Follow us on social media

Showing 138001 words to 140751 words out of 140751 words

Chapter 47 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

308

Mama!"" ""Ke nan ce min zama wata yar 18yrs ba sai ni yar renin wayo!"" Wata yar budurwa Yarta na gani tana mai gaishe ni, ta hado kan kannenta. ""Ruma beautiful familynki kenan?"" Murmushi tayi tana faWin. "" Kema ai naki suna hanya in sha Allah, ki ,zuba idanun suna nan tafe fa wallahi uku uku zaki ya dirke mata duk bayan shekara daya."" Murmushi nayi amma nasan ni ai narasa wanan damar har abada. Haka muka sha hira kafin ta wuce. Sai bayan tafiyarta na nutsu sosai. Ina son Yara, ina son Yara amma ni bani da rabon Yaran domin na gama da mahaifana. Taya xan samu haihuwa ko nayi aure? Ina ga Madadin na sakawa kaina damuwar auren gara na hakura na rike aikina, domin babu namiji da zai aure ne ba tare da ya karu da ni ba. Tab'a ni Aunty Innah tayi na kalle ta. ""Na ga tun kawarki ta tafi kike tunani, shi fa aure da haihuwa na Allah ne idan kika yi hakuri Allah zai baki wanda baki zata ba. Ki kasance mai yarda da ™addara da kuma hakuri da juriya, wallahi ba kowa Allah yake jarabta ba, sai mai imani a jarabce ka ma Allah yana sonka ne ga mutane dayawa suna saSon Allah kuma suna raye me yafi wannan muni, ki saka a ranki kome ya baki rabonki ne idan bai yi niyya ba Alhamdulillahi ba akanki aka fara haka ba. Ki godewa Allah kina muslma mai imani da ™addara."

"Alhamdulillahi da Allah ya raba ki da wancan Tsinannen da ko Abba bai bari ba, ke Alhamdulillahi kin auna arziki domin da kina nan tare da shi da kin mutu ba wanda ya san yadda kike cin azaba gashi daga rabuwarku har yau bai kara ajiye mace ba, itama Yarinyar da auro a Gyembu a kotu suka rabu, hmmm yanxu haka a Jama'aren an hana shi aure, domin kuwa cewa suke tunda ya iya rabuwa da ke babu Macen da zai samu ya rike tsakani da Allah. "" Abin sai ya zo min bazata wato idan baka da hakkin mutum sai Allah ya fito da kome sarari, a yadda nake jin labarin kamar a mafarki wai Ya Hafiz ne yake ikirarin sai"

samu wacce zata zauna da shi hm.......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 60"

"A lokacin da ya sake ni yadda yayi ta alfahari da zai samu mata na ribibinsa, sai na ji jikina ya mutu murus."

"Haka na cigaba da. Kallon amma bani da karsashi har zuwa lokacin da aka tashi karfe daya na rana muka dawo gida amma naji suna cewa zasu wuce kofar fada a can za ayi kallon na gaske. Tunda nayi sallah duhar nake kwance ina jin hayaniyar mutane. Ban kawo baki gidan aka yi ba, domin ina can uwar dakan Yadiko s gadonta. A hankali barci ya fara fisgata sai dai tashina Hashiya tayi na bude idanuna kanta. ""Mene ne?"" ""Wai kin yi baki ne fa."" ""Ni kuma?"" Na tambayi kaina, na juyar da kai na lumshe idanuna barci ya kara gaba da ni. ""Ke tashi baki kika yi daga Gombe?"" Ban san lokacin da dirko daga gadon ba. Na zare idanu kafin na fito da sauri, riko ni Yadiko tayi tana faWin. ""Ina dan kwallinki?"" Da sauri na koma dakin na hada da Hijab dinta da nayi sallah na fito. A parlourn Abba na ji ana ta hira sama-sama, daga yadda gidan ya dauki kamshin turarensa na san cewa wannan mutumin ya zo gidan mu, parlourn Mama na shiga na samu Aunty Kubra Yar Umma Uwani. ""Auta a ina kika samo mana bature? Ya Salam wani hanin ga Allah baiwa ce."" Banza nayi mata na wuce dakin Mama da take sallah, zama nayi ina kallonta idanuna cike da kwalla, taka idarwa tayi ta kwararo addu'a har da hawayenta. Kafin muka shafa da ita na ce mata. ""Dama kin san da zuwansa ne?"" ""Koransa zan yi ne?"" ""Mama zai ga kamar muna mishi ya wani abu ne?"" ""Kuma haka ko? Matsa can ja'ira. Ko ance ban san kuna turowa juna sakon Barka da shan ruwa"

"da kuma Barka da sahur ba?"" Ban kara mamaki ba sai da na ga ashe kayan da muka kawo mata na"

"wurinsa ne a jikin matar nan, rike bakina nayi ina kallon abin mamaki anyi mata Winkin riga da zani, ita da"

"yadiko kayan suka saka, fitowa tayi tana faWin cewa."" Kubra gaskiya Abdulkarim dan albarka ne jiya aka kai kayan nan da darren amma ki ga yadda ya dinka yau kaya sun min cib ni da Yadiko."

