Follow us on social media

Showing 126001 words to 129000 words out of 140751 words

Chapter 43 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

320

bar kamfanin nan ka ji na rantse!"" Kasa magana nayi na kalle shi, ""sir su bar aikin saboda ni?"" Na fada bakina yana rawa, a fusace ya juya tare da cewa. ""Kema na dakatar da ke. Tunda dambe kika zo yi a kamfanin."" Kafin ya rufe baki na hada kayana, na bar office. A ranshi kuwa haka yake son ganin mace, ba kamar sauran kamar mayyu sai hakuri suke bashi ba. Ina barin wurin shima ya wuce office Winsa, Ni kan ba zan iya wannan halinsa ba, misalin uku da rabi na isa gida na huta ban gaya musu"

me ya faru ba.

Ina samun kaina na kashe wayata su je can da kamfaninsu me shegen matsalar tsiya. Daga nan na

rufe babinsa in sha Allah ranar Monday zan rubuta takardan barin aiki.

**

"Yana tashi don masifa bai wuce gida ba, ya nufi gidan Hajiya Samirah kumo yayiwa yarta duka, sannan ya"

"dawo ya samu Badr itama yayi mata dukar har da ji mata ciwo a hannu, Mimi ma bai kyaleta ba, domin kamar wanda ya sha kwaya haka yake jinsa. Duk yadda Alhaji ELYakub ya so boye b'acin ransa sai da ya yi magana tare da nuna mishi kuskuren da yake aikatawa ai ba a haka, dama already Ubaid ya jima da nuna adawarshi a fili, Uncle Auta ne ya goyi bayansa har ya ce bai ga laifin abinda yayi ba ai ya musu warning me ya kai su wutinsa? Jin haka yasa shi shima yayi zuciya ya bar gidan, kai hatta kamfanin fushi"

yayi ya daina zuwa aikin.

---

"Yau kwana uku kenan da aka dakatar da ni, na rasa yadda zan gayawa Ya Ado, ina Gym na zurfaffa"

"tunanina sai jin wayata tayi ™ara, dauka nayi na ga alart har na dubu dari uku da hamsin an saka salary,"

"daga KPAN, mamaki nayi albashina na farko kiran Mama nayi na gaya mata ta ce na kira Ya ado na gaya mishi, nace idan na koma gida zan gaya mishi, haka kuwa aka yi ina komawa gida na nunawa Ya Ado shi"

"kuma ya karbi kudin ya turawa Mama dukka, ya tura min dubu hamsin ya ce min. ""Wannan ni na baki,"

"wancan kuma a bar mata tayi yadda take so da shi."" Murmushi nayi ina faWin. ""Allah ya kara budi."""

"Ranar wuni nayi cikin farin ciki, washi gari da safe ina motsa jiki a parlourn aka buga gidan da kaina na"

"fita na duba, Jasminah ce. ""Laa aunty kece!"" ""Eh gani nan sauri nake, don Allah ki taimaka mana Oganki yau kwanansa kusan hudu baya nan baya zuwa office ko zaki tab'a mana shi a waya!"" Sosa kai nayi ina yake nace mata. ""Aunty bani da number shi?"" Zare idanu tayi nima abin sai nayi ya min wani iri, shiga motarta tayi ta rubuta min number ta bani tana faWin. ""Don Allah ki taimaka mana!"" ""In sha Allah!"" Sannan ta juya abinta, ni kuma na shiga cikin gidan ina tunanin yadda xan kira shi. Tow me ya faru da ya bar gida? Mutum sai kace mai aljanu. Parlourn na shiga na zauna ina tunanin, kafin na haura sama."

