a kasan gadonta, ta ce min. ""Lubnah shigo mana!"" Mikawa nayi na shiga cikin dakin, ta ciro wata akwatin katako, ta fita tare da dauko wuka ta fasa kan akwatin katako, sai da ta fasa saman sannan ta saka hannu ta bude shi da kyau, kafin ta kalle ni tana faWin. ""Gashi nan ki zazzage shi!"" ˜asa kai hannuna nayi ita da kanta ta zazzage shi tas a gabana. Tow me zanyi da kudin"

nan?...............

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

GOMA

Wannan shine abinda na tambayi kaina me zanyi da kuWin? A hankali na ji zuciyata bata amince min da

"abinda nake shirin ba nace mata. ""Maman Na'ilah ki bar kudin tunda na ga yadda suke!"" Na juya zan fita ta riko hannuna. ""Me yasa kuma Lubnah?"" Murmushi yake na mata. ""Tow me zanyi da shi?"" Yadda nayi maganar sai ita kanta abin ya dame ta, ta zata ko ina zarginta ne ta ce min. ""Wallahi summa tallahi babu kwandala naki da na."" ""Har abada bana zarginki kuma ba zan tab'a zarginki ba, kawai bani da abinda zan"

"yi da shi ne."" Daga haka na bar gidan."

"Na dawo na samu Karimah da Yaranta da wata kawarta suna ta hira, yadda nayi sallama basu amsa ba"

"haka nima ban ce musu uffan ba na wuce dakina, tunda na shiga na zauna bakiWaya naji duniyar tayi min kunci, ko na rabu da Ya Hafiz Iyayena ba zasu tab'a karbana ba. Sai naji bakiWaya duniyar ta juya min baya, bakiWaya duniyar kamar ni daya ce mata amfani a cikinsu, haka nayi ta jin kamar zan mutu. Ina zaune a dakin naji sallamarshi, ban d'aga kai ba ya shigo yana faWin. ""Wani wacce irin iskanci ne da ba zaki yi abinci a gidan ba?"" A da ina ina ya Hafiz zai sauya amma by now sai nake ganin kamar har abada ba zai sauya ba. ""Bakya ji ina miki magana ne?"" ""Me kace?"" Na faWa ina kallonshi. Fita yayi daga dakin ina jin shi yana ta b'ab'atu, kiran sallah azhar yasa na fita nayi alwala na dawo dakin nayi sallah, can sai gashi"

da kaya niki-niki a leda har da kayan abinci ya saka a kofar dakina ya fita yayi ya shigo da abincin tunda

"na ga haka na fahimci wata ya shirya min, don haka ina zaune ya kawo min takeaway, kamar ba zan"

"amsa ba na amsa na ajiye na ce mishi. ""Nagode"" na cigaba da addu'ar da nake, can bayan ya fita na shafa,. Sannan na ja ledar abinci ne mai kyau, dauka nayi na fara ci a lokacin ya fara shigo da kayan abincin, yana zubawa a bayan kofana. Ni dai ban ce mishi cikanka ba balle har ya dauka ko na damu da shi ne, zama yayi yana min murmushin mugunta, ban bi ta kanshi ba ya mike ya fita, haka na gama na fita da ledar da robar na kai waje, sannan na dawo dakina bayan na wanke bakina. Tunda na shigo naji kamar jikina yana sakewa a daddafe nayi sallah Asr, a wurin dai na cigaba da zama ko kwanciya nayi"

Allah shine masanin.

"Ashe kwanakina hudu me kyau a gadon asibiti, sai ranar na hudun na farka. Naga hannuna daure da"

"abin karin ruwa, kamshin abin wanke asibiti ya tabbatar min da asibitin nake, a hankali na yi yunkurin mikewa zaune domin ina jin kamar maganar mutane sama sama, na ji kamar an mai da ni baya, bude idanu nayi a buge amma ban san waye a kaina ba can can naji ana cewa. ""Koma ki kwanta!"" Haka na kara komawa na kwanta tare da lumshe idanuna, ban kara budewa ba sai washi gari da misalin karfe biyu na rana naji Muryan Ya Ado, a hankali na kara mike jikina duk ciwo yake min. ""Sannu Lubnah!"" Inji Umma Kanwar Mama wacce take aure a azare, lumshe idanuna nayi na kara budewa akanta, ta mike da sauri ta shiga ™o™arin taimaka min na zauna ina sauke wani irin numfashi kamar mai cutar asthma."

"Kallona Ya Ado yayi a hankali ya ce min. ""Ina ke miki ciwo?"" Girgiza kai nayi alamar babu. ""Sannu ko."" Ya ce min haka ta rike hannuna muka tafi ban daki ta haWa min ruwan wanka nayi da ruwa me zafi, sannan na hada da alwala na fito na zauna a bakin gadon fita Ya Ado yayi ya bamu damar sauya kayana. Bayan na sauya na gabatar da salolin da suke kaina, ina idarwa Umma ta zuba min tea me zafi a daidai shigowar Ya Ado da Ya Umar, sai Albashir da Ya Tahir, Ya Sani, ba Ya Ubaidullahi da Ya Mustapha, suna shigowa Aunty Hindatu da Aunty Innah suka shigo, zama suka yi akan kafet, ina cin abinci a hankali."

"Hiransu suke na abin da ya shafe su bayan na gama na shiga ban daki na wanke hannuna da bakina. ""Barista ina ga mu bar maganar nan sai anyi la'asar ko kada mu fara mu katse saura minti goma a shiga sallah! "" Inji Ya Tahir, ""Ok Malam muje ko!"" Kallonsu nayi suma kallona suke yi. "" Kina son wani abu ne Auta? "" Inji Ya Sani, "" A'a bana son kome!"" Nayi shiru suma basu fita ba Ya Umar ya ce min.."" kina son tambayar wani abu ne?"" Yadda yayi min maganar a tausashe yasa na ce mishi. "" Me ya faru na ganni a nan?"" "" Baki da lafiya ne!"" Kallonsu nayi kafin na ce musu. "" Na fara hauka ko? "" Idanuna ya cika da kwalla, fita suka yi na hango tausayi a idanunsu, a for the first time da na hango yarda da aminci a tattare da su, bayan fitarsu Aunty Hindatu ta mike tare da alwala tazo tayi sallah, Umma ma haka, nima a zaune nayi sallah saboda yadda nake jin jiri. Tunda na idar da sallah nayi shiru, maganar gaskiya ko addu'a a yanzu na rasa ta me zanyi, ta rokon Allah ya saka ya Hafiz ya sake ni ne ko ta nimawa kaina mafita ne, shigowar Yan mazan ne yasa ni kallonsu, tare da Yadiko wacce take tsakiyarsu, shigowa suka yi Umma ta ce mata. ""Ina Yaya Salamatu? Yau kwanaki biyar yarinyar nan tana asibiti bata leko ba?"

"Wallahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login