Follow us on social media

Showing 9001 words to 12000 words out of 140751 words

Chapter 4 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

292

dauko shi, ""kenan ba sai an saka muku abincin ba zaku dawo ?"" ""Eh!"" Ya ce ya fita, kafin bakwai da rabi, na hada abincin Yusrah na kai mata, na tashe ta na mata wanka, sannan na shiryata tana ihu, sai ga Hajiya ta fito. "" Wai me kike mata ne? "" "" Wanka na mata Hajiya zan shiryata ne! "" "" Wanka ko mugunta? Ke fa muguwa ce ba mamaki ruwan da zafi kika yi ta kona mara mutunci, ke baki haihu ba amma salon muguntarki yafi karfinki wallahi ki ji tsoron Allah! "" Kwalla ne ya cika min idanu, na gama shiryata na kawo mata abin karyawanta, tana sha tana kukan rashin mutunci. "" Ni tea din ya min zafi, yana kona min baki kaka yana kona min baki! "" "" Ai dama nasan muguwa zata kashe ki ne! "" Hajiya ta fada tana daukar tea din ta kurba, sai zare idanun tayi tana faWin. "" Takwara ai ba wani zafi, yadda yayi sanyin nan ma kulle miki ciki zai yi! "" Kamar nayi kuka haka na bata doya ta furza min a fuska. "" Ni kin cika yaji! "" Wani irin bakin ciki naji ya cika min rai, na ce mata.. ""ayya Yusra me yasa kike min haka ne? Ki ci don Allah!"" Kamar nayi kuka nayi maganar, sai tura baki tayi tana faWin. ""Ba zanci ba."" ""Ai ba dole ba ne sai ta ci a barta haka don Allah!"" Haka na hakura na barta, na kuma wuce na barsu na kawowa su Hajiya nasu don"

ta fara min ihun ita yunwa take ji taliyar jiya bai rike ta ba.

"Haka na kawo abin karyawan, tana ci tana faWin. ""Kin iya girki amma salon mugunta irin naki sai kin"

"azabtar da mutane!"" Kaina a sunkuye na barta na riko hannun Yusra na kai ta makaranta, har lokacin ban ga Karima ba, sai da na kaita makarantar na juyo zan dawo gida, na hango su Ya Hafiz, na zata zasu tsaya su dauke ni ne, a'a sai suka yi tafiyarsu. Haka ba karasa gidan a gajiya na shiga na hada mishi abin karyawa yana zaune a parlourna, sai da yayi wanka ya dawo ya zauna yana karyawa hajiyarsa ta shigo ita da Tijjani da Yasir da har lokacin bai yi wanka ba. ""Lulu waye zai yiwa Yasir wanka ne ?"" Ya Hafiz ya tambaye ni, ""ni ce!"" Na fada ina daukar yaron da ya fara tsalla ihu, haka yayi ta ihu har kaina ta fara wani irin juyawa, gashi ya cika kashi a pamper dinsa, haka na wanke na mishi wanka na fito na shirya shi, garin shirya Yaron nan na kara fama tuntube na, wani irin kuka ne ya so kwace min, haka na daure na kai shi waje na koma daki na shiga ban daki na fashe da kuka, don sai yanzu na lura da farcen kafana ya fashe, baka hawaye yake zuba min ina jin kamar na mutu da bakin ciki, haka na gasa kafar na fito nayi wanka,"

na shirya cikin material.

"Bayan na saka kwalli da man baki na fito, na samu sauran abin karyawan nawa da yake kitchen"

"Hajiya da Karima sun dauka sun cinye, kitchen din na koma na dafa indomie da kwai, na zauna a kitchen din naci, sannan na fito na samu suna ta magana. Shi kuma yana zaune yana jin su, can aka buga gidan na zata Almajirin da yake min aiki ne, na koma daki tare da dauko Hijab na saka sannan na fita na bude gidan, wasu magidanta ne guda biyu, suka shigo gidan. ""Alhaji Hafiz yana nan?"" ""Eh yana cikin bari na mishi magana,!"" Na fada tare da nufar cikin gidan, ""tow mun gode"" haka suka jira na koma parlourn na ce mishi. ""Ya Hafiz kana da baki a waje"" ""sun iso kenan?"" Ya fada yana yatsina fuska. ""Yaya kasan likita"

"ya ce kada ka saka damuwa a ranka domin zuciyarka tana dab da bugawa!"""

