Follow us on social media

Showing 84001 words to 87000 words out of 140751 words

Chapter 29 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

328

""Na rantse ba zan gushe ba sai na saka kowa yasan waye kai, kai ko ban ce maka Allah ya sakawa Lubabatu ba Allah sai ya saka mata, amma ba kome In sha Allah sai kayi danasani sai ka ji tsoron duniya da mutanen cikinta, sai ka ji kunyar kallon Lubabatuna, In sha Allah sai ta zame maka inuwar gajimare, shi kuma wanda ka daukaka kanta in sha Allah sai ya nuna maka iyakarka."" Daga haka Yaranta suka ja ta, amma yadda zuciyarta yake tafasa ba zata iya tafiya ba sai ta gumawa Abba takaici ta juya ta ce mishi. "" Ka ji kunya duniya da lahira, ta duniya mai gushewa ce ta lahira ita ce wacce zaka kasa kallon har Ubangijinka."" Yasan halinta amma bai taSa kawowa idan wani abu ya faru zata iya mishi tijara har haka ba, bai taba kowowa ko a mafarki haka zai faru ba, amma yau ta kunyata shi a gaban jama'a ta saka kowa yana shi da abinda ya aikata. Shi akan daidai yake kuma bai ga dalilin da zai saka ya sauka akan ra'ayinsa ba. Dayawan dattawan da suke wurin hakuri suka yi ta bashi haka ya bar shagon babu wani abin annashuwa, ranshi idan yayi dubu ya b'aci."

"Karshe shima Hafiz sulalewa yayi ya gudu, domin yadda kowa yasan me ya faru, dama an ji aurensu ya mutu amma babu wanda yasan dalilin mutuwar sai yau kuma abin mamaki sai gashi an yi yadda yayi ta azabtar da yar uban rikonsa, a take wasu suka ce su ba zasu iya ba, abokansa da suke zuga shi da daura shi akan mugun hanya basu ce kome ba, amma an samu wasu kananan magana ya fara fita ai kuwa da gaske ne abinda ya faru. Dayawa sun tabbatar da haka, sai gashi mutanen da suke kallon Hafiz da wani mutunci sun daina, wasu ma har daina mishi magana suke domin gani suke ya koma shaidanin da ya raba zaman lafiya ga uban rikonshi, da yayi mishi gata wasu ai gani suke zai aikata domin kawai a ganshi"

a wurin amma abinda yake aikatawa ya wuce tunanin me hankali.

"........... Mama kuwa a motar Ya Umar aka kaita gida bata yi kuka ba, sai da suka isa gidan Yaran suka"

"zagaye ta, ta fara kuka tana faWin. ""Ku kira Adamu ku ji halin da take ciki hankalina yana kanta!"" Lokacin"

"da suka kira Ya Ado suka gaya mishi abinda ya faru, kiri-kiri ya ado ya goyi bayan Maman sannan ya gaya musu tana gida ya koma wurin aiki amma kamar barci take. Haka Tahir ya kashe wayar ya gwada kiran"

"Lubnah da wayar Mama, a hankali ta dauka. ""Ya Tahir ina Mama? Ina lafiyarta lau?"" ""Gata nan tana ta"

"damuwa ne ne halin da kike ciki?"" Daga can ta sakar mishi murmushin karfin halin ta ce mishi. ""Alhamdulillahi, ina Maman take?"" Ta tambaye shi, mikawa Mama yayi mikewa Mama tayi tana faWin.. ""Jinjira kina lafiya dai ko?"" Murmushi tayi tana faWin da sauki kaina ne kawai ke ciwo amma da sauki kin ga gobe xan tafi na amso abincin da zan fara ci na rage kiba, sannan zan fara motsa jiki."" Sai abin ya sakata jin yadda ta shanye kome ta shiga bata labarin abinda ya faru, murmushi tayi ta ce mata. ""Mamana kada ki kara fada da Abba a kaina, ki kyale shi fushi yake da ni zai sauko wata rana, nima kewarshi nake shi yasa amma ba zan kara kiranshi ba, ki yi hakuri kin ji na ki bin umarni ki don Allah ki yafe min!"" "" Waye ya gaya miki kin yi min laifi, Allah ya miki albarka, ke da yan uwanki don ki nutsu ki yi karatu har Allah ya baki lafiya."" Karshe sai ga Mama da ta gama kukan takaici ta koma hira da Autarta ta manta da wasu yaran a wurin, bakiWaya tattara kauna da tausayin ta daura akan Lubnah, sai da suka yiwa wayar fyade ta hanyar cinye katin tass, sannan ta ajiye wayar sannan ta tuna da wasu bayin Allah, nan suka yi ta bata hakuri da kada ta kara biyewa Abbansu shi yanzu kunyar zaman kasuwa ma ya ishe,"

