Follow us on social media

Showing 48001 words to 51000 words out of 140751 words

Chapter 17 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

325

karfinsa, haka yasa ya zuba musu idanun su gama abinda zasu karshe dare daya Lubnah ta koma dakinta ko tana so ko bata so, shi ba zaa zubar mishi da zumunci a karon iska ba da darajarshi da kimarsa Yara da Matarshi suna juya shi, ba zai dauka ba. Ace kamar shi sai yadda aka yi da shi. ""Muje ka ajiye ni a gida."" Haka kuwa ya wuce gaba zuwa inda motar Abba yake, don da zai zo ya kira Sani akan yazo ya tuka shi, sai gashi ya ce mishi ai baya gari yana can hanyar Jos dan"

banza yana nan bai je ko ina ba yana asibiti.

"Haka yasa ya tuko kanshi zuwa office din Yan sanda, ya je yayi belinsa, haka ya tuko Abba zuwa gida, a"

"lokacin ya samu Umar ya kawo yadiko yana mai dauke da basket din Abinci, a hankali Mama ta fito tana kallon Abba ganinsu tare da . Hafiz yasa ta wuce bata kalli inda yake ba, sama sama Umar ya gaida Abba din ya budewa Mama mota. ""Ina zaki Salamatu!"" ""Asibiti wurin Lubnah!"" ""Da izinin waye?"" ""Ai bana jiranka akan Lubnah, ka zabi abinda kake so, nima na zabi abinda nake so ai ba kuskure ba ne? Muje"

"Umar."" Tana shiga motar Umar ya shiga tashi motar suka bar gidan."

"Bayan fitarsu Hafiz ya shiga tashin hankali, kamar yayi kuka yake kallon kasa. ""Abba kayi hakuri amma"

"ba zan iya rayuwa babu babu Lubnah ba, gara na mutu da na rasata!"" ""In sha Allah ba zaka rasata ba."" Ya fada yana kara tausayin Hafiz domin har ga Allah tausayin Hafiz din. Dakyar ya shigar da shi cikin gidan. Bai iya cin abincin da aka bashi ba, kanshi a sunkuye kamar zai yi kuka ya rasa yadda aka yi har yayi"

shirme haka.

*

"Ajiyar zuciya na sauke lokacin da nake kallon Mama yadda ta zuba min abinci tare da ita, ina murmushi"

"nayi tana bani ina murmushi. "" Mama nifa ina kishin yarinyar nan!"" Inji Sani, ya fada yana hararata. "" Mama ka kalli yadda yake wani hura hanci!"" Murmushi tayi tana faWin."" Sani na, kyaleta tayi maka shigar sauri."""

"A hankali yake murmushi ya dauki spoon ya fara bani abincin shima Mama tana bashi, shigowa Aunty"

"Innah tayi tana faWin. "" Ikon Allah yau naga abinda ya ture turatu uwar Turanci a ramin tururuwa, ok nima bari na shiga."" Ta dauki spoon ta fara ci, a hankali tana mai diba itama ta bani, Ya Sani ya bata. Turo kofar da Aunty Hindatu tayi tana faWin. ""Cin amana a jinin gidan Baba Malam Umaru yake oya ku"

"matsa min."" Haka yasa ta zauna ta fara ci itama kafin ta kai loma sai da ta fara bani, Aunty Innah ta bata."

"Bayan mun gama Aunty Innah ta ce mana.""an sallame ki yar nan!"" ""Na gode sosai."" Haka muka shiga"

"tattara kayanmu dama ba wani kaya ba, gidan Ya Tahir na koma,"

A can gidan kuwa sai ga Hajiya Asiyah tazo Ita da su Aunty Nana Asma'u. Kwanansu daya suka roki Abba

"ya basu damar ganina ya ce su sami Yadiko, haka ya gayawa Mama. Mama kuwa ta ce musu. ""Kunzo ku"

"kara sa min ita ne?"" ""A'a zamu bata hakuri tayi hakuri Hafiz ya gane!"" ""Ya bita makaranta ya rufe da duka ko?"""

"""Amma ai Alhaji yace zata koma!"" Inji Hajiya tana murmushi."

