Follow us on social media

Showing 3001 words to 6000 words out of 140751 words

Chapter 2 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

290

wanka na juye ruwan zafin na yi tsarki na yi wanka, sannan na fito na shirya zuwa kitchen, na daura abin karyawa da sauri sauri. Na gama wainar fulawa da ruwan tea, na fita na dauko kular makarantar Yusrah, na zuba mata sannan na nufi bangaren Karimah na buga kofar, bude kofar tayi tana hamma daga ita sai kayan barci. ""Dama abincin makarantar Yusrah na kawo!"" ""Tow ko zaki shigo ki shirya ta ne?"" ""A'a ina da wani aiki da zanyi, zai fi kyau ki shiryata!"" Na mika mata abin makarantar na dawo bangarena, ina shirin zama na karya sai ga Ya Hafiz da Yarinyar. ""Ko Karimah bata haifi Yara nan ba, ai na kine, gashi maza ki shiryata."" Haka na mike na amshe na wuce dakina da ita na mata wanka tana ta min kukan banza, har da ihu, ina shiryata Uwarta ta shigo tana faWin. ""Wai me kika mata ne take ta ihu?"" Ni dai ban ce kome ba, tana ganin abin karyawan da na ajiye ta zauna ta fara ci, har na gama ita kuwa ta cinye. Sannan ta kamo hannun Yarta suka fita. ""Yawwa wannan abin ya yaji dayawa, sannan me yasa kika sake garlic karshe yau sai na sha wani abu domin Yayanki baya son wani abu me tashi!"" Ta fada tana murmushi, ni dai ban ce mata kome ba, kitchen na nufa na kara dibo abincin na fito na zauna na fara ci, ina kallon tv, ban gama ba sai ga Ya Hafiz da Yasir, ""shima ki mishi wanka!"" ""Tow"" nace mishi na cigaba karyawa. "" Sai yaushe"

"zaki tashi zan kwana ina jiranki ne? "" "" Kayi hakuri! "" Na mike da sauri ina kwashe sauran wainar fulawa."

""" Jaka ban san me ATBU suka gani suka baki first class honors ba, dube fa baki san kome ba sai ci, dalla ki"

"mishi wanka ki bashi abin karyawa. "" "" Kayi hakuri! "" Na fada ina amsar Yaron bayan na dawo daga kitchen, na wuce na mishi wanka na shirya shi nazo ina bashi tea, ya fara ihu yaran kamar ana gaya"

"musu , wani abu da zasu yi a lokacin Uwar ta shigo ta ci kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar kyau. "" Lulu me kike mishi ne?"" Sauke shi nayi ya wuce wurin Uwar, tana kallon kayan parlourna, lokacin haihuwar wannan Yaron Abba ya sauya min. "" Kayan parlournki kamar basu tsufa! "" Ni ban ce mata kome ba, domin tun fil azal haka Allah ya halicce ni, bana son yawan magana, a shekarun baya ina da yawan tsokana da zolaya, amma baya bayan nan bakiWaya kamar an sauya min rayuwa,. Haka nake bana son Magana ko damuwa. ""Yaushe zaki sauya wasu?"" Na gaji da tambayar renin wayo na ce mata. ""Sai kin"

"sake haihuwa!"" Rike baki tayi tana faWin. ""Wai sai dai ko ke?"" Yake na mata ban ce kome ba."

"Haka ta fita, ina zaune a wurin na gaji gyara parlourn na fara tare da shirya kome a inda yake, ina aiki"

"aka kira wayata, dauka nayi Ya Ado ne, mutanen Lagos dauka nayi ina murmushi na ce mishi.. ""Barista ya aiki?"" ""Auta"" ""na'am!"" Na amsa mishi a hankali, ""Hindatu ta kira ni, akan wani batu ya abin yake?"" Tsintar kaina nayi da cewa.. ""kawai zato take amma wallahi ba kome!"" ""Auta gaya min idan baki gaya"

"min ba wa zaki gayawa? Kada ki daka ta su Abba kin ji!"""