"haka suka bar zancen aka shiga maganar bikin Sani,"

Ranar dai Baban Bauchi a asibitin kainuwa da yake nan dutsen tanshi ya kwana saboda yadda jininsa ya

"haura, bayan ya dawo ya tara Yaransa bakiWaya ya gaya musu ya sallamawa Adamu Lubnah sannan ya cire Adamu da Lubabatu a cikin Yaranshi ya barwa Salamatu su, kamar yadda suka kashewa Lubabatu aurenta in sha Allah haka duniya zata musu alawadai da abin kunyar da Lubabatu zata kawo musu. Duk parlourn suka yi shiru Sani da yasan idan yayi shiru yayi munafunci ya ce mishi. ""Abba ba ayiwa Ubangiji kutse zanen ™addara da yasa alkalamin ya rubuta, ko kai aka hada da Hafiz sai ka yi kara amma lokaci ne kawai zai bayyana haka, Allah ya kyauta."" Shi ya fara fita daga parlourn domin idan ya cigaba da zama"

maganar da zai fita bakin shi ba kyau kuma mahaifa ne ba ayi musu magana ta rashin Wa'a.

"Bayan fitar sani yace duk wanda ya kara kula Mama da su Lubnah bai yafe ba, Yadiko da take waje tace"

"mishi. ""Wannan dai ita ce ake kira karya domin ba zaka raba su da uwarsu da yan uwansa, kai kar ku sake ku dauki wannan maganar, hakkinku ku kula da Uwarku da Yar kanwarku, kune gatanta."" Yadda Yadiko ta nuna musu nasu kada su dauki maganar shi ya kara kwantar musu da hankali, yayi ta fada"

"karshe a daren sai da ya koma asibiti, take Hafiz ya kira Jama'are ya gaya musu cewa ai ga abin da ya faru, sai ga yan Jama'are mota guda, a nan kowa ya nuna Mama bata kyauta ba, jinin halin da Abba yake ciki da kuma ganin yadda yake kwance bai da lafiya, Hafiz ne kanshi ko asibitin yasa aka yi ta zagin Yaranshi da nuna Hafiz ya zama gatanshi tunda gashi ya haife su amma Uwarsu tafi shi moransu, tunda gashi"

"kowa ya juya mishi har Yaran Yadiko, suna tsaka da maganar Yadiko ta iso wayyo ai Mama ita nata"

"karamar yaki ne, Yadiko da ta ji abinda suke fada da ta fara bala'i da cira kamar zata tashi sama............."

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 34"

'

"Shi yasa Allah ya tsinewa mai tadda fitina, domin kuwa rigima sosai aka yi kamar za a daku, wai duk akan"

"Hafiz da Lubnah. Ai kuwa lamarin har Jama'are, abinda ya dawo kunnen Mama aka yi ta cewa suna son kashe Baban Bauchi ne saboda dukiyarsa, domin su ci gado musamman Mama da yake ita ce Uwar Yara dayawa, wato ita fitina idan tana barci mafi alkhairi a barta ta cigaba da barcinta kada a tashe ta, amma wannan karon sun tashi lukutar masifa, domin Mama har Jama'are ta cimma Goggo Uwani da Talatuwa da suka haddasa rikicin, ta ce sai sun shiga kotu domin wanke mata suna, da suka ce tana son kashe musu dan uwa. Nan fa hankalin kowa ya tashi rigima ake yi tun karfe bakwai na safe har karfe biyar na yamma sallah yake tashin su dakyar da suWin goshi Mama ta hakura bayan manya daya daga Fada sun shiga lamarin, ta kuma ce a shata mata layi a tsakaninsu, idan wani magana ya fito ba zata yarda ba sai gaban kuliya manta sabo. Jin wannan abinda take shirin yi yasa kowa ya shiga hankalinsa aka fita"

harkanta da Yaranta.

