Follow us on social media

Showing 63001 words to 66000 words out of 140751 words

Chapter 22 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

304

ta yaye me sunan Baffa, sai ga wani cikin. Murna a wurin harisu da su Daddah abin ya wuce sanin kowa, haka aka haifi wannan karon namiji, a take yayiwa Yaron huduba da Jibrin suna kiranshi Aydin, bayan wannan Yaron bata kara haihuwa ba, sai bayan shekaru goma, ta haifi Fadime. A lokacin KUMO properties nigeria agency ya kai matakin da sai da aka bude mishi branch a Kano Fatakwal da Abuja. Annah Aisha itace bakiWaya CEO na kamfanin yayinda Haris yake vice President na kamfanin wanda ya janyo idanun yan uwansa ya tsaya"

akansu.

"Kusan rabin dukiyar kamfanin 65% na Annah da Yaranta ne, 5% na masu saka hannun jari ne, 20% Na"

"ELYakub ne 10% na Harisu. Annah bata yi duhun kai ba duk yaran ta raba musu hannun jarin musamman Bilal Turaki, wanda ta bashi 25% na hannun jarin. Saboda shi yana karatu a King Abdul Aziz International school Riyad tare da Ubaidullah Jibrin Kumo, haka yasa bai wani san damuwa ko tashin hankali ba, yana aji biyar na secondry School, bayan sun kawo mishi ziyara, Allah ya musu rasuwa bakiWayansu Ita Annah Aisha da Kannensa. Kuma ba a gaya mishi har sai da ya gama karatu suka dawo gida aka gaya mishi a lokacin ya zo ya samu Mahaifinsa da wata mace ba Mommy dinsa ba, kamar yayi hauka don yaji ya tsani. Haka yasa shi yayi fushi ya koma wurin kakaninsa, har izuwa lokacin Ubaidullah bai rabu da shi ba, domin da zai koma Rasha tare suka tafi a can suka cigaba da karatunsu, kaf duniya babu wnada ya fahimci Bilal Turaki sama da Ubaid, yasan halinsa yasan shi sama da sanin da zaka yiwa wani a duniya. A lokacin da Annah Aisha zata rasu a cikin kwanakin ta haWa kan hannun jarin bakiWaya ta tattarawa Bilal Turaki, domin tana jin wani strange abu yana bibiyarta, haka yasa ta haWa kome ta tura Rasha wurin iyayenta da yan uwanta. Bayan haka Haris da ya auri Zeenatu itama tana zuwa ta samu cikin Jasminah a burinta namiji zata kara haifa sai aka yi rashin dace ta haifi Jasminah, wacce suka daurawa jigon 20% na hannun jarin Haris zai bar mata. Shi kuma kamar wanda aka gaya mishi ya raba hannun jarin ya sakawa Ubaidullah 5%. Bilal 5% Hajiya Zeenatu da yarta 10% sai abin ya fisgi hankalinta akan me za a karawa Bilal a kuma bawa Ubaidullah da bai zama kome a cikin KUMO FAMILY GROUP ba. Shi kuwa ya ce ya"

yanke.

Tsakanin Alhaji Haris da Annah Aisha shekaru shida chib wanda ya tilastawa Bilal Turaki dawowa

"Nigeria, shi kan Ubaidullah ya jima da dawowa gida domin har yayi aure da zuri'arshi. A lokacin rasuwar Mahaifinsa ne ya zo gobe tun suna Yara sukan zo bikin sallah karamar Sallah da babbar sallah. Haka sai yasa Kumo Family group matan suka saka buri akan magajin KUMO properties nigeria agency, domin ya haWa degree dinsa na farko yana da shekaru ashirin cib a duniya. Wannan rashin da yayi duk da yana jin zafin mahaifinsa, ya kara pushing dinsa gefe ya saka shi kara zama wani irin mutum me murdaden hali."

"Da manya da yara na Kumo Family group kowa shakkarsa yake, bayan gefe guda gasa suke da juna."

