Follow us on social media

Showing 33001 words to 36000 words out of 140751 words

Chapter 12 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

324

kama harshe tare da wani guntun fashion English aka ce min, ""opps i hope"

"baka ji ciwo ba!"" Sai ce min sannu yake, da wani irin murya me sanyi. A hankali na matsa ina faWin. ""Ba kome!"" Na riko hannun Rumana muka yi gaba sai juyawa suke suna kallonsa, ni kuwa naki juyawa don bana ce ga yanayinsa ba sai dai yadda gabana yake faduwa yasa na yi saurin janye su muka shiga cikin Makarantar. Bikin yaye dalibai yayi kyau domin nima naci lamban yabo kala uku, a cikin kuwa har da kyautar kudin da na samu, saboda zama na daya da anyi a ko ina. A wannan ranar mai cike da tarihi har Makarantar Ya Hafiz ya zo ya dauke ni a ranar da ya fara sayan mashin dinsa Simba, tun muna Jss1 kawayena suka san da zancen Ya Hafiz. Rumah Rabi'u Mai shanu, Hafsah Faruq Babaji, Nafisa Sadi Gital, sai ni Lubabatu Shehu Umar Jama'are, sau dayawa cewa ake sunana yayi tsawo ni kuwa ban tab'a ganin"

tsawonsa ba.

"Wani lokaci shafin ™addara tana budewa a rayuwarmu, ba tare da mun sani ba. Idan da ace wani abun"

mun rike tow ba makawa da ba zamu manta da shi ba.

"Haka muka sha hutu, sannan muka dawo. A lokacin na dawo da wani irin yanayi na ciwon mara na"

"al'ada. Sati na biyu da dawowa, da yake ban yi al'adar da wuri ba sai da na shiga aji na hudu, sannan ranar ita ce ranar da na fara, ciwon ciki kamar zan mutu, zufa nake yi tare da jin wani irin zazzaSi ya rufe ni, ga ciwon ciki kamar xan yi amai. Sabon malamin Chemistry da aka kawo mana ya shigo ya fara kiran sunan kowa sannan shi zai zame mana Form master dinmu, a hankali ya fara kiran sunayen mu, har ya zo kaina ya kira sau biyu ban iya d'ago kai ba, sai da ya kara kiran na uku Ruma ta ce mishi. ""Sir tunda tazo gata nan bata da lafiya!"" A dan hanzari ya kalle da wurin da ta nuna, a hankali ya karasa wurin ya Wan taSa desk Win a hankali na d'ago kai kafin ya tambaye ni na sheka mishi amai a jikinsa bakiWaya, sai a lokacin na zaro idanu ina kallonshi. ""Sorry how are you feeling now?"" Shine tambayar da yayi min, kasa magana nayi ina rike da cikina. Shiru yayi na wani lokaci kafin ya mike ya fita can sai ga yan ss3 sun shigo tare da shi har ya sauya kayan, wata jamfa ce a jikinsa golden yellow, yana shigowa ya ga yadda suke ta irin kyamar tabani. "" Me kuke yi haka? "" Takawa yayi yana kallon yadda suke son taba ni don ni kaina nasan a i mess up, duk aka rasa dabarar da za ayi min sai gashi an buga break, yan class suka fita a dudduke na mike, dawowa bayana yayi zai magana yadda zasu rike ni ya ga hatta hijab dina ya baci da jini! "" Look koma ki zauna!"" Haka na koma na zauna ina jin wani irin ciwo ya ce yan matan. "" Ku tsaya ina zuwa!"" Haka ya fita can sai gashi tare da Malama Malika ta Jss3, dauke da sabon hijab dal a hannunta ta sallami yan matan sannan ta ce min.. ""Lubnah sannu ko!"" Gyada kai nayi, ta bani hijab din na saka, sannan ta dauki wancan ta saka a leda, ta riko hannuna muka fita waje, motar Principle aka saka ni, muka wuce gida, ban san ya aka yi ba sai da nayi sati sannan na dawo lokaci na warware, Ya Hafiz yake"

kawo ni.

