Follow us on social media

Showing 72001 words to 75000 words out of 140751 words

Chapter 25 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

329

shekaru biyu kafin aka daina tura musu yau muka 2023. Sannan na turawa Lauyar da Alhaji ya haWa ni da shi, wannan tsakaninsu da ofishin haraji na jaha ce, na gama nawa a matsayina mai shiga da fice na kamfani, sai case na biyu, Bankin First ta turo kayanta har na Naira miliyan dari biyu amma ba a tura mata ba, shima ba ni na binciko ba CEO ya binciko kuma ya turo min da sakon. Gasu nan nayi printing Winsu."" Ya hada tare da mika Mrs Thomas da take gefen ta bawa Khamis, wanda ya jike da gumi. Yadda suke wasa da dukiyar kamfanin kamar basu Allah a ransu, shi kuma CEO baya kamfanin"

amma kuma twinkle eyes dinsa suna spark a kamfanin fiye da wanda yake kwana gefen kamfanin.

"Karba takardun Alhaji Mudansir yayi jikinsa yana rawa, bai taSa tunanin kari da ragi da yake yi a office"

"Winsa zai iya fita a takarda tar haka ba, dole ya dauki mataki akan kowani dan iska ya rasa wannan rashin wayon Khamis gashi nan dai kamar me wayo amma bakiWaya daga Turaki har Ubaid suna iya kifar da shi, duk yadda yaso Abbas ya dauke idanunsa akan Khamis din amma a bayan fage sai sun nuna son"

zuciyarsu.

"Cizon lips dinsa Alhaji Mudansir yake har Alhaji ELYakub ya fita daga office din Ubaid, kanshi kamar zai"

"bindiga, ya juya ya kalli Ubaid. ""Ka kula da kanka!"" ""Ka kula da Mimih domin ba san me gobe zai haifar ba, kasancewar ita Waya ce maka."" Hadiye yawun bakinsa yayi yana kallon Ubaid , ko kiftawa bai yi ba, mamaki yadda ya iya mishi barazana da yarsa. A hankali ya fita daga office din, ajiyar zuciya ya sauke"

yana mai jin sauki da nutsuwa a ransa. Daga nan ya tattara takardun ya kira Number Lauyar da Alhaji

"ELYakub ya haWa su, ya gaya mishi inda zai kai mishi, koda ya kai mishi sama sama suka gaida juna"

sannan kowa ya kama gabansa.

***

Lubnah

"Yau tunda na dawo nake daki, abinci ma yau dakin aka kawo min, ina ci ina kallon handout, ina nazari"

"har kusan karfe tara na dare. Ban fito ba wayar da Ya Ado ya saya min kwanan tayi haske kiranshi na dauka ina faWin. ""Ya Ado?"" ""Auta ina lafiya dai ban ganki ba ne?"" ""Bari na fito mu gaisa!"" Ka tattara kome na sauko kasa, na samu suna ta hira zama nayi ina kallon Aunty Zakiyah. ""SAN yarinyar nan bata tsoron Allah!"" Murmushi yayi yana faWin, ""Auta da gaske ne kin shanya Doctor Ahmad?"" Idanuna ne suka cika da kwalla, ina kallon kasa ya cigaba da cewa. ""Tunda nace kin fara karatu hankalin Mama yake kanki tace tana son ki yi aure Hafiz sai ya rabu da ke?"" Ni dai ban ce kome ba, har ya gama maganarshi, na ce mishi. ""Zan koma na kwanta."" Na mike zan tafi ya ce min.. ""Ahmad mutumin kirki ne, ki yi nazari yasan matsalarki kuma zai tsaya miki!"" Da gudu na haura sama, ina jin kuka yana zuwa min, ni tsoron maza nake ji bana son abinda zai hana ni dasu, haka yasa na ki kula Ahmad. Kwana nayi ina kuka domin har"

yau ban manta abinda Ya Hafiz ya min ba.

