Follow us on social media

Showing 36001 words to 39000 words out of 140751 words

Chapter 13 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

319

tattaro min yaran bakiWaya, haka nayi ta hidima da su har tsawon shekaru biyar cif."

Duk wani abinda nake da shi Ya Hafiz ya ga na cigaba ne dai ya raba ni da shi hankalinsa yake

kwanciya.

*

Kiran sallah farko ne ya sani share hawayen da ya zuba min yanzu na fahimci dalilin da yasa min haka. Na

"ga tashin hankali a rayuwata na ga abinda zuciya ba zata iya karba ba, amma na amshe shi hannu bibbiyu, danginmu kowa ya juya min baya. Uwar da ta haife ni ta tsame Hannunta a kaina, Mahaifina ya watsar da ni, a koda yaushe nayi kuka Ya Hafiz xai nuna min ai ba kome ba ne, saboda kawai dan karamin mistake ai ba wani abu ba ne can babba da zai saka ni damuwa, Ya Hafiz Dan uwana ne tunda da Baban Jama'are da Babana uwa daya Uba daya, sannan Ya Hafiz ya boye munannan halayenshi ya bayyana kowa kyawawan halaye da Dabi'u, babu wanda zai ga ya Hafiz ya zata yana da mugun hali. Sai dai kowa yasan mai kyau kuma yasan mara kyau, idan da ni ce Ya Hafiz ba zan taba saka shamaki a tsakanin zuciyoyin da suka yarda da ni ba. Amma sai ya lalata min rayuwata da future dina da kuma duk"

"wanda zai kalle ni ya tausaya min, sai ya cusa min kin kaina da rashin accepting kaina."

"Ya danna min tsoron duk wani d'a namiji da kuma duk wanda zai kalle ni a matsayin mace, ya nuna"

"min cewa ni ai ba mace ba ce. Ya kuma gaya min cewa kaf duniya da zuriar Baba Umar Jama'are babu wanda zai ganni ya ji sha'awar zama da ni ko kaunar zama da Ni. Bayan ya ga bani da amfani ya cigaba da ajiye ni domin a ga yadda yake namijin ™o™arin kula da rayuwata. Ba zasu fahimci waye shi ba, sannan idan zasu shekara dubu ba zasu tab'a gano waye Ya Hafiz ba hawainiya ne shi mai sauya launi daga"

wannan zuwa wancan.....

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500*

"*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105"

ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita*

Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

SHA UKU

HAFIZ

"Da farko bai zata zai haukace akan tafiyar Lubnah ba, bai taSa kawowa a ransa tana da amfani har haka"

