Follow us on social media

Showing 21001 words to 24000 words out of 140751 words

Chapter 8 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

295

sai yau. Ba dai na kara nutsuwa ina sauraren dalilan da suke kawowa ayi shi..

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

PAID BOOK

TAKWAS

"Wato akwai wani abinda hankalinmu baya kai sai wani dalili mai girma ya shato shi cikin rayuwarmu, ban"

"tab'a nazari akan khulu'i ba, amma kuma me yasa na damu? Me yasa nake son sani akanshi? Kawai sai naji abin bai min na cigaba da nazari akai ba, kawai zan cigaba da zama da fahimtar iyayena. A bangaren Ya Hafiz kuwa nadan wata rana zai dawo yadda muke zai kaunace ni sama da baya, amma kuwa zai yi"

haka.

Bayan sallah da sati uku.

Weekend

"Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake ya jima da na sauke amma da yake yana da"

"wuyar sha'anin, sai na ta saka idanun akanshi saboda Yaran nan da zarar na sauke tukunyar fresh milk sun ta kara kaina akai kenan, har sai na hada na basu. Hankalina yana kan zobo wanda nake ta saurin haWawa. Sai naji an tab'a murfin tukunyar, da sauri na juya Yusrah ce rike da kofi ta bude tukunyar fresh"

"milk din zata har ta saka kofin ta dibo da yake na juya mata baya, a matu™ar razane na kalle ta ina faWin."

"""Gaskiya Yusrah bakya jin magana maza rufe min ki mai da kafin na zo wurin."" ""Ba zan mai da ba."" Ta"

"fada tana kallon cikin kwayar idanuna, abin da ya bani haushi da takaici yanzu ta kone Iyayenta su ce na konata. Mikewa da zan yi kuwa ta kwasa da gudu ai kuwa sai gashi ta taka ledar Bevimix ta zame bakiWaya fresh milk din ya kware a gefen kirjinta, abinka da zafi sai kuwa ta fasa ihu wanda yayi daidai shigowar Mahaifinta da fitowar Uwarta a dakin, wani irin bugawa zuciyata tayi na tsaya cak kafin na karasa da sauri nace mata. ""Kin ga abinda nake gaya miki ko?"" Na yi maza na shiga daki na dauko kamun da aka niko min zan yi kunu na sha na watsa mata a kirjinta bayan na cire mata rigar, bakiWaya iyayen babu wanda ya ce min ci kaina. Haka na zaunar da ita na cire mata rigar ba wani tashi wurin ba, amma yadda take kuka da ihu yasa Uban ya karaso ya bangaje ni sai da na fadi, sannan ya dauki yar ya fita da ita, wasa wasa basu dawo ba har dare habaici da cin mutumci babu wanda Karimah bata min ba, ni dai bance mata uffan ba, wajen karfe biyar Mama ta kira ni. ""Kin kyauta Lubnah wacce irin kishi ne haka yake damunki?"" Bata ba ni damar magana ba. ""Saboda kishi zaki kyale yarinya kamar Yusra ta kona"

"kanta?"""

"Ni dai ™asa magana nayi har sai da Mama ta ce min. ""Saboda mugun nufinki Allah ya hana ki"

"haihuwa domin da ya baki da Yaranki zasu dauki mugun halinki!"" Komawa daki nayi na zauna shiru. Haka Baban Bauchi ya kira ni ya ce sai ya ga wanda ya isa min, wasa wasa sai ga al'amarin ya girma yadda ban zata ba, yusrah kwantar da ita aka yi a gadon asibiti. Sannan wacce take gudun Mama ce. A wannan lokacin na ji duniyar ta min zafi, kaf duniya mutum daya ce ta fahimce ni Aunty Hindatu, dole na bawa Aunty Hindatu special respect a duniyata, ita kaWai sai Ya Ado suka fahimci abin domin abin ya faru da kwana biyu Baban Bauchi ya zo har gida ya saka aka kwashe kayan sana'ar aka fita da su. A wannan lokacin Ya Hafiz ya zata ni yayiwa mugunta. Ya zata ni ya rusa tabbas ya Hafiz ya rusa ni, sai da na kusan zarewa domin babu wnada ya saurare ni, kowa ya juya min baya sai Aunty Hindatu da ita Waya ce take rarrashina, kwana Yusrah biyar a gadon asibiti Hajiya da Baban Jama'are suka iso a ranar Karimah ta"

dauki matakin da Baban Bauchi ya goya mata baya.