Lumshe idanunshi yayi ya bude a kaina yana min alama da idanu wato naji dai. Sunkuyar da kai nayi

"ya fita, shi da Tijjani, Hajiya ta zauna tana ta zuba kwadayi tana bawa Karima labarin yadda ta sha wahala akan Ya Hafiz ni dai na wuce kitchen na wanke kayan da nayi amfani da shi, sai gashi ya shigo kitchen din, ""Ina takardun gidan nan?"" ""Yana dakina!"" ""Ko zaki bani aron gidan na sayar idan na biya bashin da ake bina zan!"" Rufe mishi bakinsa nayi da hannuna, ya sumbaci hannun yana cire bakinshi a hannun ya tako har jikin dogon deeper freeze na, ya haWa ni da jikin freeze din ya shiga sumbatar goshina da manyan kumataina. Abu daya nake bukata a gare shi, shine soyayya amma na rasa ni dai a bangarena bai rasa soyayyar da nake mishi ba, haka ya gigita ni, daidai shigowar Karima kitchen din ta kawo kayan da suka ci abinci da shi, ganin halin da muke ciki yasa ta jan tsaki tayi waje, sake ni yayi ya ce min. ""Maza dauko"

"min na manta mun bar mutane a waje!"" Haka na wuce dakin na dauko takardun bakiWaya, na mika mishi kamar wacce aka katse min tunanina da lissafina haka ya amsa ya fita, ban kara ganinsa ba, sai karfe daya da ya dauko Yusra, suka shigo na zuba mata abinci tana ci sai ga Hajiya ta shigo dama tuwo nayi miyar shuwaka, na kawo mata abincinta, ta fara ci tana mita. ""Kin san yadda na tsani shuwaka shine kika yi miyar fisabiilillahi gudawa zanyi!"" ""Ki yi hakuri Hajiya ban sani ba ne!"" Na fada ina bata hakuri, na kara"

"kallonshi na ce mishi. ""Yaya Mama bata ji dadi ba, ina son na je na gaishe ta!"""

"""Daga nan ki gaya musu ya sayar miki da gidanki ko?"" Inji Hajiya, girgiza kai nayi na ce mata. ""Haba"

"Hajiya wannan fa duk bata taso ba."" Hayayyako min tayi kamar zata rufe ni da duka, ""Hajiya ai ta gaya"

"miki Mama bata da lafiya ne, ki kyale ta an jima ta je. Luluna ki shirya ki tafi kin ji idan na gama zan zo"

"daukarki!"" ""Shi kenan na gode!"""

*08130269641*

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALA˜AR ZUCI*"

Ramlat Abdulrahman Manga

Mai_Dambu

HUŠU

"Wani irin dad'i ne ya lullube ni, na gyad'a mishi. Ina me da hawayen da suka fara cika min idanu,"

"murmushi yayi ya ce min. ""Tashi ki je ki fara mata abinda zaki kai mata!"" Mikewa nayi ina ta godiya. Domin ya min abinda ban zata ba, haka na wuce dakina, na sauya kayan na fito ina zuwa na samu basu"

"nan shi da Hajiyarsu, kitchen na wuce."

Hafiz

"""Hajiya me yasa baki da hakuri ne? Kina irin wannan ba sai ta fara jin wani abu a ranta ba? Hajiya gaskiya"

"ki daina min haka, kin ga yadda Allah ya taimaka asirina ya rufu akan wannan lamarin."""

""" Amma Hafiz kasan dole dai mu kula domin tunda yan uwanta suka fara zargin wani abu dole mu kara"

"mikewa. "" Murmushi yayi ya ce mata. "" Hajiya ni ba kamar ki ba, a wurin Lubnah bana bu™atar boka ko"

"Malam, idan na tsaya ga kaina ina alfahari da haka, don Allah kada ki saka mata magana a bakinta."""

