Follow us on social media

Showing 111001 words to 114000 words out of 140751 words

Chapter 38 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

318

shima na lura kamar hakuri yake bawa Mutumin bayan, shegen ikon tsiya, ni tsoron kallonshi ma nake haka muka bar First bank, muka nufi wani banki mika min table tap din da mutumin ya bawa Driban, shi kuma ya mika min. ""Zaku hadu da wasu mutane akan sayar da wasu filayen wannan ba batun hadin gwiwa ba ne, ki duba zaki ga bayanai akan filin."" Gyada kai nayi, haka nayi ta duba bayanin ina me ciro biro da littafi na fara rubutawa, har muka isa. Haka muka fito ina rike da table tap din, har inda za a zauna. A karon farko da ya kalle ni, ya tsaya kamar yana da abin da zai fada sai kuma yayi gaba abinsa, haka ya sa nima na rufa mishi baya. Koda muka isa office din mun samu ana jiran, sai da suka tattauna kafin aka miko min takardun da zan duba,na gama dubawa sannan na koma gefe na cigaba da tsayuwa, kafana ne ya fara ciwo kasance takalmin kafana yana da dan tudu, haka wunin ranar a zirga-zirga da tattaunawa abinda na fahimta shi mutum ne da ya san darajar nima,"

"haka muka dawo office a matu™ar gajiya, driban sai sannu yake gaya min sannan ya biyo ni zuwa cikin"

"kamfanin yana dauke da kayan kamar yadda nake dauke da su, har zan nufi stair ya ce min. ""No ki zo ga"

"inda zai kai mu yanzu!"" Dan murmushi nayi na ce mishi, ""tow!"" Wannan shine adalcin da zance anyi min domin daukar wannan dogon hanyar kamar cewa aka yi kafana ya karye, har office din mutumin muka isa. Muna zuwa na ga Mamar Yaran nan gaishe ta nayi. Ta ce min. ""Kin yi sallah kuwa ga la'asar ta kusa?"" ""Yanzu zan tafi masallaci!"" ""Ok gashi nan nasan baki ci kome ba!"" ""A'a Nagode Aunty!"" ""Amsa kawarki tace na baki."" Hannu bibbiyu na saka na amsa, sannan na mata godiya na bar dakin. Wannan wurin na kara bi na sauka staff office na, nufa tare da ajiye abincin da jakata na dauki wayata na tafi masallaci, sai da nayi la'asar sannan na dawo ina zuwa yadda na bar kayan ba a haka na same shi ba, which mean an bude tare da tab'awa, a hankali na dauki abincin na fito waje na nufi wurin Driban, na mika mishi. ""Gashi ko zaka ci?"" Murmushi yayi sannan ya amsa yana faWin. ""Y sunanki ne? Na ga sai Mrs Jama'are ake fada ya asalin sunanki?"" Ya tambaye ni da hausa, ""Lubnah zaka iya kira da Lulu."" ""Wow sunan yayi dad'i."" Wayarshi ce tayi ™ara ya Wauka. ""Ka turo yarinyar nan!"" ""Ok sir!"" Juyawa yayi ya kalle ni ya ce min. ""Oga yana kiranki!"" ""Ok!"" Na juya da sauri, wasu mata ne suka shigo kamfanin wata mahaukaciyar mota da wannan ne kawo na farko da na ganta, haka suka fito ba tare da wani bata lokaci ba suka nufi main entrance na kamfanin, haka muka jera da su, tunda na ga staff na gaishe su na fahimci suna da alaka da Kamfanin, lokacin da suka shiga elevator, ni kuma sai na bi stair haka nayi ta gudu sauri sauri. Har na isa hawa na uku, office Winsa na nufa. Ina shiga naga matan suna zaune a kujeran office din shi kuma yana ta aikinsa, gaban shi naje na tsaya nace mishi. ""Sir gani!"" Banza ya bawa ajiyata. Haka na cigaba da tsayuwar har kusan minti goma kafin ya ce min. "" Get them out!"" ""Na'am!"" D'ago idanunsa ta cikin glass yayi ya kafe ni da shi. ""Pardon"" na juya da sauri na ce musu. ""Ku yi hakuri yana aiki ko zaku tafi sai ku nime appointment gaba!"" ""Wacece?"" Inji wata kyakkyawar budurwa wacce ban iya kallonta bama, ture ni tayi tana faWin. ""Dallas bani wuri."" Sai da na kusan faduwa. Shigowar Mamar yaran nan da maza biyu nan ne ya sa basu sauke kwandon bala'insu a kaina ba, ina rakube a gefe. ""Aunty Sameerah ya haka ne?"" Inji Babban. Auta babu ruwanka na kawo Batul ce ya bata aiki kamar yadda aka bawa kowa aik."" Shiru yayi yana kallon yadda take ta hayagaga, mikewa Boss yayi ya kalle ni, da sauri na nufi wurinsa naga yana kallon duk wani abu a wurin sai da na dauka na saka mishi a jakarshi, kome sai da na tattara, sannan na raka shi waje, tare da jiransu har suka fita na ja office din na rufe ina jin suna masifa tare da bin stair domin yaki tafiya yana bakin elevator din. Sai da na gama na riko jakarshi muka nufi elevator din tare, haka muka fito tare na kai mishi jakarshi motar, sannan na nufi main entrance na kamfanin na tafi kayi sign kafin na hada kayana, na fito a gajiye. Motar kamfanin da aka ware na mala'ikan shi na shiga aka kai mu har inda zamu shiga motar unguwar, minti goma sha biyar na samu motar unguwar, na shiga. Na gaji tun kafin na isa nake jin barci ina isa wanka na shiga nayi da ruwan zafi sannan nayi Alwala sallah Magariba da Isha, Abinci ma yau daki Ya ado ya kawo min yana murmushi. ""Auta yau na ganki da CEO na KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY!"" Murmushi nayi nace mishi"" Ya Ado kafana yana ciwo na gaji sosai."" "" Allah ya kawo miki miji nagari yadda ba zaki jima ba kin yi aure! Bari na kira miki su Adil su miki tausa. "" "" Na gode sosai!"" "" Ina babu matsala a wurin aikin?"" Girgiza mishi kai nayi, ya fita can sai ga"