"Washi gari tun kafin ya fito na bar gidan, domin bana son Magana ya kuma hada ni da shi, a"

"makaranta na karya shima naci ne gudun kada na wahalar da kaina. Wunin ranar har aka tashi bani da walwala, ina hanyar komawa gida Baby ta kirani. ""Yan mata gani a gidanku!"" A shake na amsa mata, sannan na ce. ""Ina hanya!"" Haka na isa gidan a hankali nake takawa, har gidan, motar Doctor Ahmad na hango a harabar gidan, ba don mun yi ido hudu da shi ba da na juya. Haka na daure na shiga na gaishe shi sannan na wuce cikin gidan, na samu Aunty Zakiyah tana gida. Gaishe ta nayi na wuce sama. Baby ta biyo ni. ""Yan mata wai meye ya faru ne?"" ""Babu!"" Na fada mata, murmushi tayi ta ce min. ""Wancan hot guy din fa? Da me shi ko na Wauka?"" Da sauri na juya ina kallonta. Baby irin mutanen nan masu open mind bata iya boye what she want kome ta gani tana so baya bata wahala ta mallaka. D'aga gira daya tayi tana faWin. ""Ko dai naki ne?"" ""Yayi miki da gaske?"" Na tambaye ta domin ina jin kamar zata raba ni da matsalata ce, idan har ta ce yayi mata tow ba makawa zan samu hanyar rabuwa da shi. ""Idan kina son shi zan baku number wayarshi,"" na fada ina kallon yadda take murmushi, ""wallahi yayi min!"" ""Ok ko bari na fito wanka sai na baki number shi."" Na fada ina wucewa toilet, sai da nayi wanka nayi Alwala sannan ka fito na samu tana zaman jirana, abu take zuka na ce mata. ""Yaushe zaki daina shan wannan abin ba?"" mai da shi jakar mata tayi tana faWin. ""Ina kokarin bari in sha Allah."" Ina son gaya mata gaskiya amma kuma san yadda zata dauki maganata ba, kada ya ga kamar don zan hadata da Doctor Ahmad ne, sai na ja bakina nayi shiru na kyale ta har nayi sallah, ina idarwa Adil da Mama suka kawo mana abinci, muka fara ci a hankali, ina lura da yadda bata son abinci, na ce mata. ""Ki daina shan drugs, ki fuskanci rayuwa ki ci abinci domin wallahi zai iya haifar miki da wata matsala daga baya ayi ta kuka da juna."" Murmushi tayi ta ce min. "" In sha Allah zan bari! "" Daga haka ta cigaba da tsakuran abincin tana wasa da shi, har"

"muka gama Princess ta shigo ta ce min. """

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 28"

"""Aunty kizo Mama tana kiranki! "" Nasan batun Doctor Ahmad ne, ji nayi gabana yana faduwa, kamar zan"

"yi kuka haka na mike na shiga ban daki na wanke hannuna, sannan na saka mayafi akan riga da zanin jikina, na sauko kasa na same ta tana duba books din Yaran na makaranta. "" Lulu kin manta da Doctor Ahmad ne a waje?"" Shiru nayi ban bata amsa ba, can dai ta kara magana sannan na d'ago kai ina kallonta kafin na ce mata.""to! "" So nake na ce mata, ta sallame shi amma na kasa saboda yadda bakina yayi nauyi, hawaye ne ya cika min idanun. Komawa sama nayi na dauki Hijab na saka sannan na sauko kasa, na"

"samu tana waya da Ya Ado, kusan tare muka sauko da Baby ta mata sallama zata tafi, muka hada hanya a waje na samu Doctor Ahmad zaune. Jan plastic chair nayi na zauna ina dan matsawa can nesa da shi, Baby ta tsaya a bayana tana gaishe shi, sannan ta min sallama ta fita a gidan. Har ta bar gidan yana bin ta da idanu. ""Ki fita harkan yarinyar nan, bata dace da ke ba."" Ni dai ban ce masa kome ba, yadda ya gama"

surutunsa haka na tashi muka yi sallama.