"Wayata na dauka nayi shiru ina ta tunanin yadda xan kira shi, a hankali na saka number nayi shahadar kuda na kira Number, har ya gama ya tsinke bai dauka ba, haka na kira bai dauka ba, sai da nayi kira na uku sai gashi ya Wauka. Muryanshi very calm kamar bai san me yake faruwa ba. Na ce mishi. ""Dama na ga sakon kudi ne jiya!"" Sai nayi shiru can na cigaba da cewa. ""Dama ina son nayi submit takardan barin aikina ne."" Na kashe wayar, ina kashewa kuwa ya biyo kiran. ""Me aka miki zaki bar aikin?"" Kashe wayar nayi bakiWaya, na sauke ajiyar zuciya ina kallon wayar da nayi switch up dinsa, ina zaune a wurin Adil ya shigo da gudu yana haki. ""Aunty Lulu ki zo kin yi bako!""zare idanun nayi na ce mishi. ""Baba gaya min waye?"" ""Wannan wanda Abba ya ce oganki ne!"" ""Shi kenan!"" Na fada a raina, kafin na saka jalbab na sauko kasa, ina jin wani abu yana yawo a kaina. Wucewa kitchen nayi na dauko kunun aya da sauran breakfast din da aka yi na dumama masa ce fa sauce din kodar saniya, na kawo mishi a hankali na jera mishi. Sannan na ce mishi ""ka kaci!"" Ba musu ya saka sannu ya fara cin masar da yake miyar da dan yaji tari ya fara na bude mishi kunun aya na zuba mishi ya sha, sannan ya kalle ni, kafin ya ajiye ya cigaba da cin masar, har zuwa lokacin bai ce min uffan ba, nima kuma ban ce mishi ba kaina a sunkuye, nayi mamakin da yaci abincin sosai, ya ce min ya koshi, na tattara kayan na kai kitchen, na dawo na zauna a can gefe. Shiru muka yi kafin ya ce min. ""Gobe ki dawo aiki!"" ""Tow Allah ya kai mu!"" ""Amin Ya Allah!"" Daga haka ya mike zai fita ya ce min. ""Yaranki nawa? Mijinki yana ina?"" Bai tsaya jiran amsata ba yayi"

"gaba abinsa, wannan dan renin hankalin, shi kuma haka yake rayuwa kamar me aljanu."

"Bayan tafiyarshi Ya Ado ya fara zolayata, ""wato Lubna baki da mutunci, don kina son ganinsa shine"

"kika kira shi."" ""Ni wallahi ba kiran shi nayi ba!"" Na fada ina tura baki, dariya yayi suka yi ta tsokanata."

Washi gari.

"Na same shi a office din ne. Ga sabbin ma'aikata, da gaske koran wadancan yayi. Gaisawa muka yi da"

"wata ina ga irin kabilun arewan ko yar Kaduna ko yar Jos, sai dai ban gama tantance ta ba ta ce min. ""Sunana Sarah daga Gombe ™aramar hukumar kaltungo."" Murmushi nayi nace mata. ""Lubabatu daga Bauchi, karamar hukumar Jama'are."" ""Allah sarki akwai yar uwata Ayrah tana sama wurin CEO!"" Gyada kai nayi nace mata. ""Da kyau bari na isa office din!"" Na wuce sama, kofar dama a rufe take, sai da na"

"ajiye kaina na kunna table tap, na shiga office. Matar da na hango tafi Sarah a shekaru, cikin girmamawa"

na gaishe ta sama sama ta amsa sannan na gaishe ya amsa yana aiki na fara zayyano mishi abinda yake

"da su a a yau, ban gama ba sai ga Tajudeen........"

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 55"

"Murmushi nayi na juya ina kallonshi, a hankali na ce mishi. ""Nayi kewarka!"" Murmushi ya sakar min ya"