"A lokacin abinda Alhaji ELYakub yayi shine bawa Bilal Turaki kujeran mahaifiyarsa, kasancewar ita"

"ce mafi yawan hannun jari wanda a yanzu Bilal yana da kashi 70% na hannun jarin KUMO properties nigeria agency, sai dai haka kawai ya juya ya koma inda ya fito, ya cigaba da karatunsa. Bai kara dawowa Nijeriya ba sai rasuwar Alhaji Jibirin Kumo,. A lokacin yana da shekaru talatin da wani abu a duniya, akwai ciwon da yaji da yasa shi tattarawa ya koma Germany wurin Ellina, Kanwar Annah Aisha, tana"

"auren wani magajin garin Berlin, anan ya cigaba da aiki da babban Cibiyar nukiliya ta Germany."

"Yan mata dayawa sun yi kuka akan Bilal Turaki, amma shi ko a kwalarsa. Bai damu da kowa ba a"

"duniya sai mutane hudu, Alhaji ELYakub, Daddah, Uncle Auta da Ubaid, haka a wurin kakaninsa na Uwa"

"yana sonsu. Turaki mutum ne da baya shiga rayuwar kowa, baya kuma da rawan kai irin na yaran masu kuWi, duk da gadon da yake da shi Bilal niman kudi yake kamar ba attajirin da aka tara mishi ba, an taSa"

hira da shi. Aka tambaye shi me yasa yake niman kudi bayan yana cikin manyan matasan Nigeria masu

"arziki, budar bakinsa ya a cikin muryansa mai sanyi da dadin amo, ya ce musu. ""Wancan dukiyar ba Bilal yayi faffutukar tarawa ba, dukiya ce da mutane uku suka tara idan nayi amfani da shi akan kaina na zama cima zaune idan na nima da kaina zan iya rike kaina da kuma duk wnada zai zauna a gefena."" Idan bilal"

yayi magana mai tsawo haka yana nufin yana son maganar ce.

"Kai ko a cikin abokai ne yana iya ware kansa, ya koma gefe yana abinda yaga zai iya. Yana iya daukar"

"nauyin abokansa ayi shagali amma shi zaka hango shi can gefe yana wani aiki abinsa. Idan kana son ganin asalin Introvert tow Bilal ne, domin ko lokacin da ya fara soyayya Ubaid da Alhaji ELYakub suka sani, haka da yarinyar tayi rejected dinsa, sune suka san me ya faru. Da abin ya faru sai da yayi kusan kwanaki uku kafin ya tattara ya bar musu kasansu. A lokacin Alhaji ELYakub yaso ya je har wurin dangin Yarinyar ya nuna musu jikanshi ba talaka ba ne, amma ya ce mishi.. ""Ni mace nake so da zata so ni ba"

"tare da tasan who am I, kada ka je ina ji a jikina ita din mahadar rayuwata ce."""

"Duk da yan matan da suke hauka da fada da dambe akanshi, haka bai taSa burge shi ko jin a ransa suna"

kan daidai ko sau daya basa gabanshi.

"Hajiya Khaulatu tana da Yara biyu, Khamis da Khamis baya jin magana, niman mata shaye-shaye, fadar"

"area ta dabba. Duk wani iskanci ya kare a gindin Khamis sai yar su ta biyu Badar tare da Alhaji Abbas, wacce take zaman jiran Bilal, don tace sai dai ta mutu bata yi aure ba. Mimi yar wurin Hajiya Zeenatu tsohuwar matar Haris, bayan rasuwarsa aka hada auren da Alhaji Mudansir ELYakub, bayan Jasminah ta haifi Mimi Fatimah, ita bata damu da wani soyayya ba, don ita ce asalin Queen of Kumo Family, ana ji da ita. Zaheeda, yar gidan Hajiya Samirah itama tana son Bilal, don ita har inda yake ta je mishi. Badar kuwa"

a gidansa da yake Lekki take zaune.

