Follow us on social media

Showing 57001 words to 60000 words out of 140751 words

Chapter 20 - Alaƙar Zuci Complete Hausa Novel by Mai Dambu

29 May 2026

323

ganin yadda halinsa yayi mugun tashin nan bayan an rufe shin nan, ta tambaye shi akan me yasa ya damu da Lubnah bai boye mata ba, ya gaya mata gaskiya abinda ya faru, da kuma dalilin da yasa yake son ganin ya kara dawo da Lubnah, taji tsoro ta kuma kadu, sannan ta saka duk wani abinda take da shi a kasuwa domin a bine kome, sai dai a yanzu kan an binne kome, kome kuma ya rufu kamar yadda suke fata yanzu Lubnah ita ce harinsu, shi yasa yake ta bibiyar Baban Bauchi ya gaya mishi inda take koda a wajen kasar nan ne sai ya nimo ta, Lubnah tashi ce shi Waya daga shi kuwa babu wanda ya isa zama da ita koda kuwa zai mutu ne Lubnah bata isa tarayya da wani da namiji ba."

Wannan shine alkawarinsa.

"Yau karfe daya na dare ya shigo gidansa, da wata Yarinya a gefensa, yar lukuta da ita ya bude mata kofar"

"dakin Lubnah wanda yake nan har da kayan ba a dauka ba, karshe ma dakinsa ya mayar da shi. Yana ganin yarinyar ta shiga, ya wuce dakin Karimcy tana barci, daga gani barcin ta wahala ce domin daga ita har Yaran babu wnada yaci wani abu a cikinsa. Tashinta yayi ta bude idanun tana kallonshi. Ta gaji sosai"

"domin zuciyarta ba zata iya daukar ukubar da ya fara gana mata ba ta ce mishi.. ""Ka dawo ka bani hakuri"

"ne?"" Murmushi yayi ya ce mata. ""Ko daya nazo ne na gaya miki gaskiya ko ki fita ki fara girki kamar"

"sauran matan ko kuma bakin ciki da yunwa ma sun ishe ki"" shiru tayi sannan ta ce mishi. ""Ba zan yi ko daya ba, kai ne ma zan kafa maka sharadi. Idan kana son kanka da arziki ka ajiye abinda kake aikatawa da wanda kake shirin aikatawa. Kasan nasan abinda yake faruwa, har abinda Hajiya take aikatawa domin rufa maka asiri. Ni kasan ban da sirri ko kashe ni ka yi ina da hujjar da na bada shi ba nan kusa ba har gaba da Bauchi na saka a ajiye min daga ranar da suka ji labarin mutuwata su bayyanawa duniya tasan waye kai. "" Yadda yayi magana da confidence yasa shi razana, bafa kowa bane Lubnah ta ce mishi. "" Ni ba Lubnah ba ce da zan rufa maka asiri ba, bayan ni ba koshi nayi da kai ba. Ruwanka ne ka ja tsumar rayuwarka, sannan ina son kudi a cikin account dina, ko kuma na kira waya nace a saka labarin nan zuwa"

"ga Yayun lubnah su ji yadda ka kashe Mahaifinsu da ita Lubnah. """

"Yana murnan ya kashe maciji, ashe bai saure kai ba. Domin Karimah ita ce kan macijin da bai sare"

"kanshi ba. Duk sai ya ji kamar zai zauce domin Karimah tafi shi iskanci. Eh ai ko a shekaru Karimah ba sa'arshl ba ce. Domin tun can ta girme shi a bariki suka hadu da ita tana yawo bariki, suka haWu."

"Washi gari kuwa da Karimah ta fito ta ga yarinyar da Hafiz ya kwana da ita bata ce mata kome ba, ta"

