Follow us on social media

Showing 78001 words to 81000 words out of 140751 words

Chapter 27 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

326

kashe kaina, saboda a duk lokacin da na kalli yarinyar ji nake kamar xan mutu, ji nake rayuwata ya ™are, taya xan zauna a gidan da aka min laifi kuma aka nuna ba laifi ba ne?"" Tabbas a lokacin jininsa ya haura dubu ko miliyan domin da yana Nigeria ya san wannan abin tow wallahi dai ya cirewa Yaron nan gaba, domin a duniya ya tsani abinda zai tab'a na shi, a tunaninsa mole dinta da yake ba wani can bane a yiwa tufkan hanci ashe har kashe mishi y'a yayi da ransa. ""Idan aka kashe auren shi kenan?"" ""Idan ka min haka zan tabbatar da maganar Abba da ya ce, na daina jin zafin ka kai Ubana ne wata rana."" Kashe wayar yayi ai kuwa aka sake bude sabon case wanda ya shafi zuwa asibiti tare da bincike mai tsanani, sanin cewa idan case Win ya kara girma media ta san da zance Familyn Noma zasu iya rasa abubuwa daga political zuwa wasu power din da suke da shi, sannan zasu kara rasa wasu abokan kasuwanci da suke da tarihin sa a garin Lagos, don haka Uban Mijinta ya zauna da Fahad ya bashi takarda ya sake ta, sannan ya kai tare da niman alfarman ta janye maganar shigar kotu. Dakyar suka shawo kan turaki kawu manya yadda ya kafe daga can yana tsara kome sai ka rantse da Allah yana kasar ne, shi kan Alhaji Mudansir ELYakub cewa yayi yana kasar Iskanci ne irin na rikakken dan duniya, bayan auren ya mutu aka yi ta barka a nan yake gaya musu, duk ranar da ya iso Nigeria dai ya cire gaban yaron wallahi, kai shi fa aka"

taba mishi ya dai ya kashe mutum wannan alkawari ne.

***

Bauchi.

"Shekara daya kenan da bikin Hafiz da Matarshi mai suna Nana, yarinyar yar lukuta da ita, don Hafiz yace"

"mata sirara basu da aiki dai jaraba ita katuwar mace abu biyu ne kana fara tarayya da ita zata ce ta gaji kaima kuma dama ba wani jan lamarin yake da nisa ba, sai zaman yayi kyau. Sai dai wannan karon za a"

"iya cewa Nana irin mugayen matan nan, kamar yadda Karimah da Yaranta suka yi ta kassara rayuwar"

"Lubnah ba, ita kuwa Nana kassara mishi Yara take a hankali, gashi sun tashi daga zango sun dawo dutsen tanshi, bayan gidan Baban Bauchi, idan har ya saka kafa ya bar gidan abincin ranar da na dare a cikin gidan Baban Bauchi take karba saboda ita amarya ce ba zata fara girki ba, sai ta haihu. Idan ta karbo abincin nan Yaran nan loma biyu take basu, sannan wani abu da ta tsarawa kanta gidan a rufe yake bata barinsa a bude yadda babu wanda zai ga Yaran yace suna cikin wani mugun hali, na biyu idan zasu makarantar boko zata zuba musu abinci tare da ja musu kunne suka cinye abincin sai ta tona rami ta binne su. Wannan ya kara saka musu tsoronta, domin ta gaya musu ai Mamansu mutuwa tayi shi yasa"

"ba zata tab'a ganinsu ba, suma ba zasu tab'a ganinta ba. Yusra duk bakinta sai gashi ya mutu."

"Nana muguwa ce, idan Hafiz ya dawo zai samu suna cin abinci ne, yana shiga ciki zata dawo ta ce musu."

