Follow us on social media

Showing 81001 words to 84000 words out of 140751 words

Chapter 28 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

305

suke wurin karti ne majiya karfi, sai yan mata yan gayu masu"

"kyau da su, sai na ji na muzanta, gasu gwanin ban sha'awa yadda suke wani yauki zaka fahimci yan gayu ne da basu son tara kitse, wannan yanyin ya dauke kin dan kwarin gwiwa da nake da ita, a hankali na isa ciki tare da tura kofar sai aka bude ta ciki. ""Lubnah ko?"" Gyada kai nayi ina mai kallon cikin wurin yadda kowa yake rayuwarsa. Wasu suna motsa jiki wasu kuma suna hira can gefe da aka saka wani abu kamar labule mata ne a zaune suna yogo. A hankali nake bin wanda ya min magana, wani office ya bude mana, wata kyakkyawar bakar mace cikin shigar kamala da mutunci zata iya kaiwa arba'in amma yadda take kula da jikinta ba zaka Wauka ta kai arba'in ba, da murmushi ta kalle ni. ""Lulu!"" Ya kira sunana, sai na ji na samu nutsuwa da ita, na gaida da ita murmushi tayi ta ce min. ""Adam ya ce min wai auta zai kawo?"" Sai na rasa a ina na santa, kurban tea dinta tayi tana mai ajiye min wani kofi a gabana. ""Baki sani ba don tun kina yar yarinya muka bar Bauchi!"" Zama nayi ina gyad'a mata kai. ""Sunana Nuratu Abdulfatahi kin tuna gidansu Kafaya?"" Sosa kai na fara ina kallon kasa na tuna gidan har yau ana kiran gidan da sunan. ""Nice Kafaya."" Sai na ji kamar an yantani daga wani yanayi na musamman, muryanta na ji a kaina tana tura min cup of tea din. "" Lokacin da Dr Dijah Bala tayiwa Wasim magana ban san cewa ke ce ba, da nace kawai ki zo, sha kada ya huce "" dauka nayi na kurba ba sugar sai kamshin kayan kamshi, da lemon tsami. Da kamshin ganyen tsamiya. "" Tea din ganyen tsamiya ne, yana taimakawa. "" Ta fada tana murmushi, haka na sha sannan ta cigaba da cewa."" Adam yazo wai biya miki, kawai aka turo min shi OMG kin san rabona da Bauchi shekaru ashirin kenan fa yau ga sai dan Bauchi kuma Wan unguwarmu, dan abokin Babana."" Murmushi tayi kafin ta sha tea din nima rashin sabo yasa na sha kaWan..""Bayan rasuwar Babanmu muka dawo nan, Mamanmu ta cigaba da kula da mu har na samu miji nayi aure"

kasancewarmu Yarbawa da aka haifa a cikin arewa sai muka taso da dabi'ar yan arewa bamu manta da

"yarenmu ba."" Shiru tayi tana kallon yadda nake kallon tea din. "" Kada ki damu zaki saba da shi."" Ta fada"

"tana murmushi, ""Na auri wani dan uwana kuma kabilata, sai dai zamanmu bai yi dad'i ba haka muka rabu da dakyar shima ba ni ce na nime saki ba, mun haifi yara biyu da shi, kamar yadda kike gabana haka nima na kasancewa. "" Sunkuyar da kai tayi ina ganin yadda take dauke kwallar da yake zuba mata, haka na rabu da shi na cigaba da rayuwa, sai Allah ya haWa ni da wani dan kasar ghana yazo nan yana kasuwanci ya koma, wani abu da ya faru shine yadda aka yi ta cin zarafina da kibar da nake da shi."" Ta kalle ni yadda nake kokarin toshe bakina, saboda kukan da yazo min. ""A lokacin kaf narasa wani wanda zai dafa min ga tsohon mijina da yake yawan d'aga min hankali, haka Mr Anwar wanda ya kasance bako a cikin mu, shi ne mutum na farko da ya fara kallona a matsayin mutum mai daraja, duk da an san cewa mijina shi ya sake ni don kanshi amma sai da aka yi ta hango gazawata da nuna min halayyata ce bai da kyau domin tunda ya sake ni bani da hali mai kyau ne, haka na cigaba da taimakon Mr Anwar ya gaya min cewa dole na rayu domin har na fara fama da ciwon damuwa, a irin haka na rasa Yarona karami a wani ruwan saman saboda ya je wurin Babansa, a hanya dawowa ya fada cikin lambatu, sai da na ji ina ma da nice na mutu, sai mace da take tare da ni, Mahaifiyata ta kaWai ta fahimci yadda nake rayuwa, hatta yan uwana sai da suka na tsani kaina na ji bana kaunar kaina. Wannan yayiwa tsohon Mijina dad'i"