"Ina zaune wurin karfe biyu na rana aka yi sallama a gidan, fitowa nayi ina amsa sallamar. Yan sanda ne"

"mata biyu suka shigo. ""Sannunku da zuwa!"" Yadda nayi magana a matu™ar tsorace. ""Kece Lubabatu Usman Umar Jama'are?"" Jikina ne ya dauki rawa. ""Eh nice!"" ""Ok ko zaki zo muje office din Yan sanda!"" Ji nayi kamar ina yawo a saman iska. ""Akan me zan bi ku Office dinku bayan ban yi kome ba?"" ""Eh tow idan muka je zaki ji abinda ya faru!"" ""Tow bari na kira mijina;"" na shiga kiran Ya Hafiz amma bai dauka ba, haka nayi ta kiran Yan uwana har Baban Bauchi na kira Babu wanda ya dauka, sake magana suka yi na fito ko su shigo dakin. Haka na fito a sanyayye da hijab har kasa. Ina kara kiran Aunty Hindatu. Daidai na shiga bayan motar. Dauka tayi tana faWin ""Auta yi hakuri bana kusa ne!"" ""Aunty Yan sanda sun zo zasu tafi da ni!"" ""Akan me?"" ""Ban sani ba Aunty! Don Allah ki zo!"" ""Shi kenan gani nan zuwa!"" Haka ya kashe wayar muka Office din Yan sanda da yake dutsen tanshi, anan na samu Karimah ashe shirinta kenan ita da Uwanta da iyayenta, muka shiga suka amshi wayata da kome suka tura ni cell suka ki min magana, ina zaune wata yar sanda ta shigo ta d'aga hannu tayi ta kifa min mari, yan uwan Karimah suna faWin. """

"Saboda kishi ne ita Allah bai bata haihuwa, koda yake ta kashe mahaifarta da maganin hana daukar ciki"

"shine bari ta kashe yar kishiyarta, Allah ya sa yarinyar ta auna arziki!"" An tozarta ni, an ci mutuncina haka"

"na kasa ko kuka sai sunkuyar da kai da nayi idanuna bana gani. Muryan Ya Hafiz da naji yana ta fada a waje. "" Akan me zaki shigo da hukuma cikin maganar? Ko an gaya miki ban san yadda zan yi ba ne?"

"Gaskiya kin bata min rai yanzu da wani idanun xan kalli iyayenmu?"" Yadda Ya Hafiz yayi ruwa yayi makarbiya yasa ni shiga rud'ani amma ai ya ga kirana. Fada sosai yayiwa Karimah, Aunty Hindatu da Ya Umar da Ya Albashir suka karbi belina, haka na fito kamar wacce ruwa ya mata duka, fuskana ya dan kumbura saboda marin da yar sanda tayi min. A hankali nake takawa har wurin motar Ya Hafiz da ya nuna shi xan bi na je nayi wanka. Haka muka bar office din zuwa gida, a hanya yake cewa. "" Kin san ina sonki, sannan abinda ya faru nasan bakida laifi Yusrah ta gaya min, amma kuma ita mahaifiyarta ba zata ji dadi ba idan na nuna baki da laifi don haka ki amshi laifinki ta haka ne kawai zaki wanke kanki kowa zai gane cewa bada wata manufa kika yi ba!"" "" Ya Hafiz me yasa?"" Na tambaye shi, "" Me yasa ka zabi kuntatta min? Me nayi maka da yake damunka har haka? A sanina ban maka wani abu ba? A sanina ban cutar da kai ba, ina saka ran wata rana zamu koma kamar baya kamar farko-farkon aurenmu, Ya Hafiz duk irin shirun da nayi na cancanci haka daga gare ka?"" Shiru yayi da alamar maganar ya ratsa shi kenan. "" Ka saka kowa ya tsane ni, ka saka kowa yana jin haushina, idan abu ya faru ba zaka gaya musu gaskiya ba sai ka bar maganar a daura min laifi me yasa sai ni? Ya Hafiz rabon da ka nemi ni a shimfidar aurenmu shekara kusan guda dawowarmu zango na gaji wallahi na gaji ka sawwake min nima na gaji!"" Na fada ina kuka domin sai yanzu nake jin kamar bakina ya buWe. "" Ko na sake ki ai baki da wanda zai aure ki?"