"""Murmushi Mama itama tayi ta ce mata. "" Ba mamaki idan na fitar da gawata Lubabatu zata koma gidan"

"Hafiz kamar yadda ya ce ta haramtawa wa wani da namiji in sha Allah ya haramta mishi. Idan kina ganin karya ne ki same shi ki ce ni Salamatu Galadima nace Lubabatuna ta haramtawa Hafiz ya ce bata haramta ba."" Yadda take d'aga murya shi kanshi Baban Bauchi yana ji amma ba yadda ya iya ta kara da cewa. "" Ni ba haifi lubnah kuma naga wanda ya isa mata dole! Wallahi tun daga karamin kotu har babban kotu sai an jimu da shi, ku fita kafin na haukace muku lokacin da kuke musguna mata kun manta tana da uwa ko? Kun zata kowa haka yake, ke baki ji kunya ba ita da take juya zaki biyo ai Lubabatuna ta"

"gama da danku sai dai wani ba shi ba."""

"Ba sai ga gagarumin rigima kai karshe suka dauki ai Hafiz bai sake ni ba, magana har kotu, abinda ya"

kara lalata lamarin.

"Kamar yadda Ya Ado ya ce, ranar da yasa Yayuna maza da mata suka raka Jos tare da rakiyar Mama,"

"haka nayi ta kuka da xan shiga jirgin. Na k'amk'ame Mama ina kuka.suna tsaye har jirginmu ya tashi, daga nan suka wuce gidan Aunty Raliya, taji haushi tayi ta mita suna sallah la'asar suka baro Jos."

Nan suka sami bugun Bala'i da masifa na Baba Malam ya ce shi ya bada umarnin a mai da auren Lubnah

"Mama kuwa ta ce babu mahalukin da isa wannan aikin rigimar da ta kaure har Abba ya ce mata.. ""Sai ki zaba aurenki ko Na Lubnah domin ba gaji da lalata min zumunta da kuke da sunan kuna bayan"

Lubnan?.........

Alhamdulillahi bakiWaya anan na kawo karshen Free pages.

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 18"

Lagos

"Mun bar Jos karfe biyu da rabi, karfe hudu cib muka sauka. Garin yayi wani irin yanayi na alamar da ayi"

"ruwan sama. Tun daga Murtala Muhammad International airport na shaki kyakyawar iskar da babu hadi a cikinta. A hankali nake takawa ina jin kamar an sauya ni rayuwata ™addarata. A yadda na fahimci mutanen garin kowa akan kafarshi yake, yadda suke kujiba-kujiba. D'ago kai nayi ina niman Ya Ado, daga can nesa na hango shi a wurin Arrived, da dan sassarfa na isa babban wurin taruwan baki tare da masu"

barin kasar da komawa jahohinsu.

"""Lubnah"" ya d'aga min hannu, murmushi nayi wanda kana gani kasan yake ne. Hannu ya mika min na"

"isa gare shi ya Wan rungume ni, irin side hug din, sannan muka jira kayana ya iso, ya tambaye ni ba gaya mishi sannan ya dauko min. Ya riko hannuna yana faWin. ""Welcome to lagos!"" Yake nayi har muka shiga mota, ina zaune kamar wata bakuwa, duk na kasa sake jiki da shi. Haka muka bar airport din minti goma"

"sha biyar ya kai mu estate din da Ya Ado yake zaune. Royal Garden Estate, close alausa Mitv, alausa Ikeja."

"A kofar wani gida me kyau muka yi parking, ya kalle ni a hankali ya ce min.. ""welcome to home!"""

"Murmushi nayi na bude kofar na fito ina kallon yadda tsarin kowani gida yake ba kamar mu nan arewa ba, karya ka yi parking a kofar gidanka, aka bi motar har cikin gidan ma aka dauke. Sai naji na samu nutswa musamman da garin yake hade rai, alamar zasu sha ruwa don gari ne na ruwa. ""Sweet haka muje"

"ko?"" Gyada kai nayi na bi bayansa da yar karamar hand bag dina, har muka shiga cikin gidan. Aunty"

"Zakiya ta zo ta rungume ni hannunta dauke da ludayin miya. ""Baby sai yanzu ka dawo, Auta barka da"