"Shiru Hajiya tayi tana faWin. "" Tow shi kenan amma ka kula domin kuwa Malamin nan ya ce a cigaba"

"da kulawa."" "" Na gaya miki ni ban yi wani aiki da abinda ya fada ba, ni kaina Aljanu ma tsorona suke."" Daga haka ya bar gidan, duk sai Hajiya ta shiga damuwa, ta dauki wayarta ta kira Malaminta, ta gaya"

"masa abin da yake faruwa. Shiru tayi kafin can ta ce mishi. "" Toh bari na turo maka da kuWin!"""

*

"Ina ta aiki gyara kayan miya sai gaKabiru almajirina, mikewa nayi ina faWin. ""Ka iso? Ko zaka fara da shara"

"sai kazo ka sayo min kaza."" Durkusawa yayi yana faWin. "" Ina kwana Aunty? Eh na iso shi kenan!"" "" Shi"

"kenan kayi sharar ina jiranka!"" Na cigaba da aikina ya shiga share filin gidan bakiWaya, ni kuma na cigaba"

"da aikina. "" Kai Uban waye ya baka izinin shigowa?"" Dariya Karimah tayi tana faWin. "" Hajiya ai almajirinta ne. "" "" Eh samun wuri!"" Yana cikin sharar sai ga Ya Hafiz tare da Tijjani, suka shigo ganin Hajiya a filin gidan suka tsaya. "" Hajiya lafiya? "" "" Ina lafiya ashe gidanka har yayi arahar da kowani kare da doki zasu shigo? "" Kallon Kabiru yayi ya hade rai. "" Idan bai shigo ya taya ta da aiki ba me kike so nayi? Ita wannan me ta iya? Kin ga Hajiya ban kira ki, ki zo ku rusa min gida kamar yadda kika rusa gidan Nuru ba, ba"

"ruwanki na gaya miki!"" Shiru tayi tana da wani sunkuyar da kai."

"Ina gama hada abinda nake ya shigo. "" Luluna sannu ko zaki zo ina son magana da ke?"" "" Tow ""na fada"

"wanke hannuna, a bakin kofar parlourn na ji muryan Kabiru na fito na same shi mika mishi atm dina nayi na ce mishi. "" Kaji guda uku, zaka sayo sai kifi kilo biyu da rabi ka ga bani da lokaci ka dawo da sauri don Allah!"" "" Tow Aunty!"" Ya saka kai ya fita, na bi bayan Ya Hafiz zuwa dakina. Ina shiga na same shi a tube, yasan ina da aiki me ya kawo irin wannan lamarin yanzu? Kamar nayi kuka na ce mishi..""Ya Hafiz ko!"" ""Hakkina nake so!"" Yadda yayi min magana take ya koma Ya Hafiz din da na sani, kwabe kayan nayi na haura gadon, .kamar yadda na sani ko minti goma ba ayi ba ya fara nishi daga nan ya sauka ya saka kayansa ya fita, ni kuma na wuce ban daki nayi wanka na sauya kaya, ina fitowa na sami Hajiya da Karima a parlourn, sai wani irin kallo suke bina da shi. ""Akuya tana haihuwa domin ana kwasar Yaranta zuwa kasuwa, ke kuma sai dai ki tsotse min Yaro, bakya gaba ba kya ba."" Shiru nayi na wuce kitchen na wanke shinkafa na zuba karasa da pea da green beans da karas ,na daura akan wuta na juye ruwan zafi a kai. Na daidaita wutar ina jin kamar na hadiye zuciyata. Ina cikin aikin Kabiru ya yi sallama na fito na amshi kayan na wuce ciki suna parlourn suna cigaba da zagina. Abin karyawar da na hada mishi na kawo mishi, sannan na ce mishi..""ko xaka dawo an jima ban gama ba rana ba!"" ""Ba kome Aunty na gode!"" Yayi sallama ya tafi ni kuma na cigaba da aikina wurin karfe biyu saura na zuba abincin yan gidan, sannan na shiga wanka na sauya shigata cikin wata lace peach colour na fito ina gyara daurin dan kwallina, kitchen din na shiga turus nayi cike da mamaki. Hajiya ce ta bude kular abincin da miyar da xan kaiwa Mama, ban ce mata cikanki ba na ce wuce inda na daura farfesun kifin na sauko a hankali, na dauko wata kula na juye shi a hankali, kamar wacce kwai ya fashewa haka ta saka kai ta fita. Bayan fitar ta na d'ago tare da isa wurin kular na kara gyarawa sannan na dauko sauran da na rage na karyawa na kara sannan na gama kome na saka a basket na fito, daidai isowar Kabiru na koma kitchen na dauko mishi nashi sai godiya yake ta min, bayan na sallame shi na dawo na shiga dakina, na tattara duk wani abina me daraja na boye shi, domin nasan ba a abin mamaki ba ne gobe na gani a jikin Aunty Nana ko Haulatu, haka yasa na rufe dakin da kome nawa, sannan na saka key Win a jakata na fito na bar gidan, don shi kan Ya Hafiz"