***

"A cikin kwanaki biyu ko waje bana lekawa, zai yau da Aunty Nuratu ta zo da kanta. Sai na ji kunya ya"

"kama ni, a hankali na sauko muka shiga mata hidima. Sai da ta Wan sha ruwa sannan take kallona. ""Ina ta jiranki ina lafiya?"" Murmushi nayi duk da rashin sabo a tsakaninmu, amma yadda take damuwa da lamarina yasa zuciyata sakewa da ita nace mata. ""Ciwon kai da habbo ya hanani fita!"" ""Kina yawan tunani ko?"" Kallon Aunty Zakiyah da ta kawo mata snacks nayi domin ta amsa mata da cewa. ""Ai kullum muna magana akan tunanin nan."" Kallona tayi can ta ce min. ""Duk abinda zai faru ba zai tab'a kai na baya ba, you need to move on. Kin tab'a tsammanin zaki samu freedom haka?"" Murmushi tayi tana kallon yadda na rike hannuna da juna. ""Ba laifinki ba ne, ™addara ce ta zo miki a haka. Sannan idan da kowani mutum yana da iko da ™addaransa da dayawa basu yarda ajn haife su a low background ba, amma da yake mu musulmai ne masu bin tafarkin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama."" Muka karasa salatin tare ta daura da cewa."" Me kike tsoro wanda da baki gani ba? Me kike gudu wanda da bai same ki ba, me yasa ba zaki yi accepting din kanki ba? Tsoro yana da kyau amma rashin karban kai shine asalin tsoron da ake gudu, dayawa masu kashe kansu a duniya tsoron karban kansu suke, accepted yourself, love yourself, and move on, idan kika yi haka zai matu™ar wahala wani ya rusa ki, ko yan uwanki zasu kara jin dadin you accepted yourself, zasu iya miki yaki ne idan sun ga kin karbi kanki a yadda kike, a duniya ma zata girmamaki ne idan kin amshi kanki, ko waye zai girmama ki ne idan yaga kin amshi kanki a yadda kike, duniya da mutanen cikinta basu damu da ka mutu ko ka rayu ba, damuwarsu shine taya zaka gaza a maka dariya, amma daga lokacin da kika nunawa Duniya zaki iya survive idan da mutanen cikinta, ko babu ita da mutanen cikinta zaki iya tafiya da kanki, daga lokacin duniya zata dawo bayanki, zata koma tana yayyataki ai ke jaruma ce, a kowani raunin dan adam zaka samu na kusa da shi sun bada gudummawar maganin warka da raunin, amma idan raunin ya gaza warkewa kowa zai watsa a kan rauni, ki kaunaci kanki, duniya sai ta kaunace ki. Ki koyo saka kanki farin ciki duniya sai ta taya ki farin ciki. Ki kashe tsoron da yake ranki sai ki tayi cikin sallama, idan har kika rayu da farin ciki babu wnada ya isa kallonki ya gaya miki magana, shi mutumin da yayi gwagwarmayar domin ya rayu don lafiyarsa zai matu™ar wahala bai samu soyayyar gaskiya ba, kina bukatar ki girma da kanki ba tare da wani ya ce shi"

ya saka ki girma ba.

"Open your heart and make a wish, kina son ki rayu ki ga idan Allah bai raya ki ba, ko da zaki yi addu'a"

"matukar baki yarda da kanki ba, matukar baki saka yakinin ba tow babu inda zaki domin Allah yana amsar Addu'ar wanda ya yarda da shi ya kuma saka yakinin zai taimaka mishi, idan kika ga matan da suke gym din nan, akwai wacce mijinta har sayar da ita yayi ta tafi karuwanci, akwai wacce Mijinta watsa mata ruwan battery yayi bai samu fuskantar ba ya zube a bayanta. Akwai wacce kullum dukarta yake"