"""Na samu kun lamushe sai na yanka ku!"" Tana da wata wukarta me sheki, haka sai ya firgita Yaran basu da katabus sai yadda ta ce, shi kuwa Hafiz gani yake tana kula mishi da Yara. Amma a zahirin gaskiya duk wanda ya kalli yaran sai yasan suna ciki. Azabar rayuwa da ukuba ita dai bata duka amma fa yaran suna"

girban abinda Uwarsu tayi da Ubansu

Yadiko ce kawai ta fahimci halin da Yaran suke ciki domin kuwa ta tab'a zuwa gidan Nana tana barci ya

"buga kofar Yusrah da take tsallen kwado, tayi kuka ta yi zufa sharaf, ta ™asa tashi sai Yasir ne ya zo ta buWe kofar Yadiko ta ga halin da suke ciki salatinta ne ya tashi Nana ta fito tana zare idanun tasan ma karya tayiwa Yadiko reni domin ya gaya mata koda wasa kada ta ce zata rena mishi iyayen Lubnah domin zata dawo, ita kuwa ta saka a ranta ko mutuwa zai yi ba shi ba wata Y'a mace. Yadiko tayi ta mata fada tana nuna mata illar abinda ta aikata tayi ta bawa Yadiko hakuri ba zata kara ba, haka yasa Yadiko ta"

watsar da lamarin don be shafe ta ba.

Bauchi Central Market*

U.U.J textile and fabric

"Shagon sayar da kayan sawa irinsu atamfa da shadda, lace, da sauransu. Sannan yana da shagunan"

sayar da kayan wuta irinsu tv da sauran electric.

"A gaban wasu tika-tikan shagon sayar da atamfofin wasu yan mata ne suka zo fitar da Ashobe, yadda"

"daya take wani yauki zaka Wauka karkashi ce, tunda ya ga Hafiz take wani kashe murya, shima kuma ya fada mata domin yana masifar son mace yar gayu lokacin baya shi da Lubnah idan tayi gayu ba karamin tafiya da duk wani lissafinsa take ba, shi yana son mace mai gayu duk muninta, ko Lubnah abinda yasa shi ya daina ganin gayunta wannan shegen kibar da ta yi sanadin maganin hana daukar ciki da yayi ta"

"bata, amma idan tayi kwalliya kamar ya boye ta yake ji, wannan kallon da yayiwa yarinyar ya dawo mishi"

"da Lubnah haka yasa shi kallon zoben hannunsa. Yana nazari da shaukin yadda zai hadu da Lubnah, duk"

"ranar da suka hadu kuwa duk rintsi ba zai tab'a yarda ya barta ba, sai ya dawo da ita rayuwarshi tsamo- tsamo......."

(Hafiz kada ka ja min lukutar masifa don Allah Innalillahi wainnalihir rajoun )

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 31"

Shi hala dole fa sai ya dawo da Lulu gidansa hankalinsa zai kwantar. Daya daga cikin yaran shagon mai

"suna Ukasha ya ce mishi. ""Oga Ashobe suke suna son wannan atamfar kamar turmi hamsin."" ""A duba idan akwai a saka sunan Amaryan da Unguwar da suke."" ""Tow!"" Ukasha ya samu Amaryan da kawayenta. Daya daga cikin yan mata ta ce mishi. ""Babu ragi ne? Muna son cotton da roba ne?"" ""Akai cotton 9k Akwai roba 5500 yake!"" Juyawa Amaryan tayi ga wannan kawarta ta ce mata. ""Mansi kin ji kudin kayan yayi?"" Wani juyawa yarinyar tayi cikin yauki da yanga ta ce mata. ""Duk yadda kika ce haka za ayi."" Murmushi Amaryan tayi tana kallon Ukasha ta ce mishi "" shi kenan ka gaya mishi muna so amma kuma. "" "" Bari na mishi magana! "" Ita Mansi ta samu Hafiz cikin yanga tana mishi bayani, kallo daya yayi mata ya dauke kai yana faWin. "" Ki bawa Ukasha number wayarku da za'a saka jikin kayan. "" Ya fita daga shagon, binsa tayi da idanu, duk wannan abin da take Baban Bauchi yana kasuwa duk iskanci da fitsaran Hafiz baya tab'a yarda ya gwada halinsa a gaban Baban Bauchi, domin ya iya takusan, Alwala suka yi tare da Baban Bauchi suka nufi masallacin da yake cikin kasuwar, amma a ransa ya kyasa da yarinyar addu'a"

"yake yasa Ukasha ya amshi number yarinyar. Nana yar uwarsa ce amma yau ganin Mansi ta fama mishi ciwon Lubnah tana budurwa yar shaf-shaf da ita ba kiba ba tarin tumbi, ga ta kamar ka goyata ka gudu da ita. Don haka idan ya koma kafin a tashi sai ta amshi numberrta yarinyar ta matukar burge shi. Don haka yana komawa ya dauki littafin da ake saka sunayen yan Ashobe ya gani sannan ya ajiye bai kuma bi"

ta kan zancen ba.