"Tun daga lokacin Malamin nan ya saka min idanun, sannan shi ya rubuta min note akan duk ranar biyar"

"ga wata, matukar ba jarabawa ba ne ba'a bukatar nazo makaranta idan kuma nazo, na fara zuwa clinic na makarantar na amshi magani da sanatery pad ni sai ya shiga sani jin kunya haka kawai zai saka ni jin"

"na zama yar iska, akwai wani program da kamfanin Always suka yi a lokacin, tabbas sun bamu kyautar"

"pad din, haka na ga mutumin nan yana kallona. Ni tun a wurin nayi kyauta da shi domin na tsani yadda yake bina da idanu. Sau biyu na taba kallonsa, idan na Ganshi bana iya d'aga kai na kalle shi domin zubi yake min da gardawan almajirai. A gefe guda soyayyarmu da Ya Hafiz kamar mu cinye kanmu, haka yasa yan gidanmu suke ta ganin ina gama secondry School za'a aurar da ni, ban damu ba. Amma kuma zuwa lokacin da muka shiga ss2 mutumin nan ya fara damuna, don ya saka min idanu yadda ni ban zata ba, sannan duk wani abu nawa yana jin sa ne a bakin Ruma ita kuma sai Allah ya daura mata sonshi da ni, ita tayi ta ziga ni har na fara kula shi, amma ba a makarantar ba a gidan Aunty Inna, domin a lokacin Aunty Hindatu tana tare da Ya Hafiz, Nafisa Sadi Gital kuwa cewa tayi na ci kuWinsa kawai don mun lura wallahi kamar bai da wayo, duk abinda zance ina so zai bani, kuma bai taSa jin zafin cire kudi, Yaran Aunty"

Innah kuwa wani irin kashe musu kudi yake domin ni a wurinsa na taSa ganin wasu chocolate.

"Amir dan Aunty Innah ya cika shekara biyu, nake gaya mishi ai sati na zagayowa sai ga tarkace har da"

"Cake, lokacin Blackberry sai wane da wane ina fama da wata yar Nokia da Ya Hafiz ya kure a daka ya saya min, sai ga Malam Bilal ya kawo min sabuwa dal, ai kuwa Aunty Innah yana kara zuwa ta mai da mishi ya ce shi me zai yi da shi, dukkanmu kallon mai fama da albashi muke masa, bana sonshi domin Ya"

Hafiz ya cika min raina da soyayyarshi.

"Lokacin da muka shiga Ss3 ya gabatar da kanshi a wurin Abba, maganar gaskiya Abba ya amince da shi"

"amma lokacin da ya tambaye ni, kai tsaye na ce ni fa Ya Hafiz nake so, shima kuma Ya Hafiz din ya amince ni yake so, haka da ya kara dawowa Abba ya bashi hakuri tare da gaya mishi an tsayar min da miji domin ya tambayar da yayi min na gaya mishi gaskiya. Koda na je makaranta na samu sakon yana min fatan alkhairi, Malam Hamza Adam ya kira ni office dinsa ya min.. ""Lubabatu gaya min me yasa bakya son Malam Bilal?"" Shiru nayi ya rasa yadda zai saka ranshi.. ""kin san waye kika yi rejected dinsa"

"kuwa? Kin san waye shi? """

"Kasa kasa nace mishi. "" Kayan lambu ne da zan tsaya dai ya nuna zan zabe shi. Ni ina da wnada nake so!"""

""" Wanda kike so kin san waye shi? "" "" Dan uwana ne fa! "" Na fada ina Wauke kai daga kallonshi. "" Shi kenan Allah ya baku zaman lafiya!"" Daga haka na mike na bar mishi office din. Kafin mu gama makaranta na ji labarin wai ai Wan masu arziki ne, Malam Hamza ya gayyace shi bikin Yaye dalibai shine ya zo. A bakin Ruma naji wacce ta ce min ya bar min sako a wurinta. "" Ki rike na baki sakon da ya bani! """

Tayi ta mamaki.