"zuwa welcome to home!"" Murmushi nayi ina kallonta. ""Muje na nuna miki dakinki a sama!"" Kallon stair din nayi na kalle su a hankali na ce musu. ""Na gode!"" ""Never mind!"" Muka haura saman, dakin farko aka bude min. Juyawa nayi na kalle su a hankali na furta da cewa. ""Tsarki ya tabbata ga Allah gwanin da babu irinsa!"" Ba don kome ba sai don yadda aka tsara min dakin sai nake gani kamar ban cancanci zama a dakin ba. ""Shigo dakinki ne, bamu gama gyara dakin ba amma ki yi maneji kafin a gama!"" Gyada kai nayi ina faWin. ""Na gode sosai Allah ya saka da alkhairi."" Ban daki ta bude tana faWin. "" Look at the toilet yayi miki? "" Gyada kai nayi ina kallon ban dakin. "" Shi kenan bari na karasa abinci, sai ki yi wanka da sallah muna jiranki. "" Gyada kai nayi, na zauna bayan fitarta na cire kayan da zan saka na shiga nayi wanka da Alwala na fito, nayi ta kallon inda zan fahimci gabas ne, turo kofar Ya Ado yayi yana faWin."" Jikina ya bani kina niman alkibla!"" Karamin murmushi nayi ya nuna min gaban gadon."" Shimfida abin sallah nayi na gabatar da sallah asar sannan na zauna a wurin ina addu'a. Bayan na idar ne na sauya kaya riga da zani na daura, sannan na cigaba da zama a wurin na tsunduma cikin tunani, wanda ni kaina ban san me nake tunawa ba, ni dai na b'ata shiru. Turo kofar dakin aka yi ta zuba min idanu. Juyawa tayi ta sauko kasa, ta ce mishi. ""SAN kazo don Allah!"" ""Wani abu ne?"" Ya tambaye ta yana mikewa da sauri, ""just come!"" Ta fada tana haurawa. Haka suka nufo dakin ya shiga ya ja stool ya zauna a gabana har lokacin ban san sun shigo ba. Itama zuwa tayi ta zauna a gefena. ""Lubnah!"" Ya kira sunana, ban amsa ba, ya kara kiran sunana a karo na biyu, shima shiru dafa ni yayi, na wani irin zabura tare da fasa ihu. Rungume ni Aunty Zakiya tayi tana faWin. ""Sorry Baby girl we're here!"" Ta fada tana shafa bayana, kuka na fashe da shi, tayi ta shafa bayana tana faWin. ""Ya isa haka, muna nan babu me cutar da ke!"" ""Tsoro nake ji, ina jin tsoro!"

"Don Allah ku boye ni!"" Har lokacin shafa bayana take tana faWin. ""Wanda zai cutar ke, you in safe place. Daga ni har SAN ba zaku bari wani ya tab'a ki ba!"" Mikewa Ya Ado yayi ya ce mata. ""Doctor ina son ki mana booking ganin neurologist please!"" ""In sha Allah, SAN!"" Haka tayi ta bubuga bayana, har nayi shiru karshe dai barci ne yayi gaba da ni, ta kwantar da ni. Sai da ta gyara min kwanciya lokacin Yaran gidan sun dawo daga makaranta, har sun fara ihu ta ja su zuwa daki ta zaunar dasu. ""Aunty Lubnah tazo, and please bata son ihu ko hayaniya, yana iya dakata faint ko tayi loser control, please ku zama good children, kunji ban da fada Ummu Salma, Adil kai ne Babba kada ka yarda su saka ka magana. Prince kada ki yi ihu ko kukan banza kin ji! "" "" Mommy me ya same ta? "" "" Bata da lafiya ne idan kuka yi sallah"

"ku saka ta cikin addu'arku ko?!"""

"Gyada mata kai suka yi, suka fito bayan sun sauya kaya. Yaransu uku ne Adil sunansa Usman sunan"

"Abba, sai Ummu Salma me sunan Mama. Sai Princess me sunan Maman Aunty Zakiya wato Hauwa'u."

