Follow us on social media

Showing 18001 words to 21000 words out of 140751 words

Chapter 7 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

293

na"

"sha kafin na sha magani na fito waje aiki. Sosai na mai da hankali kan aikina, buga gidan aka yi na mike na je na bude makotanmu ne, na bude suka shigo suna ta fara'a. ""Sannun da zuwa, sannu mu shiga daga cikin."" ""A"" a waje ma ya isa wannan zafin ai kuna shan fama musamman wacce take wannan dakin zata fi kowa shan zafi ita da jin sauki sai ko damina ko hunturu."" Murmushi nayi bayan ma shiga daki na dauko musu kafet na shimfida musu. Sannan na shiga na dauko musu pure water na ajiye musu ina kara gaishe su. Sun amsa sannan na ce musu ."" Bari na kira muku abokiyar zamana! "" Na tashi na buga kofar Karimah dakyar ta fito tana wani hade rai, suka gaisa sama sama, sannan ta koma wata yar yarinya ce ta bani sha'awa, na dauke tana ina faWin. ""Ina Mamanta!"" Murmushi Mamar tayi tana faWin. ""Sunanta Suleimin"" gashi yarinyar tasha wanka an gyarata. ""Allah sarki sunana Lubabatu amma ana kirana da Lubnah!"" Fitowar Yusrah ta ce min.. ""Lulu zan sha tea!"" ""Tow ina zuwa!"" Na shiga dakin da kananun"

"kofina uku na hada har da na yarinyar na fito waje na mika musu itama yarinyar na mika mata. ""Har da"

"dawainiyya!"" Murmushi nayi ina kallon yarinyar, don ta shiga raina duk inda zan ga Yaro kamar na dauke"

"shi nake ji, haka muka yi ta hira ina leka kitchen din, dab Magariba suka min sallama, sannan suka min bayanin gidansu ne a bayan na mu, ita babbar cikinsu sunan ta Maman Abidah ta aurar da ita ma, sai yan mata biyu Na'ilah da Na'ima, sai ta gefenta ita kuma Maman Boy da alamu ita kamar yare ce, Yaronta daya Boy tana sayar da kayan miya da sauransu, sai Maman Suleimin, sai wata kamar Amarya ta ce min. ""Ni amarya ce! Akwai Maman Salim da Maman Yaya basu gama aiki bane amma zasu shigo gobe!"" Na"

"musu godiya na rako su waje, suka tafi. Na dawo na karasa aikina tare da jollop din macaroni."

Wurin karfe bakwai ya shigo shi da likitan ya kara duba ni ya saka min ruwan karshe sannan ya bani

"shawara yadda xan kula da kaina, sannan ya tafi Ya Hafiz ya ajiye min leda bag din da ya kawo min, ya shiga buWewa, yana faWin. ""Gashi nan ki ci, amma ki sani kudin wannan abin da nake miki shima dai rantowa nayi!"" Gyada kai nayi nace mishi. ""Na gode!"" ""Ba fa batun godiya biya zaki yi ai kin sani biya zaki"

"yi a tow!"" Daga nan ya mike ya bar dakin."

"Sauran kwanakin da suka biyo baya, na ji sauki makotana sun shigo, bayan kwana biyu nima na"

"shiga musu muka gaisa sannan na dawo, nayi haka ne don fita hakkinsu, sannan a gefe guda Karimah tana d'aga min hankali rigimar yau daban na gobe daban, haka yasa kullum ya dawo sai ya ji kamar ya"

"rufe ni da duka, haka xan ta bashi hakuri."

"Kusan wata mun Waya a zango, Ya Hafiz bai tab'a cewa na kira gida na gaya musu mun tashi ba, sai da"

"ya ji a ransa. Ya kalle ni da zai tafi kasuwa ya ce min. ""Yau ina ga zaki yi baki me nene babu a gidan?"" Shiru nayi kafin na ce mishi. ""Kayan miya, shinkafa ma ya kare"" nayi ta mishi lissafin abinda babu, koda ya fita wurin karfe goma sai gashi da kayan abinci niki -niki, ya kawo dakina ya ajiye su kwalin madara da milo duk ya kawo dakina ya zuba, sannan ya sakar min murmushi. Tunda na ga haka na fahimci akwai wani abu a kasa, sai dai kamar kullum ina mishi fatan shirya sannan ina da yakinin zai daina abinda yake"

yi.