"Haka muka gama makaranta na manta da shi domin ya cikin lissafina, a 2017 muka gama har da"

"Jamb, na kuwa cika ATBU, ba laifi point dina ya ja, suka bani business administration, a shekarar da na fara a wannan shekarar Ya Hafiz ya kawo lefena da sadakina har dubu hamsin, duk da a lokacin sadaki yafi haka amma ba yanke mishi ba, Dangina kowa ya goyi bayan auren Yayuna maza da mata kowa yana"

"san barka, haka yasa bikin ya zama irin na yar gatan nan, gidan da Ya Hafiz zai zauna Haya ce ya kama a"

"fadaman mada, layin gidan Mamar tsohon gwamnan Bauchi Isa yuguda. Duk wani kayan gata an saka"

"min anyi min auren gata kowa ya sani, shi kanshi Ya Hafiz yasan yadda Iyayena suke kaunata."

Yadda muka fara da soyayyarmu me tsayawa a raina kowa ya ganni sai ya yi maganar aure ya amshe

"ni, gashi dai nice karama amma ayi min goyon auta ba don na koyi girki a gabansu Mama da Yadiko, haka yasa nayi ta kula da mijina, watanmu uku da aure Ya Hafiz ya kawo min shawarar tunda ina karatu na fara shan maganin hana daukar ciki yana tausayina nayi karama ga kuma karatu, cikin soyayya da kulawa ya bani wannan shawarar, ni kuma na amsa hannu bibbiyu. Saboda Abba ya gaya min Ya hafiz ba zai tab'a cutar da ni ba, kuma na yarda da wannan magana, haka Kakanmu Baba Malam wanda shi yayi ruwa yayi tsaki akan lamarin ya gaya min haka, ashe kiransu yake yayi ta gaya musu yadda yake kaunata,"

shi baya fatan na mutu na barshi gara shi ya fara mutuwa.

Haka nayi ta karatu ina kuma shan magani ban tab'a fadawa kowa ba. Nayi imani da Allah nice

"sanadin matsalata. Duk abinda Ya Hafiz zai aikata ban tab'a ganin laifi ko kuskure ba. Shekararmu daya na fara tsintar wasu abubuwan a jikin wandonsa ko rigarshi wato condom, ban tab'a magana ba, na zama makauniya akanshi bana fadar aibunsa, bai sauya min ba sai da na fara wani irin kiba, wai ashe maganin da nake sha ne. Idan da xan gaya muku yadda Ya Hafiz yake min a lokacin kwanciyar aurenmu ni har mamaki nake, domin kamar wata yar iska haka zai ta min, ni kuma bana son ya ji ba dad'i sai na"

"hakura na barshi yayi yadda yake so, kibar da na fara sai ya sa na kasa tabuka abin arziki."

"Lokacin ina aji hudu na jami'a, an tura ni IT, wani bank na samu horo. Ranar ya kasance Juma'a haka"

"yasa na dawo da wuri kuma mun yi zan tsaya gidan Ya Umar Aunty Azizat ta haihu. Na manta kayan barkan a kan gadona. Na koma gidan dauka, yadda na shiga na ga motarshi jikina yayi bala'in sanyi, domin kuwa ya ce min zai yi tafiya ne zuwa Kano. A kofar shiga cikin gidan na ga takalmin mace, haka na shiga cikin gidan domin ina ga ko Kannensa ne da yake suna zuwa. Koda na shiga ban kawo kome a raina ba, haka na shige can dakina ina d'aga labulen mace na samu akan Ya Hafiz suna masha'a, bugawar da zuciyata yayi yasa na juya parlourn da sauri na zauna, jin karar takuna yasa suka fito, lokacin da suka fito suka same ni ina kallon, murmushi nayi mishi nace mishi. ""Dama baka tafi ba ne?"" A dan razane, ya ce min. ""Eh!"" Yana kallon yadda nake kallon tv, haka yarinyar ta fito tana kallonshi. Shi kuma ni yake kallo. Tana fita na koma dakin na dauki abinda xan dauka na fito. "" Ina zaki? "" ""Ka manta dai sunan Aunty Azizat ne? "" ""Muje na ajiye ki! "" Ya kai hannu zai tab'a ni nayi maza na matsa, ina murmushi na ce mishi."