"ba sai da ya wuni yana bibiyar dangi da yan uwa ko ta je wurinsu, amma babu labarin kai ko a mafarki babu labarin Lubnah haka yasa hankalin kowa ya tashi ban da yan dakinsu da sun san mafarin. Yadda Ya Hafiz yake playing victim sai ka rantse da Allah, ba shi yake yi sanadin barinta gidan ba, aikuwa Washe gari sai ga Baba Malam, shi da Baban Jama'are da Hajiya Asiyah,Goggo Alti da Goggo Uwani sai Goggo talatuwa. Hankalin kowa yayi bala'in tashi, rayuka sun b'aci. Tambayar da Baban Jama'are da Goggo Alti suka mishi ya sake cillashi cikin wani tashin hankalin. ""Me ya haWa ka da Lubabatu da har ta dauki wannan matakin?"" ""Wallahi na rantse da Allah ban mata kome ba, kishi yake janta."" ""Yarinyar da magana ma bai dame ta bane zata yi kishi har na fitina? Hafiz kasan ina da labarin abinda kake aikatawa!?"" Inji Mahaifinsa, take Baba Malam ya rufe shi da fada. ""Ya ana cikin wannan tashin hankalin zaku kara mana da wani. Ku barshi da ji da damuwar da yake damunsa ba a kara masa wani ba, gaya min me kuke son cewa."" Goggo Alti ta ce mishi. ""Baba Hafiz munafiki ne, ba kan Lubnah ba hatta Sirajo sai da Hafiz yayi sanadin barinsa shagon Shehu, yanzu haka ya koma wurin Babana yana zaman shagon, Allah ya gani tunda ka yi sanadin da Babana ya bar shagon na fara tunanin ya kuke zaune da Lubnah kowa yasan yadda kake nunawa ka damu da ita bayan kuma kai ne shaidanin da kake rabata da duk wani farin cikinta, Shehu da kanshi ya kira ni yana gaya min ya kori Sirajo ina laifin ya ce min na ja mishi kunne, bayan abinda Sirajo ya sani gaskiya ne, Ali ka ganshi idan akace min zai dafa mutum ya ci zan yarda domin munafiki ne na gaya muku gaskiya. "" "" Alti ina magana! "" "" Baba dole fa mu fadi gaskiya domin Lubnah kaWai ba zata iya fadar abinda take ji ba, azzalumi mugu hatta dukiyarta sai da ya lalata mata ya kwashe maha'inci, kai akanka ba ka bar kanka na balle wani haba don Allah wacce irin rayuwa kake yi ne haka? Wacce irin manufa kake so ne? Ina tausaya maka Shehu yaranka da ka watsar ka ce basu tausayinka wata rana su zasu dafa maka domin. Wannan munafikin ya hmm! "" Tayi murmushi mai ciwo, tsoro ya kama Ya Hafiz haka dai aka tashi zuciya ba dad'i. Mama ita kanta yanzu ta fara tsoron kada wani abu yake faruwa Lubnah ta bar musu Bauchin, take hankalinta ya dawo kan Lubnah bayan Goggo Alti tayi mata tas, ta ce mata. "" Idan baki tsaya mata ba, wallahi zaki kashe yarki shi Shehu bai da asara haka"

"Hafiz bai da asara gara ki tsaya mata kafin lokaci ya kure mata."""

"Wannan maganar ya rikita Mama da Yadiko, don haka tayi ta addu'a Allah yasa Lubnah tana hannu na"

"gari, wasa wasa sai da aka kwashe kwana biyar babu labarin Lubnah, haka ya kara fusata Abba wato Baban Bauchi, wanda kai tsaya ya tara Yaranshi da suke Bauchi ya ce ko su dawo da Lubnah ko kuma ya sake Mama, kuma ta bar mishi gidansa wallahi zai aikata, abinda yasa yayi haka faduwar da Hafiz yayi a"

"kasuwa, aka kai shi asibiti akace jininsa yayi azabar hawa, ba sai ga Hafiz ya fadi ba. Abin kamar alamara,"

"sanin cewa Lubnah yake bukata yasa Abba ya fadi haka, shiru Umar yayi kafin ya ce mishi. ""Gobe idan"

"Allah ya kai mu zata dawo abin bai kai har ha..."" Tass Mama ta wanke shi da mari ta kara wanke shi da mari. ""Dama kasan inda take kayi shiru!"" ""Dukkanmu mun san inda yake ni na bata kudin motar na kaita tasha!"" Inji Ya Tahir, ba sai yadiko ta rufe shi da duka tana kuka ba, abin fa ba karamin al'amari bane, haka yasa a ranar suka kira Almu shi kuma ya ce ayi hakuri ranar juma'a zai zo. Domin Lubnah ma ya kaita 44 ganin likita bata da lafiya. Da wannan aka kashe case din sai ta zo, kasancewar kowa ya gama jin"

ranar da zasu sake haduwa tunda ranar talata aka yi zaman.