"wuce gaban Masifatu ya ajiye document Win da ya kawo, sai lokacin na mai da hankali kanshi ashe ya shaka, wani irin kallon rashin mutunci yake min, yayi shiru rubutu yake a laptop ya rufe ta da karfi tare da mikewa ya fita ya bar ni nan tsaye, anya mutumin nan bai da aljanu? Fitowa nayi na same shi yana magana da Taj, wucewa nayi dan zauna ya ce min. ""Kin gama report din ne?"" Kallonshi nayi cikin mamaki yanzu fa ya fito a office din, ban gama ba sannan ya zo yana tambayar na gama nima share shi nayi kamar ban ji ba, mamaki ya kama shi. Na kuwa hade rai domin ga irin kallon da matar take min na kusa da shi. ""Ina jiranki a mota!"" Ya saka kai ya fita sai da na gama abinda zan na taso na nufi kasa, don ma na bashi haushi stair zan bi ba zan bi elevator ba, kuma a hankali nake sauka ya jima bai kore ni ba. Sai da na shafe minti goma kafin na iso, na hango Taj yana ta leke ta ina xan fito. ""Gani ta nan!"" Na fada ina nufar hanyar waje, ina zuwa na same shi ya cika kamar balloon, sai kallon agogon hannunsa yake, hango matar nan da nayi sai na koma gaba na zauna kuma ai dama gaba nake zama, muka dauki hanyar inda zamu. ""Sir maganar zuwa Japan din yana nan ne?"" Shiru yayi yana kallon table tap din da Taj ya mika mishi. ""Kamfanin Rivers sun tara kayan sosai, dole sai an je da su Japan."" Shiru yayi sannan ya ce mishi. ""Na Kano ma haka, Abuja babu kayan gaskiya."" ""Ka shirya tafiyar har da sakatariya."" Jin an ambace ni yasa na juya na kalli Taj,"" tafiya ina? Har da ni kuma?"" "" Eh ai aikinki har da tafiye-tafiye!"" Yana sane ya fadi haka ya ji ko ya zata fuskanci Mijinta. Hadiye yawu yayi yana kin zuciyarshi kamar aka lugude a kai, wani irin yanayi yake ji a kanshi, yana tsoron kada ta ce tana da miji. ""Amma gaskiya ba zai yiwu ba, domin ko ka tambayi iznin zuwa ba zaa a bar ni ba, ka duba ni mace ce kuma Bahaushiya idan nace zan yi tafiya wata ™asa da wani namijin ai abin ba zai making sense ba, ina ga a cire sunana a bar ni"

"anan, abinda ya shafi gida Nigeria. """

"""Idan don Mijinki ne, ki bada passport Winsa sai a tafi da shi, but i need you! "" Daga haka ya fita a motar"

"domin har mun iso bankin UBA, gaba yayi na fito airah ta ja min tsaki, kallona Taj yayi yana faWin. ""Kina sa'ar Oga, tunda har da mijinki zaku tafi."" ""Ni fa ba zan bishi ba."" Haka na cigaba da tafiya, ya juya yana kallon yadda nake bawa Taj amsa, tsaki yayi yarinya karamar da ya sani a wancan shekarun bata da wannan kula kowa, amma wannan da aurenta ma, sakewa take da kowa shi yaushe zai zama dan iska irin Mijinta, idan da shi ne Mijinta, zai ga yadda zata kula kowa domin a banza zai ta sare kan mutane ne, tsaki yayi ya cigaba da tafiya. Har inda aka yi zaman muka isa sannan muka fita inda aka ajiye kayan, na shiga ina rubuta abubuwan da Taj yake gaya min, har muka gama na juya kenan kawai muka ci karo da shi, kamar xan fadi ya riko hannuna, ya tsayar da ni. Ya harare ni cikin masifa ya ce min. ""Idan Mijinki baya kishinki, ke ba zaki iya kishin kanki ba ne? Kin zauna sai wangale hakora kike da wani? Ki sani ba zaki janyo min masifa a kamfanina ba, idan aurenki aurenki idan kuma kule-kule ne sai ki bar min aikin na gaya miki, kuma xan gayawa SAN yasan abinda kike aikatawa."" Irin kallon da nake mishi na tausayi ne, domin bakiWaya masifarshi ta rufe mishi idanun kawai fada yake kamar zai dake ni, wani abu da yake bani mamaki shi fa idan yana masifar ma baka tab'a jin tashin muryan sai dai ayi ta maganar cikin wuya da baki, irin kada a ji yana fada, tattara kayan nayi na rab'a gefenshi na wuce, kafin na isa wurin motar"

"na shiga Taj na min magana na ki kula shi, shima da yazo ya zauna a motar muka bar bankin muna hanya"