"""Ba kome wallahi!"" Na fada ina lashe bakina. ""Auta gaya min gaskiya meke damunki?"" ""Nima haihuwa"

"nake son nayi na ga Yarana koda zasu na min kukan banza ne?"" Murmushi yayi ya ce min. ""Shi kenan Allah zai kawo kin ji, sannan zan tafi wani course Canada idan na samu dama zan turo ki tafi kin ji sai a"

"duba lafiyarki."""

"""Yaushe zaka dawo?"""

"""Shekara daya da rabi ne, kin ji kiyi hakuri ba zan jima ba! "" "" Allah ya bada sa'a ya bada abinda aka fita"

"nima!"""

""" Amin Ya Allah! Kin ki aikin gwamnati ko?"" Murmushi nayi kawai, ya ce min.."" Gashi nan zan turo miki"

"jari sai ki fara wani abu ko za a dace! """

""" Allah ya saka da alkhairi! "" Na mishi godiya, ya kashe wayar, can nayi shiru ™aran shigowar sako na ga"

"ina dubawa na ga Naira dubu dari biyar ya turo min. Kiranshi nayi ya katse ya kira ni. ""Kada ki damu ki"

"fara wani abu, Lulu kada ki gayawa Mijinki, ki sami Hindatu ko Inna ki gaya musu, zasu fi baki shawarar da ya dace kin ji."""

"""Na gode sosai! Allah ya kara lafiya da nisan kwana, na gode!"""

"Amin yayi ta amsawa, bayan na gama na kira Aunty Hindatu, na gaya mata a take ta saka na tura mata"

"dubu dari hudu ta ce min, zata gayawa Mama da Abba, ta bar min dubu dari sannan ta gaya min kada na tab'a fadar dubu dari biyar ya turo min, kawai na ce dari ne, kamar yadda ta tsara min haka nayi shiru ta kira Abba ya gaya mishi, ina cikin girki ba sai ga Ya Hafiz ba kamar an wurgo shi, a razane na kalle shi. ""Ina kudin da Adamu ya tura miki?"" Dama na goge alert din farko, ya amshi wayar yana ta dubawa ya ga"

"dubu dari ta opay dina, kallona yayi irin kallon kurilla nan. ""Yanzu ke mi zaki yi da kuWi?"" ""Sana'a?"" Na"

"fada ina kallon kasa, tura dubu saba'in yahi ya bar min dubu talatin,"" zan ajiye miki, kada ki gayawa"

"Hindatu dai na karba!, yawwa ki bawa Karimcy dubu goma, nima ki bani ladar ajiya!......"

08130269641

*Mai_Dambu*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

BIYU

"Nasan haka zai faru, sai na tura mishi tare da ita matar nashi. Tow me zance? Na hanata ya min rashin"

"mutunci. Yana ganin na tura mata ya ce min. ""Ke matar arziki ce, duk wanda ya zauna da ke sai ya ci daga arzikinki, shi yasa na tsani wani ya shiga min rayuwarki domin Allah ya gani ina sonki ina son zama da ke!"" Gyada kai nayi ina aikin hada abincin rana, yana fita na cigaba da abinda nake a cikin dubu dari biyar ba don Aunty Hindatu ta amsa ba, tabbas da na tashi babu kosisi. A duk lokacin da na samu kuWi haka yake min, ni kuwa kamar wacce yake wankewa bana iya mishi musu, a yanzu ma nasan sai ya"

"bididigin ya ji nawa aka turo min, Ya Hafiz dai."

"Ina cikin wanke busashen kifi sai ga Matarshi. ""Ashe kyauta muka samu Hajiyata, to mun gode mu"

"ga dubu goma amma nasan yafi haka ko darling ne ya karba? Ina ta son na gaya miki."" ""Nima dubu goma suka rage min!"" Na fada daga haka nayi shiru, jin yadda na fada babu wanda a cikin maganata yasa tayi shiru, sannan ta kuma ja bakinta bata kara magana ba, ta bar parlourn ban san me yasa suka mai dani haka ba! Koda yake ni ce na mai da kaina haka. Zan iya cewa a duniya duk yadda Ya Hafiz xai ce koda wuta ne zan iya bin sa ciki domin ina sonshi. Kuma zan iya kome domin shi, don na taso da wata mahaukaciyar kaunarshi ne. Shi yasa duk abinda zai min bana tab'a fushi ko nayi ma Baba zai saka dole"

na sauko.