Bayan sun tashi Baban Bauchi da Hafiz suka wuce kasuwar wunti inda nan ma aka zuwa wasu kayan. Sai

"da ya gama ganin yadda kome yake tafiya sannan suka fito tare a gidan ya sauke Baban Bauchi tunda ya dawo dutsen tanshi ya zama kamar driban Baban Bauchi. Buga gidanshi yayi Nana tazo ta bude. ""Sannu da zuwa!"" ""Yawwa!"" Ya shigo tana bin bayansa a parlourn ya samu Yusrah da Yasir suna cin abincin,, kallonshi suka yi ya wuce bai musu magana sai murmushin da ya musu. Suka cigaba da cin abincin, har ya fito suka mike tare da cewa. ""Aunty Mun koshi!"" ""Sai kun cinye kullum haka kuke barina da abinci!"" ""Kyale su sun koshi ne, ba ayiwa yaro dole ya ci abinci."" Cikin mita ta ce mishi ""shi kenan kana son ka bar ni da abinci."" Haka ta saka yaran a gaba suka wanke hannu suka tafi dakinsu, suka kwanta. uban ya gama"

abinda yake ya fita.

"Tunda ya sauke Baban Bauchi ya ce mishi. ""Jeka yau naga yaran nan ne a gidan zuwa an jima ka dawo"

"ina son mu magana."" Gyada kai yayi yana faWin.. ""tow shi kenan!"" Ya juya zuwa gidanshi, babban"

damuwar Hafiz ya san me yake faruwa a cikin gidan yadda yaga motar Umar da ya sauya wata Jeep

"Cherokee Ave, shi fa Umar tun da ya bar shagon Baban Bauchi Allah ya haWa shi da wani Imyamuri suka fara sana'ar mashina sai gashi Allah ya yi sanadin mutumin nan hanyar arzikinsa yake, haka yasa kome ya"

tab'a yake da albarka.

Dalilin zuwan su kuwa bikin Ya Sani da bude shagon shi na sayar da kayan maza a winti na biyu yana

"saro agogo da wayoyin zamani a China, kusan shekarar biyu kenan ya fara da sayar da takalma ne, sai ya fara gwada dinka kaya yana sakawa tare da daura hoton a IG da Twitter, Allah da ikonsa da buwayarsa kasancewar Uwa tana tare da da shi, yan uwansa kuwa masu hadin kai ne, sai gashi cikin buqatar mai kowa da kome ya bunkasa ya isa inda ba a zata ba, yanzu haka yana iya dinkawa ango kayan fitar biki, don bikin da aka yi kwanan nan dan gwamna Bauchi state, shi yayi ta kula da shiga da fitar angwayen, ba karamin kudi ya samu ba. Dama yana taru wurin Aunty Hindatu, ai kuwa ganin haka ya samu kudi aka kara mishi ya sake habbaka kayan auren, da sadakinsa da kome na shi, yana nan a hannu yanzu sun zo"

ne a gayawa Baban Bauchi shirinsa. Shine ya gayyaci yan uwansa.

"Bayan sallah isha, suka hadu a parlourn Baban, suka gaisa aka yi yan hira sama-sama, kafin Umar ya"

"kawo zancen da ya haWa su. Daidai shigowar Hafiz da ya koma gefen Baban Bauchi ya zauna kamar zai koma cikinsa tsabar munafunci, ran Tahir ya b'aci. Shiru baban Bauchi yayi kafin ya ce musu. ""Tow Allah ya nuna mana, amma naso da zaku amince da Firdausi, domin naga ai yarinyar itama."" ""Abba Yarinyar da yake so ba jiya suka hadu ba, ba yau ba akala sun kai shekaru hudu suna tare, don tun tana makaranta suka hadu, yanzu kuma sai a kawo wani batu Firdausin da."" ""Tunda kun shirya mishi yadda zai me yasa zaka kawo min batun amincewata."" Yadiko da take bakin kofa ta ce mishi. "" Ai kasan kuwa yadda ka hana Sani zaman shagonka wallahi ba ka da hurumin bashi abinda baya so, Lubnah ma da ya ta kwashe a hannun Hafiz kai ku tashi idan yaso kada ya bashi kwandala yarona ya yi duk wani abinda ya dace wa"

"kansa ko ni da na haife shi bai jira ni ba, haka kuwa ba wanda zai mishi dole!"""

