Follow us on social media

Showing 120001 words to 123000 words out of 140751 words

Chapter 41 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

303

muka shiga ya samu wuri ya zauna aka fara dogon turanci nan, aka fara gabatar da kai, nima na kalle shi ya dauke kai, sannan na gabatar da kaina. Sannan na fadi abinda ya kawo. Bayan na gama na zauna. Cikin abinda bai wuce minti talatin ba, aka fara gabatar da abinda ya kawo an sayar da kayan shi akan kuWi me yawan gaske wasu yaci riba wasu ya fadi sosai, kuma dama kasuwa ta gaji haka, amma ribar tafi asarar yawa, yana gamawa. Muka fito , wani dan kasar China ne ya ce mishi. ""Mr Turaki ko zaka zo mu ci abincin rana ne?"" Sai lokacin na tuna fa na zo da abinci, ""Mr Ma na gode."" ""Haba ko ita ba zata ci ba!"" Kallona yayi ya ga yadda nake kauda kai. ""Itama!"" ""A'a Mr Turaki barta muje ta ci!"" Haka muka wuce aka kai mu wani wurin cikin abinci irin VIP nan! Wurin ya hadu kamar me iya haduwa zama nayi, aka kawo abincin hatta yadda abincin yake tururi sai da ya sa naji cikina yana wani irin ™ara irin ina jin yunwa. Kallonshi nayi na kai hannuna cikin, bai wani damu da ya kalle ni, abincin ya fara ci ina kallon abincin, ""Dig!"" Ya ce min, haka nayi ta juya abincin ina hadiye yawu, tashi yayi tare da barin wurin, da sauri na fara cin abincin, ina"

"ci ina kallon ta inda ya bi kada ya dawo ya samu ina ci, na kai loma kenan na hango, haka na ajiye cokalin. Na bar abinci me shegen dad'i. Da yazo ya ga yadda na ci ba sosai ba, haka ya ce min. ""Zan tafi fa!"" Mikewa nayi kamar na juye abincina, sau biyu yana kamani ina kallon abincin har ga Allah ban koshi ba,"

"haka yayi gaba abinsa, sai da muka shiga mota sai ga masu aikin wurin sun kawo min leda me dauke da"

"Chinese dish, kallonshi nayi naga shi ba ma tani yake ba, a hankali na risina ina faWin. ""Na gode!"" Daga"

"nan bai tsaya da ni ko ina ba sai Lekki. A kofar wani hadadden gida ya tsaya, fitowa yayi yana mai nufar cikin gidan nima na bishi, muna shiga Yaran nan suka lullube shi da murna, suna ganina suka fara ihu."

"Haka na shiga na same su, ya fita ya shigo da ledojin nan, daga nan ya juya yayi tafiyarshi."

"Cikin gidan muka shiga ina tambayar su. ""Ina Mamanku?"" ""Ta tafi Kumo Family Mansion"" abinci na"

"juye mana muka ci ina kallon yadda suke ta wasa da abincin, na ce a raina Yaran attajirai fa haka suke basu damu da abinci ba kamar irinmu yan medieun class, kazar guda ce muka ci rabi me aikin ta dauki sauran ta saka a frij, muka cigaba da hira har bayan la'asar da malaminsu ya zo, sai lokacin Mamar ta shigo tare da shi, tana kuka idanunta yayi jajjur ganin yadda bakiWayansu suke kallona yaushe nazo. ""Ke me ya kawo ki?"" Kafin na bashi amsa ya shigo yana waya , da hannu ya min alama da na fito mu tafi."

"Haka na fita muka wuce gida, kular abincin da nazo da shi na dauka sai nayi wayam, babu kome a ciki, s hankali na ajiye ina satar kallonshi, wani hade rai yayi irin baya son wasa, lokacin da muka isa gidan na fita tare da Waukar kular na rufe mishi kofar, na shiga cikin gidan. Ina shiga cikin gidan na zube a parlourn ina nishi, na gaji sosai. Duk da ban yi wani aiki ba amma kuma zama wuri Waya ya dame ni. Da wuri na"

"kwanta bayan mun sha waya da Mama, kai na ji dadi."