Haka na dawo dakina na kara kintsa dakin na fito na daura abincin rana. Ina waje wayata da babu

"chaji yayi kara na shiga dakin. Ya Umar na gani kamar nayi kuka na Wauka. ""Yanzu Lubnah kin kyauta baki gaya mana kun tashi ba? Har shi Hafiz din ya iya gaya mana?"" ˜asa magana nayi ina jin shi. Yayi ta fada sannan ya kashe wayar, Aunty Hindatu ta kira ni. ""Auta me ya faru?"" Murmushi nayi mata nace mata. ""Ba kome Aunty!"" ""Lubnah idan kika cigaba da shiru taya zamu taya ki wannan yakin, wannan ba hujja ba ne, Lubnah ki bude baki kiyi magana ki gaya min me ya faru?"" ""Ba kome!"" Na kara fada mata, ""Lubnah ina takardun gidan can?"" ""Don Allah kada ki tambaye ni, don Allah kada ki saka min magana! "" Na fada kamar zan yi kuka, murmushi tayi ta ce min. ""Shi kenan idan kina bukatar kudi zan turo miki da"

"dubu dari!"" Ban ce mata kome ba, ta kashe wayar. Zuwa yammacin ranar sai ga Aunty Innah ta shigo ita"

"da Aunty Jamilah matar Ya Umar, ganin gidan yasa duk suka yi shiru. Ni dai ban ce musu kome ba, shine"

"dai yayi ta fada yana faWin. ""Ai ban san me ye matsalar Lulu ba, ace bana gari domin Allah ya gani nayi tafiya kusan wata guda nayi tare da Karimah kuma na bar mata yaran jiya da muka dawo nake tambayarta ashe bata gaya muku, ai har nayiwa Baban Bauchi bayanin dalilin tashinmu, amma in sha Allah kafin nan da wata shida zamu koma wani hatsari ne ya faru amma an shawo kansa. "" ""Allah ya"

"kyauta ya kiyayye na gaba!"""

"""Amin Ya Allah, Luluna idan zasu tafi ki diba musu tsaraba nan, akwai wasu a dakin Karimah bari na"

"kawo sai ki hada musu."" Ya tashi ya fita, can sai gashi dauke da jaka cike da fruit, ya kawo musu da Naira dubu goma a ciki wai su yi kudin abin hawa, Aunty Innah ce ta kawo su a motarta, bayan fitarsa da ya ce musu bari ya tafi muda lawan akwai kayan da aka kawo zai je ya duba, ya fita Aunty Innah ta kalle ni yadda nayi shiru. ""Tunanin me kike yi?"" Ta ciro kuWin da yake cikin jakar ta ajiye min a gefena. ""Mu yan uwanki muna jiranki duk lokacin da kika shirya ba zamu kashe miki aurenki ba!"" Tana gama fadar haka suka mike tare da barin kayan ma bakiWaya basu dauka ba, domin tun kafin su fita Karimah ta fita da"

"Yaranta, aka bar ni a gidan ni daya tal."

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

BAKWAI

"Zama nayi ina nazarin makomar rayuwata, me nayi na kuskure? Duk da ina son Ya Hafiz amma ban san"

"me yasa yake jin dadin daura min laifi ba, shi ya hana ni gayawa mutane, yanzu yazo yana faWin ni ce me yasa yake min haka ne? Me yasa tow? Dama soyayya tana zama kiyayya ne? Ina cikin wannan tunanin Baban Bauchi ya kira ni, wato Abbanmu yayi ta min fada yana faWin nayi haka ne don ba lalata zumuncin da yake tsakaninsa da Wan dan uwansa, wallahi ban isa ba. Haka ya gama fadar shi nace mishi yayi hakuri. A hankali kuka ya zo min can kuma na fara dariya kamar mahaukaciya, domin haka ne kawai zai saka ni"

jin dadi.