tun dazu ya sake fita da wasu mutane.

*Dutsen tashi*

"Daidai gidan Marigayi Malam Idris anan gidanmu yake, kafin ka isa gidan Malam Idris, anan aka sauke ni"

"da basket guda uku, kafin na samu napep a unguwarmu sai da na fito bakin titin tambari housing estate,"

"na sha zama don ma Maman Ummi da zata fita ta rage min hanya zuwa bakin hanyar unguwarmu, na"

"tsaya kafin na samu abin hawa, haka muka iso gidan."

"Yaran unguwarmu yan matasan suka taso da sauri suna faWin. ""Lubnah barka da zuwa!"" Murmushi"

"nayi suka dauki kayan ina amsa musu. ""Yawwa Amir kai ia girma haka? Lallai girman dan mutum, Jamal ka ne haka ka zama kato!"" ""Kai Aunty Lubnah ba wani katon da na zama, ga Waheed naj baki ga girmanshi ba sai ni! "" Suka fada murmushi nayi muka isa kofar gidanmu me dauke da shagunan provision. "" Lubancy ke ce daga sama haka? "" Murmushi nayi na ce. "" Eh Malam Anas ni ce! "" Na wuce Yaran suna bina da kayan har cikin gidan, yadda muryata ya karad'e cikin gidan sai da kowa ya fito har da Aunty Innah dama tazo ne? Wani murmushi suka min na karasa har da Aunty Munah. "" Aunty Munah yaushe a"

"gari?"" "" Korata kike kenan? Ke dai mugun halinki na kin mutane yana nan har yau baki sauya ba."""

"Murmushi nayi na koma inda Yadiko take alola na durkusa har kasa na gaishe ta. ""Da fatan da"

"izininshi kika fito? "" Gyada kai nayi ina kallon kasa. "" Tow sai ki gama ki koma da wuri don unguwarki da nisa!"" "" Haba Yadiko daga zuwa kamar mai Waukar wuta sai a fara mata maganar ta gama ta koma! "" Inji Aunty Munah, daga can dakin aka ce mata. "" Ai baki ga kome ba, sannan yadiko ta mata da kauna tsaya ki ga yadda Mama zata mata. "" Inji Ya Sani da yake dakin yana cin abinci. Ya fito dauke da plat din abinci, "" dube ta kamar Bakuwa"" ya fada yana mita. "" Aunty xamu tafi sai mun kara shigowa. "" "" Ku tsaya mana! "" Na fada ina buWe jakata na dauko dubu daya na mika musu. "" Ban san zan ganku ba, ban saya muku tsara ba;"" "" a'a yayi yawa mun gode ko Waheed! "" ""Maza karba kafin na saka ki wanke gidan! "" Inji Ya Sani, karba suka yi tare da fita da gudu suna godiya. "" Mama tana ciki? "" "" Eh! "" A hankali na ja kafa na nufi parlournta zuciyata tana wani irin tsalle. A hankali na shiga parlourn tana addu'a, ga Aunty Hindatu da take ta fama da laptop dinta. ""Yar renin hankali tun yaushe na gaya miki bata da lafiya!"" Zama nayi a gefenta, tare da daura kaina a kafadarta. ""Am soweer."" Na fada ina wasa da yatsuna. Shafa addu'ar muka yi abinda ya fito a bakin Mama yafi kome dukana.. ""Me ya kawo ki? Da izinin waye kika tawo?"