"Yaran don ma mun sallah isha, haka suka yi ta min tausa abincin da ban ci ba kenan barci yayi gaba da ni."

"Duk yadda suka yaso ya kamata da laifi ko na wani abu sai ya lura bata da matsala, haka yasa shi kara"

"saka idanun yadda suka yi kome ba tare da saninsa ba, haka zai ci taransu. Bayan sallah isha ya shirya"

"cikin kananun kaya ya nufi can family house Winsu tare da Tajudeen, koda suka isa fita yayi Tajudeen ya"

"dauki wani kwali ya bi bayanshi, har cikin gidan. Inda ake jiranshi. Da sallama ya shiga Daddah ta mike tana murna, rungume shi tayi tana faWin. ""Turaki ko baki da lafiya ne? Naga har yau baki Maganar aure? Haka zaki cigaba da zama?"" Sai a lokacin duk wunin da suka yi da yarinyar nan bai ga ta dauki waya ba, abin ya bashi mamaki tow ina Mijinta ko ta kashe wayarta ne? To ina ruwansa? Wannan personal life dinta ne. A hankali ya sakarwa Daddah murmushi. Haka suka hadu familyn bakiWaya aka fara cin abinci. ""Baffa ka tambaye shi me yasa yau ya fita da mace akan aiki me muhimmanci?"" Kallonshi Alhaji ELYakub yayi amma ganin kamar ko a jikinsa, ya kuma zubawa Alhaji Mudansir idanun yana son jin dalilin tambayar, amma gogan yana cin abincin a nutse kamar ba shi ake magana akan shi ba. ""Eh Baffa sabuwar dauka ce bata goge kamar Badr ba akan me zai dauke ta, sannan idan har aikin zai dauke su ba"

"ga Mimi da Badr ko Batul ko Hanif ba? Irin wannan aikin me muhimmanci taya za a janyo bare a cikinsa."""