"Ina gama hada abincin, Almajirin da yake min aiki ya buga kofar gidan, na je na bude ina faWin."

"""Kabiru sai yanzu zaka zo? Kasan kana zuwa sayo min kayan lambu?"" ""Aunty kiyi hakuri, na zo Alhaji ya ce ba kya nan."" Shiru nayi kafin na ce mishi. ""Ok shigo ba ka kudin alyahun da zaka sayo min!"" ""Tow Aunty!"" Ban san me yasa Ya Hafiz yake min haka sai dai duk lokacin da yayi min wani abu, na fushi ina jin"

haka amma bana iya maida abin.

"Kamar yadda aka saba na tura Kabiru ya tafi min aika, don bana son Yaran su dawo ban gama ba, ya ji"

"haushina. Shi kuma Kabiru ya fara shara da yan aikace-aikace da yake min. Bayan mun gama na saka mishi abincinsa sannan yayi min sallama ya fita wurin karfe daya saura, ina ganin fitarshi na rufe kofar party dina nayi wanka, na shirya cikin doguwar riga. Sannan na dan yi kwalliya sama-sama. Domin nasan ko ya gani dariya zai ta min, haka na gama shiryawa na gabatar da sallah azhar, ina addu'a ya iso na je na bude mishi, kallona yayi kafin ya wuce na ce mishi. ""Barka da zuwa, ya kasuwa?"" Bai ce amsa min ba, ya wuce abinsa ya nufi daya daga cikin sofa na parlourn ya zauna yana hararan parlourn. ""Na kawo maka abinci?"" ""Kin ga na miki kama da wanda yunwa ya koro?"" Shiru nayi ya kara daka min tsawa. ""Nace kin ga yunwa a jikina?"" ""A'a kayi hakuri!"" ""Hakurin Uban me kike ba ni ne? Akan me kike bani hakuri ne?"

"Munafuka annamimiya?"" Shiru nayi na koma gefe ban kara motsi ba, domin zuciyata wata irin tsinkewa take. ""Nawa Adamu ya baki?"" Bakina yana rawa nace mishi. ""Dubu dari.."" ""me kika ce?"" ""Dubu dari biyar!"" Na fada muryana yana rawa, murmushi yayi ya mika min wayata da take kujeran parlourn ya ce min. ""Maza ki kira Hindatu ta dawo da kudin nan ko na miki dan bura uban duka, kuma na sake ki."" Jikina yana rawa na amsa, ya ce min. ""Wallahi ko nutsu ki yi waya da ita. Kuma ki nuna kece kike bukatar kudin ba ni ba!"" Gyada kai nayi nayi na kira ta, a hankali ta dauki wayar tana faWin. ""Auta lafiya kuwa?"""

"Murmushin yake nayi idanuna yana cika da kwalla na ce mata. ""Aunty ki dawo min da kudin nan zan."""

"""Hafiz ne ko? Ki gaya mishi kudi naci ko uban waye zai kira ya kira amma ya sani ya daina ci da guminki,"

"sai an jima little girl!"""

""" Ni dai ko turo min idan ba so kike gobe ki samu gawata a gidan ba Ni dai ki tura mishi don Allah! Idan"

"har da gaske kina kaunata! "" Na fada kamar zan yi kuka, shiru tayi kafin ta kashe wayar, zubawa wayar idanu nayi kamar ina son hango ta cikin wayar. "" Lallai Hindatu tana nima na da magana. "" Ya fada yana kwafa tare da hararan inda nake, wayarshi hannunsa ya ciro. Sannan ya kira Malam Baba. "" Don Allah kada ka gayawa kowa zata dawo da kuWin."" Watsa min harara yayi kafin ya cigaba da kiran wayar har aka dauka. ""Dattijo! "" Daga can bangaren aka amsa mishi da."" Na'am!"" "" Dattijo na gaji da wannan auren, bakiWaya yan uwan Lubnah sun saka min idanu! "" Kamar zan fashe da kuka haka nake rokonshi."