"Wato wani irin rigima ake a family house Winsu, akan Jasminah sun matsa lallai sai ta koma dakinta , ko"

"kuma ta bawa Fahad Yaransa. Ita kuma ta ce sai dai ta mutu da ta bashi Yaranta, akan idanunta ma aka yiwa yarta fyade. Wannan abin ya tab'a Turaki, don haka ya ce a shigar da maganar kotu domin ta bata damar rike Yaranta, uwarta kuwa ta ce idan ta haifeta kuwa ta kai Fahad kotu, sai ta mata baki shine, abinda ya d'aga mata hankali, wani irin kuka take wanda yake damun dan uwanta. Yana ajiye Lubnah ya wuce gidan Noma family, ana cewa gashi nan ya zo a lissafinsu ya zo basu hakuri su kyale ta, sai dai lissafinsu bai zo yadda ya dace ba, domin yana shiga gidan da shi da Barista Abdul Hakim, wanda ya samu yana jiranshi a kofar gidan a tare suka shiga cikin nan, yan gidan na ganinsa suka fara dariya, zama yayi ya ce. ""ina son ganin Alhaji Noma."" Fitowa Dattijon yayi yana wani buWewa kamar kifi ya samu wurin zuba kwai, yana kallon Turaki gabanshi ya fadi amma kuma sai ya dake har ya shigo cikin parlourn ya zauna. ""Na ji ka kafa dokar ko Yaran Jasminah ko dakin Mijinta."" Tashi turaki yayi yana kallon parlourn bakiWaya ya ce mishi. ""Ni kuwa sai naga kamar wannan gidan da duk abinda Noma yake da shi, aro Alhaji"

Haris Kumo ya bashi domin akwai sa hannun a wurin nan......

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 52"

"Ya mikawa Barista abdulhakim hannu, sai ga takardu. Da aka saka abu kusan shekaru ya kalli Baristan ya"

"ce mishi. ""Amma kasan takardun nan sun yi kura? Dai dai kuma kome tar kamar yanzu aka saka hannun!"" Ya fada tare da kardakade takardan, yana mai daura takardan a kan table, ya kuma d'ago kai ya kalli Alhaji Noma. ""Na baka awa ashirin da hudu ina bukatar kudin nan, ko kuma kilu ta ja bau, idan"" daga haka ya mike zai fita Alhaji Noma ya ce mishi. ""Me kake bukata?"" Shafa sajensa yayi yana kallon kanshi a madubi. ""Duk wata matsalar da yake kunno kai a kashe ta ta hanyar da aka bi, ko kuma ni na"

"kashe ta, ta irin wannan hanyar?!"" Ya fada yana d'aga kafad'arshi. Yadda ya juya yana faWin. "" Ina da"

"thousands of this copys"" sannan ya juya ya kalli mutumin da akalla zai yi sa'ar Babansa ya saka yatsu biyu"

"ya saka a saman idanunsa alamar ina kallonka, daga nan ya wuce yana mai barin gidan shi da Barista abdulhakim, "" Amma baka niman zaman lafiya, yanzu kana ganin haka zai yi aiki?"" ""Sosai kai, zuba idanu"

"ka ga ikon Allah."" Daga haka suka rabu."

"Kamar yadda ya shiga tsakaninsu, haka lamarin ya mutu kamar daukewar wuta. Ai idan kana da kudi"

"babu abinda ba zai yiwu ba, sai ikon Allah. Da wannan Jasminah ta samu zaman lafiya, Fahad ya kirata ya ce ya janye ta rike Yaranta idan yaran suka samu lokaci su zo hutu, ta amince aka kashe maganar"

"bakiWaya kamar bai tab'a faruwa na, dama ai zancen kenan."

***

"Kallon Ya Ado da yake waya da Ya Umar yake tambayarshi. ""Na shiga maganar ne domin na kara nisanta"

"ta da shi, sannan yadda suka yi juya hankalin Abba yasa na shiga lamarin amma idanun kamfanin yana kanshi a duk inda yake saboda sun ce suna da case nasu a kasa tow sai CEO din ya kama shi yana ™o™arin cutar da ita ba wani abu ba ne, shi a nashi lissafin ya razanata ne ta amince da shi, amma akwai wani abu"

"da na fahimtar da nayi mishi, kamar akwai sanayya da juna!"""