"""Sata na samu yarinya take aka ce na danne ta, ai gara na dauki bare idan na danne ta xan bata kudi"

"zata yi shiru da bakinta "" ya kai hannunsa tare da jan baki kamar zip. Ba yawwa ba dad'i, kallonshi suka yi tayi suna mamakin wannan bakar maganar. ""Tow Turaki me yasa baka dauke su aiki ba?"" Murmushi yayi bai kara magana ba sai da Uncle Auta ya amsa. ""Basu fa turo bukatar haka ba, idan aka ce kowa alfarma"

"za ayi mishi ai kuwa ba za'ayi aikin da ya dace ba, idan har aiki suke so su je Hamma Babba ya dauke su!"""

"""Wannan wacce irin magana ce!"" Tauna kashi Turaki yayi da karfi sai da suka yi shiru. ""Duk me son aiki"

"ya tura shaidar bukatar haka, babu wata alfarma kowa nima yake!"" Inji Alhaji ELYakub yana kallon Turaki. Murmushi yayi tare da gyada mishi kai, ai kuwa haka suka gama cin abincin tare da kawo korafi kamar zasu mutu amma Turaki tun maganar farko bai kara magana ba. Haka aka tashi a taron cin abincin. Masu"

aiki suka kwashe kayan da aka zuba abincin.

"Haka suka dan bude hira wanda korafi ya fi yawa, amma gayen nan ko a jikinsa kusan duk bayanin da"

"suke yiwa kakanshi shima bayan jikanshi yake bi, abin har mamaki yake basu, sai wurin tara suka bar tashi zasu tafi ya ce musu. ""Da kuke maganar mace ina gurbin Mrs Thomas ta maye?"" Yadda yayi maganar bakiWaya sai suka yi shiru, haka ya fita daga cikin gidan, Uncle Auta da Ubaid, shi kuma da Taj. Haka suka nufi unguwarsu. Bayan tafiyarshi ne suka saka Ubansu a gaba da roko har sai da ya amince da"

batun sauran jikokin su fara aiki a kamfanin.

---

"Wato jiya na gaji yau ma a tsaye saye na karya, ina gamawa na shiga mota ina duba abubuwan da suka"

"faru jiya, domin abinda Driban ya gaya min kenan ina tattara abubuwan da aka yi zai taimaka min. Karfe bakwai da arba'in yayi min a kamfanin, Ya Ado sai dariya yake min yana faWin. ""Da alamu boss Winki yana da zafin kai!"" ""Ya Ado ba zaka gane ba ne."" Dariya yayi kawai, har na isa office dinsa. A rufe dawowa kasa nayi na zauna na cigaba da zaman jira, dayawan ma'aikanta sun same ni ne a kamfanin, sai ya zamana ana ta gulma. Karfe tara ya iso, karban jakar hannun driban nayi ina tambayarshi. ""Yau me"

"ake da shi?"" Mika min table tap din yayi, na ce mishi. ""Thank you!"" Har muka shiga elevator, shi ogan"

"yana gaba mu muna baya, office dinsa muka shiga, na ajiye jakar a kan table din na koma gefe na fara"

"duba abinda ake da shi, babu fita akwai ganawarsa da masu saka hannun jari, yara zasu zo daga wata gidan marayu zasu gana da shi, haka nayi ta tattara kome ina sakawa a littafina, sannan ka mikawa Driban tables din. Ya kai ya ajiye sannan muka fita da driban ya nuna min inda zasu tattauna. Abin sha muka kawo aka jera sannan muka fito. Wurin sha daya suka shigo bakin, ni da driban muka tarbe su har inda zasu yi meeting din, ina mai musu iso, kafin na haura sama na same shi. ""Sir sun iso!"" Kallona yayi ya ce min. ""Bakya ganin ina aiki ne?"" Yadda yayi maganar kamar a tafashe yake, ""kayi hakuri!"" Na fada ina kallon kasa haka ya gama abinda yake ya dauki top dinsa ya saka sannan ya kalli laptop din na tafi da sauri na dauka, na rufe tare da bin bayansa, kamar zan kifa haka na bishi a cikin elevator ma ina kaf-kaf da da laptop din, haka muka sauko a lokacin na ga wasu team na yan gayu sun iso kamfanin, na bi bayanshi har inda ake meeting ina Kai mishi na juyo zan fito ya ce . ""Have sit!"" Juyawa nayi na kalle shi naga ba ni yake kallo ba, bakinsa yake kallo, zama nayi aia fara meeting, kallonshi nayi ta yi yadda yake magana da turanci da kuma France sai Russian haka yana nufin yaji yare, can kuma naji ya koma harshen"