"shiga kitchen ta dauko itace ta shiga dakin Lubnah Hafiz yana barci ta rufe Yar mutane da duka. Dakyar ya kwace ta, tana haki ta ce mishi.. ""Ni ba Lubnah ba ce, wallahi baka isa kawo min wata mace cikin gidana ba. Idan kuwa kayi haka ka saka a ranka nice ajalinta."" Shi fa ya zata kowacce mace kamar Lubnah take, sai gashi lokaci guda Karimah ta goge mishi zero. Sannan ta masa barazanar sai ta kai ™arar shi wurin Baban Bauchi, tunda shi ya zama Wan akuya zata tona mishi asirin da yake rufawa tunda tasan sirrinsa. Wannan abin yasa shi kara shiga hankalinsa, ya koma mata biyayya bai kara shigo mata da mace gidan ba, domin kuwa ta rike mishi wuya, kuma bata girki kudin dai tana samu son ranta. Kuma shima tana cin ubansa dai-dai gwargwado. Duk ya fita hayacinsa bai da hankalin da zai fahimci barnan da yake shi dai burinsa asirinsa ya rufu, a irin wannan yanayin ne aka Baban Jama'are ya fadi jininsa yayi mugun hawa, haka suka dauko shi daga Jamaare aka kawo shi Bauchi, Teaching hospital Bauchi, wannan abin ya"

sake gigita Hafiz yayi ta ji kamar yayi hauka. Domin hawan jini da diebetis suka buga shi da kasa..........

"[12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA ŠAYA"

"Duk da wannan abinda ya faru, daga Mama har Yadiko sun kyale Baban Bauchi yayi yadda yake so, suka"

"bar mishi gidan shi kuwa ya dauki dokin zuciya ya daura a kansa tare da wani irin girman kai da son kai, suma Yaran maza da mata suka zuba mishi idanu yayi yadda yake so ba dai Hafiz ne suka bar mishi."

"Sai da Baban Jama'are yayi kwanaki kafin ya dawo hayacinsa, ya kalli Hafiz cikin tsananin bakin ciki."

"""Hafiz maka baki ba, ba zan ce zaka gani ba. Amma matu™ar Lubabatu bata zalince ba, kai da nutsuwa har abada idan kuwa ita ce ta zalince ka Allah ba zai barta ba, kai Hafiz bana jin yarinyar nan zata iya abinda ya raba ku. "" Juyar da kai yayi domin maganar Allah yana jin zafi da ciwo, yana ji kamar ya cire zuciyarsa idan ya tuna yadda Yaransa suka mai da Lubnah idan ya tuna yadda suke mata wulakanci har akan idanunsa sai yayi kamar laifin nasa ne, donin bakidaya yayi kuskuren da har abada ba zai gyaru ba, kusan da iyayen Lubnah suka juya mata baya, kasa yin kome yayi amma shi dansa yana yadda ya so."

"Akwai wani abu da yake faruwa a wannan duniyar daga lokacin da kace na wani bai isa dariya ba, har abada naka ba zai tab'a maka daidai ba, a lokacin da yake ji yake gani ana azabtar da Lubnah shi a lokacin yayi kamar bai gani ba sai ya rufe bakinsa da kunnensa yayi kamar bai ji ba bai gani ba. Share"

kwalla da ya zubo mishi yayi.

"Sai dai tun daga ranar bai kara yiwa Hafiz magana ba. yadiko taxo ta ga jikinsa, bayan ta koma gida ta"