"saboda ta haifa mishi yarinya handicap, baki godewa Allah ba da ya miki ni'imar da sauran basu samu ba? Idan da zan bude miki file din kowacce, sai kin ji kamar taki matsalar ba kome ba ne, mu anan ™abilarmu babban abin tashin hankali namiji ya sake ki, za a nuna miki iyakarki, ina son ki zama mace ta farko Bahaushiya daga arewacin Najeriya da ta san kanta ta kuma yarda da kanta. Idan har kin yarda da kanki,"

"Auntynki Nuratu Kafaya tana kiranki, idan kuma kika sake tsoron nan ya mamamye ki. "" Murmushi tayi ta mike tana me daukar jakarta tare da yiwa Aunty Zakiyah magana. "" Madam zan tafi! "" Fitowa Aunty Zakiyah tayi muka rakata. Cikin wata motar alfarma ta shiga, ta d'aga min hannu, haka naji kamar anya xan iya zama mutum kamar yadda ta ce? Jiki a ma ce na shigo cikin gidan. Ina kallon kasa. ""Ya kamata ki kara gaba, sannan ba zaki bikin Sani ba, ke da Bauchi yanzu sai wani Ikon Allah. Ba zaki ko ina ba, ki zauna ki gina kanki na jima da sakawa a raina ba zaki Bauchi ba, ita dai wacce aka koran nan sai ta zama wacce ake kwadayin ganinta, idan Mama kike son gani Allah ba zai hana mu kudin kawo ta nan ta kwana biyu ba, zamu tafi Bauchi ni da Yayanki, ke da Yara zaku zauna anan, a matsayina na wacce makarancin likitanci, idan muka je Bauchi aikin da muka sha wahalar yi dare daya Hafiz da Abba zasu rusa mana, babu inda zaki kin ji aiki domin ba zamu yi gini wani ya rusa mana ba. "" Ji nayi kamar an kara yanta ni, murmushi yayi ban ce mata kome ba muka shigo cikin parlourn na tayata kwashe kayan da ta kawowa Bakuwa muka kai kitchen. Nan na wuce dakina na kwanta sai lokacin sallah ka tashi nayi, a cikin addu'ar"

da nake har da Allah ya bani ikon yarda da kaina.

"Sai dai kuma ina gama addu'a naji wasi-wasi a raina, haka na lumshe lekowa har na wani lokaci. Kafin"

"na bude ina kiran sunan Allah. Wasi-wasi ya saka ni a gaba, washi gari na shirya na tafi makaranta, karfe biyu na taso, sai na tsaya a gym din, yan wurin na ganina. "" Lulu!"" Fuskarsu cike da fara'a suna ta min barka da zuwa. "" Tunda kika zo baki kara zuwa da fatan dai lafiya domin dukkanmu nan mun zama daya."" Gyada kai nayi ina faWin. "" Ban ji dadi ba ne?"" Ai kuwa a rud'e suka yi ta tambayata meke damuna, na ce ciwon kai nan suka yi ta min sannu sannan na shiga wurin Aunty Nuratu Kafaya, na samu tana tattaunawa da wata mata sai kuka matar take. Itama dai katuwa ce. "" Ku yi hakuri ba ri na jira a waje! "" "" A'a gashi ki tafi daya office din ki bawa Wasim zai miki bayani."" Gyada kai nayi ina faWin. "" Na gode sosai!"

""""

"Na fito na tsaya a bakin kofar ina raba idanuna, yarinyar ta Nasiba na gani zata fita ta ce min. "" Aunty"

"kina son abu ne? "" Gyada kai nayi mata ina mika mata.."" office din Uncle Wasim zaki! Muje na kai ki."" Ina bayanta ta kai ni har office dinsa, da sallama muka shiga, shima yana bako, yadda yake magana a nutse zaka fahimci shi din Coach ne da yake ganin mutane daban-daban. ""Kanwata shigo!"" Ya fada yana murmushi, kafin ya kalli mutumin ya ce mishi. "" Yawwa kamar yadda na gaya maka, zaka iya kawo ta mu"

"fara ganin yadda zamu gina lafiyar jikinta. "" Mika mishi hannu Mutumin yayi sannan shima ya mika mishi"

ya mike matsawa nayi mutumin ya fita ya zauna yana nuna min wuri na zauna. Mika mishi takardan