"Germany, ba sai ga bakin suna tafa mishi tare da mika mishi hannu alamar alakar ta kullu......"

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 48"

"Duk da sun ji dadin tarban da ake amma haka sukai ta jan da hira.. tare da da nuna mishi bukatarsu,"

"mutumin nan dan renin hankali ne, maganar ma da kyar yake yin hayaniyar da ake yi ne yasa shi kallona, na mike zan fita daya daga cikin bakin ya kai hannunsa zai tab'a ni ya mishi magana da da Russian, da sauri ya janye hannun da sauri yana mai bashi hakuri, nima kuma yana mai bani hakuri. Ina fita waje na samu rigima ake tsakanin driban da Yan gayun nan. Na tambaye shi ya gaya min shiru nayi domin suna tabbatar suma suna da iko da kamfanin. ""Ok ku kira baki su tafi sai ku shiga!"" ""Uban waye ya baki damar gaya maka magana haka?"" Inji wata yar zafin kai, komawa gefe nayi fitowa yayi da bakin take suka yi tsit kamar basu suke ihu ba, kallonmu yayi da driban muka rufa mishi baya. Har inda motarsu take. Sannan muka dawo dawo a hankali yake yiwa Driban magana yana gama magana muka shiga kamfanin. ""Duk sun shiga halinsu, saboda irin kallon da naga yana wulla musu sai na ji dadin haka ko ba kome shi din jarumi ne akan kome, minti goma da shigarmu ya saka aka kori Yaran zuwa daya building din. Wurin karfe daya sai ga Yaran nan, haka suka shigo suna ta murna, ban yi mamaki ba amma kuma yadda yaran suke murnan ganinsa kamar dama can sun sanshi. Mika min musu hannu yayi suka rungume shi."

"Kallonsu nayi yadda yake hira da murna.. ""Wadannan Yaran marayu ne, tun lokacin Maman oga kamfani ta sayi filin gidan marayun, suka yi ta rokon arziki a bar musu filin tow kasancewar filin yana under Christian sai ta basu, tare da cewa ita me zasu bata. Saboda adalcin da ta musu shine suka amshi Muslunci, bayan rasuwarta Baban oga ya rike su da kula da su, haka yasa koda ya rasu shima sai aka cigaba da kula da kamfanin ko bai je ba, haka zai yi video a turo da fadar sunansu, sun sanshi sosai domin ko sabon baby aka kawo za a tura mishi ya saka mishi suna, hatta sunan gidan Marayun sunan"

"Mahaifiyarshi ce."""

"Gyada kai nayi, wunin ranar akan Yaran nan muka yi shi, ni kan tafiya sallah nayi da na tafi ban dawo"

"ba sai La'asar, tunda na dawo kallo daya yayi min bai kara magana ba. Driban yake tambaya ta dalilin zaman da nayi nace mishi ai na tsaya Sallah la'asar ne. Wurin cin abinci Driban ya ja ni muka tafi, shi kuma muka barshi da Yaran da suka ci nasu. Ganin kusan ganye nace a saka min sai kifi da Dan wake"

"kaWan, sannan na dawo na zauna. Haka muka fara cin abinci, ji nayi kamar abu me sanyi yana tsara jikina"

"ashe ruwan sanyi ake zuba min, ni kamar na santa. "" Karuwa bakiWaya kin makale mishi, kina abu kamar"