"bani da zabi dole ya cigaba da abinda yaso. """

"Turo kofar aka yi wata matashiyar budurwa ta shigo tana faWin. "" Momma! Daddy yana ta kiranki fa!"""

"Daukar wayar tayi tana faWin.."" Tuba nake Sarkin da yake mulkar zuciyar Kafaya!"" Ban san me ya faru ba sai ga tana dariya tana faWin."" Idan ka sake na kama ka zaka sha wuya! "" Fita yarinyar tayi tana faWin."" Momma baku girma ke da Daddy;"" ta jima kafin ta katse wayar ta ce min. "" Sorry Mijina haka yake baya iya minti talatin bai ji muryana ba."" Murmushi tayi sannan ta daura da cewa. "" A lokacin na rasa kowa dai Mr Anwar shi ya tallafe ni da shawara da yadda zan tsaya domin har rasa aikina nayi, shi da kanshi ya bude min shagon saloon na fara Allah ya saka albarka a shekara daya na samu damar komawa makaranta, shi ya kara bani shawarar na rage jikina, ina cikin haka sai ya bijiro min da soyayyarshi, duk yadda naso kauce mishi haka ya shiga duk inda xan ji maganar mutane, yayi min hidima da ba xan iya tsallake bu™atarshi ba, a lokacin na tsaya da kafata da taimakon shi na san wacece ni, bai taSa nima na da wani fasikanci ba, sai dai gina ni da yayi da soyayyarshi wanda ya saka na fahimci kaina na fahimci ashe nima mace ce, tunda ni na bukaci mu yi aure idan har da gaske yake, bayan wannan yarinyar da take waje, Nasiba, sai Abdullahi da Hafsa, da na haifa da shi. Sannan shi ya kara tsaya min har na bude nan ina aiki da ma'aikatan gidajen kurkuku na jahar nan, a can na hango Mijina Babansu Nasiba, kinsan me yasa na baki labarin nan?"" Girgiza kai nayi, ina share kwalla murmushi tayi ta ce min."" Saboda ki gane kafin ki zo nima ban gina nan domin niman kudi ba, sai da labarina ya gina min nan, asalin nan Labarina ne ya gina min shi ™addarata tana da nasaba anan, a duk lokacin da aka kawo sabuwar daliba abu daya nake tambayar me ya kawo ta me yasa ta zo? Idan tana da past dinta Mai duhu sai na daura mata nawa labarin ta gane nima ban gina nan ba sai da nawa labarin, akwai mata victim irina da irinki, anan muke bude zuciyarmu, ki saki jikinki Adam ya gaya min kome ya kuma bukaci mu taimaka miki, idan har da gaske sauya kanki ke kanwata ce dole na baki special class domin bana son na hada ki da kome, na tuna lokacin da Babanmu ya rasu har kudin da aka biya na motar da zaa dawo damu Alhajinku ya biya mana hatta abincin da zamu ci na tsawon wata shida, kafin mu bar tsohon unguwarmu Alhajinku yana mana aika duk bayan wata shida, kayan abinci da sutura daga baya fitinar dangin Babanmu yasa muka bar"

"unguwar, daga muka rasa taimakonsa. Yau ga Lulu da na tafi na barta tana Yar shekara shida a gabana!"""