"Kallon Ya Ado nayi da kyau kafin na kara mai da hankalina, kafin ya gama wayar anan na fahimci wato"

"da wancan Masifaffen rufe shi yayi, da yadda aka fito da shi, sai na ji kamar ni aka ceto daga farmakin Ya Hafiz. Tunda na ji haka sai na ji mutumin ya Wan yi abin arziki, kuma sai ban damu da na ji wani abu daga gare shi ba, washi gari ya kama Monday, sai da na jira Ya Ado ya sauke ni,da wuri na isa na fara aikin da na ga an jibga min, sai da na harari kofar ya kai sau goma, ina tura baki gaba. Tun karfe takwas nake abu daya har wurin karfe goma da ya shigo, na tashi na bi shi na karanto mishi menu na yau bakiWaya. ""Yau bana son ganin kowa!"" ""Ok sir!"" Na fito na cigaba da aikina wurin karfe sha biyu saura wasu mata shigo da sauri na fito na gaishe tare da cewa. ""Yau ya ce ba zai gana da kowa ba, yana da aik. "" Saukar wani"

"gigitaccen mari na ji a gefen fuskana, wanda yayi daidai da fitowarshi zai fita. Ban san wacece ita ba amma yadda ta mare ni, ya saka ni jin wani abu. ""Me tayi miki?"" Ya tambaye ta, ""Ubanta ne ya gina kamfanin da zata dakatar da ni!"" ""Ba Ubanta ba ne, amma Ubana da Uwata suka tsayar da kamfanin haka,. Kin yi dacen na fito da sai ta rama domin na gaya duk shegen da ya taSa ta ta rama!"" "" Ni ce shegiya?"" Gefenta ya bi ya wuce, ta kama ihu da fada akan ya kashe mata auren yarta, ni dama tunda na ganta nasan ba arziki ya kawo ta ba, don haka ban wani damu ba. Ganin yadda Jasminah ta zo tana kallonta cikin fushi da b'acin rai. "" Na rantse da Allah, idan baki rabu da shi ba sai nayi ruined rayuwarshi."" Duk yadda ta kai da dakewa, sai da ta ce mata."" Ba zaki iya ba, tun yana Yaro kike kokarin haka me yasa baki yi nasara ba, rayuwarki xa kika cika shi da karya da yaudarawa babu abinda kika sani. Anya ke uwa ce? Shi bai tare miki kome ba, ko ba kome zan ji kamar Abba yana raye!"" Rike ta nayi ina girgiza mata kai, ina faWin. "" Kada ki. Aikata haka, Uwa ce ba a wasa da lamarinsu. "" Kwace hannuna tayi"

"tana faWin."" Kyale ni na gayawa wannan matar Abinda take aikatawa, da fari ta ci Amanar Mss Annah"

"A'ishah kasancewarta sakatarinyarta, tsiyar ka dauko mutum daga poor background ka ja shi jikinka"

"kenan, wannan masifar da bakin ciki na talauci da haushin masu arziki... "" Tass aka dauke ta da mari, wanda ya nuna mata yatsa, tsabar ya bani tsoro haka na koma gefe na na tsaya ina zare idanu. ""Ki girmama ta, koma me take miki."" ""But she hate me! Bata kaunar farin cikina, idan na kara haduwa da ita sai na kashe ta, wallahi i will kill you;"" daga haka ta bar wurin ni dai sai na zama yar kallo. ""Duk yadda ka shiga rayuwar wani kai ma sai an shiga naka, bar ganin Allah ya baka aron numfashi ka zata ya kyale ka ne, ni bana bukatar fansa iyayena. Amma ki sani akwai wani Yaro a garin Kano mai suna Khalid yana nan zuwa."" Daga haka ya wuce ya barta a tsaye a matu™ar razane, domin bata kawo Jasminah zata yi magana ba, har zai shiga cikin office dinsa ya ce mata. ""Daga yau kada ki kara shigo min office har ki Mari sakatariyata!"" Sannan ya shiga cikin, sai da suka bar office din ya kira ni ta wayar landline, na amsa tare da shiga office din, d'ago kai yayi na wani lokaci kafin ya ce min.. ""Mijinki yana dukarki ne?"" Maganar tazo min a bazata sai nace mishi. ""Me ye?"" Wani haWe rai yayi yana min wani kallon bana son renin wayo. Tura baki nayi ina dauke kai. ""Ni kin iya min rashin kunya amma su da suke marinki, baki iya ramawa ba!, daga yau duk wanda ya kara miki kallon banza ki rama idan kika kara sakewa wani ya mari wannan"