"amma naki kula Taj, ganin haka yasa shi cewa Taj. ""Ka kai mu Chinese dish."" ""Ok sir!"" Bayan mun dauki"

"hanya naji muryan Airah. ""Turaki ni ban ga wani aikin da sakatariyarka take ba, maganar tafiya kuwa sai na yi replace dinta."" Duk muna jinta, ni sai na fi kowa murna cikin farin ciki na ce mata.. ""Alhamdulillahi Ubangiji ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, kai Masha Allah."" Ganin yadda na nuna farin cikina tare da musu addu'a, ya cika da mamaki yana ta taSa table tap amma zuciyarshi kamar ta dirko daga kirjinsa, har sai da ya kai hannu ya danne kirjin, ko da muka iso shagon ita da Taj ya tura shagon. Tunda na ji ya ce ita da ita da Taj su je su fita su amso na fahimci zai hau masifa ne, dauko airpies na saka s kunnena na kunna wayata. ""Cire!"" Ya fada a fusace, na cire daga kunnen na juya ina kallon titi raina yana b'aci, ""tafiya da ke xan yi idan kin so ki ajiye aiki yau!"" Daga haka ya cigaba da aikinsa. Haka suka dawo muka bar shagon, koda muka iso office mika min abincin Taj yayi na ce mishi. ""Ina azumi!"" ""Yau wacce rana kenan?"" Banza nayi mishi ban kara kula shi ba. Har aka tashi na wuce gida, ina isowa gida abin mamaki na same shi har ya rigani zuwa gidan, na samu suna magana da Ya Ado. Wuce su nayi na tafi cikin gidan. Ban san tafiyarshi ba, sai ganin Ya Ado nayi ya zauna yana kallona. ""Kuna da tafiya ne a kamfaninku?"" ""Eh amma ni nace ba zan samu zuwa ba, saboda."" ""Zaki je, abu daya nake so dake ki kama kanki, sannan ki rike mutuncinki. Kada ki manta Allah yana ganinki, kada ganin bamu nan yasa ki fada wani irin yanayi, ki sani Allah yana kallonki."" Idanuna ne suka cika da kwalla, haka yayi ta min nasiha duk da ni na nuna bana son zuwa amma ya ado ya ce na je, haka na cigaba da jin wannan abin haushin, ranar juma'a ba wani zama muka yi ba, aka tashi yau kan shi da kasan yazo kamfanin don haka da aka tashi, na fito zan je Garej ya tsaya tare da cewa. ""Shigo!"" Kamar ba zan shiga ba, sai kuma na shiga na ja belt na daura, muka cigaba da tafiya. Wannan dan renin hankalin ba abinda ya ce min, har muka isa gida na cire belt din xan fita ya ce min. ""Are you angry?"" Share nayi na bar shi a wajen ai tun da naje ya ga yadda fuskata take masifar haWe, haka yasa shi fahimtar raina a b'ace yake, wai kuma don renin hankali yana tambayata wai ina jin"

haushi ne?

"Ranar asabar, ina tsaka da barci domin duk jikina a gajiye nake tun daren jiya Aunty Zakiyah ta ce"

"zata shiga asibiti. Wurin karfe goma, mai aikin ta ce nazo ina da baki, saukowa nayi shine da su Ilham. Cike da mamaki yaran suka taso da gudu na sauko nima na rungume su. ""Aunty Lulu!"" ""Na'am yau kunne!"" Zama nayi nace mishi. ""Ina kwana?"" Hankalinsa yana kan wayarshi sai latsawa yake, kamar bai ji ni ba, sai da na sake gaishe shi ya amsa, kitchen na nufa na shiga aikin gaggawa domin Yaran gidanmu sun tafi Islamiyya. Babu wani abin karyawa don dumamen tuwo suka ci, doya na fere na turara musu, tare da miyar sauce din kwai, sai kunun tsamiya da na dama musu na shiga fito da shi, na hada bakiWaya a gabansu, yaran na zuba musu. Sannan na koma na matse fruit nayi musu juice da shi na fito na zuba musu. Abin ya bani mamaki yadda yake cikin abincin kamar bashi ba. Komawa sama nayi, wanka da brush nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa, na karya dan daurin dan kwali, Ban san me ya ke fisgana ba, amma na samu kaina da shafe jikina da humra mai kamshi, sannan ka fito na samu ya gama yana fama da wayarshi ne, lokacin da na iso parlourn kura min idanu yayi, sai da na kama shi yana kallona ya wayance kamar bai yi kome ba, na wuce kitchen na zauna a can na karya sannan na fito yaran suka gama cin nasu na tattara na kai kitchen. Sai Santi suke. ""Aunty Lulu zaki raka mu, muje birthday party na yar class dinmu, kuma ance anan son two parent su zo ne, kin san Mom ba zata amince ba,"