**

Lubnah

"Tun daga ranar da na isa gidan ban kara samun damuwa ba, sai dai rashin lafiyar da nake a tsaye, bana"

"cin abinci sosai. A lokacin da Ya Almu suka kai ni asibiti na ciro takarda asibitina na nuna musu. Kallona Likita yayi ya ce mishi. ""Kanwarka ce?"" ""Eh likita."" Basu takarda yayi ya ce yaje yayi test yana jiranmu, haka muka tafi aka yi min test din sannan na zauna zaman jiran, idan mutane na magana sai nayi ta jin maganar har cikin kwanyana yana wani irin ciwo. Haka yasa ina karban result din na kai mishi. Shiru yayi ya ce min. ""Akwai ciwon kai?"" Gyada kai nayi ya gyada kai yana mamaki ya ce min. ""Akwai test din da zan baku sai dai ina ga kamar a Kano ake yi ban sani ba ko an samu asibitin da suke yi anan din."" Bamu hoton ™wa™walwa yayi muka tafi Ya Almu ya kai ni aka min, sannan na dawo kiran wani likita yayi ya zo, yana mai gaya mishi case Win. Kallon Ya Almu suka yi kafin suka ce. ""Officer maganar gaskiya, kanwarka akwai wani sanadarin da yake sakata jin ciwon da take ji, na farko akwai drug din da take sha ta daina wanda ya ke hana wancan sinadarin aiki sosai, na biyu abin ya tab'a mata ™wa™walwa da yasa take jin ciwon kai, a takaice dai Mentally healthy dinta ya tabu, sannan tana fama da rashin lafiya resilant, daga yadda take gabanmu kawai dai saka ka fahimci tana fama da kanta, amma zan bata magani!"" Anan ya Almu ta gaya musu ai ina ganin likita a Bauchi, take suka ce zasu so ganin record dina, shiru Ya Almu yayi kafin ya ce musu, ""daga Bauchi take idan aka ce sai anyi haka zai iya daukar lokaci!"" Haka suka yi shiru suka kallona, kafin daya likitan ya ce mishi. ""Ko zaka samu wani da yake da alakata da ita akan matsalar."" Tunawa yayi da Aunty Innah, don haka ya kirata ya gaya mata abinda yake faruwa. Shiru tayi ta ce ya bawa likitan wayar, ya mika mishi suka gaisa kafin suka shiga tattaunawa da yake abu na masu ilimi da"

"sanin ya kamata, na wane da wane,a fagen da kowa ya kware."

Maganar da suka yi da Aunty ya sakawa likitan tabbaci da hasashensa. Sannan ya tambaye ta

"maganin da nake sha, ta gaya mishi sannan ya canza min wasu magungunan. Ya kalli Ya Almu ya ce mishi. ""Yana da kyau ta ga asalin likitan ™wa™walwa da na zuciya."" Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. ""Cikin fahimtar da nayi duk da ban duba Sangaren zuciyar ba yana da kyau a san da zuciyar na da matsala ko babu."" Sun jima suna magana wanda rabin maganar ba fahimta nake ba, bayan mun bar asibitin Ya Almu"

"ya mai da ni gida, tunda muka isa na zauna a parlourn don shi ya umarce ni na zauna ya kawo min ruwa"

"da magani ya bani na sha. Sannan ya ce min. ""An samu matsala a gida, ranar juma'a zan mai dake gida"

"kin ji!"" Gyada kai nayi ya cigaba da cewa. ""Zamanki a daki bai da amfani kin ga Saliha bata nan, ki zauna a parlourn kafin ta dawo. Akwai abinci."" ""Yaya tafi zan kula da gidan!"" ""Are you sure?"" Gyada kai nayi ina mai kallon gefe. Amma idanuna kwalla ne yake taruwa a hankali. Fita yayi ya bar gidan na lumshe idanuna na kwanta a wurin, dama ko na zauna a dakin ba barci nake yi ba, ina zama ne nayi ta nazarin yadda Allah zai kawo min mafita tow ina ganin kamar na tsira amma ashe ina zan koma gidan jiya, hawaye ne suka zubo min a hankali nayi ta zubar da hawaye ban sani ko don ina son na samu iskar yanci ne amma ni dai nasan na gaji, ban san lokacin da na dauka ina zubdar da hawaye ba sai da barci yayi"

gaba da ni. Ina ga a cikin maganin da nasha akwai na barci ne.