"Tunda na fahimci dariyata tafi kuka saka ni nishadi, na saka a raina na daina kuka akan Ya Hafiz, zan yi"

"dariya. Aunty Hindatu ta zo ita da Ya Sani suka ga gidan, babu wanda yayi magana har suka fita. A ranar Aunty Hindatu ta kira Ya Ado ta gaya masa. Murmushi yayi yana faWin. ""Hindatu dadina dake baki da hakuri, mutane biyar suke da iko akan wannan lamarin Baban Bauchi, Baban Jama'are, baba malam, sai ita Lubnah idan ta ce bata yi duk inda nake zan kwana a Bauchi, amma fa sai ita da kanta ta ji a ranta bata yi duk abinda zamu yi ba yadda muka iya."". ""Amma kasan ya sayar mata da gidanta na Tambari?"" ""Tow ya za ayi tsakanin mata da miji sai Allah idan ita ta bashi fa!"" ""Ado kasan sai Lulu bata da hankalin da zata bashi gida ya sayar ko? "" "" Tow waye ya sani kin ga idan tana bukatar wani abu ayi magana batun gida dama ai an saya mata ne domin su huta da Yawon gidan haya tunda ya sayar ya sayi wani."" "" Amma ai a getto area ne! "" "" Ba gashi ta zauna har na wata guda ba ta gaya miki ne?"" Shiru tayi ya cigaba da magana. "" Baba da Mama sune suka involved din rayuwar Lubnah, idan da zasu tsaya mata Lubna zata samu yanci amma fa sai taso idan bata so ba, kuwa koda su zasu shiga ba zata matukar bata bada hadin kai ba. Babu yadda zamu karshe sai dai shara'a tayi aiki kanmu haka magatakarda kin manta da dokar ce. "" "" Ba dokar na manta ba, na hango tashin hankali da bukatar taimako, bata bukatar kome amma kuma"

"idanunta yana kukan tsoron da niman taimako, wallahi Lulu da ka sani ba ita ba ce a gabanmu"""

"Dakyar ya shawo kanta Ya Sani ya ce mata, ""Ni dai na rasa me shegen Yaron nan yayiwa Abba ne da"

"baya kaunar laifinsa, ki ga yadda Lulu ta koma don Allah? Ko ni da nake zukar wiwi wallahi ban ga dalilin dariyar da take ba, ki ga yadda take abu kamar wacce take cikin tashin hankali."""

"Kwafa yayi suka cigaba da tafiya,"

***

"Ko Ya Hafiz ya ji abinda yake faruwa ne, yadda Yayuna suka fusata, sai gashi ya tafi har Jama'are wurin"

"Kakanmu, suka tawo tare yadda mutumin nan yake da mugun hali na tsane na bude idanun na ganshi, domin shima ya taka rawar lalata min duk lissafina, haka yayi ta fada da nuna kada ya ji kada ya gani domin yaji labarin ana son a kashe auren Lubnah da Hafiz, idan suka kashe auren waye zai aure ni?"

"Sannan ga misali a gabansu Jalilah tunda aurenta ya mutu waye ya zo da sunan zai aure ta, kada ya ji"

kada ya gani.

"Abin da basu sani ba ita Jalilah Ya Hafiz take so kamar tayi hauka, duk aurenta uku da tayi ta kasa zama a"

"gidan aurenta ne domin tana da yakinin wata rana ya Hafiz xai dawo gare ta. Haka abin ya cigaba da tafiya ba dad'i, a lokacin Ya Hafiz ya tsiro da wani hali shi da Matarshi."

"Abinda suke mun ba kome ba ne, sai nuna min da suke ni rayuwata bata da amfani, domin ido da"

"ido ya ce min. ""Lubnah baki da amfani a rayuwata, amfaninki kalilan ne, idan aka cire amfanin rashin"

"amfanin yafi yawa, kin ga wallahi ko bukatarki na dabi'ar da namiji bana ji, ke kanka dube ki, yanzu ace"

"na sake ki waye zai aure ki? Wallahi babu namijin da zai tab'a sha'awar aurenki domin baki da wani abin burgewa mace sai kace saniyar huWa! "" Ire-iren waWannan maganar da yake gaya min ya haifa min da"

wani irin yanayi.