"Nasiba tayi tana faWin.. ""Uncle ni fita zan yi, naji wai an sake sakamakon Allah yasa ina cikin wadanda zasu diba."" ""Allahummah Amin Daughter Allah ya bada sa'a."" Ya fada yana mata murmushi fita tayi, ya kalle ni. ""Shekara biyu kenan tana niman aikin masu kula da fasinjoji na jirginsa, bata tab'a sarewa ba. Bana ma haka har azumi take da sadaka Allah ya bata sa'a. Kin ga kuwa dole mu taya ta da addu'a Allah ya bata sa'a ko?"" Ya fada yana kallon takardan hannun.. ""Da kibar aka haife ki?"" Girgiza kai. ""Bana son body language, speak!"" ""Tow!"" ""Kin tab'a haihuwa ne?"" ""A'a;"" kallona yayi da kyau, kafin ya ce min.. ""kin taSa birth control ne?"" Anan na sunkuyar da kai ina matse hannuna, bude drower yayi ya ciro wani irin ball ya mingiro min, ""idan kika shiga irin wannan yanayin us it, kina matsawa yana rage damuwa. Me yasa kika sha birth control?"" ""Tsohon Mijina ya bani."" ""Amma yana sonki!"" Matsa ball din nayi murmushi yayi sannan ya ce min.. ""duk mutumin da yake sonka baya naka abin hana daukar ciki am sorry!!"" Shiru yayi ya cigaba da cewa. ""Zaki ragu amma sai kin saka a ranki zaki ragu, kina da saurayi ne?"" Da sauri na kalle shi. ""Oops babu ko?"" Ya tambaye ni yana murmushi. ""Tow daga yau ki saka a ranki, kina son ki burge saurayinki ne, kin san waye saurayin?"" Girgiza kai nayi, murmushi yayi ya ce min. ""Kanki, kanki zaki burge ki ji a ranki soyayyar da zaki yiwa jikinki don kanki zaki yi ba don wani ba. Kin san me? Dole ki fada soyayya da kanki haka zai baki damar kula da kanki, sannan ki yi hakuri da kowa ki yi hakuri da kome kada ki sake wani ya ba'ta miki rai, ki ji a ranki kina da kanki da ya tsaya miki all I want to you love"

"yourself, ki yarda da kanki ni kuma zan yi ™o™arin baki step by step na kula da kai."

"Wannan sune tsarin abincin da zaki fara ci kullum da wanda ya haramta miki,. Idan kina da soyayya da"

"bread da fanta irin naku na Fulani ayi hakuri daga yau an daina shan duk wani abu me zaki, kin ga kibar nan naki idan da za a bincika ba za a rasa uric acid da Diabetes ba, sannan akwai tarin kitse da dole a narka da shi, sai kuma rage cikin abinci mai yawa, idan za a ci a sha ruwa sosai, sai a hada akwai bayani"

"akan nan duba ki gani."""

Ga wasu hanyoyi da za su taimaka miki wajen rage kiba da kuma wasu shawarwari a kan abincin da ya

kamata ki ci:

Hanyoyin Rage Kiba da Inganta Lafiya

1. Kula da Abincin da Kike Ci

"* Rage Abinci Mai Sukari da Mai: Ki rage cin abinci mai zaki (kamar su alewa, lemo na kwalba, da waina"

mai sukari) da kuma abinci mai yawan mai (kamar soyayyen abu).

"* Yawaita Cin 'Ya'yan Itace da Ganyaye: Su na Wauke da sinadarai (fiber) da ruwa da suke sa™i da ciki,"

kuma suna da ™arancin Kalori (calories).

"* Cin Abinci Mai Wadataccen 'Protein': Irin su kifi, ™wai, nono marar mai (yogurt), da wake/gyaWa."

Protein yana taimakawa wajen rage yunwa kuma yana ™arfafa tsoka.

"* Rage Cin Abinci Mai 'Starch' (Carbohydrates): Abinci irin su shinkafa, taliya, burodi, da fura. Idan za ki"

"ci su, ki ci da 'ya'yan itace ko ganye."

2. Yin Motsa Jiki (Exercise)

* Yin Tafiya: Ki fara da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login