"Lubnah ki kalli kanki da kyau har abada babu namijin da zai tab'a jin sha'awarki, Lubnah na ajiye ki ne domin kowa yasan ina ™o™ari da mugun halinki, ke har kina da bakin da zaki gaya min magana? Bayan na rufa miki asiri ne, jaka me kama da alade kalle babu abinda wani zai gani na burgewa a tare da ke kazama wawuya, kuma daga hau sai na hana ki farin ciki."" Haka muka isa yana zagina da cin mutuncina har nayi wanka kai karewar masifa kofar ban dakin ya shigo yana cin zarafina. Haka na gama na shirya muka tafi cikin gidan inda Yusrah take da iyayenmu, anan ya min barazanar matukar nayi magana sai ya"

sake Baban Bauchi wato Babanmu ya tsine min shi kuma ya sake ni domin ba zai zauna da tsinanniya ba.

"Lokacin da muka isa gidan Baban Jama'are yana nan haka Hajiya ma, sai Iyayena da yan uwana."

"Tunda na zauna aka bude taron da Addu'a. Aka rufe ni da fada babu wnada ya ji yadda kome ya faru haka na sunkuyar da kaina ina jin Baban Bauchi yana faWin. "" Munafuka ban da kishi da munafunci me kika ajiye ace har degree gare ki ya zama na banza. Sai bakar kishi tow da abinda kike takama da shi na kwashe dama yana gaya min tunda kika fara sana'a kika sauya bakya jin maganarshi, kin yi sabi iyaye masu daura miki mugun abu akanki wallahi kin ji kunya."" "" Amma Baba ya kamata a ji me ya faru? "" Inji Aunty Hindatu, da take wani irin cirra, juyawa yayi a fusace ya zabga mata harara, ya rufe ta da fada da cewa ai ita take zuga ni, haushi ya sa ta bar parlourn ma don bakin ciki haka Baba Malam ya amshi fadar yayi ya ce min. ""Yanzu kin kyauta abin da kika aikata? Da Asiya kike kishi ko da Uwar Asiyah? Yanzu ban"

"da mun fi karfin yarinyar nan ina sai dai kotu ta shiga lamarin nan?"""

"""Malam wallahi ban san cewa haka dai faru ba,.Malam na rantse da Allah ban yi haka domin kona yusrah"

"ba yayi hakuri ba da gayya ba ne!"""

"Zuba min idanu Malam yayi yana faWin..""Allah ya kyauta amma ina amfanin kishi irin naki? Akan ki aka"

"fara kishiya ne?"" Cikin shashekar kuka na ce mishi. ""Wallahi ban san zata shiga ban dakin ba, ka yarda da ni!"""

"""Kai yanzu Hafiz me ka gani?"" Juyawa yayi ya kalli Baban Bauchi wato mahaifina ya ce mishi. ""Duk abinda"

"Baban Bauchi ya ce ai shi kenan!"" ""A'a Hafizillah kada ka cutar da kanka, na ga ™o™arin zaman da ka yi da"

"Lubnah idan ba zaka iya da mugun halinta ba sakota na gaji da kullum ana abu daya a cikin shekaru goma kullum Lubna tana saka ni magana."""

"""A'a Usman, Lubna ko bata auri Hafiz ba, akwai alakar jini balle kuma alaka ce da ta haWa da ta zuci,"

"ai ta ce ba da gayya ta konata ba kuma yadda ake ta ririta al'amarin da na ga ciwon ai ba wani babban al'amari ba ne, lamarin mata ne kawai da ririta lamarin da bai kai ya kawo ba, yi shiru Y'ata share hawayenki. Kul na kara jin wani yayi magana da cewa za a kai batun nan ga hukuma kunar da bai wani tashi ba, ga yadda yayi baki kasan ai ba zai tashi ba, sannan kai Hafiz ka tuna akwai ranar da zamu tsaya a gaban Ubangiji, ka ji tsoron Allah kada son zuciya ya kai ka ya baro ka, kawai jikina yana bani haka kawai"

"Lubna ba zata aikata kome ba."""