"Sai Nasmat wacce take nan lagos a gidan Uncle Auta, shima Uncle Auta da yake da Iyali Yaranshi"

"maza hudu ne, kuma kanana ne, Yakub wanda suke kiranshi da Amir, sai Harisu wanda suke kiranshi da Akhi, sai Jibrin wanda suke kira da Aalim. Kaf duniya daga Ubaid sai Uncle Auta suka san meye Turaki yake so, me yake bukata ja'iri bai da alkibla, akwai wani zuwan da Turaki yayi lokacin Alhaji ELYakub bai da lafiya an dauka mutuwa ma zai yi aka gaya mishi, zuwan da yayi ya tashi wani tashin hankalin da ba taba gani ba, domin ya zo gidan duk babu kowa a gidan domin bai gaya musu yana hanya ba, a lokacin da ya iso gidan domin drop ya dauka har gida, da farko security din basu gane shi ba, domin shigar da yayi sai da ya cire facemask dinsa suka gane shi ne, haka ya shiga gidan akwai wata yar mota da take kai mutane har cikin gidan, ita ya shiga aka kawo shi, zuwan da yayi ya shiga bangaren Daddah anan ya samu Mimi tana yiwa Daddah barna, shi kuwa ya kamata ya zane ta, karshe ya rufe part din Daddah ya"

"tawo asibitin, ana ta murnan ganinsa sai ga kira daga gidan, aka kira Hajiya Zeenatu tana isa gidan ta ga"

"abinda yayiwa Yarta, ai kuwa ta kawo yarinyar, jin haushi da kishin yadda aka wani zagaye shi ta saka"

"hannu a kai tana kuka wai yayiwa Yarta fyade. Wannan abin ya daki Turaki. Kiri-kiri Badar tace mata. ""Karya kike Maman Mimi!"" Da yake yaran a sangarce suke ba wanda ya kwabe ta."

"Case Win sai da aka hura shi ya zama babban al'amari, hankalinsu ya kwanta Alhaji ELYakub yana ji yace"

"su bar mishi gidansa, bai lalata na wasu ba, zuriarsa ba zasu lalata nasu ba. A lokacin Turaki yayi fushi ya bar musu kasar, suna son ya dawo ko don yanzu a raba matsayi a kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma yaki dawowa, yaki yin wani motsi su kansu basu san inda yake ba, idan ka cire Uncle Auta"

"da Ubaid, babu wanda zai baka labarin inda Turaki ya™e."

"Ita kuwa Daddah cewa take aljanun sun aure mata jika domin yaki maganar aure, ko irin kiranshi Uncle"

"Auta yayi haka zata gama surutunta baya ce mata cikanki, har mamaki yake yadda bai damu da magana ba, sam shi magana tafi kome bashi wahala. Don da yayi magana gara ya shiga daki ya kwana ya wuni. Shi har mamaki yake idan ya ga mutane na magana, idan da zai yi magana tow abun da zai magana a kai"

me muhimmanci ne.

***

Lulu.

"Na samu wata biyu, ina zuwa wurin Mrs Dije Bala, sannan gefe daya ya haWa min wani tables na abincin"

"da nake ci, domin maganin da haifi yake bani sun yi sanadin da kitse da uric acid ya taru min, haka yasa nake samun wani irin gajiya. A hankali nake bin kome, kullum haka zan tafi wurinta na dawo. Ya Hafiz"

"yaso kashe ni ne, Allah bai nufa ba."

"A hankali na dan fara samun nutsuwa, ina cika wata uku na gama iddana, a lokacin naji kamar na"

"samu yanci, har da wannan iddar ya saka min traumatic domin gani nake kamar Ya Hafiz zai iya cewa ya dawo da ni, a wurin da nake zuwa akwai Reheb, a nan idan na je naji matsalar wasu ashe ni nawa mai sauki ne, domin gashi wasu yaran masu kuWi ne wasu matan masu kuWi amma rayuwarsu ta lalace, akwai wata yarinyar da muka hadu sunanta Baby Mahaifiyarta yar Jos ce, mahaifinta kuma bayarabe amma gata yasa ta lalace, sai gashi ta samu miji shi ya kawo ta wurin Dr Dijah Bala, yarinyar tana da saurin sabo,"

"duk yadda naso na ki biye mata, haka take makale min."

"A bangaren Ya Ado abokan aikinsa har mutum uku suna niman izinin aurena, ce musu yayi su yi hakuri"

har yanzu Lubnah she still small girl...