"Bayan ko yau sai da Mijinki ya gaya mana baya gari idan ya dawo zaku zo tare."" Wani irin abu ne ya tsaya min a rai, yaushe Ya Hafiz yayi tafiya, amma sai na yi shiru ban ce mata kome ba. Ta kara da cewa. ""Ya gaya mana Tijani zai kawo Hajiya Asiya an jima Asibiti kuma ya kamata ace kina gidan."" Yadda Mama take shiga ba nan take fita ba, sai naji zuciyata tana wani irin ciwo kamar kaikayi. Ni dai kamar yadda aka saba kaina a sunkuye, wayar Mama ne yayi kara ta dauka tana faWin. ""Na'am Alhaji gata nan tazo!"" Ta mika min wayar. Yadda ya balbale ni da fada yasa nayi shiru kamar yana gabana ya cigaba da cewa. ""Kin san Abokiyar zamanki bata gari, sannan ta bar miki Yarinyarta taya zaki kai yarinyar makota? Ke wacce irin mahaukaciya ce? Don Allah bai baki haihuwa ba sai ki na wulakanta mishi Yarshi? Wai ma da izinin waye kike fito? Ga Hajiya Asiya can da Tijjani sun je gidan ba kowa, ke a rayuwarki idan baki saka mu magana ba, bakya jin dadi ne?"" baba yana yin nashi a waya, ta yadda yake shiga ba nan yake fita ba, haka Mama tana yin tana kamar ta rufe ni da duka. Nasan cewa duk lokacin da zan zo matu™ar ba shi zai kawo ni ba, tow na rantse da Allah kamar yar riko haka nake komawa amma idan ya kawo ni kowa yayi"

ta ririta ni. Aunty Hindatu na ta kasa jure fadar Mama ta ce mata.

""" Mama dai, ya kamata ku fahimci Lulu ba zata fito don kanta ba, sannan taya zata fito a ce! "" ""Gafara"

"can, an gaya miki bamu san yadda kike hure mata kunne ba ne? Ko an ce miki bamu san yaddA kika mata"

"wayo kina rabata da kuWinta, me yaron nan ya rage ta da shi? Ko an gaya miki ban san me nake yi ba ne?"

"Wallahi Hindatu idan baki daina shiga rayuwar Lubnah da gidan aurenta ba na rantse da Allah sai na miki Allah ya isa, kuma ki zauna yanzu su Hajiya Asiya zasu tawo ku koma gida Wallahi, ina zaman lafiya da Mijina ba zaku kashe min aure ba ke da Yan uwanki! "" Cikin fushi Aunty Hindatu ta shiga hada kayanta Ya Sani daga waje da Aunty Munah, suka shiga kananun magana, yadda Ya Sani yake mita yasa Yadiko ta dirko musu kamar zata rufe shi da duka, har tana faWin. ""Idan wani ya kara shiga rayuwar auren Lubabatu sai na mishi Allah ya isa, tunda burinku shine ku kashe mana aure, idan da kuna da hankali"

"tausarta zaku yi ba ku tsaya kai da fata bata yin kuskure, tun kafin ta iso muka san cewa gaban kanta tayi, haba me yasa Lubabatu take haka ne? Yaron nan yana girmama ki amma ke kin dage sai kin zubar da"

"mutuncinki."""

Kiri-kiri suka hade kai suka min tas Aunty Munah da haushi ya mata itama barin musu gidan tayi ta nufi

"gidan Ya Umar da yake makama jahun, Ya Sani ma haka ya bar gidan babu shiri, ni daya kamar mayya haka suka yi ta fada bayan sun gama, kuma suka sauko tare da min nasiha, har Yadiko ta shigo da abincin da na kawo suka ci da Mama, ni dai kaina yana kasa har lokacin ban d'ago kai ba, sannan ban ce musu cikanku ba. Kai mai karatu wannan sai ya zame maka sabo amma a wurina ba sabon abu bane, da na san haka zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login