"Sake baki nayi wato gidan nan an iya zaga ka ayi abu daga baya ka sani,ji nayi kamar nai kuka. Ina"

"tsaye Yadiko ta shigo da wasu roses irin na da can sai wasu dangaran aka shiga zuba cin-cin da na kiya, tangaran kuma aka zuba cake da donut, ke dai Mama da Yadiko sun ci amanata, asalin cin amanata matan nan dun yi shi, sai na rasa bakin magana Hashiya suka kira tayi ta kwashe abincin ta kaiwa parlourn Abba, ni kuma Mama ta ce min. ""Zaki tashi ki gyara jikinki, ke tafi ka kiyi sabon wanka wannan tsamin ranar da kike yi Allah kaWai yasan hakurin da muke yi da wannan lamarin tsamin."" Kallon kaina nake ina mamakin yadda Mama suka ci amanata, ban gama wartsakewa ba Yadiko ta ce min. ""Auta tsayuwar me kike don Allah je ki yi wanka!"" ""Ni wani wanka xan kara?"" Na fada ina tura baki. ""Ai gara ki nuna musu ke kyakyawar kazama ce."" Inji Mama sake baki nayi anya Mama bata ci amanata ba akan Sir Turaki, tura baki nayi ina fadin. ""Mama cin hancin da ya baku ne zaku mai da ni bare?"" Wani d'ago kai tayi ta kalle ni sau daya sannan ta cigaba da aikinsa, make kaina Yadiko tayi tana faWin. ""Wuce maza kafin na kwala miki murfin nan a katon kanki!"" Daga haka na wuce simi-simi, wankar da ban yi niyya ba, shi suka saka ni nayi bayan na fito na samu Mama bude akwatinta wata riga da zani dinkin born style aka yi mishi, ta ciro min ta ajiye da mayafinsa babba me kyau sai turare wanda Yaranta suke saya mata ta ajiye min, da wani takalmi me kyau ga tsada ta ce min. ""Ibrahim ya turo min daga kasar waje ga jakarshi nan, Munah taso na bawa Innah domin ta hannunta ya fado, ni kuwa nace ba zan bada ba, ita Yadikonku ta bawa matar Sani nata. Na ce autata zan bawa."" Ta fada tana ajiye min, ta cigaba da zaro min kaya daga akwatin tana faWa min wanda suka bata, amma ni ta barwa tasa ayi ta dinka min koda nayi aure dangin miji ba zasu ce suturarsu nake sakawa ba. Murmushi nayi nace mata. ""Na gode sosai Mama!"" Na rungume ta ina jin kuka. ""Ke kada ki bata fuskarki!"" Ta ce min tana murmushi, haka na fito bayan wani lokaci Hashiya ta ce min. ""Aunty ki shiga Abba ya koma parlourn Yadiko!"" Tunda ta fadi haka na kai"

"kusan minti goma a wurin sai da Mama ta fito na tashi a hankali, na fito waje ina jin gabana yana faduwa. A hankali na tura labulen parlourn na shiga da sallama, idanunsa yana kaina. HaWa idanu muka yi na sunkuyar da kai, ina me shiga parlourn da sallama, na samu wuri na zauna a kasar kafet. ""Barkanku da sallah?"" Muryan mutum biyu na ji sun amsa, shi bai amsa ba. D'ago kai nayi zan kara tambayarsu ya hanya na ga idanunsa a lumshe. Sunkuyar da kai nayi kasa. ""Ya Hanya da fatan anyi sallah lafiya!"" ""Alhamdulillahi!"" ""Lubnah ashe a Lagos yanzu kike aiki?"" Ba zan manta da muryan Malam Hamza ba, cikin murmushin yake na ce mishi. ""Eh Malam!"" ""Jamil ka ji ikon Allah, kuma a kamfanin Malam Bilal"

"take aiki ba"" tabbas yanzu na tuna da asalin shine malam Bilal? A raina na fadi haka daidai bude idanunsa wanda yayi kicibis da d'ago kaina, muka zubawa juna idanun. Wani abu nake ji s cikin idanunsa, wanda har jikina yana amsawa, nayi kasa da kaina ina wasa da yatsuna, shi kuma ya cigaba sauke sirrintaccen ajiyar zuciya a hankali a hankali. Yarinyar nan ta shammace shi fiye da yadda yake"

"tsammanin, ya zata yana da wayo ne amma shi bai san cewa ita din kallonsa take ganga ba rufi ba,"

Two hours ago.