"Yana yawan gaya min cewa a yanzu dangi ma basu bukata na, babu wanda ya damu da ni, itama"

"Hindatu don kudina da yake hannunta ne, idan babu ba zata kara kula ni ba,haka muka cigaba da jin kamar ba ni da wata amfani a rayuwar Ya Hafiz. Tunda ban haihu da shi ba, bani da wani abun da zai burge kowa. Ni kaina nasan be zama dole wani ya bukaci ni a rayuwarsa ba. A hankali na dinga jin kamar"

ni din ba kowa ba ce bani da sauran amfani.

"A haka watan azumi ya karato, ba zata Baba yayi mana, ya biya mana umara ni da Yayuna. Sai dai me?"

"Ya Hafiz najin haka yayi ta kunci da bakin rai tare da rigima da fitina kala-kala, karshe dai ban san yadda aka kare ba Baba ya ce ya cire sunana a cikin masu tafiya yayi replace da Jalilah. Wani irin bugawa zuciyata tayi kamar zata fito, a hankali na kama dariya ina jin kamar ni daya ce bani da amfani a duniyar nan, haka watan azumin nan suka yi shi a can ni ina gida, a lokacin na kara koyan yadda xan bawa kaina nishadi. Sai na fara tunanin sana'a bayan sallah, wanda shima a wunin sallah ya ce ba zan je ba. A Jama'are zamu yi sallah, nan ma na amince muka tafi. Muna dawowa nazo da madaran kuka. Na fara sayar da kankara da Pure water, ta nan bai hana ni ba. Sai dai ya daina bani kudin cefane. A hankali na kara har da zobo da kunun aya da fresh milk. Haka su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka zo min gidan, wuni da Yaransu nayi ta hidima gashi bana iya zama idan nayi baki abu ba abu ba sai dariya. Haka suka yi"

"ta kuka a daki, wunin da basu yi ba kenan."

"Wani abin da na fahimta shine Ubangiji ya saka albarka a kayan ruwa, domin lokacin sallah layya, nayi"

"ciniki har na ji tsoro, ana kawo min ruwan pure water har gida ake sauke min rabin mota, a lokacin da Ya Umar yazo gidan ya dauke karamin firji din a ranar aka kawo min babba deep freezer, wnada nake zuba jakan pure water ashirin ga kayan sanyina a gefe. Yadda kudi suke shiga da fita yasa Ya Hafiz ya fara tashin hankali na fara kudi xan rena shi, idan nayi abinci bana saka nama a wadace ai da can ba haka nake ba, nayi ta bashi hakuri ashe zai zare min tallafi da yake ne, domin ya daina kawo abinci gidan. Haka dai na kara tsayawa a tsaye sai Allah ya yaye mun dariyar da nake, sai dai duk niman da nake ina bawa"

Ya Hafiz ne domin bayan na cefane da nake yi kudin kusan shi nake bawa.

"Maman Na'ilah ita ce ta tambaye ni aron kudi, na ji tsoro ban iya bata ba. Karshe kamar wacce ta"

"matse ni na gaya mata ai kudin wurinsa yake, zuba min idanun tayi kafin ta ce min. ""Lubnah da hankalinki kuwa?"" Shiru nayi kafin ta cigaba da cewa.. ""wacce irin soyayya kike yiwa mijin nan naki ne? Kin san mun san kece kike dauke da hidimar gidan?"" ""Ba kome ai dan uwana ne."" ""Na ji ba wannan ba,"

"daga yau zaki na kawo dubu uku akwai adashe da muke yi zaki shiga ai zaman tare ta wuce haka, ga"

"yayarki nan wata siririya muna haduwa a asibiti ba karamin taimako take min ba, don Allah ki na kawo kudin! "" "" In sha Allah!"" Na fada tun daga ranar ban yarda na kai mata ba, domin kamar wanda aka"

"gayawa Ya Hafiz, kullum sai ya kirga abinda nayi yasan na kudin da yake ciki, idan ya dawo zai tambaye ni."