"Wani irin rikici aka shiga tukawa aka kuncewa, kafin kuma aka kyale kowa yayi yadda ya so, Baban"

"Jama'are ya zo da wasu maza , wanda suke dangin Yadiko aka je nimawa Sani auren Halisah, yarinyar danginta yan Tilde ne, don haka suka tafi aka nima mishi aurenta, ganin yadda suka fito daga babban zuri'a kuma yaro yana da abin yi sannan shima Uban yarinyar ya shirya tsaf, kawai aka karbi sadaki da"

yanke rana. Wannan lamarin yayiwa kowa dad'i domin domin kuwa dangi kowa ya fara shiri.

"An saka ranar bikin wata uku masu zuwa, a cikin wata ukun gidan da Abban ya bashi wanda yake"

"kusa da gidan Ya Umar, aka fara gyarawa ana cire tsohon tsarin gidan, aka fara yin gyaran na zamani. Cikin kasa da wata guda da sati biyu aka gama gyaran gidan."

"Ashobe kuwa a shagon Aminu da Zubairu, Innah ta cire aka kai dinki na su Lubnah domin Mama ta ce"

dole ta zo.

***

Lubnah.

"Bikin sani zai zo lokacin mun gama jarabawa, sai dai har zuwa lokacin gabana yana faduwa da maganar"

"zuwa Bauchi. Domin gani nake kamar duk wani abu zai kara faruwa, haka na sake raina na cigaba da abinda yake gabana. Duk da na dan sauka kaWan, amma kuma ni kaina sai nake ga kamar da sauran yanayin domin jikina yana min nauyi, wani lokaci haka zan ta fama da haki, sau biyu ina zuwa ganin likita da Dijah Bala take hada ni da su, na farko ya ce kitse ne ya taru a zuciyata, na biyu kuma yace wai a cikina sai abin ya saka ni rud'ani, na shiga cikin wani irin tashin hankalin mara misaltuwa nayi shiga, na rasa me ke min dad'i. Ban gaya Ya Ado ba, don yana gayawa Mama zata iya cewa ayi aikin yaushe aka cire min karin mahaifa yanzu kuma wani aikin ni na koma kamar wata kazar mayu, ga shi na daina ganin Baby sai kaina yayi zafi,, ranar wata Alhamis na tafi wurin Dr Dijah Bala. Ta kalle ni a hankali, tana faWin.. ""Ni na ga kamar kina cikin damuwa?"" Jinjina kai nayi a hankali ina wasa da yatsun hannunta. "" Me yake damunki? "" Gyara zama nayi na rasa yadda xan yi magana domin har yau bani da kwarin gwiwa yin dogon magana a gaban jama'a, duk da tana kokarin nuna maka kai ma mutum ne kana da damar fadar abinda yake ranka. Matse hannuna nayi ina motsa bakina nace mata. ""Nan da wata biyu za muje Bauchi bikin Yayana!"" Murmushi tayi tana kallon yadda na matse hannuna da ™arfi. Na kasa fada mata abinda nake son fada, gogewa da tayi da masu irin laluranmu yasa ta matso da kujeran kusa da ni ta rike hannuna da kyau, ""ina tsoron kada Abba ya ce ki koma gidan Hafiz ko?"" Hawayen da nake dannewa ne suka shiga wasan tsare akan fuskana. Cikin shashekar kuka na ce mata.""ba iya shi ba ina tsoron abinda mutane zasu ce ne."" Nan ma nayi shiru ina kallon gefe, jinjina kai take a hankali ta ce min. ""Mutane sun daina maganar kina da kiba ne?"" Da sauri na d'ago kai ina girgiza mata. ""Ashe kuwa tunda basu daina ba, akan me zaki yi kuka? A yanzu Mama da su Barista suna tare da ke, tare da su Innah da Hindatu. Kina jin zasu bari a mai dake gidansa ne? Kada ki manta har yau baki yarda da kanki ba ne. "" Kallonta nake, "" har yau baki yarda kina da goyon bayansu ba ne, baki sani ba ko?"" Hawaye ne ya zubo min, gyara zama tayi tana juyawa akan kujeranta ta cigaba da cewa. "" Me yasa Ahmad ta daina zuwa?"" Shiru nayi ina kallonta na zata ko don an mishi magana ne, girgiza kai tayi tana kallona kamar tasan abinda yake raina ta ce min. "" Kina tsammanin Barista ya hana shi zuwa? A'a ni na gaya mishi ya rabu da ke, a halin yanzu ba namiji kike bukata ba, kanki kike bukatar you need tow love yourself."" Cigaba da kallonta nake, ta mike tana mai isa gaban frij ta dauko min ruwa ta ajiye min tana faWin. ""Har yau baki san yadda zaki kwanci kanki ba, har yau baki san yadda zaki yi fada don kanki ba, yaushe kike tsammanin zaki iya zaman aure bayan nasan wacece matar Ahmad, ya zo nan ya gaya min kin ki kula shi nace mishi ai ke yanzu baya ga kanki bakya bukatar ™arin wani a rayuwarki. Sannan idan ya nace ya aure ki rayuwarki ta baya zaki koma, me yasa muna janyo ki present zamu mai daki past dinki? Daga lokacin da kika fara sanin ciwonki, a lokacin zaki fara tantance waye yake kallonki da idanun basira waye yake kallonki domin biyar bukatar kanshi, ni na gaya mishi ba zai iya gina soyayyarshi yadda ya dace a tare da ke ba domin zuciyarki a rufe yake. A"