"Murmushi nayi ta ce min.."" zaku school ko?"" "" Karfe bakwai muke tashi idan kin taso sai ki zo ki amshi"

"tips dinki! "" Godiya na mata sannan na bar office din, sau yawa mukan yi alkhairi ba tare da mun san zai dawo ko ya tafi ga mizaninmu, duk da abinda Abba yayi amma yau alkhairinsa da rokon marayu ya saka na samu nima wata alkhairin da shi ya aikata. Murmushi nayi duk da laifinsa yau naji ina sonshi ina kewarsa. Don haka da na shiga motar da zai kai ni makaranta, na fito da wayata ina kallon wayar number shi ne don ko na rasa number kowa bana iya manta number shi da Yadiko da Mama, haka nayi ta kallon wayar. Har muka isa makaranta na biya kudin na fara tafiya, sai da na shiga makarantar sannan na samu wuri na zauna. Da yake karfe daya zamu shiga class na kira Number Abba, haka wayar yayi ta ringing bai dauka ba, na sake kiran bai dauka ba, sai a karo na uku ya Wauka. ""Waye ke kira haka?"" Haka yayi ta magana na kasa magana sai hawayen da yake zuba min haka ya gaji ya kashe shi wayar, kuka nayi ta a wurin na rasa abinda yake min dad'i, sake kiran Mama nayi tana dauka na ce mata.. ""Mama ina kewar Abba ina son ganin Abba Mama ina son Abbana, Mama ki koma wurin Abba ko don ni, Mama ina son Jin muryansa da farin ciki da annashuwa, amma na rasa Mama."" Abinda ba zai tab'a sauya our Afrika mother, wato da ta danna min wani Ash'ar tare da zabga min warning idan na kara kiranta akan Abba sai ta ci Ubana sai na tsinci kaina da yin shiru, ban kara magana ba, kai na ga jidali da lukutar masifa, tass ta wanke ni kafin kuma ta sauko tana rashina, daga haka nayi shiru bayan mun gama waya sai ga kiran Aunty Innah ina gamawa Aunty Hindatu ta kira ni, sai ga Ya Umar da Tahir, ban gama nutsuwa sai ga Ya Ado. Ina zaune a wurin ya kira ni na dauka ya tambaye ni ina aji ne? Nace a'a gani a lambun makaranta bari na fito, har a lokacin kuka nake a hankali na dauki jakata na fita yana tsaye ina isa wurinsa na goma gefen da yake tsaye na kifa kaina a gefen hannusa ina kuka. ""Kina kewar Abba ko?"" Jinjina kai nayi, kiranshi yayi bayan sun gama gaisawa ya ce mishi. ""Abba kai min wata alfarma daya?"" ""Ina jinka!"" ""Zaka yi magana da Lulu ne tana kewarka, gata nan."" Kafin ya kara magana ya manna min wayar a kunnena, sai dai kuma nayi danasanin kiran Abba da Ya Ado ya min, Abba ya kara watsa min bakin fentin da ba zan tab'a mantwa da shi ba, sau gani ina wani irin hakki zuciyata, ta kasa Waukar mugayen kalmomin Abba, tun ina jin shi a tsaye a har na jingina da motar na zame kasa, domin kafana sun kasa Waukar nauyina, zuciyata ta gagara daukar maganar da Abba yake gaya min, wani irin nauyi na ji tare da bude bakina ina niman numfashi, fisge wayar Ya Ado yayi ya saka a kunnenshi ya ce mishi. ""In sha Allah ba zan kara kiranka akan Lubnah ba, ba zan kara ce maka ga ta ba, Abba idan ka yi sanadin mutuwar Lubnah Allah ba zai barka ba!"" Kashe wayar yayi ya d'ago ni tare da saka ni a motar domin har an fara taruwa, ruwa wani dan ajin mu ya mika mishi yana faWin. ""Bata tana bukatar ruwa!"" Amsa yayi ya bude min ya kafa min na shanye, sannan aka kira class rep dinmu aka gaya mishi halin da nake ciki ya ce a je da ni gidan, da taimakon Allah na samu nutswa, daga haka na rufe idanuna, a hanya Ya Ado ya kira Mama ya gaya mata, halin da na shiga amma bai san me Abba ya gaya min ba, ai kuwa Mama kamar ta dirko ta wayar fada take yi kamar zata aro baki ta kara. Kuma tayi alkawarin sai ta kunyata Abba shima kamar yadda ya min a"