"Kunya ce da bori tasa shi, kame-kame amma a cikin ranshi bai so haka ba yasan Baban Bauchi da za a"

bar shi sai ya mari Lubnah shi yanzu yadda zai bakanta mata rai yafi bukata akan wannan abin.

"Duk da an ce yau da gobe bai bar kome ba, Iyayena da dangi babu wanda ya hango mutuwar"

"tsaye da nake yi saboda Ya Hafiz, Babu wanda ya yarda da cewa ina cutuwa, a'a kowa gani yake kamar ba cuta ba ce ni ce nake cutarsa saboda shi mutumin kirki ne, bayan shi ya shiga rigar mutanen kirki ne. Yayi ado da kwalliya a cikinsa, sannan babu wanda zai kalle shi ya ce mutumin banza ne. Amma bakin maciji ne sanye da tufafi yan adam, haka muka bar gidan, bayan an mana nasiha. Ni dai nasan cewa zuciyata ta gama mutuwa bani da wata amfani. A hankali gidan ya zame mini kamar hell fire, bani da kwanciyar hankali bani da sukuni, idan abin ya dame ni sai na rufe kaina a daki na ki fitowa, a hankali abubuwan suka ta tsanani domin kuwa na daina sayar da kome na daina yin kome, shi kanshi Ya Hafiz da ya fahimci bani da wani amfani sai ya cigaba da azabtar dani da abubuwan da zai saka na ji har na tsani"

"zaman gidan, damuwa ya kara tsananta min domin ba wani abu ba ne su min gorin haihuwa."

"Bayan wata biyu kusan watan Mauludi, Ya Ado ya dawo, ni ya fara kira a lokacin babbar wayar hannuna"

"na sayar domin Ya Hafiz ya zo ya saka ni a gaba yana son kudi haka na hada da wayar da sarkata ta gwal na bashi, kunsan me a duk lokacin da zai same ni yana bukatar wani abu tow ba irin yaudarar da baya min, haka zai zo da soyayya ya cutar da zuciyata, har yau ina da yakinin zai shiryu ya daina abun da yake"

min don na fara tunanin kamar shiga tsakaninmu aka yi.

"Cikin murmushi na ce mishi. ""Barka da dawowa yasu Aunty Zakiya? Kun iso lafiya?"" ""Alhamdulillahi"

"Auta nace ke zan fara kira ki san na dawo!"" ""Masha Allah sannu da hanya madalla!"" Yadda muke wayar"

"naki sake jiki da shi, ya sa shi kashe wayar da zai kira wani lokaci, tunda Ya Ado ya dawo Nigeria kullum"

"zai kira ni, zamu gaisa daga nan zan yi shiru. Haka zai ta ja na da hira, har ya gaji ya kyale ni."

"A hankali abin sai ya zame min jiki, sannan ban kara yarda mun yi tashin hankali da wani abu cikin gidan"

"ba, wani abu daya da na fahimta idan na kashe auren ma bani da wani amfani, haka yasa babu amfanin na gayawa kowa halin da nake ciki, sannan kwasar bakin ciki a wurin Ya Hafiz da danginsa kamar shafa ce ta alola. Haka yan uwansa zasu zo musamman Aunty Nana, haka zata yi ta min kome da gadara da iko"

"iko, idan nayi magana zata ce gidan dan uwanta ne."

"Haka zan zuba musu idanu, kome zai wuce amma idan ban mutu ba zan sha kallo. Idan ka kalle ni"

"bani da matsala sam, amma deep in side ina cikin wani irin mugun yanayi ne. Sai dai ba wanda ya san da haka sai wanda Allah ya jarabta da irin halin da nake ciki."