"fuskar naki sai na kore ki! Kin ji ko?"" "" Hmm!"" Nace ina tura bakina gaba. Bai kara min takaina ba ya nuna min hanyar waje, bakin da yayi aka kira ni daga kasa aka gaya min. Na je na tarbe su, sannan na dawo na kai su dakin Meeting na koma zan shiga elevator, ina shiga Khamis yana shiga, wani irin tsoro ne ya cika min rai, na koma gefe na tsaya.""ki bani abinda kike bawa Oganki mana."" Ni dai ban tanka mishi ba, addu'a kawai nake yi domin wallahi na gama razana, jin yana takowa, na rintsa idanuna da karfi. Jin kofar ta bude nayi saurin xan fita ya dawo da ni, wanda haka yayi daidai da isowarshi bakin kofar. Lashe baki Khamis yayi ina kokarin kwace kaina. ""Sake ta!"" Amma yaki, kafin ya kara wata magana na gantsara mishi cizo, da sauri ya sake ni yana faWin. ""Na gode da cizon kauna!"" Ya fada yana kallonshi, ban san me zai aikata ba, haka yasa ya nufi kofar a fusace shi kuwa Khamis ya rufe kofar da sauri yayi kasa. Da gudu yayi stair na ce mishi. ""Ba fa shi bane me muhimmanci, kana da baki masu muhimmanci. Idan ka cigaba da biye mishi kullum sai ya yi abinda zai bakanta maka rai, zuwa yanzu na fahimci duniyar da kowa yake, tunda na fito daga duniyar da ba kowa yake fahimtata ba, don Allah ka kyale shi ka fuskanci abinda yake gabanka, ni ba abinda nayi kawai kwatar kaina nayi! "" Kallona ya shiga yi yana son yayi magana na ce mishi."" Irinsu haka suke idan aka cigaba da kula su kamar an basu damar yin abinda a so ne, don Allah kayi hakuri ban san dalilinka na jin ba dad'i ba, amma duk da haka nasan don kare mutuncina ne."" Daga haka yayi gaba na bi bayansa har inda aka yi taron, ban san mene ne shirinsa ba, amma tunda aka gama"

"taron y sallame ni, na bar office din."

"Daga nan Gym na wuce nayi motsa jiki na na gayawa Aunty Nuratu Kafaya halin da nake ciki. ""Ki yi"

"hakuri na tsawon wata uku idan baki ga canji ba sai a bar aikin a nime wani ko!"" Anan na karasa wuni lokacin tashi na wuce gida, washi gari da wuri na isa office din, sai dai ban samu shiga ba. Saboda wani tsarin da wannan Masifaffen yake ta kawowa, a yanzu ko kazo sai an baka wani kati idan zaka shiga ka"

"nuna, ban san an raba ba da yake da wuri na tafi."