"gayawa Mama ta waya, ai kuwa ranar talata bayan laasar Mama ta zo da matar Ya Umar, suka samu Abba wato Baban Bauchi. Yadda yake wani jiji da kai yasa Mama itama ta nuna mishi daga fada take. Ta wani dauke kai suka gaisa da Baban Jama'are, ya yi kasa da murya ya ce mata. ""Don Allah Hajiya Salamatu, ki koma dakinki haka yanzu ku ba yara bane."" Murmushi tayi tana me faWin. ""Idan na gaya maka gaskiya zaka yarda?"" Ya jinjina kai ta ce mishi. ""Zabi ya bani har abada ba zan dawo gare shi ba kamar yadda Lubnah ta haramtawa Hafiz, idan kuwa ka ga ta dawo ga Hafiz tow mutuwa nayi kasa ya rufe min idanu kenan. Kai ko gawar Lubnah da ta koma gida Hafiz gara wuta ya cinye ta."" Ta fada tana murmushin bakin ciki domin ita Waya tasan yadda take jin ciwon halin da Lubnah take ciki, mikewa tayi tana faWin. ""Muje kin ji Allah ya kyauta,."" Haka ta fita Abba ya ja tsaki yana faWin ""Sai me idan ba ta dawo ba ita Yadiko idan bata koma ba wallahi sai dai aurenta ya mutu don ya gaji ai ba da ita yake rigima ba, ita kuwa da yake tafi shi kwaya tace a gaya mishi ita bata tsoron saki ai idan har ya iya Hajiya Salamatu haka babu wacce ba zai yiwa haka ba, ba zata koma ba Hajiya Asiya su mishi replace abinda suka gaza mishi. Sosai aka yi ta rigima yaran kuwa sun koma gefe dama kowa ya gaji da abinda yake yi, ganin haka yasa Manya gaba cikin family uku suka taru aka dawo da Yadiko domin ya kafe Mama ba zata dawo ba, idan kuma zata dawo sai dai ta dawo da Lubnah kafin shi, ita kuwa Mama ta ce bai ji ka ba tukun, ai yanzu ba da bane Lubnah kuwa tayi musu nisa. Wannan abin ya bala'in bata mishi rai. Shi yasa shima ya kafe ba zata dawo ba. Ita kuwa ta ce tafi nono fari. Faruwan wannan al'amarin ya kara sakawa Baban Jama'are damuwa sosai domin yana ganin ai duk abin nan ya faru ne ta silar danshi. Sannan masu ganin laifin Lubnah yanzu sun dawo bayanta, domin abin da ya faru ya nuna sun so kansu duk abin nan gashi ita ta rasa iyayenta amma shi da yake shafaffe da mai ne gashi nan yana zaune tare da kowa na shi, sai yaji tsoron Allah ya shige shi dansa yayi sanadin auren da aka Wauki shekaru, sannan a lokacin da ya rasa madafa su wadannan mutanen sune suka tsaya mishi. ""Innalillahi wainnalihir rajoun!"" Ya nanata kalmar"

nan tafi sau dubu ya tsani kanshi da zuciyarsa.

"Lokacin da ya dawo Jama'are, sai kunya da kuma yadda mutane suke ganin laifin Hafiz ya kara susuta"

"shi ya dinga blaming kansa wannan abin sai ya kara hurt din zuciyarsa, har sati biyu ya cika Babangida ya"

"mai da shi ganin likita. A lokacin da suka hadu da Hafiz ya ce mishi. ""Ban san me kayiwa Lubnah ba,"

"amma ka sani ba zaka tab'a farin ciki da jin dadin rayuwa ba, sai kun sake zama duk da kowa yana son yaji matsayata akan Lubnah abu daya zan gaya maka a duk lokacin da ka ji inda take kafin wani ya rugaka samunta ka kara niman soyayyarta a karo na biyu, ka dawo da ita rayuwarka idan ta amince idan bata amince ba, tabbas ka tafka mummunar asara a rayuwarka, ka dube ka kai kanka baka da nutsuwa ka cutar da ita ka cutar da iyayenta. Ina ji kamar na mutu da bakin cikinka! "" Ya fada yana jin kuka na zuwa mishi. Haka ya ga likita sannan Hafiz ya kawo shi kasuwar Central. Yadda Baban Bauchi ya ga dan uwansa ba karamin dadi ya ji ba, haka ya dauke shi suka yi ta zaga manya shagunansu, yana karawa bawa dan uwansa hakuri akan batun lubnah wanda yake niman wata guda da faruwa. Ya kuma yiwa Wan uwansa al™awarin. "" Matukar ni na haife ta kuma ina raye Hafiz shine mijin Uwata, ba zan tab'a sauka"

"akan kalamai na ba. """

""" Ya Shehu, ka sani matu™ar Lubnah ta gama Idda tana da damar zabawa kanta abinda take so, sannan"

"ita kanta zuwa yanzu tana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali. Hafiz ya mata laifi. "" "" Ai dan uwanta ne idan bata rufa mishi asiri ba waje zata rufawa? Iskanci ne da rashin mutunci ni kuma ina daidai da ita"

"duk inda taje zata dawo ko shekara dubu ne!"""

"Wannan ya kara nuna son Kai da son zuciya irin na dan Adam, bakiWaya suka saka a ransu idan har ta"

"dawo su ke da iko da ita. Anyi hiran nan a gaban Ya Sani shi kuwa ya kira Ya Umar ya gaya mishi, ai kuwa maganar ta fada kunnen Mama, kwafa tayi ta ce Allah ya basu Sa'a tana jiransu."

***

IKEJA LAGOS

GRA

ELYAKUB MUHAMMAD KUMO St.