*

"Yau Dan wake nayi shima dai nice nayi cefanen, musamman duk ranar da ya tashi rashin mutunci ni ce"

"zan yi kome har na gidan, ya daina kawo abinci domin kuwa Karimah ta ce mishi ai idan aka kawo kayan abinci sayarwa nake sai dai idan ya tashi ya auno mudu idan ya gadama idan bai gadama ba zai ce na"

"ranta mishi, yasan bani da kosisi. Haka zan ta kame kame har na hada abincin aci."

"Har lokacin Maman Na'ilah bata bani fuskar da zan tambaye ta kudin ba, abu daya take gaya min. ""Duk"

"ranar da zaki yi aikin alkhairi wa rayuwarki in sha Allah zan baki kudinki amma idan har wa Mijinki ne wallahi kwandala ba zan baki ba, karshe ma zance sharri kika min!"". Murmushi nayi da yake tasan ba zan"

"yi magana ba, shi yasa nima na barta."

"""Ke Yusrah kawo min kular Babanki na saka mishi abincinsa tun dazu sai magana nake kin ki kula ni!"""

"Cikin rashin kunya ta ce min. "" Eh din ba zan dauko ba ko dauko da kanki mana! Tunda bake kika haife ni ba. """

"Haushi yasa na zo na dauka na kuwa zungure kanta, ai kuwa ta fasa ihu. "" Sai ki yi mara kunya kawai! """

Na je na dauka ina mai komawa kitchen na zuba musu abincin.

"""Ina kika san zafin d'a ke kin san yadda wahalar daukar ciki da reno yake ne? Ina zaki sani bayan an lalata"

"mahaifa da alluran family planner, kawai don ta ce ba zata ba sai ki saka min ita a gaba da fada idan fitsari banza ce kaza tayi mana!"" Ka sake nayi ina kallon Karima tana gaya min magana akan nayiwa"

"Yusrah fada taki dauko min kular da xan sakawa Ubanta abinci. Shigowa yayi yana faWin. ""Ya dai kaza"

"uwa Yaya mai ya faru Agwagwata uwar albarka?"" ""Waye ban da juyar matarka da ita bata san haifa ba sai dai kashi a masai."" Kumshe bakinsa yayi yana dariya mai sauti. ""Yau kuma waye na samu da suna juya"

"au lulu love ce!"" Ya fada yana kallon yadda jikina yake rawa. ""Ita mana ita dai da bata san ciwon kanta ba, wacce dad'i miji ya kaita aka ta zuba mata alluran hana ciki!"" Cikin isgilanci ya ce mata. .""tow waye zai yarda ni ne bana son haihuwa da ita? Bayan nasan ba sonta nake ba kin san idan iyaye suka ga kana kula yarinya sai su dauka wani abu ne a tsakaninku, musamman idan Iyayen yarinyar suka gano cewa yarsu"

"bata jin maganarsu sai naka!"""

"""Ya Hafiz da bakinka kake fadar haka? Kada ka manta da mahaifina da naka Uwa daya Uba daya!"" ""And"

"so what? Dube ki kitse ya taru a jikinki ke kanki ba zaki iya gudun minti goma ba, dube ki don Allah har kunya nake na ce ke matata ce, domin dariya zaa ayi min, balle kuma."" Dariya yayi ta min yana fadar cewa..""wallahi matse matsinki wari suke balle kuma can kasar idan kika kwanta kamar an zuba kashi a"

"bola!"" Sai naji jikina yayi sanyi duk abinda zai gaya min naji ciwo ya san ni."

"""Ka sake ta mana Habibi wannan mai kama da dorinar ruwan tsoro take bani!"" Dariya yayi sosai ya ce"

"mata. ""Karimcy ba zan iya sake ta ba, kai ko da na sake ta waye zai aure ta? Kada ki manta yadda take tafiya da kyar da kyar waye zai aure ta? Abin dariya nama na jan kare."""

"A hankali na bar abin da nake na wuce daki, na zauna na fashe da wani irin kuka. Ina jin kamar zuciyata"

"zata buga wallahi naji zafi amma ya zanyi, ina son ya Hafiz sosai ba wani abu bane fadar da yayi, shigowa dakin yayi ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login