"Ban san ya suka kare ba, sai dai kwana biyu da zuwan shi ya kira ni a waya yana tambayata me yasa"

"na bawa Baby numbersa, shiru nayi bani da ta cewa. Ganin naki magana yasa shi katse kiran, washi gari sai gashi ya zo, shiru duk muka yi yana kallon yadda nake wasa da yatsu hannuna na kasa magana tunda na gaishe shi ban kara magana ba. ""Kin san yarinyar nan bata kyauta ba? Sannan ta gaya min cewa kece kika bata number ta? Akan me zata na kirana any how? Har matata sai da ta fahimci akwai wani abu a kasa."" Sai a lokacin na d'ago kai ina kallonshi. Wato shima dai irin Ya Hafiz ne na shiga gidansa ya gana min azaba da Matarshi, to idan ba mai mata ba, waye zai aure Ni? Ni dai ba samun saurayi xan kara yi ba a karo na biyu, duk tsiya idan ban auri mai mace daya ba zan auri me mata uku na shiga ta huWu."

"Wannan abin ya saka min wani irin tsoron shi Ahmad din kansa. Duk mutumin da bai da ikon kasan a gidansa har abada ba mijin aure ba ne. Don haka na tashi na bar shi a wurin haka ya kira Ya Ado ya gaya mishi, lokacin da Ya Ado ya dawo gida ina daki ya shigo dakin, jan stool yayi ya zauna yana kallon yadda nake takure wuri guda. ""Lubnah me yasa ba zaki bawa Ahmad dama ba?"" Yadda yayi magana yasa na d'ago ina kallonshi, idanuna cike da kwalla har ya gama magana ban ce mishi kome sai kukan da na fara ganin yadda nake kuka da gasken gaske yasa shi zuba min idanu cike da mamaki, har washi gari ban fito ba don bamu da class, ina daki a kwance gashi garin an tashi da ruwan sama, haka yasa nayi luff a dakina suka tafi aiki sannan na fito na karya na wanke kayan na koma na kwanta. Karfe uku na fito saboda hayaniyar Yaran na fito na tsaya suka shiga kafin motar islamiyya ya zo ya dauke su na koma na kwanta. Karfe biyar duk suna gidan ban kara lekowa waje ba, na cigaba da kwanciyata. Wurin karfe goma na dare sai gasu nan su biyu yaran sun kwanta ina kwance, kunan wutar dakin tasa nayi kamar ina barci, zama a bakin gadon Aunty Zakiyah tayi tana kallon yadda na sake jikina. ""Ko tayi barci ne?"" Inji Aunty Zakiyah, ""idonta biyu!"" Shima ya ja stool ya zauna yana kallon yadda nake kwance. ""Tashi mun zo magana ne akan Ahmad!"" Tashi zaune nayi ina kallon gefe guda. Tunda kuka fara kawon farillah da musta'abin halin Ahmad, kasancewar shi mutumin kirki ban san lokacin da na fara kuka me karfi ba, sai suka zuba min idanu. ""Me aka miki to?"" ""Kawai ku mai da ni Bauchi na je can ko kashe ni ne gara su yi! "" Shiru Ya Ado yayi yana kallon yadda nake kuka. "" Me yasa tow? "" "" Tsoro suke bani tsoro yake bani, duk wanda zai zo gare ni tsoronshi nake, ku gane ni tsoron maza nake, wallahi cutar da ni zai yi don Allah idan kuna son"

"farin cikina ku kyale ni!"""

"Ganin yadda nake kuka abin dai yayi ta basu mamaki, har suka fara ganin kamar basu so kansu ba,"

"don haka Ya Ado da kanshi ya rarrashe ni, na bar kuka suka hada min abinci na sha tea, sannan suka tafi"

"na kwanta kusan raba dare nayi ina gayawa Allah kukana, tsoro nake ji shima Ahmad din akwai abinda ya"

"gano yasa yake bina, ban san yadda Ya ado ya fahimta da shi ba, amma kuwa na ga ya daina turo min sako ko wani abu sai dai duk ranar juma'a yana turo min da sakon barka da juma'a wato ba zai tab'a give"

up ba.