"Aka rubuta da karamin allo, wanda aka yi zanen da wata golden paint, babban gare da zai sadaka da"

"cikin gidan irin kafceccen nan ne, mai nauyin gaske nan ne, a hankali hancin wata kyakyawar mota kiran kamfanin Roll Royce , ta cigaba da tafiya izuwa kantamemmen gidan da yake cikin unguwar wanda yake tsakiyar unguwar mai zubin fadar sarki. A hankali yake wuce gidajen da suke yiwa wannan kyakkyawan gida kawayan, har ya isa zuwa kofar da zata sada shi da wannan kyakyawar fadar. Ya jima a cikin motar yana shiru kafin ya tattaro duk wani abinda zai Wauka sannan ya fito daga motar, ya nufi hanyar da zata sada dashi da asalin kofar da zata kai shi main Street na gidan, kofa ce mai security service, yana zuwa wani kare ya fara mishi haushi tare da kad'a mishi bindi a hankali ya isa gaban karen da ya tawo da gudu yana kawaye mutumin murmushi yayi ya ce mishi. ""Max ya kake?"" Ya shafa wuyar karen wanda kana gani zaka fahimci karen Ya sanshi irin sosai din nan. Mikawa daya daga cikin security din key yayi ya ce mishi. ""Akwai abincinsa a boot!"" Daga haka ya isa bakin kofar computer din tayi screening dinsa tare da"

"scanner. A hankali ta ce mishi. ""Barka da zuwa Captain Ubaidullah Jibirl Kumo, na'ura ta tantance ka."""

"""Na gode Husnah ina sonki da zan kara aure ke zan aura."" Ya fada yana murmushi yana jin ta ce mishi."

"""Bani da kawazuci sannan ni na'uran AI ce."" ""Ai na sani shi yasa nake kara kaunarki."" ""Na gode Ubaidullahi. "" Daga haka tayi shiru ya wuce idan da sabo ko su, security din wajen sun san draman AI"

Husnah fa Oga Ubaid

"A hankali ya ke tafiya har zuwa cikin gidan, kyakywan Yara yan mata suka tawo da gudu. "" Uncle"

"Ubaid, oyoyo!"" Rungume su yayi sannan ya mike tare da ciro chocolate a aljahunsa ya mika musu yana faWin. ""Oya cigaba da wasa."" Ya wuce su, bai kai entery na gidan ba, sai ga Maid sun fito cikin girmamawa suka bude kofar suna mishi. ""Barka da zuwa Sir!"" Jinjina kai yayi ya cire takalmi a wurin suka rufa mishi baya masu gyara zaman takalmin suka gyara shi kuma yana shiga inter door na gidan ya samu"

wasu takalma an zuba mishi maid din tana mishi sannu da zuwa.

Kamshin turaren wuta zamani na FAMAS SCENT OF LEGEND GIDAN TURAREN WUTA ya daki

"hancinsa, wani irin kamshi ne mai hade da sanyin Ac ya bada wani irin perfect kanshi me shegen dad'i, daga shiga cikin gidan zaka fahimci how yanayin kamshin yake ratsa zuciya da gangan jiki, wata maid ya samu ta ce mishi. ""Barka da zuwa sir muje ta wannan hanyar."" Duk da ba yau ya fara zuwa gidan nan ba, sannan kusan rayuwarsa bakiWaya yayi ne domin gidan nan, amma duk lokacin da abu me muhimmanci ya kawo shi, jagora ake mishi. Har zuwa babban main entrance parlourn na gidan, da sallama ya shiga wani kyakkyawan bafulatani dattijon da ya sha gwagwarmaya ya gyara zaman glass din sa ya zuba mishi"

idanun cikin wani irin murmushi yana me amsa sallamarsa a nutse.

"""Ubaid!"" Ka rasa yayi gaba wani karamin abin wanke hannu ya ajiye file din sannan ya wanke"

"hannunsa, tare da shafa hand sanitizer, sannan ya dauki file din ya isa gaban dattijon ya ce mishi. ""Barka da hutawa Alhaji!"" Gyara zaman glass din yayi ya ce mishi.. ""Barka dai Captain! Yau kai Waya ne ina Amaryan lalle?"" Gyara zama yayi yana faWin.. ""tana lafiya, Alhaji Hajiya Dadda tana nan kuwa?!"" ""Tana nan zata fito ai idan ita ce."" ""Allah yasa mu gama bata fito ba."" Ya fada yana murmushi, abin motsa baki aka fara kawo mishi, ana jera mishi a gabansa, har suka gama Alhaji ELYakub Kumo ya ce mishi. ""Fura zaka zuba min."" Mikewa yayi ya zuba masa sannan ya mika mishi shi kuma ya dauki hadaddiyar fruit da"

"ya sha madara, ya fara sha yana sauraren Alhaji ELYakub Kumo."