"Lokacin da ya iso Bauchi awa biyu da suka wuce, yana hanyar Gombe har ya kusan shiga alkaleri ya kira"

"Number Malam Hamza duk da sun jima basu gaisa ba, amma akwai wani abu da yayi da har yanzu alakarsu take nan, shine bayan ya bar Bauchi sai da ya bawa Malam Hamza aiki a daya daya cikin kamfaninsu na kano, yanzu haka a can kano yake aiki. Shi kuma Malam Jamil dama karatu zai koma ya mishi hanya ya koma yanzu haka yana koyarwa a jami'ar jahar Bauchi na gadau. Kuma sanadin da suka tsaya da kafarsu, yana kiran Malam Hamza da yake suma basu manta da halaccin da yayi musu ba, yana fada mishi gashi nan a Bauchi shima ya kira Malam Jamil ya gaya mishi, take suka shiga musun inda zai saka, nan suka. Kara kiransa suka gaya mishi rigimarsu, dariya yayi musu ya ce su jira shi zasu tafi gaisuwa ne gidansu Iyayen Lubnah. Mamaki yasa Malam Hamza ce mishi. ""Kana nufin kun dawo da soyayyarku ce?"" Jim yayi kafin ya ce mishi, ""sai na zo dai!"" Ya fada musu, lokacin da ya iso gidan Malam Hamza suka wuce wnada yake Fadamar mada, suka ci abinci sama sama ya tab'a domin tun ranar da Mama ta kira shi tare da mishi godiya,ta ce mishi yaushe zai zo Bauchi? Ya ce mata washi garin sallah zai zo, don haka ya dauko hanya ba ruwansa, a can ma hawan sallah da ayi amma ya gudo. A yanayin da yake tafiyar da rayuwarshi bai san cewa zuciyarshi take janyo shi ga Lubnah ba, duk yadda yake son nisanta kanshi daga gare ta domin bai san matsayinta ba, matar aure ce ko bazawara ce. Shi dai ya san yana son ya zo amma ba zai ce ba don ita ya zo ba, sai dai yadda yake jin a ransa saboda Mama ya zo, amma ko tukin da yake yi so gani yake ba gudu yake ba. Haka ya iso ana ta hawan sallah suka wuce Fadamar mada, bayan sun nutsu ne Malam Hamza ya ce mishi. ""Kun dawo soyayya da ita ne?"" ""A'a muna tare dai a lagos tana aiki a KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY."" "" Wannan shine ake kira almara"" Malam Hamza ya fada yana kallon shi. ""Ita tasan kai ne?"" Girgiza kai yayi yana faWin."" Duk yadda naso ta tuna bata tuna ni ba!"" Jinjina kai yayi yana faWin."" Akwai daure kai, amma kasan bata da aure!"" Wani irin zabura yayi, cikin kallon mamaki Malam Hamza ya ce mishi. ""Baka san bata da aure ba dama? Duk ganinta da kake ka zata tana da aure kai ka ce ina taimaka maka da labarin zaman da take duk tura maka da nake baka duba ba? Har labarin mutuwar aurenta da jinyar da tayi da barinta Bauchi na tura maka ta email dinka!"" Dafe goshinsa yayi yana faWin.. ""Innalillahi wainnalihir rajoun Innalillahi wainnalihir rajoun, innalillahi wainnalihir rajoun. Da na ga baka samu lokacin min reply ba na turawa Alhaji ELYakub da yake tab'a tambayata maganar ka da Lubnah na tabbatar masa da gaske ne domin a lokacin gani suke kamar gamo ka yi ba da gaske ba ce."" Mai da kanshi yayi ya kwantar da shi a saman kujeran yana jin wani irin sara mishi da yake yi. ""Wannan karon dole ka tsayawa kanka, fight for yourself, domin ina jin cewa kamar zata koma hannun dan iskan gaye nan."" Bude idanun yayi akan Malam Jamil ya ce mishi."" Yaushe ka ji zata koma?"" ""Tun kwanciyar babansu a Lagos, Matata Yayarta kawar Yayar Lubnah ce, take cewa Mamansu ta ce da ta koma gara ga gawarta."" Ware idanunsa yayi akan Malam Jamil, kafin ya ce mishi. ""Ku tashi muje!"" Rike hannunsa Malam Hamza yayi ya ce mishi. ""Ina son ka bi kome a hankali, in sha Allah sai inda karfinmu ya kare ba zamu kara barinka, ka rasa ta ba a karo na biyu."" Zama yayi yana sauke ajiyar zuciya, idanunsa sai wani kyalli suke. Malam Jamil yake bashi labarin wahalar da ta sha ji yayi kamar ya bude idanunsa ya ga Hafiz no wonder ya mishi wannan dukar ranar sashe kishi da takaici suka kwashe shi yayi daidai kenan, yana zaune har wurin daya da wani abu suka fita zuwa masallacin suka yi sallah sannan suka dawo suka zauna daga nan ya bawa Yaran Malam Hamza barka da sallah na dubu hamsin, haka suka wuce dutsen tanshi, wurin karfe biyu da wani abu sakamakon unguwa ya cika dakyar"