"baki san kome ba idan baki kyale shi ba sai na saka an kashe min ke jaka wawuya mummuna baka katuwa!"" Ji nayi kunya ta kama ni kamar na nutse a wurin, "" Badr meye haka?"" Inji Mamar Yaran nan. "" Amma kin san duk wani abu idan na Brother Turaki ne yana da muhimmanci ko? Ita din sabuwar sakatariyarsa ce, sai ki san yadda zaki mishi bayani ya fahimta."" Sai a lokacin tsoro da kunya ya kamata"

"Driban da naji matar ta ce mishi.."" Taj baka gaya musu replace Mrs Thomas tayi ba ne?"""

"""Ma na gaya musu na kai musu a rubuce basu dauka da muhimmanci ba ne!"" Riko hannuna tayi"

"Mamar yaran zuwa office dinta, a hanya muka hadu da shi, bai mana magana ba, itama bata mishi ba.. office dinta muka je ta bani kayan da na saka nawa kuma ta kai wani daki ta baza min shi. ""Zauna!"" ""Na gode!"" Murmushi tayi tana faWin. ""Sunana Jasminah ni kanwar Brother Turaki ce, mu biyu muka rage a cikin mu shida. Iyayenmu sun rasu."" Yadda take bani labarin sama sama yasa na dan ji ta bani tausayi. Buga kofar aka yi ta ce a shigo Taj ne ya zo da paper Bag ya mika min. ""Ki sauya kayan!"" ""Na gode na riga da na sauya ai."" Amsa tayi tana faWin. ""Mun gode"" ta amsa tare da mika min,"" yace Idan kin gama akwai aiki da abubuwan da za ayi gobe! "" Mikewa nayi na bi bayan shi, ban jira ta cewar ta ba, muka nufi sama muna hira har muka isa office Winsa. Da dariya a fuskarmu muka isa. Da harshen yarbanci yayiwa Taj magana da sauri ya fara faWin.."" am sorry sir!"" Hakuri yayi ta badawa. Fita yayi ya bar ni a office din ni Waya. Wato da mutumin nan yayi ta min fada da masifa tare da nunawa ban san aikina ba, nazo sai dariya nake kamar wata shashasha, mutumin nan ya ci mutuncina. Haka na sunkuyar dakai nayi ta kuka. Cikin kalmomin da basu wuce a kirga ba ya ce min. ""Zan kore ki."" Haka nayi ta bashi hakuri, karshe na fita. Koda na fito waje stair na biyo a hankali nake tafiya ina kuka. Sai da na sha kukana sannan na koma can staff office na dauki kayana sai kallona ake na nufi office din Aunty Jasmin na dauki kayana. ""Me ya same ki Mrs Jama'are!"" Kasa magana nayi sai kuka nake, a lokacin ya shigo ni kuma na dauki kayana zan fita ta ce min.. ""Wannan fa!"" ""Na gode na jikina ma ya ishe ni!"" Na wuce shi zan fita. ""Koma ki dauki kayan!"" Kamar wanda ya dasa ni haka na tsaya cak kafin wata zuciya ta ce koma ki Wauka, ba musu na"

koma na dauka na fita daga office din.

"""Brother me tayi maka?"" Wani haWe rai yayi ya fara muzurai kamar Wadda aka mishi karya. Haka na fito"

"na dawo gidan ban yarda wani ya fahimci yadda nake ki ba, washi gari ya kama Alhamis, kamar ba zan je ba don karfe takwas na isa. Sai gulmar da ake yi naga sauran mala'ikan nayi, karar aka aiki a can sama yasa nayi mamaki me ya samu saman kuma? Staff office na shiga na ajiye kayana a locker na, sannan na rufe na fito ina mai nufar sama office din Jasminah na fara zuwa na ajiye mata kayan sannan na fito, kafin na haura ma uban yan masifa, na ga kofar shi aka cire aka saka na glass sai wajen ana ta haWa karamin parlourn da office ne, wurin yayi kyau sosai. Juyowa nayi na sauko kasa ina jin kamar yau na koma gida, haka na zauna har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login