"A bangaren Mama kuwa har zuwa tayi akan matsalar sai dai tana zuwa lagos, ganin yadda ta saka ni a"

"gaba da maganar aure, ban ce mata kome na tafi makatanta na dawo, na same ra bata daina maganar auren nan ba, bata san yadda abin yake ba, ni dai ban san me ya faru ba, sai dai na bude idanuna na ganni a dogon kujeran parlourn, su Ya Ado suna ta min sannu, dakyar na tashi. Rike hannuna Aunty Zakiyah tayi zuwa dakina Yara na kwanta, ta kawo min magani da tea na sha, yana fada min nayi sallah na zo n kwanta tuni barci yayi gaba da Ni, sai karfe daya na dare na farka a lokacin na samu tana kan abin sallah, tashi nayi na shiga ban daki nayi alwala na zo na gabtar da sallah Magariba da Isha, ina idarwa na daura da nafilla. ""Lubnah?"" ""Na'am!"" Na kalle ta, yadda take kallona tausayi na take ji, haka yasa na matukar jin tausayin kaina. ""Tsoro kike ji ko!"" Hawaye ne ya zubo min, ashe ta sani? Ashe tasan ina jin tsoro; bude min hannu tayi na shiga ina wani irin kuka, ""Ya isa haka ba zan kara miki maganar aure ba, ba xan kara cewa wani ya miki magana aure ba. Jiya naji kamar na rasa ki kenan, ban san ashe haka abin yake ba. Lubnah ko wani ne yace baya son abu ba zan mishi dole ba, balle ke da na yi miki laifi masu tarin yawa, ina jin idan baki yafe min ba Allah ba zai yafe min ba, "" ni dai ina jikinta tare da jin wani dumi me dad'i, haka tayi ta rarrashina tana gaya min nayi hakuri da ™addarata haka ta zo min, satinta uku, ta koma Bauchi ta bar mu da kewarta. Haka na cigaba da rayuwata cikin yanci da walwala lokacin da na samu hutu kamar na je Bauchi, amma haka na hakura duk abinda zai hada ni da Hafiz ina kin sa, a zuwan Mama ne muka ji labarin ya kai sadaki da kayan aure a can garin Mamansa. Wai Abba ya sauya mishi gida, ni dai ban ce kala ba har suka gama hiransu. Karshe barci nayi a parlourn ban san lokacin da"

suka gama hiran aka tashe ni na je na kwanta ba. Bayan tafiyar Mama na sha hutu na koma school.

"Shekara daya da wasu watanni a lagos wnada yayi daidai da wata na bakwai da fara karatu, haka yasa"

"na kara nutsuwa zuwa yanzu karatun shine mijina da duniyata, course mate dina tun suna kirana silver spoon saboda sun gano nice aka musu kashedi akai, suka yi ta min tsiya da tafiya tayi nisa sai suka watsar da makamansu suka kuma janyo ni muka zaka Family, duk yadda zaka so ka kebe da ni na shata layi ba ruwana da soyayya, tsoron maganar namiji nake, department dinmu har sun gano tsoron mazan da nake ji, wani irin tsoron maza da nake ji duk abinda za ayi ayi na karatu amma bayan nan kana fara wani abu, xan fita harkanka. Duk yadda kowa yaso yasan matsalata da maza ban tab'a magana ba, haka"

"yasa suka kyale ni, na kuma kame kaina na saka a raina ba ruwana da duk wani dan balaja'u."

"Haka kuwa muka kasance har muka kusan gama karatunmu, a lokacin ina da shekaru biyu cib a jahar"

lagos.

***

KUMO FAMILY MANSION.