"Ina ga rabona da barci me kyau tun muna tambari housing estate, yau sai gashi nayi barci kamar bani"

"ba, sai karfe biyar na farka shima muryan Zunnur ya saka na bude idanun yana tambayata Aunty barci kike yi baki yi sallah ba! "" A hankali na tashi ina faWin. "" Na gode Babana da ka tashe ni! "" Ya Almu da yake aiki a laptop dinsa ya ce mishi. "" Father akan me zaka tashi Yarka! "" "" Dady tayi Sallah! "" Murmushi nayi na wuce dakin da nake nayi sallah kasancewar kasaru zan yi, bayan na idar na zauna sai ga Aunty"

Saliha da abinci haka na taSa sannan na cigaba da zaman dakin.

"Da dare yayi Ya Almu ya kara bani maganin na sha nayi barci sai na samu sau™in ciwon kan, sannan na"

"samu barci a hankali tunanin da nake yawan yi ya ragu, sai tsoron yadda zan isa gida, ya zamu kare da Iyayenmu? Sai tsoro ya kara kamani. Haka kwanakin suka tafi har zuwa ranar da zasu mai da ni, da wuri muka bar Kaduna, domin ya ce yana son ya dawo ranar ne, haka yasa muka fita da wuri da yake maganina ya saba da jinina ba wani barci, sai dai nayi kaWan kafin muka iso saminaka. Ya Almu ya sayi tsaraba muka cigaba da tafiya har zuwa rahama rishi, tunda muka iso nabardo na ji tsoro ya kara mamaye ni, kafin karfe biyu na rana mun iso garin Bauchi. Sai a lokacin na rude kamar zan shiWe, har muka iso kofar gidan aka bude get din gidanmu ya shigar da motar, kasa fitowa nayi bayan yayi parking. ""Darling sister shiga gani nan zuwa!"" ""Tow!"" Na fada ina jin wani irin tsoro yana cika ni, ina saka kafana a waje naji kamar an kwashe min karfina haka na cigaba da tafiya har cikin gidan a dan barandar da zata kai ni cikin gidan anan na hango Ya Hafiz tsaye, wani irin bugawa zuciyata tayi naji kamar na juya da gudu. Kanshi a sunkuye da alamu waya yake cikin farin ciki da nutsuwa, kamar ance ya d'ago kai sai a kaina. Ji nayi kamar zan takowa yayi nima na fara yin baya ji nayi an janyo ni baya. Sai da na sake wata irin ajiyar zuciya da naji kamar numfashina zai bar jikina. Baya Ya Almu ya dawo da ni. ""Wani irin hauka ne haka?"" ""Ba ruwanka Malam matata ce!"" Ya fada yana kokarin kai hannu ya riko ni, kunsan a binka da soja ba sai Ya Almu ya sake ledar tsarabar ya kai mishi wata mahaukaciyar naushi ba, sai da ya fasa mishi baki, sai da ya zube a kasa yana mai d'ago kai yana faWin. ""Ni ka nausa?"" Ya fada yana kallona murmushi yayi sannan ya mike tare da nufar cikin gidan, haka na rike rigar Ya Almu. ""Yaya ina jin tsoro."" Shigar Ya Hafiz shi ya sanar da yan gidan mun iso, Ya Ado ya fara fitowa. Ganin yadda nake rike hannun Ya Almu na tirji na ki shiga gidan, isowa yayi ya riko hannuna yana faWin. ""Princess welcome back!"" A hankali na kalle shi. ""Abba yayi fushi ko?"" Girgiza kai yayi ya riko hannuna muka shiga cikin gidan, wanda yayi daidai"

"da fitowa Hajiya tana faWin. ""Aure sai kace na jaraba dole ne sai ka zauna da Kanwarsu? Ace kamar Almu"

"ya d'aga hannu ya zabga maka naushi akan Kanwarsu aka fara samun matsalar aure ne!"" Lokacin da"