"suka gano gidan, sai da ya kira Mama ya gaya mata gashi nan a kofar gidan ta tura Hashiya ta shigo da su,"

"lokacin da suka shiga parlourn Abba ta kai su, ta gaya mishi ga Shugaban Lubnah daga Lagos ya zo musu"

barka da sallah.

"Koda suka shiga Alhaji yayi dattako domin yayi ta mishi tambayar da kure hankali, yadda yake bashi"

"amsa tare da fadar waye shi, yasa bakiWaya ya nutsu. ""Yanzu me ya kawo ka Bauchi?"" ""Nazo zumunci da kuma gaisawa da abokan arziki da aka zauna."" Shiru Abba yayi kafin ya ce mishi. ""Kamar shekarun baya ka zo nan kai da wadannan abokan naka ko idan ban manta ba?"" ""An yi haka Alhaji shekaru goma da wani abu;"" gyada kai yayi yana kallonsu, duk da ba shi bane ya bada amma amma kuma sai ya ga yadda suka zo wancan lokacin da kuruciya yau dashi sun zo da shekarunsu. ""Masha Allah;"" nan suka yi ta hira"

amma shi bai ce kome ba har aka fara shigo da abincin Abba ya bar musu parlourn.

Present

"Mikewa nayi xan bar parlourn ya ce min. ""Me yasa kika boye min baki da aure?"" Tambayar ya zo min a"

"wani irin bazata, ""ka sani ko tana da wani dalili?"" ""Which dalili zata boye min bata da aure?"" Zubawa kofar parlourn idanun nayi kafin ns cigaba da tafiya. ""Baki gaya min dalili ba?"" ""Ka tambayi Alhajinku yafi ni sanin dalilin haka!"" Ta kowa yayi bayana kafin ya zagayo gabana yana mai zuba hannunsa dukka biyu. ""Na zata idan wani zai boye min kome ba zaki aikata haka ba? Me kika dauke ni?"" ""Malam Bilal ka yi bincike! Kada ka yanke hukuncin da sauri haka."" ""Jamil"" sai kuma yayi murmushi ya juya ya fita, wani irin abu na ji ya tsaya min a raina, ba zan iya barinsa ya tafi haka na, lokacin da na biyo bayanshi na samu Hafiz a harabar gidan, suna kallon kallo tsakaninsa da Bilal. ""Sir ka tsaya mu yi magana."" ""Me yasa zan"

"tsaya mu yi magana!"""

""" Ka saurare ni Please!"""

"""Ashe da gaske abinda ake fada min yana faruwa da gaske ne, kwartonki kik..."" Ganin Hafiz nayi a can"

"kasa kamar zai tashi amma saboda yadda ya sha bugu. ""Kaci zarafina zan dauka, ba yau na sha jin"

"kazaman kalamai daga bakin mutane ba, amma ita din kaunata idan bana nan xaka yi yadda kake so amma ina tare da ita ni kamar inuwa nake mata ka kiyayye kalaman ko na rufe ka har abada."""

"Tashi yayi yana faWin. ""Idan har ina raye aure sai dai ki ga ana yi Lubnah ki dawo rayuwata idan ba haka"

"ba wallahi sai dai kowa ya rasa."""

"""Na rasa gane kai wani irin jahili ne, amma a yau zan gaya maka abinda ka sani ba. Har abada ba zan"

"tab'a komawa rayuwarka ba. "" Kallon CEO nayi a hankali na kai hannuna tare da rike rigarshi. "" Tun daga lokacin da na hadu da shi yake bawa rayuwata kariya ka koyi yadda ake mutunta mutum. "" Na fada tare da sake rigar na juya cikin gida hawaye na zuba min. ""Lubnah!!!!"" Dukkansu biyu kira sunana a lokaci"

guda. Alhamdulillahi anan na gama book 1 waye zata amsawa

(In sha Allah ranar Monday zan cigaba abubuwa dayawa na tara a gabana don Allah ku bani hutun idan

na fara in sha Allah sai na gama zan tsaya amma yanzu ina son na hutawa nima bana jin dadi ga Yarana ma haka basu da lafiya amma zuwa ranar Monday in sha Allah zan dawo da karfina da abubuwa dayawa

da ba zaku manta da shi ba Team Lulunhafiz da Team Lunanturaki)

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login