Kallon Hajiya Khaulatu Daadah tayi cikin wani irin takaici take kallon yarta da son zuciya ya gama rufe

"masu idanu. ""Daddah ki bawa Alhaji hakuri wallahi Khamis ba zai kara ba, kuskuren fahimta aka samu!"" Ta fada tana sunkuyar da kai kallonta Daddah tayi cike da mamaki da bakin ciki mara iyaka. ""Yake"

"yaronki ce tayi laifi kin zo na saka baki na bawa ita baffanki hakuri Khamis ba zata sake ba."" Murmushi"

"tayi irin na manya, sannan ta cigaba da cin mutuncin Hajiya Khaulatu. ""Wato ita wancan Yaro Turaki da bata da kowa sai Allah, kika jifeta da shaidar zur, ita kuma Yaronki da take da Uwa da Uba ka zo kare shi saboda shi ne mai gata, ita wancan tana da waye? Bata da kowa sai Allah. Wai na tambaye ka Khaulatu me Yaron nan Aisha da yayunku suka muku da kuka tsane su haka? Ni a sanina basu muku kome ba idan har akwai abinda zaku yi bai wuce tsayawa da Anne Aisha yayi a Kamfanin Alhaji ba, amma kun tsane shi tare da ita yar uwarku."" Yadda Daddah take shiga ba nan take fita ba, karshe haka suka yi shiru ta kori"

Hajiya Khaulatu daga cikin gidan.

"Wurin karfe uku na yamma Jasminah ta shigo cikin gidan, ta samu Uncle Auta da Hajiya Samirah. """

"Barka dai datti! "" Yay gaida Alhaji ELYakub Kumo, sannan ta juya ga Hajiya Samirah ta ce mata.. ""Aunty Barka dai ya kike? Yasu Munawara da Abid?"" ""Lafiya lau Jasminah, kin leka Hajiya Zeenatu?"" Yatsina fuska tayi tana kallon Daddah, ""Daddah ya kike ?"" "" Kaci gidanku! Da kazo ai baka gaishe ni ba sai yanzu zaka ce wai ya nake ba yadda nake ina shure-shure."" ""Allah ya baki hakuri!"" Banza Daddah tayi mata, Alhaji ELYakub ya kalli Jasminah. ""Ina jinki!"" Gyara zama tayi ta ce mishi. ""Gaskiya na gaji, tunda shi Turaki ba zai musu magana ba ya kamata a bani damar nayi magana tunda ina da hakkin akan kasona da yake cikin kamfanin!"" Kallonta yayi yana murmushi ya ce mata. ""Turaki yayi magana ki ce ya fito da sonkai? Ke kika ce Turaki yana nuna iko dayawa ko za a bada matsayin CEO baki amince a bashi ba, yanzu kuma ki dawo kina blaming Winsa shi da ba a kasar yake ba. "" Yayi mata magana yana murmushi, bakiWaya ta ji kamar ta nutse a wurin. "" Ita Turaki ta ce ba zata dawo ba, da irin wannan masfar da kuke yi gara kada ta dawo a sakata ta rame. "" Daddah ta fada tana hararansu. "" Yanzu dai me Jasminah take bukata haka kawai Jasminah bata zuwa akan abinda tasan waye a kai ba?"" Shigo da tiren abincin Alhaji ELYakub, tuwon alkama ce miyar kuka wanda yaji kayan kamshi da hadi na musamman. Ajiye tiren abincin Maid suka yi ta yi, har gaban Jasminah. "" Ina jin Jasminah? "" Alhaji ELYakub ya kara magana, yasan abinda ya kawo ta amma tunda ba zata yi magana ba shima shiru zai yi abinda ya fahimta shine ganin Samirah yasa tayi shiru taki magana, suna zaune a wurin har ya gama cin abincin, Uncle Auta ya shigo suka gaisa shine ma Ya kalli Samirah ya ce mata. "" Ya dai na ganki anan? "" "" Yanzu zan tafi, amma Mujitafa me yasa Matarka da Matar Ubaid basu zo birthday din su Abid ba?"" Ta fada tana wani hade rai ita nan an bata mata rai. "" Saboda basu fito daga babban zuri'a masu arziki irin naku ba, su zo anayi ta musu kallon banza da basu isa ba! "" Ya fada yana kallon Daddah da take gyada kai. "" Baffa barka da warhaka, Ubaid ya mika sakon wasu bayanai ga Turaki sauran kuma da a ji da shi, gaskiya Khamis yayi"

"laifi dayawa sai dai yana da kyau a dawo da shi, domin ko babu kome yana lura da shashin tallace-tallace. Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login