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 24"

"Wannan kalaman ya saka aka shafa min lafiya, tabbas ina bukatar spaces sosai Ina bukatar nutsuwa"

"wanda zai saka naji nima mutum ce kamar kowa, ina bukatar farin ciki da nutswa amma ta ya? Ta hanyar bani duk wani tazara da zata saka ni farin ciki, a hankali rayuwata ta mike, har watan azumi ya zo farkon watan azumin Ya Ado ya mana albishir da zuwa Umara a can zamu yi sallah, Yadiko Abba ya biya mata da ita da shi, Mama kuma Ya Ado ya hada mu ita xata tashi ta Bauchi, mu kuma ta lagos, wani abu da ya kara d'aga min hankali wannan kibar yana damuwa duk yadda nake son rage shi kamar kara shi nake, haka yasa Doctor Ahmad ya hada ni da wani likita anan lagos a cikin wata azumin kafin mu tafi Umara, lokacin da na ga likitan, ya sake tsara min abinci sannan ya hana ni shan kowani magani da zai saka ni nayi slimming domin na fara shan wasu ganyen shayi, ya hana ni. Kamar da wasa na fara shan kiyayye maganin da yanayin, sai dai kuma ko ana gobe zamu Umara, sai da ciwon ciki ya taso min, haka nayi ta daurewa har muka tafi umara a can kuwa kasa mai tsarkin na fadi na suma haka aka tafi da ni asibiti hankali a tashe, lokacin da aka min test anan aka hango cutar fabroid a cikin mahaifana manya guda biyu sune suka hura min tumbina, suka ce aiki nake bukata, Ya ado yace su bani magani da abinda zasu bani kawai mu koma gida ayi min domin bai zo da shirin aikin ba. Lokacin da ya samu Mama da yadda suka yi da likitan, ta ce mishi. ""Wani ba a shirya ba kuma? Kawai mata aikin na hakura guzurin yanzu akwai abinda za a bukata a rayuwar lubnah nace babu shi? Ayi aikin Allah ya bata lafiya kowa rai ya amfana"

"baya ga mai shi ne, ni yanzu bata kaina nake ji ba, ta ita nake ji"""

Haka aka yi min aiki a washi gari ranar da aka kai azumi ashirin da uku. An cire tare da kashe waWanda

"suka fara zuba karin, sannan aka fito da ni. Yayuna a Bauchi kamar su tawo, don sun tabbatar zasu zo Lagos ganina. Sai nake jin kamar ni daya nafi kowa gata, daren ashirin da uku ake ta saka ran alamun laylatu kadr, yadda ake pretending din yanayin sai bai kasance a wannan daren ba, aka wuce zuwa daren 27, wanda tun wunin ranar Mama da take kula da ni take addu'a nima kuwa Addua nake, karshe Mama kasa hakuri tayi ta saka aka bamu keken mara lafiya muka wuce harami, ranar na ga gundarin kauna a wurin mahaifiyata, mantawa da kanta tayi tana zagaya da ni Ka'aba tana ""Allah ga Lubabatuna, Allah ka bata duk abinda ta rasa a baya, Ya Allah ka bata miji na gari. "" Sai da naji kamar buga min guduma tayi domin gabana ne ya fadi. Tsoron maza ya kara shiga zuciyata. Haka take addu'a miji na gari har wasu yan Nigeria da Nijar suka yi ta mara dariya, wai tana ta addu'a kamar ita Waya ta haifa murmushi take kawai ta ce musu, da kun san irin Izayar da na mata zaku ce ta cancanci haka. Wannan ranar Mama bata mai"

"da ni asibiti na har aka Sha ruwa, ta mai da ni, sannan ta dawo harami yin sallah tahajju."

"Asibitin kuwa ana tasowa sai ga Yadiko da su Ya Ado, da Yaran da Aunty Zakiyah, ai kuwa na ji dadi"

"murmushi nake idan suna hira, haka suka yi sahur bayan sun gama suka tafi masallaci, nima a nan nayi sallah bayan sun dawo, Mama ta koma ma sauki ni kuma aka barni Asibitin. Ai kuwa Yadiko suka yi fada da Abba ya ce ta nime abokin tafiyarta ta ce mishi.. ""da yake makauniya ka kawo ba."" Rigima fa wai akan me tazo duba ni, haka ta fada mana da tazo ni dai umarana ta bana a gadon asibiti nayi shi, ranar ya"

"kasance juma'a, don haka nima an fitar da ni domin ita ce Juma'a ta karshe, ranar Litinin ake saka ran"

"karamar sallah, haka yasa aka fitar da ni. Nayi addu'a Ubangiji ya kawo min nutsuwa da kwanciyar"

"hankali, Ubangiji ya bani kwarin gwiwa, Ubangiji ya cire min tsoron wani abokin halitta a raina, na roki Allah ya mantar da ni rayuwar baya. Ya saka min hakuri da dangana."