gaban Jama'a domin ranta yayi mugun b'aci.....

(Kuna ganin mu bar Mama tayiwa Baban Bauchi tijara a bainar nasi? Yes or no

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 33"

"Gida Ya ado ya kawo ni na kwanta, duk da bana jin barci amma na zaSi nayi lumo. Ina jin kamar na ni ba,"

"taya mahaifin da ya haife ni zai tsane ni ya kira ni da karuwa? Abba ya kira ni da karuwa! Naki zaman aure na biyewa Adamu ya yanka min tikitin karuwanci a lagos, tow in sha Allah idan n kwaso kwanjamau sai dai na kare ni daya na domin suma guduna zasu yi. Bude idanuna nayi tar ina kallon hannuna. Wani irin sarawa kaina yayi kamar an hada karfe da karfe a hankali na ji abu yana zubewa daga hancina, ban kula ba sai da na ga zubar yayi yawa na tashi zaune ashe jini ne, yadda kaina yayi wani irin nauyi haka na koma na kwanta tare da lumshe idanuna, bana son karawa Ya Ado wani damuwar a hankali nayi ta ambaton Allah har na samu sauki na tashi zuwa ban daki na sakarwa kaina ruwan sanyi, can kuwa jinin ya tsaya, na jima a ban dakin na fito na sauya kaya. Na sauko kasa ba kowa sai mai aiki haka na zauna a"

parlourn har lokacin sallah yayi na wuce nayi sallah na kwanta barci ya dauke ni.

***

"Mama kuwa da suka gama waya, tashi tayi gaban wardrobe dinta, kayanta tayi ta sauko da shi, ta ciro"

"wabujejen wando mai matu™ar girma kamar palazzo, ta saka ta dauko wani babban hijab dinta ta saka, sannan ta fito zuwa bangaren Umar ta bugawa matar gidan kofa da sauri aka bude tana ganin Mama ta ce mata. ""Mama ke ce? Fita zaki yi? Lafiya dai?"" ""Central zan je!"" ""Lafiya dai ko? Ai da an gayawa Baban Nawwara ya miki ba sai kin je."" ""Yanzu xan dawo"" ta juya ta fita yadda zuciyarta take tafasa idan ba tsinkawa Abba rigar mutunci tayi a idanun duniya ba, ba zata tab'a jin dadi ba. Don haka ta nufi waje,"

"tana fita matar Umar tana kiranshi, sai aka yi rashin dace ya shiga sallah, baya kusa da wayar ma."

"Mama kuwa tana fita ta samu me keke napap, ta ce ya kaita Central ya fada mata kudin bata damu ba,"