""" Huta kawai! """

"Haka na bar gidan, a can na wuni anan ake gaya min umarar bana ma za a tafi damu, sannan Abba ya"

"cire zakkar da yake cirewa duk shekara an bawa Ya Ado kudin ya haWa da na wanda yake hannunsa an saya min gida Tambari housing estate, ina jin haka na ce musu kawai zamu koma can, ganin haka kuwa"

"suka mara min baya domin yadda kowa yake sonshi saboda ina sonshi ne, laifin da yayi min sai na barshi"

"a matsayin ajizanci. Muka cigaba da rayuwar har muka taso daga unguwar da muke muka koma sabo bayan sallah.. shekararmu biyar cib wanda yayi da yin bautar kasana, Ya Hafiz ya fara kulafunci Yara, a"

lokacin hankalina ya tashi nayi ta zaryan asibiti amma babu labari.

"Bani mantawa wata rana ina kwance wurin karfe tara na dare ya shigo da wata mata, don zata girme ni."

"Ya ce bata daki ta kwana. Haka nayi kuwa na bata daki da na ware shi don bakinmu, kwana Waya sai ya zama kwana biyu kai a takaice dai sai gashi ta share kwanaki a gidan. A cikin wannan yanayin na kama shi da ita, a lokacin na saka a raina gara ya aure ta, yaki har da gaya min wai karuwa ce, na ce haka zai yi hakuri, a cikin lokaci kalilan na shawo kanshi, ya kai sadakin karima, kowa a dangina yaji maganar aurenshi, hmm mutum sai Allah sai ga magana ya fito ta Jama'are cewa ai dalilin aurensa don ni na kashe mahaifina da shan kwayar hana daukar ciki, a lokacin dangi kowa ya juna min baya nima kuwa na tashi da rikici na ce ba gidana ba, Abba da Baba Malam suka zo har gidan suka ci mutuncina tunda ni"

bana kaunar Hafiz shi yasa na sha maganin hana daukar ciki ban isa ba a gidan zai zauna da Matarshi.

"Haka nayi hakuri na dauke kai, aka yi auren. Suka yi ta min iskanci da renin hankali. Wallahi tun bana"

"iya dauka har na fara, abin da ban sani ba akan shi kai kara, abu kaWan ya kai ™arata, ayi ta zagina ana ganin laifina. Kwatsam sai ga Matarshi da ciki aka yi ta murna ana farin ciki. Nima dai nayi murna, nayi farin ciki. Sai dai watanin cikin da auren bakwai, da safe muka samu hatsaniya da ita, kuma Ya Hafiz din Yana nan shi ya raba rigimar, bayan ya fita kasuwa kawai jini ya Salle mata, haka aka kwashe ta zuwa asibiti. Haka muka je ko awa daya na ayi ba ta haifi Yarta mace, aka fito aka gaya mana, muka yi ta murna haka na koma gida na gyara inda jini ya bata na wanke gidan, wurin karfe biyar na yamma aka sallame ta, suka dawo gida washi gari Ya Umar ya zo ya min shegen duka, wanda ya fusata Aunty Hindatu a lokacin tayi ta fada tun daga nan ta tsaya min, wai ashe labarin abinda ya faru Ya Hafiz ya gayawa Baba Malam shi kuma ya kira Abba yake ce mishi ga can Lubabatu zata kashe mata da ciki jini ya Salle mata.. shine Abba ya ce ko a samu wani ya min duka. Ko kuma ya sake Mama. Wannan abin ya"

fusata Ya Umar..