"Ganina a dakin Ka'aba ya saka min yarda da cewa Ubangiji yana nan yana jina, shi din rayayyen nan ne"

"da baya mutuwa, bai haifa ba, ba haife shi ba. Sai nayi kukan farin ciki ya saukar min wani nutsuwa na musamman. Naji nauyi da zafin da nake ji yana sauka a raina, na ji farin ciki da rabona da naji shi tun ina JIBWIS, a ranar Mama sai da suka yi magana da su Aunty Zakiyah wai sun ga kamar ba ni, haka muka yi ta ibada, har ranar sallah. Wayyo yadda kowa yayi wanka sallah amma ni ba hali saboda dinkina. Haka na saka abaya mai sauki. Sallah da kwana biyar muka dawo gida, haka na cigaba da jinya satin mu daya da zuwa dai ga Aunty Hindatu da Aunty Innah, Aunty Munah da Aunty Raliyah, wato wani abu da na kara fahimta shine yadda suke yiwa Aunty Zakiyah shatara na arziki, ban yi mamaki ba domin basu isa biyanta Alkhairin da take min, bamu isa biyanta biyan ba, Dr Dijah Bala da Baby sun zo min ya jiki, haka Aunty Zakiyah ta cire musu tsaraban da ta musu. Tace musu nice nayi musu sai nayi ta mamaki, wani ikon"

Allah satinsu Aunty Hindatu daya suka koma.

"Wata na biyu goshin layya ina jin duk wanda ya ganni sai ya ji na burge shi, domin jikina ya ragu, a"

"lokacin da Ya Ado yake basu labarin jinyar da nake fama da shi, Aunty Munah sai da tayi ta Bala'i ita sai ta shigar da Hafiz kotu, aka ce a kyale shi tunda na samu sauki yanzu ai da sauki sosai sai a tafi gaba."

"Haka yasa suka tsayar da shawarar ko zan koma makaranta, nima zaman gidan ya dame ni. Don haka na ce tow, na amince da shawararsu na koma jami'a a karo na biyu. Zanyi MBA wato Master Business Administration and specialization, a tsarin tallace-tallace, Ya Ado. Kullum tambayata yake. ""Lulu zaki iya kuwa? Idan kin san har yanzu akwai abinda yake damunki a hakura da shi, kin ga saboda result Winki yayi kyau sun baki shekara biyu da wata shida, idan kina ganin akwai matsala a hakura."" Yadda Ya Ado ya saka hope a kaina sai naji kamar idan nace mishi ban warke ba ban yi mishi adalci ba. Haka na ce zan iya amma har yau ina tsoron shiga Mutane, ya zanyi tow? Zan tabbata ina zaman gida ne, haka na daure sabon shekara na shiga cikin daliban da aka diba, na kwantar da hankalina, a yanayin acadamy calendar dinmu ba zan wuce shekara daya da wata tara zan gama. Haka yasa na nutswa, daga yanayin shigar da nake yasa an Makarantar suka fahimci na fito daga arewa ce, sannan yanayin fuskata, kuwa face mask nake sakawa saboda har yanzu fuskata kamar an buga donut, haka nayi ta rayuwa da tare da mai da"

hankali kamar ina yi da wani.

Yadda an ajin mu suke mamakin domin kusan nice karama amma yadda nake mukekiya sai ka

"dauka na shekara arba'in, a hankali na fara fuskantar body a shame, haka yasa na fara tsargu. Wani lokaci a tsorace nake shiga ajin. Sai ta min dariya ko tsokanata wani lokaci sai naji ana faWin luxury, ko naji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login