"Murmushi yayi yana faWin. "" Dattijo, kamar ni har sai Adamu ya zartas da hukunci a cikin gidana ban isa na sani ba? Gaskiya na gaji zan sako musu yar uwarsu. Tunda basu fahimci irin abinda nake yi ba, ban san me yake faWa mishi ba, amma naga yadda yake gyada kai, can ya koma bashi labarin kome kafin ya daura da cewa. ""Dattijo ni me zan yi da tsiyarta dama wai na adana mata ne tunda me take nima ta rasa, amma tunda abin har ya kai haka, shi kenan ai ba yau Adamu da Hindatu suke shiga min rayuwar gidana da iyalina ba, dattijo kasan yadda nake zaune da ita, kasan halin da nake ciki da ita, ban da ni waye zai zauna da ita a haka mace babu ciki ba sai dai ci baya."" Ji nayi kamar zan mutu, yadda yake gaya min maganar kamar wanda na aikata mishi wani laifi, yana gama wayar ya mike yana faWin.. ""Na baki nan da kwana uku ki karbo kudin nan ko kuma wallahi sai kin bar gidan nan na gaya miki!"" Daga haka ya fita, na"

rasa yadda zan yi da rayuwata.

"Yana fita na dafe kaina, na rasa meke min dad'i. Wayata ce tayi ™ara na duba Aunty Inna ce, ina"

"dauka na ji kwalla ya cika min idanu. ""Auta me Hindatu take gaya min?"" Kuka ne ya kwace min na kasa bata labarin abinda ya faru. ""Kina nufin a dauki kudin a bashi?"" Kamar tana gabana na gyad'a mata kai"

"ina faWin ""eh!"" ""Bakya tunanin da matsala kudinki ne fa, wai ma tsaya waye ya gaya mishi kin samu"

"kudin?"" ""Ban sani ba wallahi iya na wurina ya amsa saura dubu bakwai!"" ""A cikin dubu darin da yake hannunki?"" Shashekar kuka na ja, ta ce min. ""Anya Hafiz ba asiri ya miki ba? Ai shi kenan zan mata"

"magana ta turo miki kuWinki sai ki bashi."" A yadda tayi magana kamar ranta ne ya b'aci, kashe wayar tayi."

"Haka na zauna a parlourn har zuwa wani lokaci kafin na mike na wuce dakina, na wanke fuskana"

"sannan na fito, na samu Yasir ya dauki remote dina yana dokawa da kasa, ""Yasir bari kada ka bata min!"" Na amsa da gudu ya fita yana ihu, ban kula ba na shiga kitchen na zubo musu abinci, ina dawowa parlourn Ya Hafiz suna shigowa da shi da Karimcy. ""Uban me ta mishi Yusrah?"" ""Rankwashinsa tayi!"" Ta fada tana me kallona, takowa gabana Uwarsu tayi ta amshi abincin ta ajiye sannan ta d'aga hannu zata mare ni ya ce mata. "" Kyale ta! Bashi taci ko ta biya ko kuma ta ji a jikinta."" Daga haka suka juya suka bar"

parlourn har da Yaran.

"Zama na cigaba da yi har lokacin sallah yayi na tashi nayi sallah, na zauna a cikin uwar dakina ban"

"fito ba, abincin da nayi shi zamu ci har dare tunda gidan ba lafiya gara na dumama da dare, ina zaune can wurin karfe biyar na yamma Husnah ta kira ni, dauka nayi muka gaisa ta ce min. "" Auta me ya hadi ki da Ya Hafiz kuma?"" "" Babu kome! "" Shiru tayi kafin ta ce min. "" Hala baki leka Whatsp ba ko?"" ""Eh bani da data ne amma zan leka yanzu!"" ""Gaskiya abin ba dad'i, sannan idan kin san akwai wani abu don Allah ki warware domin dai ba dad'i ayi ta rigima akanki kullum !"" ""Na gode in sha Allah zan yi yadda kike ce!"" Na kashe wayar, ta banki na sayi kati na saka account dina sannan na sayi data, na bude Whatsp dina, a hankali na ga sako yana ta shigowa kasancewar na jima ban bude ba, sako ne dayawa, kamar wanda aka wurgo shi ya fado min daki, kallonshi nake shima ni yake kallo, tsoro da tashin hankali suka ziyarci zuciyata da fuskana, hadiye yawun tsoro nayi, zuwa yayi ya zauna a hankali ya cigaba da kallona. Amsar wayata yayi yana faWin. ""Luluna, ki yi hakuri maganar kudin nan a barshi Hindatu ta rike kuWin kawai ai zaifi kyau ta rike miki kuWinki ko? Yanzu haka Baban Jama'are zai kira, domin Hindatu ta kira shi ta gaya mishi. Don Allah baby girl kada ki kunya ta ni, kada ki kara d'ago tashin hankali akan wanda aka yi kin ji, ki gaya mishi cewa ai mun sassanta kanmu. "" Gyada kai nayi ina kallonshi cike da tsoro, wayar ce tayi ™ara ya saka a kunne yana faWin. "" Gata nan! "" Ya mika min wayar, kamar wacce aka danne min ciwon da"