"shine muka zo da Uncle ko zaki bi mu. Please!"" Yadda suka yi maganar kamar nayi kuka, domin na"

"fahimci ba wai zuwan kansu ba ne ba mamaki shi ya shirya musu haka. ""Bari ka kira Mijina na gaya"

"mishi!"" Na tsinci kaina da fadar haka, bai d'ago ya kalle ni ba har na haura sama na gama abinda zan yi ja fito sanye da wata laffaya akan kayan jikina. Na fito a hankali nake takawa, yadda na iso yaran suka yi ta"

"murna, haka muka fita satar kallona yake sau biyu ina kama shi, amma sai wani haWe rai yake.."

"A wurin Birthday din hidima sosai aka yi, mu kanmu iyayen yaran sai da suka saka mana wani gasa."

"Kusan a tare muka ci gasar, karon farko da naji wata irin soyayyar Yara ya kama ni, domin saboda Yaran nan sai da nayi kawaye Iyayen Yara, dayawa a wurin dauka suka yi ni Matarshi, ce kasancewar an san shi sai ya zamana idanun mutane akanmu, a kyautar da ya bada har da dollar guda ashirin, sai gift da yaran suka bada. A waje haka mutumin nan yana da mutunci, rashin mutuncinsa a office suke. Haka muka gama bikin muka dawo suka ajiye ni a gida, fitowa yayi daga motar yana dan matsa hannunsa, ni duk a tunani na crwa zai yi na gode. ""Idan kika shiga ki yi wanka domin turarenki."" Kambu, banza nayi da shi na wuce humran nawa ne zan yi wanka akan shi wanda idan ba kazo kusa da Ni Rufe bakina nayi wata"

"irin kunya ta kama ni, kenan turaren ya. Da gudu na shige parlourn tare da haurawa sama, yayi gaskiya Innalillahi wainnalihir rajoun, wanka nayi tare da tsarkake jikina. Duk kunya ya kama ni, haka nayi ta juyi har lokacin cin abinci yayi, ina cin abincin kawai sai naji gabana yana faduwa, sakamakon tuno maganarshi, gaskiya tafiya Japan ba zai yiwu ba, don ma azumi ya kusa. Haka nayi ta cakalar abincin har Ya ado yace min.."" idan ba zaki ci ba ai ba a miki dole ba! "" Mikewa nayi na dawo parlourn da Yorghurt ina sha a hankali, ni fa yanzu na lura wannan aikin ya kara ramar da ni, domin yan dukiyar fulanina basu"

zama a cikin yar bra da nake sakawa.

"Haka nayi ta juya maganar, nan har barci ya dauke ni,"

"Washi gari lahadi, sakon da na gani ya turo min ya ce min. *Daren yau zamu tafi please kada ki hada"

"kayanki d wannan perfume din yana da karfi bana sonshi* kambu mutumin nan ya rena min hankali, buga kofar da Ya ado yayi na ce mishi. ""Na'am!"" ""Dazu oganki yake gaya min tafiyarku karfe shida na yamma!"" ""Tow!"" Haka na shiga hada kayana bakiWaya dogayen ruguna ne, humran nan barinsa nayi na dauki body spray sai roll on na hammata, saukowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login