"Aunty Zakiya da Ya Ado sun hadu a BUK ne, kusan shekarar shi biyu da fara karatu ta shiga a lokacin ta"

"samu medicine ne, wani abun da nake son a sani Aunty Zakiya Bajara ce daga Dass, iyayenta yan boko ne, sosai sannan tana da yayu maza da mata, a lokacin da suka hadu har magana tayi nisa Abba yaki auren, Baban Jama'are ne ya tsaya aka yi kome, domin a lokacin shi Abba Aunty Nana Asma'u yaso Ya Ado ya aura, amma yaki aka yi ta rigima, Baban Jama'are ne ya kashe maganar bayan ya gaya mishi ai Nana Asma'u tana da wanda take so da wannan aka kashe rigimar, itama Aunty Zakiya kamar tasan an yi wannan rikicin, ita da danginta da aka fara zancen auren sun tsaya sosai kuma sun yi abinda ya dace duk"

wasu iyayen zasu yi akan Yarsu.

"Sun nuna mata fada da gaya mata gaskiya. Ta rike su a matsayin nata, tayi kuma hakuri da kome. Haka"

"kuwa aka yi ta zo gidan a matsayin wacce bamu amshe ta ba, saboda Abba ya nuna bata mishi ba. Amma wani ikon Allah ba a shekara ba sai gashi da kanmu muke sonta. Tana da wani irin kyawawan halayen da sai ka ji kana matu™ar kaunarta, a lokacin da aka yi aurensu Ya Ado saro kaya yake yana turowa shagon Abba, a lokacin duk yan makarantasu gani suke kamar ya cika zakewa akan niman kudi, idan aka ce musu dan Bauchi ne. Sai su ce dama yan Bauchi suna kasuwanci haka, domin da kanshi yake shiga kwari yayi sayayya ya cika manyan motoci a turo Bauchi, dayawa idan aka ce musu dan Bauchi ne sai su ce a'a ba dai yan Bauchi ba, domin basu damu da kasuwanci haka ba. A lokacin Ya Tahir yana da shagon"

provision haka dai shiga singa ya mishi sayayya ya turo mishi.

"Koda ya gama karatunsa, sai da suka tura shi school of law Lagos, ya shekara daya. Bayan ya dawo ya"

"tafi service na wata tara, sannan ya dawo BUK a lokacin itama tana gab da gama karatu, a shekarar aka haifi Adil, wanda yadiko da kanta ta zo Kano ta zauna da ita, da har Iyayenta suna damuwa da maganar tazo wanka gida, sai suka ji labarin Yadiko tana nan, abin da yasa Abba ya sauko ya bar Yadiko tazo, don jin Haihuwar da namiji aka yi kuma Ya Ado ya gaya mishi sunansa yayi masa huduba da shi, itama kuma ta tabbatar da haka. Tare da mishi Alkunya da adil. Sai take ta tara mishi nauyi da kunyarta, musamman yadda yake share ta, idan ta zo gaishe shi yayi kamar bai ji ba, wannan soyayyar da ya wayi gari da shi akan Jikansa na farko ya matu™ar amfani iyayen, domin a Bauchi ma har walima aka yi na sunan Usman Adil Adam Usman. Yadiko bata bar Kano ba sai da suka yi kwanaki Hamsin haka Abba ya ce tayi, sannan da zata dawo Ya Ado da ita Aunty Zakiya suka mata shatara na arziki kasancewar tana da jarabawa, yasa bata zo ba sai da Yaron ya cika wata biyu da rabi, sannan suka zo ganin gida. Tunda suka iso dutsen tanshi, Abba ya dauki Yaron ya lullube a wurinsa sai nono da wanka kawai ke sakawa ya bada yaron ko idan zai tafi central. Wannan kaunar yasa ita uwar Yaron bata wani saka yaron a ranta ba, haka da ta tafi gida da Yaron Abba kullum sai saka Mama ta kira ta, a saka mishi muryan Yaron, dan wata biyu iyayenta da dangin sun fi kowa farin ciki, da tayi kwanaki zata koma suka hada mata kaya har da na su Mama da"

Abba aka hada mishi zuma da zabi aka kawo musu anan fa ta kara daraja da kima.