"ta ce su je. Kawai yadda zata yiwa Abba rashin mutunci kawai take hasashe. Duk da gudun da me Napep din yake amma Mama gani take kamar ba tafiya yake ba, kamar ta rufe shi da duka haka take ji, haka ya sauke wasu mata a unguwar Jaki, sannan ya fito ta masallacin Shehi dahiru Usman Bauchi, ya iso daidai office din Yan sanda na Central ya tsaya ta fita ta biya shi kuWinsa,. Sannan ta tsallaka cikin Central, sai da tayi tafiya sosai kafin ta isa layinsnu Baban Bauchi, an taru a kofar shagon ana cin abincin da ake kawowa kasuwa kullum daga gidan domin saukakawa Yaran shagon kashe kudin abincin. ""Usman Jama'are nazo wurinka ne?"" Da mamaki kowa ya juya yana kallon Mama. Wacce ta hade rai sosai kamar ba ita tayi maganar ba. Da kamar ba zai kulata ba sai can ya ce mata. ""Ki je gida zan zo!"" ""Ba isa ba! Ka gaya min yaushe ka ci maita da kake son kashe min Y'a? Mai Lubabatu tayi maka da zafi har haka?"" Shiru yayi kai dan kanzagi ya taso yana faWin. "" Mama kasuwa ne nan don Allah ki yi!..."" Tass Mama ta wanke shi da mari, ta kara wanke shi da mari sai da yayi baya kamar zai fadi, Baban Bauchi ya ce mata. "" Wacce irin hauka yake damunki? "" "" Irin wanda kake dauke shi! Irin wanda yake kanka, irin wanda ya saka ka yi fatali da zancen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kowa Ni shugaba mai kiwo ne, kuma za a tambaye shi akan kiwonshi. Gaya min kuskure ne don na kashe Auren Lubnah da wannan Tsinannen yaron da ya bata maganin hana haihuwa? Laifine don ka kashe aurenta da azzalumin Yaron nan da ya nemi haukata min ita? Me yasa Victims na mata yafi na maza yawa? Me yasa? Yau da Lubnah daukar wuka tayi ta soke shi wannan shagon ka rufe shi kenan saboda abin kunyar da tayi, amma daure ta yayi a cikin gidansa yana gana mata azaba, muka rufe idanunmu saboda zumunci! Eh kalmar zumunci tana"

"daga cikin sunayen Allah, gaya min me yasa ka saka min ita cikim Ukuba? Yau ni Salamatu Galadima na"

"zo gabanka da muryata da Muryan Y'ata, idan wani abu ya same ta. Zan tabbatar da na tab'aka na kara"

"tab'a ka sai na mai da kai zero plus zero yadda kowa sai ya yi tir da kai. "" Wani abokin shi ya ce mata. "" Hajiya don Allah ki yi hakuri a karasa a gida don Allah, anyi miki laifi muna rokon arziki a bar maganar nan! "" Ta kalli mutumin ta ce mishi. "" Alhaji Imarana! Idan maita ce ni da shi Bismillah, idan kuma ina ganin babu maitar hali ce kawai Ni dashi shege ka fasa! "" Daidai isowar Tahir da Umar hankali a tashe. Har ta juya ta ce mishi. "" Usman Jama'are! Na rantse da Ubangiji Adamu da Muhammad, sai na tsayawa Lubnah, sai na bata kariya sai na hanata kuka akanka da shi wancan Tsinannen yaron, Usman Jama'are idan ka isa da Tsinannen Yaron nan kace ya fita harkan zuriarta ba Lubnah ba wani cikin Yarana wancan shegen. Ya kara mu'amala da su sai na yi Shari'a da kai da su. "" Har ta cigaba da tafiya ta juya cike da takaici ta ce mishi. "" Wallahi billahi azim na kara ganinka tare da Yarana sai na ga uban da ya tsaya maka a Bauchi, ku ai ba mutane ba ne dabbobi ne a cikin shigar mutane. "" Huci tayi kafin ta juya a hankali Umar da Tahir suna take mata baya ta juya tana kallon Baban Bauchi dariya tayi ta ce mishi.."" kamar yadda ka yarda min Y'a a cikin makaranta ka saka kowa ke mata kallon tausayi da hauka yau kai ma ka ji yadda take ji! Feel it I said it how lubnah she survived, ka ji kunyar da taji a duk lokacin da ta fita hayacinta,. "" Ya kara takawa har habansa "" how you feel it? Da kunya ko? Haka take kallon kowa yana jin tausayinta, kun mai da min yarinya wata iri ta koma kamar ba bil adam ba. "" Aunty Innah da suka iso kasuwar da Hindatu ta rufe mata baki, fisge bakinta tayi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login