"""Yau ma sakon ya baka ka kawo min?"" Ya tambaye shi yana murmushi, irin murmushi irin na manya."

"Cikin wani deep sorrow voice ya ce mishi. ""Ko don ba ni ba haife shi bane? Amma ai ni na haifi Mahaifinsa."" Sai yayi murmushin takaici irin wanda kana ganin abinda kake so amma kana ji kana gani yafi karfin ka. ""Ubaid ina da ikon hana ™addara ikonta ne?"" Girgiza kai Ubaid yayi yana tausayin dattijon. ""Kayi hakuri Alhaji!"" Murmushi yayi a karo na uku wanda kamar ita din anyi ta ne domin fuskarshi kuma tana kawata mishi fuskarsa da wannan kyakkyawan murmushi. ""Amma kasan ban yi mishi kome ba ko? Ban cutar da Turaki ba, duk abinda zanyi domin ya zama karaya a gare shi nake yi. Amma kasan na tsufa ko? Me yasa Turaki yake gudana? Da farko na dauka don rasa mahaifiyarsa ne yake gudun Ubansa, sai mutuwar Ubansa yasa na hango kiyayyar da Turaki yake min, bani da wani abu da zan rike Turaki. "" Tari"

ya fara a hankali yana me ajiye furan ya dauki ruwan da Ubaid ya mika mishi. Kurba yayi yana me

"ajiyewa. "" Kowacce rayuwa tana da fuskar da ™addara take bude mata, Turaki shine kaddarata, ban rena"

"iyawarsa ba amma ya dawo gabana im dead in side, ya dawo yazo ga tsohon nan da baya jin kome sai kamshin mutuwa! "" Shafa kai Ubaid yayi yana tuno abinda ya faru anan parlourn, numfashi ya sauke a hankali, yaji muryan Hajiya Dadda tana faWin. "" Ba zan ci ba, shima maganin ba zan sha ba. Wuce ki baka wuri tun ban haifi Ubanta ba nake jinya har na haifi Ubanta haka yasa na mutu ne? Ta je can ta cigaba da zama ai dama nasan bayinta ba ne, domin ko jiya wani malami ta gaya min bakin asiri aka mata, sai kuma macen aljan da suke tare wanda har sun yi aure har da zuri'a. Shi yasa bata son zaman cikin mutane."" Ta isa wurin dattijon ta zauna cikin ladabi da biyayya irinta matan da suka ga koya suka ga yau, gashi har gobe ana saka musu ran zasu gani cikin harshen fulatanci ta ce mishi. "" Jam na?"" Kallonta yayi na wani lokaci kafin ya ce mata. ""Lafiya lau Hajja!"" Gyara zama tayi cikin ladabi ta ce mishi. ""Ina son na"

"gaya miki, ko zaki yiwa Auta magana ta kira malamin nan zata turo abin nan da ake tura kudi ta ciki!"""

"Murmushi yayi ya ce mata."" Hajja kina tsammanin Turaki zai dawo ne?"" Cikin tsantsan biyayya ta ce"

"mishi. "" Nasan bayin kanta bane zata dawo, waye nake da shi bayan Harisu? Turaki ita ce nake kallon a matsayin Harisu, ki yi hakuri ki bada umarni ta tura mata kudin. """

"Wato dariyar da Ubaid yake kamar cikinsa zai kulle, ya tab'a zuwa gidan nan bai fita bai dara ba ai"

"kuwa? Babu ranar domin ita kanta Hajja comedian ce. Alhaji ELYakub kuwa so yake ta daina yarda da wannan maganar domin wanke ta ake yi. "" Alhaji baki ce kome ba?"" Murmushi yayi yana kallonta. Hango yar karamar kanwarsa da suka hada Iyaye maza wacce aka ce ya je ya ganta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login