"Adil na shekara daya a duniya ta fara service inda aka tura ta Niger minna, ai kuwa ta kai Adil wurinsu"

"Mama ta tafi service dinta inda zata yi sati uku ta dawo Kano ta karasa domin mijinta yana ta shige da fice akan haka. Yaro kan da ya saba da ganin Abba don haka kawai zai bushi iska ya zo kano ganin Adil kada ku manta yana da wasu jikokin na Yara mata amma shi wannan gani yake kamar na shine bakiWaya, yaron ma ya saba da shi. Ai kuwa shekarar da aka kawo shi Abba ya tafi da shi Umara, saboda gata da soyayya. Iyayen Yaron hakura suka yi suka barwa Abba Yaron. Har suka gama karatunsu. Kwatsam Ya ado ya samu aiki a Abuja yana can ita tana aiki a Bauchi, Allah ya kara mishi wani nasibi a lokacin tana goyon Ummu Salmah, a shekarar suka koma Lagos domin wani Shari'a yayi kuma yayi nasara, sai gashi cikin ikon Allah suna ta gaba a Lagos itama tayi master dinta, wnada ya kara d'aga darajarsu. Abba ya"

basu dansu domin zai fi dacewa su daura shi yadda suke so.

"Shekararsu daya a lagos ta haifi Princess, yanzu shekarar su biyar kenan. Bayan sun ci abinci, suka yi"

"sallah Magariba, sai a lokacin Ya Ado ya zo ta tashe ni. Bayan na farka na bude idanuna addu'a nayi sannan na tashi na shiga ban daki, nayi alwala nazo na gabatar da sallah Magariba, ina idarwa Aunty Zakiya ta shigo tana waya. ""Gata nan Hindatu kada ki fasa min dodon kunnena."" Ta fada tana murmushi."

"Mika min wayar tayi tana faWin. ""Gashi idan kin gama muna jiranki a kasa zamu ci abinci."" Karban wayar"

"nayi ina kallon kasa. "" Auta kin isa lafiya? Na kira dazun wai kina barci. "" Inji Aunty Hindatu, "" Eh ban jima"

"da farkawa ba!"" Na fada a sanyayye. "" Ya kika ga garin? Yayi miki ko? "" Ko bai min ba dole na amsa da dai na cigaba da zama a Bauchi Ya Hafiz yana min barazanar zai sace ni. "" Yayi min! "" Na furta a hankali, ina wasa da bakin hijab din jikina. "" Auta ki saki jikinki kin ji ko."" "" Ehmm! "" Nace mata bayan nan shiru nayi, , Ya Ado yace zaki fara ganin likita ko?"" Shima sai da nayi shiru kafin nace mata. "" Amma ai lafiyata lau."" ""Eh lafiyarki lau kai, amma ana son ki ga likita da kyau."" Shiru nayi ina jin yadda take ta bayani da ta fahimci ba zan iya cewa kome ba, sai ta kyale ni. "" Auta ki tafi ki ci abinci!"" "" Tow sai da safe.""nace mata ina me kashe ki wayar, na nufi hanyar waje, suna ta hira sama-sama cikin nishadi da jin dadi, haka ma sauko na gaishe da Ya Ado da Aunty Zakiya, yaran suka gaishe ni yadda na amsa musu yasa suka fara kallon iyayen, har yanzu akwai rashin sabo a tare da ni, izuwa yanzu ban san yadda zan gyara kaina na fahimci mutanen da suke gefena ba, tsoro nake ji kada a kwana biyu su juya min baya. A hankali na zauna Aunty Zakiya ta saka min abinci, ta ce min. "" A kara miki ne! "" Kallon abincin da ta zuba min nake"

ina tunanin.

"""Auta lafiya? Tana magana baki ce kome ba."" ""Abincin zata rage yayi yawa!"" Na fada muryana yana"

"rawa. ""A'a bai su yawa ba, kici kawai idan zaki kara sai a kara miki ba."" Kalaman Ya Hafiz ne suka shiga yawo a kaina. _Jaka sai aikin ci ba haihuwa! Dama a jaka ya dace ki zo ba a mace ba, jakar ma mara haihuwa_ da sauri na tura mata nace mata. ""Don Allah ki rage!"" Haka ta rage rabin abincin, shima ban iya ci a gabansu ba, juya abincin nake ina kallon yadda suke ci, tashi Ya Ado yayi ya dauki plat din ya riko hannuna muka bar parlourn dakina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login