"nake ji, na amsa wayar muka gaisa da Baban Jama'are."

""" Lafiya lau Babana!"" Na fada ina kame-kamen me zance, a na shi bangaren ya ce min.."" Ummina gaya"

"min me ke faruwa ne? "" Murmushi nayi na ce mishi. "" Babana babu kome ai mun daidaita kanmu."" Murmushi yayi yana faWin. "" Ummina nasan waye Hafiz na san me yake so na san abinda baya so, na san halinsa ciki da waje. Gaya min me yake faruwa? "" "" Babu kome babana, wallahi mun daidaita kanmu;"""

""" Idan dai da wani abu ki gaya min kin ji ko? Allah ya muku albarka, Hindatu ta ce Adamu ya baki kuWi,"

"amma Hafiz ya amshe sannan wanda yake hannunta ma yana harinsu. "" Kallonshi nayi naga yadda ya wani razana, irin yadda nake tsoronshi haka yake tsoron na bude bakina,"" A'a Babana, ba magana makamancin haka, sannan ai kudin ni ce na ce ta turo min na bashi ya rike min!"" Na fada ina kallon"

"yadda yake gumi. "" A'a Hindatu ta rike miki kudinki dai, ba batun ya rike miki ta ce ta baki dari kudin"

"yana nan ko yayi amsa! "" Kafin nayi magana ya nuna min alamar na fada cewa kudin yana wurina bai"

"amsa ba, haka na faWa ajiyar zuciya ya sauke har Baban Jama'are ya gama min tambayoyi sannan ya katse kiran ko magana bai yi da shi ba, wani irin ajiyar zuciya ya sauke yana na kalle shi, fauce wayar yayi yana tsaki. ""Babu babbar munafuka irin Hindatu na tsane ta!"" Daga haka ya fita a dakin tana mita, nasan Ya Hafiz duk abinda ya saka a gaban sai ya cimma nasara akansa. Duba what'sp nayi bayan fitarsa, ashe rigima ake tsakaninsa da Aunty Hindatu, yadda yake mararaicewa yana bata hakuri tare da nuna shi na fi karfin kudin da ake magana a kai awurinsa, don Allah kada ra kara hada shi da mahaifinsa, idan don yana kula da dukiyar Baban Bauchi yasa take haka zai bar shagon yasan ba suna yin haka don ni ba ne suna yi ne domin yana rike da duk wani dukiyar baban Bauchi ne, amma in sha Allah zai janye hannunsa, Lubna dai Matarsa ce kaf duniya babu wanda ya isa ya raba mu, sannan shi dai ya so Lubnah kuma yana zaune da Lubnah yadda yake girmama lubnah kaf duniya babu wnada yake haka, sannan idan har tana ganin kaunar da yake yiwa lubnah ba don Allah bane, tayi duk abinda za tayi. Wato idan ka ga yadda yake magana cikin nutsuwa da kaskantar da kai zaka rantse da Allah, ya Hafiz na musamman ne, koda yake shi din ai dama can na musamman ne. Sai ya bawa Kowa tausayi har Yaya Umar da yake Maiduguri ya cewa Aunty Hindatu."" Don Allah ki bar maganar nan haka!"" Haka ya Amaar ya ce mata, a kashe zancen duk kannenta maza da mata sai suka shiga kare Ya Hafiz, murmushi takaici tayi ta zabga Left a group din,"

dama Aunty Hindatu akwai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login