"Haka zan dauki kudin cinikin na bashi na mishi lissafin abinda aka kashe, ita Matarshi bata kome ni ce"

"dai akansu, haka dai muka ta mikewa abin ba dad'i, kwatsam aka tashi wani biki, Aunty Innah ta kawo min aikin Kunun aya da zobo, domin suma ina bayarwa a kai musu har gida, a lokacin aikin zai min yawa na shiga gidansu Maman Na'ilah na roka su zo su tayani. Haka muka yi aikin dasu. Sannan ka zo aka dauka, washi gari muka sake yi sai da muka yi kwanaki uku muna aikin kafin aka kawo mana kudin aikin naira dubu hamsin, na dauki 20k na basu talatin, Maman da tazo ta kwace ashirin din ta tafi da shi, ban san me yasa matar nan take min karan tsaye ba, amma naji haushi, wasa wasa sai ga Mamansu Na'ima ta saka ni a gaba da amsar kudina ko ina so ko bana so zata dauka, haka muka yi ta fama da ita daga baya da kaina nake tura mata kudin ma, ta daina zuwa. Ban san manufarta ba amma tabbas ta wani"

gefen tayi min abinda jinina suka gaza min.

"Haka watan azumi ya kara zuwa, ita ta bani shawarar na ajiye kayan za™i na koma sayar da ™an™ara. Ba"

"sai ya Hafiz yayi tsaye ya ce bai yarda ba. Sai dai idan zan sayi generator, na ce mishi. ""Ya Hafiz tow ka ba Ni a cikin kudin wurinka mana!"" Ai kamar ya rufe ni da duka. ""Ba zan bayar bada wutar gidana kike amfani."" A lokacin na rasa yadda xan yi ina jin kunyar amsar kudin wurin Maman Na'ilah, sai na kira Ya Sani na tambaye shi nawa ne kudin generator? Tunda sune suke sayarwa. Ashe nayi wayar a kusa da Ya Albashir, sai cewa yayi me zanyi da shi? Na gaya mishi gaskiya washi gari sai ga Mikano daidai da zata"

dauki freeze na har da karin freeza.

Nayi ta godiya aka turo masu aiki suka min aikin tsaf na sauka akan wutar gidan Ya Hafiz shima dai ai

"yana morar generator tunda kowa yasan watan azumi a lokacin nepa suka tadda iskancinsu, ga lokacin ana wani irin agazarin rana."

"Duk yadda xan fada farin cikin da nake ciki, kamar na boye ne. Ganin duk yadda zai Sullo min ina"

"toshe hanyar don bana son muna rigima, ba sai ya tsiro da fitinar cewa sai dai na kama haya dakin da nake ina biyan kudin wata wata da ruwan da nake tarawa a wajen shima ina biya. Haka na amince na ce nawa xan biya? "" "" Duk wata dubu goma! "" Shiru nayi kafin na ce mishi.."" tow Ya Hafiz ba ragi ne? "" "" Sai dai ku fitar min da kayanki a gidana!"" "" Shi kenan! "" Haka na amince ai ba wani abu ne, haka nayi ta niman kudi ya Hafiz yana amsa da sunan nashi, da sallah yayi nayi musu Winkin sallah don ya ce min hakkina ne nayi musu tunda ai ina samu, nayi mishi nayiwa Yaranshi da matarshi da Yan'uwansa na tura"

"har Jama'are aka kai musu, har da Baban Jama'are nayiwa Baba Malam ne ko da wasa ban mishi ba, ai"

"kuwa na sha zagi ya kira Baba ya gaya mishi, Hafiz ya bani kudi nayi musu kayan sallah amma naki, haka"

"Ya Hafiz ya fada. Sannan ya kara da cewa har su Mama da Yadiko nayiwa, amma a kuWina a lokacin sai da na kwashe kome nawa na sayar har da dan kunnen gwal dina, tow bani da kudin ina sana'a kudin na"

hannunsa.

"Bayan sallah ina cikin azumi sitta shawal, na fara sauraron karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i"

wanda ban tab'a jin kalmar ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login