"muka isa parlourn ina rike da Ya Ado, har muka zauna jikina bai daina rawa ba, ba zato ba tsammani Mama ta rufe ni da duka, Ya Ado yayi maza ya kare ni, Ya Tahir shima ya taso suka kare ni, haushi ya kama Mama ta dauki takalmi tayi ta dukan mu da shi haka Yayuna maza da matan nan da ake zaune dasu a dakin suka rufe ni, kallonsu na tsaya ina yi, madadin na ga damuwa sai naga suna murmushi. A hankali na daura kaina a kirjin ya Ado na rufe idanuna har Mama ta daina dukarsu ta fashe da kuka, hannu Ya Almu ya saka ya toshe min kunnena. Bude idanun nayi ina kallonshi, murmushi yayi min hawaye na zuba daga idanunsa, ban san me Mama take fada ba, amma yadda suke kuka ya sani zare hannunsa a kunnena. ""Kin zame min ™addara ko numfashi bana iya ja mai kyau kin lalata min suna a ko ina kowa gani yake ina daure miki kugu ki yi yadda kike so, da wanda ya kai ya gaya min magana da wanda bai kai ba mai na miki na cancanci haka Lubnah wannan shine kyautar da zaki min na"

"haihuwarki."""

"""Idan na isa da ita, ta bi mijinta bana son jin wata kalma su kuma duk wnada ya sake shiga rayuwar"

"auren Lubabatu Allah ya isa ban yafe masa ba."" A wannan zuwan Baban Jama'are bai zo ba su Goggo ma basu zo ba. Haka Yayuna suna ji suna gani na bi Ya Hafiz da Hajiya Baba Malam yana faWin. ""Allah ya maka albarka dole ka ga alkhairi a rayuwarka dole kayi gba ba zaka tab'a ganin baya ba."" Wannan"

addu'ar da Uba yake yiwa dansa duk saboda yabi son zuciyarshi ne.

Haka na cigaba da bin su Ya Almu ya biyo ni da wata karamin akwatin da kayana da maganina yake ciki

"sai wayata da Aunty Hindatu ta bashi ya bani, sai da ya bani ya juya ya kwashe ya Hafiz ya buga shi da kasa tare da take wuyarshi. ""Wannan kashedi na maka, abinda zai faru yana zuwa idan na samu labarin ka mata wani abu sai na maka dukar da ba zaka moru ba."" ""Amma dai baka da mutunci!"" Inji Hajiya. ""Ga mara mutunci nan a kasa ya nuna mata Ya Hafiz, tashi yayi ina kallonshi yayi murmushi ya ce mishi. "" Yadda kuka min Allah yana gani kome dai wuce! "" Daga haka ya budewa Hajiya gaban mata ta zauna sai ni na bude baya na shiga. Tunda muka fita a gidan suka shiga zagina. Dakyar ya iya danne kanshi. ""Ina"

"shiga dakina ya biyo ni."""

"Ban san yadda zan fada ba, amma a ranar Ya Hafiz ya cika min raina da wani irin tsoro he tell me kaf"

"duniya babu wnada ya isa kashe mishi aure, sannan babu wanda ya isa ya kara takowa ko ni na fita, gidansa shine kurkukuna har na mutu be with keep me saboda ya nunawa Yan uwana babu wanda suka isa su mishi. Kun san abinda ake kira tsoro? Anya kusan ma'anar tsoro, to kada Allah ya jarabce ku da tsoro domin tsoro mugun abu ne me kashe rayuwa da kome, sai da ta kai Ya Hafiz ya birkita min ™wa™walwa, ko karar kwano naji sai na ji kamar na mutu, domin ko yaya naji kara zan dawo daki da gudu nayi ta kokarin rufe kofar, domin yadda yake dukana yana min barazanar zai kashe ni, kuma Hajiya tana"

gani tana ji. Bata hana shi ba.

Wata daya zuwa biyu na manta da wani zancen magani tow ya kwashe yana kawo min wnada yayi

"mishi, ko ban sha ba zai matse ni sai na sha, ganin yadda nake kin sha sai ya shiga jika maganin a gora ya daura min sai na shanye, duk saboda me yasa? Saboda yadda aurenmu zai yi survive haka abinda ya"

"aikata zai rufe har abada, da bakinsa ya ce min."

"""Idan na sake ki, zan kara gaya miki ba zaki tab'a samun wanda zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login