"duk lokacin da irin wannan abin ya faru ana bawa masu irin matsalarki lokaci ne, don haka kina da lokaci"

"ki cigaba da kula da kanki da lafiyarki. Sai me kuma?"" Shan ruwa nayi kafin na gaya mata yadda muka yi"

"da likitoci biyu. Murmushi tayi tana faWin, "" na gaya miki dole ki shiga ajin motsa jiki, kina cin abubuwan da na hana ki ci, har yau baki ware abinda zaki ci don lafiyarki ba, da kin kula da haka da tuni wata"

"Lubnah ake magana ba wannan ba."""

"Sai na ji kamar nayi knocking heart dina tare da bude kofar ta ce min farka Lulu. "" Yes dole ki fara motsa"

"jikinki, ki biya kuWi a unguwarku ai akwai inda ake motsa jikin, sai ki fara ina son na ganki nan da wata biyu."" Kallonta nake ta yi cike da mamaki. "" Kina nufin. Idan nayi zan samu lafiyar jikina? Amma kuma ai kunya nake ji wurin za ayi ta kallona."" Na fada kaina a sunkuye. "" Kina jin kunya ko? Kada a miki dariya, bari na haWa ki da wani yaron da na sani sunan Wasim!"" Gyada kai nayi ina wasa da yatsuna, har ta kira Yaron ta gaya mishi, ashe a unguwar yake ta bani number wayarshi. Sannan na mata sallama na dawo gida, bayan na yiwa Ya Ado bayani ya ce gobe zai tafi har wurin da kanshi ya ga yadda Gym din yake, haka muka kwana ina ta addu'a Allah yasa kada na samu matsala da kowa Allah yasa na kasance jaruma wacce zata iya daukar duk wata matsala, wurin karfe tara na gama shirin zuwa makaranta Ya Ado ya kira ni ya ce min. ""Ki je zasu baki wasu tips and abincin da zaki ci, sai ki amsa idan kin dawo muje a saya ko?"" ""In sha Allah zan amsa kafin na tafi."" Na fada ina shiryawa, bayan na gama na fito na nufi titin unguwar"

"da kafa, na je shagon babba ne na gaske....."

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 32"

"A hankali nake tafiya ina kallon mutanen da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login