"Danginta da kowa yana jin haka, har shi ya Hafiz din, sai da nayi zazzaSi, yan uwanta don gulma sai"

"sun zo duba ni. Haka na daure na yi ta hidima dasu har aka gama suna abu daya na musu fintinkau, iyayenta talakawa ne na fitar hankali hatta abubuwan da aka yi na suna daga gidan Iyayena ne, ranar sunan da yamma na shiga naji suna min dad'i. Ni ban kula su ba sai Aunty Raliya da ta wanke su tas ta ce musu. ""Ai ku san tarbiyya irinta gidan yasa aka zane ta kada ta kara aikata shirme, gidan da Yarku take abincin da Yarku take ci daga arzikinmu ne, shi kanshi mijin dai bai da nashi na kanshi sai na matarshi don haka mu yar mu tana da tarbiyya domin bamu sake ta tayi ta bin titi kwaro-kwaro ba. Ga sittin ga degree. Haihuwa kuwa ba akanta aka fara rashinsa ba, Allah ya karawa Nana A'ishah yarda itama har"

"tayi wafati Allah bai bata haihuwa ba. Mun san islamiyya domin mun zauna gaban Malamai "" daga haka"

"suka yi shiru. Tun daga nan ta koma bayana, Yan uwan ya Hafiz suka koma jikinta hatta Hajiya komawa"

tayi jikinta.

"Haka aka watse wani renin hankali, sai su bawa yarinyar maganin barci su kawo min ita haka zasu ta"

"iskanci wani lokaci kuma haka zasu kawota ko za mutu tana kuka ba zasu amshe ta ba, haka na ci wahalar yarinyar nan. Gashi da na gama bautar ™asa result dina yana fitowa aka so niman min aiki Amma da yake mugunta na ransa ya hana.."

"Haka nayi ta rayuwa da kunci da wahala, gashi ya hana ni cigaba Umaran da muke zuwa ya dauke min"

"damuwa, idan ya Hafiz yana son wani abu a guna tow wallahi a lokacin zai ta kashe ni da soyayya har sai na fara jin anya ba rashin fahimta bane, amma ina haka dai muka cigaba. Akwai shekarar da Abba ya biya musu Umara shi da Karimah kanta yayi ta rawa haka suka tafi watan Mauludi."

"Bayan sun dawo takuma daukar ciki, a lokacin Firdausi ta zo ta zauna a gidan, na ga iskanci ganin"

"idanuna. Na gama secondry School ina sha shekaru goma sha bakwai, na gama jami'a ina da shekaru ashirin da biyu, a duniya. Haka kafin ta haihu ya ado ya zo ta sauya min kayan gidan ashe ya samu karin mukami ne, a lokacin na ji labarin tun dukana da Ya Umar yayi suka daina magana, dama shi ne mai tsaya mishi akan kayansa da yake shigo da su ya cire hannunsa. Kai abin fa sai da aka yi zama sosai domin a ganan Abba Ya Ado ya ce mishi.. ""wallahi billahi azmin, duk wnada ya kara taSa Lubabatu sai kotu ta raba ni da shi, saboda me aka sauke Suratu hujara?"" Akan wannan rigimar Ya Umar Win ya shirya min birthday da na cika 23, ina zaune aka zo aka dauke ni, sai gidan Ya Umar a can aka yi birthday party din ya bani motar da kowa sai da yayi mamaki ya ce min na kira Ya Ado na gaya mishi, na kira na gaya mishi na tura mishi motar ya gani shine dalilin shirinsu, tun daga lokacin Yayuna suka dauki nauyin tura min kudi, Amma ya Hafiz ya shiga kwacewa, duk shekara idan muka je Umara sai na sayi yan kunne gwal kamar yadda su aunty Hindatu suke yi domin dukkanmu Yaran Abba mata yake biya mana, har su Aunty"

Munah aunti Raliya.

"Karimah ta haihu ana saura kwanaki uku ba dawo haka na saya mata kayan Baby, lokacin da na dawo na"

"samu an gyara min parlourn, ai kuwa na dawo da kwana biyu aka yi suna yan'uwana a parlour, ga girkin da aka yi musamman ni da muke shiri da yan unguwar suka yi ta shigowa saboda ni, bayan suna shima"

"suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login