"Ina wurin a zaune wata bwn karama ta shigo harabar kamfanin, wani kyakkyawan matashi irin"

"larabawan nan, amma yadda ya fito da fara'arshi, yana gaida kowa yasa na fahimci irin ruwa biyu nan ne, ina zaune ya zo ya zauna a gefena. ""Hey Yan mata?!"" Ya d'aga min hannu, kallonshi nayi na ce mishi ""barka!"" Mika min hannu yayi yana faWin ""Tarik Mustapha Takai, babana yana cikin masu hannun jarin Meeting din aka yi jiya, ina shigowa na ga kin yi min! Nice to meet you?!"" Ya mika min hannu yana murmushi, kallon hannun nayi kafin na bude baki zan yi magana sai ga motar Masifaffen nan ya shigo, mikewa nayi na tsaya. Shima ya mike yana murmushi. Da dan saurinsa ya isa wurin motar Yana fitowa suka rungume juna, irin sun san juna nan. ""Uncle B!"" Ya kira sunansa a hankali, daidai na isa wurin na amshi jakarshi shi kuma ya amshi nawa, yana faWin. ""Uncle B taya zaka bawa Miss World jaka kawo na rike miki."" Ya kwace min jaka, wani kallon da Masifaffen mutumin nan yake min ya kashe min jiki, haka yasa na ki bashi jakar na amsa har da nashi, koda muka je ya mika min katin na shiga, shima haka. Tunda muka shiga Tarik Mustapha Takai yake wasu abubuwan sai dai ba halin magana, ni kuwa yadda ya like"

"min, sai na ga kamar Masifaffen nan yana wani haWe rai."

"Bayan na gama mishi duk abinda zan yi, na sako kasa na amshi ruwa ashe Tarik ya biyo ni, ai kuwa"

"muka je har wurin abinci da shi, a yadda na tambaye shi shekarunsa ashirin da biyar ne, murmushi nayi nace mishi. ""Kai kani na ne, na baka shekaru huWu don haka ka girmama ni!"" Daga ni har shi haka muka yi ta zolayar juna, madadin mu bi elevator, sai ya ce mu bi Stair, haka muka ta bi har muka isa office din, wato bawan Allah nan da ya ce mishi. ""Shiga cikin office ina zuwa."" Yana shiga ya rufe ni da fada kamar zai dake ni, nayi shiru ban kara cewa uffan ba, don tunda na ce yayi hakuri ya kara hawa yasa na yi kasa"

"da kaina. Bayan ya gama ya shiga, tsabar haushi lokacin tashi bai yi ba na tashi abina, na bar office din."

"Wasa gaske sai shakuwa ta shiga tsakanina da Tarik, irin mugun shakuwar nan Yaro ne da bai san kome"

"ba sai wauta da shirme, idan ya zo office kuwa ba damuwa ba ne ya fita ya kashe min kudi, ina zaune da karfe daya na rana aka kira ni a waya da yake ranar asabar ne, na dauka ina faWin. ""Waye?"" ""Baki yi saving number na ba?"" ""Sorry na manta ne, Tarik ya kake? Lulu yau ina jin wani irin gajiya ne kuma ina kewarki!"" Murmushi nayi na ce mishi."" Ayya ai zuwa gobe jibi mun koma aiki!"" "" Ni dai ki gaya min gidanki na zo!"" "" Kallon Ya Ado da yake aikinsa na ce mishi. ""Ok!"" Na mishi kwatance, na mike da sauri na nufi kitchen na fara hada abincin da Aunty Zakiyah ta gama na diba mishi na hada fruit salad, sannan na duba samosa na fara soya mishi, sannan na hada abinda xan hada can sai ga kiranshi. Da sauri na dauki wayar na saka a kunne. ""Gani nan!"" ""Ok gani nan fitowa da Yara!"" Haka na fita leke can na ganshi da wata mota ni sai yau na fara ganinta. Horn yayi min na sake murmushi, na d'aga mishi hannu. Yana zuwa yayi parking tare da fitowa da wasu jakukunan, murmushi yayi min ya ce min. ""Sorry na tsaya sayan abu ne, ban karaso ba."" Girgiza mishi kai nayi muka shiga har cikin gidan, ya ajiye kayan yana gaida Ya Ado. ""Tarik Mustapha Takai."" Murmushi Ya ado ya mishi ya ce mishi. ""SAN Adamu Usman Jama'are."" Ya mika"

mishi hannu.

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: 53"

"Cike da mamaki nake kallon yadda yake son sabawa da kowa, ba tare da b'ata lokaci ba Ya ado ya mika"

"mishi hannu suka zauna ana ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login